Showing 129001 words to 132000 words out of 294767 words

Chapter 44 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

hannu ya dauki wayar dake gabansa,sai ta tsinci kanta da satar wayar da kallo,ta janye idanunta da sauri tana miqewa. Buqatarta tabar wajen,sam batason kunnuwanta su dinga ma sha'aninsa shishshigi,hakan tamkar tana batawa kanta da tunaninta lokaci ne,da hakan gwara taje ta karanta abu qwaya daya da zai zameta jagora a aikin jaridarta

"Na fara jin bacci ne ama" yaji tana bawa ama din amsa sanda ta tambayeta sai ina?,sai ya janye idanunsa yana maidawa kan wayar.

Suhail ne yake kira,ya kara wayar a kunnensa lokacin da take sauka a hankali daga step din area din,ya dauka dubansa daga kanta a hankali daya fahimci tana shirin hardewa

"Surprise" suhail ya soma fada yana dan dariya

"For what?"

"Ina nijer"

"Bana wasa dakai" ya fadi kansa tsaye

"Tuwo ne a idonka da baka fahimci code din NIJER ne a number na ba?"

"Ma sha Allah..... but munyi da kai ni xan daukoka a airport fa?"

"Kada ka damu,tunda na sauka a qasar nan karsashina ya qaru......haka kawai jikina yake bani kaman zanga crush dina fa, yarinyar haram" dogon tsaki maina yaja,har ransa yana jin haushin tada zancan,baisan me yasa ba,amma yana haushin yaga namiji na yima mata rawan qafa. A nashi ra'ayin ba kowacce mace namiji ya kamata ya budewa zuciyarsa ba,qalilan ne suka cancanta

"Zaka iya qaryata zancena ko ka gasgata,nidai gaskiya na gaya maka......ka turon Adress zan taddaka har gida,zan baro niamy gobe in sha Allah"

"Karka damu,kana isowa airport ka kirani zanzo na daukeka"

"Yayi......godiya,sai na qaraso".


*_Tofa,ga suhail nan zuwa,ko ya zata kaya?_**_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 page 67


Tsaye yake jikin motarshi dake cikin tashi da saukar jirage na garin marad'i cikin shigar cikakken buzu da ta fidda sigar kyau da cikakkiyar kamalar da yake dashi,yadda rawanin ya zaunawa kansa kadai abun burgewa ne,kyawawan idanunsa da hancinsa da bai cika tsaho ba sun zauna das saman fuskarsa. Sumar fuskarsa na kwance luf, zakayi tsammanin usulinsa balarabe ne bawai ba'abzine ba.

Wayarsa ce a hannunsa yana sauraren laila,sam ya rasa amsar da zaya bata,daga jiya zuwa yau gaba daya ta soma rikice masa kamar wadda ake mintsinin zuciyarta

"Na fara kaiwa stage din da bazan iya juriya ba......ban taba cewa inason kowanne namiji ba saikai please maina......ina gaya maka da gaske ne,i really love you......kuma zaka iya ganina a nijer any moment" zagayayyun lion eyes dinsa yadan fidda kadan,tazo nijer ta qara wuta fetur?,yana kan lallaba aba fa har yanzu?,yace masa meye?.

"Cool down laila.....na fahimceki,amma banason kina zafafawa haka da yawa......kibi komai a sannu" idanunta ta lumshe tana dora hannunta saman qirjinta hadi da fidda siririyar iska daga bakinta

"Don bakasan yadda nakeji bane ya haidar......shi yasa kake cewa haka,ni dama kawai nake buqata ka bani cikij rayuwarka,basai ka tayani ba"

"Ki nutsu please......ga suhail can ya iso,zan daukeshi mu wuce gida,zamuyi waya in sha Allah"

"Nadai kiraka as usual" ta fadi murmushin yaqe yana fita daga fuskarta,sai ya rasa amsar da zaya bata. Cikin kafatanin rayuwarsa sam sam bai bata soyayya ba,bai kuma san ta yadda zai tattaro wannan kaya da laila keson aza masa ba,shi dukka dabararsa akan aikinsa take,a kanta ta qare,so baqo ne shi ta wannan fannin

"Ba damuwa,kiranma wata damar ce,na gode da ita,bye......take care dear" ta furta a hankali tana katse kiran.

Iska ya furzar shima yana gimtse kiran,ya sake daga kai yana hango tahowar suhail,sai ya dan tashi daga jikin motar ya soma nufarsa tare da qoqarin sanya murmushi kan fuskarsa.

Wayar ta ajjiye gefe tana cusa yatsunta cikin sumarta hadi da jan iska sosai cikin hunhunta. A hankali Sarah ta miqa hannu ta dafa ta

"Duka wannan daga qafan da zagaye zagayen idan nice bazan iya shi ba......aliyyu yana ganin kima da martabar mahaifinki ya yayanki,me yasa ba zakiyi amfani dasu ba?,ina kyautata zaton wannan kadai ce hanya da zaki samu yadda kikeso ba wani dogon kwana kwana,ba cutar dashi kikayi ba ai,sonshi kike,kuma kina da tabbas a soyayyar da kikeyi masa,sannan kuma zaki bashi duk wata kulawa data dace,anayin aurenku ya samu yadda yakeso namiji ne fa,nan da nan zai mance matsayarsa ya biye miki kuyi soyayyarku me dadi" daga fuskarta Laila tayi tana duban sarah

"Nafison ya nutsu ya gamsu da kanshi kafin akai wannan matakin sarah......amma kuma na fara sarewa da haka, zuciya ta ina jin tana min ciwo lokaci lokaci,inajin zaiyi wuya gaba kadan muddin ban shawo kanshi ba......komai zai ya samuna" ido sarah ta fiddo

"Me yasa?,da gatanki?,kuma da chance hundred percent na samunsa a hannunki ki bari ciwo ya kamaki?,ni zan gayawa mummy maganar nan tabbas" ta fadi tana miqewa. Caraf sarah tayi ta riqo hannunta

"Kada kiyi haka sarah don Allah,aminci na dake yasa na gaya miki sirrin da ya shafeni,a zaton mummy yayi accepting soyayya na ne, soyayya mukeyi,please ki barsu a haka" a sanyaye ta dawo ta zauna,saita kasa cewa komai daga ita har laila din.

Hannu ya miqawa suhail sukayi shacking,idanun suhail a kanshi ya soma magana

"Kai mutumina......ya naga kaman nijer na shirin karbarka fiye da ko ina?,kaga yadda kake zama fresh?" Dan tureshi baya kadan yayi yana amsar luggage dinsa ya soma ja sannan ya bashi amsa

"Indai kaine zaka fadi fiye da haka,ka wuce muje ko na tafi da iya jakarka" ya amsashi yana fara takawa don barin wajen

"Baqonka annabinka dai,muddin kace zakamin wannan halin naka zan koma inda na fito"

"Ga fili ga me doki ai" ya kuma bashi amsa,sai suhail din ya saki dariya sosai. Indai shida maina ne sun saba irin haka,sardauna ne sam baya jurewa irin wannan wasan,wani lokacima shi yake zama dan rabiyar fada a tsakaninsu.

"Bayan wancan BMW din wannan kuma yaushe ka siyeta?" Suhail ya furta bayan ya zauna a seat me zaman banza yana shafa gaban motar,saboda sosai ta tafi dashi,sabuwar shigowa ce da duka duka batayi wata biyar da bayyana ba

"A satinnan,wannan ne hawa na na biyu gaba daya" ya amsa amsa yana tada motar,sai suka zarce da hirar motar,qirar motar na sake burge suhail din don shima ma'abocin son hawa motoci ne.

Hayaniyarsu benazeer ne ya farkar da ita daga baccin data koma a sassan ama,hayaniyar tasun ce kuma ta sanyata baro sassan bibi tunda safe ta dawo sashen ama din,sai gashi bata tsira ba sun sake biyota da kalar rigimarsu. Qaramin tsaki taja tana saukowa daga gado,ta jawo hularta data dace da cotton night gown dinta me kauri ta lullube gashinta me santsi,ta zura flip floppy dinta ta miqe tana nufar qofa,sai tayi punishing nasu yau,tabarar da sukeyi tanason ta fara yawa hakanan.

Tana bude qofar dakin nata ta hangesu suna fita daga lobby din,duka su biyun kamar ko yaushe kamar kuma kowanne lokaci sanye da pink pyjamas masu wando kawunansu fake da tafkeken pink ribbon da yazo cikin mahadin kayan, qafafunsu wasu lausasan slippers ne rufaffu duka cikin set din kayan sukazo,wannan kusan shine shigarsu daga dare zuwa safiya,tana kuma kalla tasan lallai basuyi wanka ba sai uban karadi da suka cika gidan dashi,basa ma duba cewa ama bata jin dadin. Maida qofar tayi ta rufe bayan ta fito daga dakin,kai tsaye tabi qofar fita daga lobby din inda zata sadata da falo.

A tsaye ta hangesu a dining area kowannensu dauke da mug dinsa wanda ke dauke da sunansa baro baro a jiki,tanja na tsaye tana qoqarin hada musu juya madarar data zuba musu a oat,su kuma baki abun magana sai sambada mata zance sukeyi

*BB" ta kirasu da sunan da goumar ne ya fara rada musu,zaiyi kuma wahala kaji ta kirasu dashi din. A tare suka daga kai suna dubanta,sai ta daga hannu ta yafitosu,ba jinkiri suka soma saukowa daga dining din suna nufota.

Kamar yadda suka koya suka kuma tashi dashi,dukkansu rusunawa sukayi suna gaidata da harshen faransanci da ya zauna a bakunansu

"bonjour, tu t'es réveillé sain et sauf ?"

"bonne santé" ta amsa musu tana murza goshinta saboda hatta gaisuwan ma kowa so yake yaga shine ya fara yi mata

"Ihun mene ne kukeyi haka?,kowa yana bacci?" Junansu suka kalla,don a wajensu yanzun sha dayan safiya ba za'a kirata safiya ba,basu iya baccin safe ba Sam,barsu da baccin rana dai

"Batoul ce......"

"Allah bani bace aunty........bena"

"c'est assez(ya isa haka)" ta fadi yana daga musu dogayen yatsunta,don ta tabbatar idannta tsaya tana kallonsu sunyita yi kenan.

"Banason na sakejin hayaniya,yau zamuje gidan tante aminata da tante yasmine......but.....duk wanda ya qara cika mana kunne zaiyi gidan gidan nan ne" murna sosai ta kamasu harda tsallensu,duk kuwa da cewa already goumar ya kaisu.

Qarasowa tanja tayi tana murmushi

"Ai gwara kije din gaskiya kafin lokaci ya qure"

"In sha Allah yau zanbi mutanen gidan......ina kwana tanja?"

"Kin tashi lafiya?"

"Lafiya alhamdulillah ya yaran?" Ta tambayi tanja data fara raba musu oat din,don kullum tanjan takan tambaya kwanansu tare dayi musu sannu ko ita ko ama

"Lafiya qalau alhmdlh"

"Ma sha Allah......ama bata samu fitowa bane?"

"Tana ciki kam,tunda ta fito tare dasu batoul ta barsu a nan"

"Badai jikin ba?" Ta tambayi tanja cikin kulawa tana takawa zuwa tsakiyar falon tana qoqarin daukan madarar dake ajjiye tana tsatsafar sanyi,da alama an ajjiyeta ne tasha iska. A kwanakin shan madarar ne yakeson dawo mata sosai,wani abu data bawa shekaru sosai rabonta dashi

"A'ah jiki alhamdulillah mana,naji ma tana waya dazun kamar tace zata leqa shagonsu benazeer don tana da lissafe lissafe dasu"

"To alhamdulillah,bari na dubata " ta furta tana wucewa kai tsaye zuwa dakinta dake benen saman sashen,don tasan aba baya nan,tun daren jiya sukayi sallama akwai gajeruwar seminar da zasuyi,koda kuma yana nan din sunfi zama a sassansa dake manne da babban falon ama din.

Da sallama ta tura dakin ta shiga,ama dake zare tattausan socks din dake qafarta ta amsa mata,idanunta akan sultana din. Duk sanda zata kalli fuskarta sai ta samu kanta da yi mata addu'a,Allah ya dawwamar da farinciki cikin rayuwarta,dukkan wani qalubale da cakwakiya da basu da mafita a kanta Allah ya bada hanyar warewarta.

Da kwantacciyar fara'arnan me laushi saman fuskarta ta qarasa gefan sofa bed din ama ta rusuna har qasa kaman yadda ya zame mata al'ada tana gaidata,can qasan zuciyarta tana jin wani dan nauyinta da a yanzun takanji kuma har yanzun batasan meye dalilin hakan ba,tadai alaqanta hakan da girma da kuma gankali dake sake lulluneta kullum kwanan duniya,sannan uwa uba takan tuna da wasu abubuwa da suka faru tun kan cikinsu benazeer din zuwa haifesu da tayi. Bayan bibi da tanja da tayi rainonta duk gidan ama itace mace ta biyu data taba ganin jikinta zahiri,tayi biqinta ta kuma yi jegonta kamar jaririya.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 68


sannan ta bita da tambayar jikin nata

"Alhamdulillah na samu sauqi" itama ta amsata cikin kulawa

"Allah ya qara afuwa yasa kaffara"

"Ameen ya hayyu ya qayyumu" ama ta amsa mata tana shafa cleanser a fatarta,da alama shirin shiga wanka takeyi.

Tadan dauki mintuna suna tattaunawa da ama din wanda kusan duka akan komawarsu ne da kwanaki kadan suka rage,sannan ta miqe tana cewa

"Zanyi wanka ama,yau din naji kaman yaran gidan nan suna cewa zasu gidansu aminata,zan daure na leqa kada mu wuce banje ba,bansan kuma sai yaushe zan dawo ba" kai ama ta gyada

"Eh gaskiya yana da kyau,saura kadan atta ya karbi key din motar da kike hawa,na hanashi nace ya dauki wata wannan din duk bubbugemin mota yakeyi,bai iya tuqi a hankali ba" murmushi ta danyi kadan

"Da kin bar masa ama,nima tunani nakeyi nabi motocin gida"

"A'ah bashi yiwuwa,nex time idan mun dawo ma dole a siya mota a ajjiye miki,ko don su benazeer da suke tasowa" ama tayi maganar tana cirar key din ta miqa mata

"Idan bakijin driving ma ai almu yana nan,saiku fita tare" hannu biyu ta saka ta karba,koda yaushe kulawar ama a kanta daban take,ta banbanta da wadda take bawa 'ya'yan cikinta ma.

Tana komawa daki ta wuce bandaki,don tana fitowa suka hadu da ummeeta dake shaida mata

"Tante.....ba zamu wuce sha biyu zuwa daya ba zamu dawo" tace da ita. Cikin nutsuwa ta fidda bath set dinta,tsadajjen shower gel da sauran tarkacen wanka wanda kusan ama ce nauyin komai,sai daga bisani da tayi hankali ta soma saving abinda take samu take wuf tayi wasu hidindimun kafin ama din takai ga yi mata.

A nutse ya wuce gate din farko na gidan,ya kuma zarce sashen ajiyar motoci dake gidan ya fara yiwa motar tasa mazauni. Tunda suka shigo gidan suhail ya kasa cewa komai,yana dai bin sassa sassa na gidan da kallo yana mamakin ya za'a yi mutumin da ya fito daga mansion house na alfarma irin wannan ya zabi yayi rayuwa qarqashin wani kuma yazo masa a yaronsa?.

Sanda ya kashe motar yake qoqarin cire seatbelt suhail ya kasa haquri lokacin da wasu security dake sanye da uniform suka gaidashi suka wuce

"Mamaki na yaketa kamani fa haidar,na kasa nayi shuru" qaramin murmushi na gefan baki maina ya saki,ya sani dole ne suyi mamaki,tsahon zamansu tare shekara kusan hudu ba wanda yasan asalin wayeshi,ba kuma wanda yasan komai daya danganceshi,illa dai ama aba da sunan sultana da suka sani,shima din cikin mafarkanshi ne da yakeyi wadanda sukan bayyana masana a zahiri wani lokaci idan yana baccin har ya ambaci sunansu.

"Zaka sani ai yanzun ko?"

"Sardauna zaifi kowa yin mamaki" suhail ya fadi yana bude murfin motar kamar yadda maina ya bude na bangarensa.

Cikin atamfa ta shirya kanta riga da skirt me launin army green da adon light orange kadan a jiki,ya lullube kanta da Chantilly veil daya dace da shigarta,siraran abun hannu da wuya ta sanya da sue mahadi da agogon da zoben hannunta,kaman yadda jakarta da takalminta dukka suka kasance na kamfanin Hermes brand hakanan turarenta dukka na kamfanin ne. Kusan komai nata tafi ta'ammali da wadannan Brand din guda biyu Hermes ko saint Laurent. Sosai fuskarta ta fita das cikin daurinta data kawoshi gaban goshi,qirar jikinta ta fita da kyau saboda yadda driver din ya qware sosai wajen fidda shape din dinki,ta fita a bahaushiyar nigeria zam,ta kuma yi kyau ainun,saboda shiga ce da ba kasafai ta fiya yinta ba. Tafi ganewa dogayen riguna a yanzun abayas sai English wears masu skirt ko budadden wando irinsu palazzo.

A nutse ta fito daga dakinta ta samu ama tana shirin yin makararren breakfast dinta saboda bata sauko da wuri ba. Dubanta ama din tayi,a yau din karon farko taji kishi ya darsu a ranta. Irin kyan da sultana din tayi tasan ba kowanne namiji bane zai iya dora idanu a kanta yaso janyewa ba tare daya sake marmarin kallonta ba,komai nata cif da cif Masha Allah,kama daga yanayin tsaho da halittar qibar jiki,batayi qiba ba kaman yadda sam sam bata da rama,idanunta sun sake fitowa sun kuma qara wani haske sosai,santala santalan qafafunta da hannayenta dake dauke da shimfidaddiyar fata dake nuna zallar hutu da ta samu

"Tun dazun suke jiranki,amma nace musu suyi gaba baki kammala shiryawa ba,su benazeer din ma maybe sun bisu,don an shiryasu,nasan kuma zaiyi wuya su iya tsayawa jiranki"

"Shikenan kam,na huta da rabiyar fada" ta furta tana dariya. Murmushi ama ta saki tana mata fatan dawowa lafiya tare da binta da kallo. Ajiyar zuciya ama ta sauke sanda ta fita din,a wannan yanayin ta tabbatar idan haidar ya ganta zaiyi wuya ya iya shanyewa,tasan tsananin kishinsa,wanda shine yayi musabbabin tilastawa qannensa sanya atamfa ya kuma sanya aka bayar da duk wani English wears nasu,suka kuma dinga fada da samun sabani da sultana.

"Mu wuce ka fara hutawa tukunna saika shiga cikin gidan" maina yace da suhail yana nufar sassansa

"A'ah,a ina ake haka?,kazo baqunta kaqi fara duba kowa?,fara kaini wajen grandma tukunna sai mu wuce wajen ama din" qaramin murmushi maina ya saki

"Bibi rigima,Allah yasa ta barmu mu fito da wuri,kasan dai zuwa yamma zamu shiga company mu duba engines dinnan ko?"

"Ina sane"

"Alright" ya furta a taqaice,sai yayi kiran daya daga cikin security din gidan,ya bashi luggage din hade da key din sassan nasa yace ya saka masa a ciki yabar gurin a bude yanzu zai shiga.

Tare suka jero har suka isa sasaan bibi,sun sameta a falo tana ta fada,fadan kuma da maina yasan rigima ce kawai irin tata,kayan sawa take warewa tana fadin wannan batason ayi musu guga,a qyale mata abunta haka

"Ayita danawa kaya wuta b gaira ba dalili" ta sake jaddada mitarta daidai sanda suka shigo falon,ta daga kai tana amsa sallamarsu.

Tun asali mutum ce meson baqi da kuma girmamasu,wannan ya sanya ganin maina tare da wani saita dan saki fuska,maina din ya qaraso kan kayan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login