Showing 150001 words to 153000 words out of 294767 words
Chapter 51 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
gamsu da zancansa ba.
Kafin lokacin ya cika sai ga suhail din ya shirya tsaf harda jakanshi da wasu kayan daya musanyo daga ainihin masaukinsa gidan kakanninsa. Maina din baice masa komai ba,don haka ko cikin jirgi ma kowa sabgar gabanshi yakeyi.
Awa biyu rak ta iso dasu marad'i,cikin drivers na gidan mayak'i daya daga ciki yazo ya daukesu daga airport cikin daya daga cikin motocin maina dake gidan.
"Wanne kalan malalacin tuqi kakeyi ne?" Maina ya tambayi driver din yana kallonsa ta cikin madubin. Waiwayowa suhail dake qoqarin kunna wayarsa yayi ya kalli maina,sai ya maida dubansa ga driver din wanda yake qoqarin take motar ya qara mata gudu
"Kada ka damu tuqinka yayi dai dai ba laifi,muje a haka" sai ya juya ga maina. Ya fahimci kaman bashi da nutsuwa daga jiyan zuwa yau
"Fake wife din naka ka matsu ka gani ne?" Ya tambayeshi cikin muryarsa akwai sautin tsokana me yawa. Wannan karon gaza daurewa maina yayi,ya kaima suhail wani mummunan duka a kafadarsa,saiga suhail din ya gantsare yana runtse idanu hadi dayi masa nuni da driver dake cikin motar. Dukka girarsa ya daga yana nuna masa ko a jikinsa
"Gaba idan ina sabgogi na nida iyalina ka sake shiga,na rantse da Allah da Allah saidai su sardauna suzo su daukeka a kakkarye"
"Amma dai kai mugu ne wallahi,koda yake na fuskanci inda ka dosa,kishi ne yake dawainiya dakai,kuma kada ka manta......ba sauke kafada ba,ko meye zaka yimin idan tace saini saini din" tafin hannunsa kawai ya sanya ya lullube fuskarsa,ya fuskanci ko meye zai cewa suhail bazai daina fadin abinda ke ransa ba,tun ba yau ba,yasan shi din dan kai tsaye ne,amma yanzun ya soma fahimtar abinda yakeyi masan kamar akwai wata a qasa.
Ana kiraye kirayen magarib motar ta daidaita a farfajiyar babban gidan nasu,ya sauke ajiyar zuciya yana dan yawo da idanunsa wai ko zai hangi benazeer ko batoul. Yanason shiga ciki ya gansu,to amma kuma muddin ya shiga din zai iya rasa jam'in sallah,don haka ya daure ya cire agogonsa da sauran kayayyakinsa ya miqawa attah yace ya shiga masa dashi wajen ama. Atta din nason masa bayanin saidai ya kaiwa bibi yaga har ya juya yana amsar ruwan alwala daga hannun daya daga cikin ma'aikatan gidan,don yace bazai qarasa famfunan dake jere a farfajiyar gidan.
Tare suka wuce masallacin shi da suhail almu atta da saddi. Sukayi sahu daya har aka idar,bai zauna azkar ba yasan kafin ya isa gida ya kammalasu a hanya,suka sake rankayawa cikin gida tare.
Sassan ama ya soma wucewa kai tsaye,saidai tun bai isa ba ya fuskanci sashen a kulle yake,ya dubi almu da suke tare
"Ina ama?"*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 79
"bata nan" ya amsa masa yana dan sosa kanshi,don shi bashi yaso ya shaida masa tafiyar tashi ba kada ya debo rigimar da tafi qarfin shekarunshi. Ido yadan qanqance yana kallonsa
"Kuma aka rufe sashen gaba daya haka?"
"Eh...... zata.....zata danyi kwana biyu ne" dan jim yayi yana jinjina abun,har yanzu ama fushi takeyi ne dashi haka da har zatayi wata muhimmiyar tafiyar da zatayi kwana biyu amma bata gaya masa ba?. Kai ya gyada yana juyawa a hankali,har yayi taku biyu kuma sai ya waiwayo
"Ita da waye tayi tafiyar?,na ganku dukka a gida kai dasu saddi?"
"Benazeer da batoul sai mamarsu......a gida dama mu muke,ba zamu iya dadewar da sukeyi a can ba" ya amsawa maina kai tsaye duk da kaucewar da yaso yi. Duka maganar saita dunqulewa maina waje daya,wanne irin dadewa sukeyi?,a ina kuma suke dadewar?,ina suka tafi?.
"Ina suka tafi?" Ya tambayeshi yana jin fargaba cikin ranshi,don maganar data gaya masa ta qarshe ce ke dawo masa ka
"Da dai Austria suka fara zuwa,amma daga baya sun canza qasa,ban dai tantance ba"
"Hasbunallahu wani'imal wakil" ya fadi cikin ransa,indai hakane kenan ama ta sake debe masa iyali sun yi nesa?,nesan da baisan waye zai masa cikakken bayani cikin gidan ba?.
"Amma wanne iri ne kai?,ta yaya mahaifiyarka zatayi nesa dakai irin haka amma kuma bakasan wanne qasa take ba?"
"Bata gayamana ba ya maina...."
"Okay saita gaya maka?!" Ya tambayeshi a tsawace,tsawar data ratsashi sosai. Qas yayi da kansa yana dan ja baya gudun kada yakai masa duka
"U are not serious at all" ya fadi yana juyawa zuciyarsa na masa susa.
Yana takawa zuwa cikin sashen bibi amma gaba daya hankalinsa a dagule yake,da gaske take kenan da tace basai ya dawo ya sameta ba?,wanann din duka plan ne kenan?,plan kuma harda saka hannun ama?,kenan ama tafi son sultana a kanshi?,tafison farincikin sultana akan nashi farincikin?. Da wannan tunanin a ransa yayi sallama murya can ciki a falon bibi,idanunshi a kanta tana zaune tana amsa waya da wayar hamaissa ta sashen oncle umar.
Zamewa yarinyar tayi ta gaidashi ta soma barin falon,duk da bai jima da dawowa cikinsu ba amma halinsa ba baqo bane sannane ne,kuma har yanzu babu wani abu daya sauya game da halin nasa tunda suna gani.
Zamewa yayi ya zauna sosai gaban bibi kanshi a qasa,kunnuwansa suna sauraren wayar da bibi din takeyi,amma kuma saidai gaba daya hankalinsa yayi nisa da wajen,saidai ya fahimci waya takeyi hankalinta kwance,kenan babu abinda ya shalleta ko ya dameta?.
Kokawa yaketayi da zuciyarsa da kuma harshensa don kada fushi ya sanyashi fadin abinda bai kamata ba. Yana zaune bai motsa ba har ta ida wayar ta aje gefanta tana dubansa. Bacin rai fushi da kuma motsuwar zuciyarsa baya boyuwa a idanunta. Bata kai ga magana ba ya daga idanunsa da shi kansa yakejin sun sauya launi
"Abinda akeyimin bibi ya fara kaini maqura......ayimin hukunci kawai a wuce wajen amma ba'a yimin ba?,sai a dinga yimin wani irin bahagon horo?,zuciyata akeso ta buga?, saboda inata kawaici?" Bude baki bibi tayi kawai tana kallonsa,kafin ta tattara mamakinta tsaf ta alkinta bayan ta tuna waye ALIYYUN
"yanzu wannan baqi da farin da kazo kana ja da waye kake?" Ta furta fana jefa masa wani kallo a kaikaice
"Kun tattaramin matata da 'ya'yana kun cillasu wata duniya,bada sanina ba,bada izini na ba,wannan dai dai ne?" Ya qarashe maganar yana duban bibin. Motsawa tayi tana sake daukar wayar gefanta
"Af.....wannan zancan ai hamidou ya kamata na kira maka saika gaya masa kai tsaye,kasan waqa a bakin me ita tafi dadi ko?" Ta fadi tana lalube cikin wayar.
A nutse ya sanya hannu ya zare wayar daga hannunta,saita bishi da kallo sanda yake aje wayar gefe
"Meye na gaggawa bibi?,zan fadi mishi a sanda na lalubosu da kaina ba tare da neman taimakon kowa ko qarin haske daga gurin kowa ba.....zan tabbatar muku ina matuqar qaunarsu,kuma su din jinina ne....... numfashi na sannan kuma rayuwata.......saidai kuma,daga sanda na nemosu da kaina,a barni da matata saboda halalina ce ita din.....,inason ki isarmin da wannan saqon" baki bibi ta kama tana kallonsa,dukka ya gama sanyata jin kunya da nauyin kalamansa,data rasa abunyi sai kawai ta buge masa da borin kunya
"Nice marainiyar wayonka kenan kazo ka zauna ka sakani a gaba kake gayamin?" Wani malalacin murmushi ya saki,don yanzun bashi da kowanne energy na biyewa bibi akan maganarta,sai ya miqe tsam,ya matsa gaba ya kama hannunta yayi kissing bayan hannun nata a kasalance yana cewa
"Karki rigima dani,don nima gobe zan koma inda na fito in sha Allah" yana ganin yadda jikinta yayi sanyi saboda maganarshi ta qarshe,ya juya a nutse ya fita a dakin.
Bai samu suhail cikin dakin ba,amma kuma yaji tashin muryarsa a harabar gidan shi da security,yasan halinsa dan rudu ne,yanzun haka wata hirar ya samu a can shi yasa yayi zamansa,dadewarsa da yawa kuma ya bashi tabbacin qilan ya wuce wajen mutuniyar tasa wato bibi. Sanda almu ya kawo masa abinci ya tabbatar masa da haka.
Ba wani taste yaji a abincin ba,don ba abincin ba hatta gidan a daren salam yake jinsa,kafin suhail ya shigo dakin tuni ya kade passport dinsa ya sanya a yanka masa ticket,gwara ya koma Paris ya soma rage wasu abubuwan kafin binciken inda sukayi ya kammala,don yaci alwashi yadda yayi mata alqawari to sai ya cika,sai ya zaqulota ko a ina take cikin fadin duniya.
Yayi sa'a qwarai ya samu ticket na jirgin da zai tashi daga abuja zuwa Paris direct kwanaki biyun da zasu zo a gaba,ba haka yaso ba, yaso ya samu wanda zai tashi a gobe,to amma haka dole ya haqura ya karba a haka,saidai iuma yaji yafi masa sauqi ya wuce Abuja gidan daya daga cikin kawunnan nasa ya jira kwanakin, uncle abdulhakeem ko uncle tahir.
Sai washegari da safe yake gayawa suhail zai koma,yayi mamaki suhail din ya kuma tambayeshi me ya kawo wannan tafiyar haka ta gaggawa
"Lokacine yayi" kawai ya amsa masa a taqaice
"Alright,yayi,ni zan qarashe weekend dina a nan gidan,kasan gidan masoyi dadi gareshi,ga kuma sabuwar granny na samu,ina jin kusan sai sabon wata zan taddaka a Paris"
"Allah ya kaimu" ya amsa masa a taqaice. Ya lura akwai damuwa me yawa cikin idanun maina din,to amma yasan hali sarai,ba lallai bane ya bashi amsa idan ya tambayeshi,don haka sai kawai ya tayashi da addu'a cikin ransa.
***********Jiran mintuna kadan yayi bayan ya shaidawa uncle tahir yana cikin filin sauka da tashin jiragen sama na garin abuja aka kirashi da wata baquwar number.
Cikin matuqar yauqi da iyayi take magana ta cikin wayar
"Hello......mr haidar?"
"Yes" ya amsa a taqaice
"Sunana ayana tahir me kano......kana ta wanne guri?,ina jiranka zanyi picking naka"
"Gani nan qarasowa" ya amsa mata a taqaice daga inda yake yana hangota. Idanunsa ya sauke daga kanta,duk da ya jima rabon daya ganta,tun batafi shekara sha takwas ba amma hakan bai hanashi ganeta ba,saboda tsananin kama da sukayi da uncle tahir din.
Straight gown ne a jikinta na wani yadi wine color,ta yane kanta da mayafi gray color me haske. Kana kallonta zakasan ta hada jini da abzinawa sosai,sai ya sanya wayarsh a aljihu ya jawo luggage dinsa yana nufarta.
Garin waiwayen neman ta inda zaya bullo idanunta suka fada kanshi,sai ta tsaya cak tana goye hannayenta a qirji, murmushin da bata shirya ba ya subuce mata
"Tun ba yau ba,na jima ina fadin ya hadu,ya hadu,ya hadu......maganata ta tabbata bayan shekaru bakwai rabona dashi" ta furta cikin zuciyarta saidai kuma labbanta suna motsawa,hakanan murmushi yana fita daga saman fuskarta.
"U are welcome" ta fadi cikin karairaya sanda ta iskeshi a hanya tana amsar luggage din hannunsa. Hannunsa ya zame yana bar mata tare da danyin gaba yana amsa mata da
"Thanks"
"Saura kadan na wuce ai daddy yace na tsaya lallai na dauko yaya na" ta fadi tana murmushi sanda take bude masa side dinsa. Dan qaramin murmushi da yafi kama dana yaqe ya saki yana girgiza kai
"Lallai naci sa'a kenan"
"Sosai ma kuwa" ta fadi da zaqi da kuma kambama abun. Shiga kawai yayi ba tare da ya sake cewa komai ba,ta zagaya ta shiga itama ta rufe motar tana qoqarin tashinta.
Ko cikin motar ta dameshi ta hira,tana ta sako mishi hirar da yake ganin sam bata shafeshi ba,hasalima ba lissafinta bane a gabanshi a yanzun. Sam yadda yayi bakam ita bai dameta ba,abubuwa da yawa take shiryawa ranta a kanshi,take kuma tsara yadda komai zaya kasance.
Bayan tsahon shekarun batayi tsammanin koda rabin haka zaya kai ba,sai gashi ya zarta dukka tunaninta a ganin data yi masa,ya darata kyau ya darata ilimi,kaman yadda take da tabbacin dukka gatan da take gani tana dashi ya darata,saidai duk ba damuwa bane wannan a wajenta.
Sai daya fara shiga a tsaitsaye ya gaisa da matar uncle tahir sannan ayana tayi masa jagora zuwa dakin da aka saukeshi. Komai sai data tsaya ta masa bayani dalla dalla tamkar yace mata yana da buqata,minti sha biyar kacal ta bashi ta dawo dauke da kayan abinci ta shirya masa komai, yayi tsammanin zata tafi ta barshi ne amma sai yaga tayi sabon zama,surutunta ya fara damunsa,don bacci yakeso yayi isashe,hutu yake da buqatar samu wanda zai bashi daman aiwatar da komai tsakanin kwanaki biyun da zaiyi a Nigeria zuwa tafiyarsa paris,amma ya fuskanci ba zata barshi ba
"Zan iya samun space please,ina buqatar hutu"
"Oh sorry,bari na barka ka huta,na sha'afa inata zumudin ganin dan uwa.....daddy baya nan,amma na tabbatan gobe war haka yana gida......idan kana da buqatar wani abu ka kirani,kada ka damu, number dana kiraka dazu a airport itace number na......a huta lafiya" ta furta tana murmushi hadi da waving hannunta. Kai kawai ya daga mata ya maida idanunsa ya rufe,yana irge da takunta a haka har xuwa sanda ya fuskanci ta fita,ya miqe da hanzari ya isa bakin qofar ya murza key ya rufe yana furzar da iska daga bakinsa
"Muddin a gidansu wannan yarinyar zaiyi kwana biyun nan to tabbas zata sabauta masa kunnuwa da dan banzan surutunta,wannan da suhail tafi dacewa" ya fadi qasan ransa hannayensa zube a aljihun wandonsa yana komawa inda ya jona system dinsa da yakeson ya fara aikun binciken location na ama ko sultana..*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 80
Bashi yabar kan system din ba sai da yaji ana kiraye kirayen sallar magariba,duk da yaji an masa knocking kusau sau uku,sannan kuma yaga musicals na ayana amma ba wanda yabi takai. Wanka ya soma sakewa,ya canza kayansa suwa abaya na Maza,ya Sanya slippers da ya gani a sashen wanda ya tabbatar an ajjiyeshi ne saboda baqi ya wuce masallaci.
Magariba da ishai duka acan yayi,bai dawo ba sai bayan ishai din. A farfajiyar gidan ya zauna yana amsa wayar suhail.
Tun daga nesa ya hangeta sanye da English wears riga da skirt da suka zauna mata daidai jikinta,ta yane kanta da qaramin scarf kunneta manne da earpiece,kansa ya dauke kadan kamar bai ganta ba yana ci gaba da wayarsa. Baisan ya akayi ta hangoshi ba,ta iso wajen fuskarta dauke da fara'a
"Ashe kana ta nan kana hutawa,nayita knocking na jika shuru" . Dan shuru suhail yayi daga bangarensa sannan yace
"Wacce babe ke magana?"
"Excuse me,zan kiraka" maina ya fadi yana katse kiran,don bayason taratsin suhail,yanzu sai ya qara masa damuwa.
A nutse ya daga kai ya dubeta,saita sakar masa murmushi
"Nayi disturbing naka ko?,am sorry bansan waya kake bane" ta sake fadi tana neman wajen zama kusa dashi. Miqewa yayi yana maida wayarsa aljihu
"Zan shiga ciki"
"In qaraso na tayaka hira idan ba matsala?" Ta tambayeshi tana karyar da kai,har cikin zuciyarta tana jin wani abu yana mata suka game dashi
"Idan ba zaki damu ba kiyi zamanku a nan,akwai aikin da nakeyi ne a ciki,but idan na gama i will let you know" yace da ita yana dan soma takawa
"Alright" ta amsa masa a sanyaye tana binsa da kallo.
Sai da ya bace mata sannan ta sauke ajiyar zuciya
"Ya hadu,ya isa mijin aure" ta furta qasa qasa tana sakewa kanta murmushi,addu'a takeyi cikin ranta Alllah yasa zai dade cikin gidan nasu,wala'alla ta samu damar da zata gabatar da qudurinta cikin sauqi a kanta. Ta tabbatar komai zaizo da sauqi,tunda dai jini daya suke ita dashi din.
_ni kuwa nace hmmmm,hala bata yiwa aliyyun cikakken sani ba_
Washegari dukkansu suna dining suna cin abincin dare,shi uncle tahir daya dawo tunda yammaci daga tafiyar da yayi din,sai kuma ayana da qannenta mata guda biyu,hajar da nusaiba. Gaba daya tabi ta addabi motsinsa,ko yaya ya motsa sai tace
"Akwai wani abu da kakeso ne?" Saidai kawai ya girgiza mata kai. A haka har sukayi nisa da cin abincin nasu,suna dan taba hira da uncle tahir din kadan kadan.
"Ina zaka koma yanzun?"
"Paris daddy"
"Wow......paris?,daddy na samu abokin tafiya kenan" ayana ta tari zancan tana nuna zaquwa da murna cikin muryarta. Da alama uncle tahir din dan boko ne na gaske,sai ya saki murmushi yana duban maina
"Ashe fa qanwarka cikin watannan itama zata wuce paris din,kaga shikenan na samu me kulamin da wasu al'amuran nata ko?" Uncle tahir din ya fada yana murmushi.
"Ma sha Allah" kawai maina ya iya