Showing 147001 words to 150000 words out of 294767 words
Chapter 50 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
yabo ba fallasa,shuru ya biyo baya sai kokaye kokayen benazeer da batoul. Agogonsa ya kalla yana cewa
"Akwai aikin bude wani company din ubangidana a niamy da zamuje ama,kwana daya zamuyi gobe zan dawo in sha Allah,ayimin addu'a" maganar taji tayi mata banbarakwai har ta kasa hadiyewa,ta waiwayo tana duban idanunsa
"Company din uban gidanka?" Ta tambayeshi cike da mamaki. Kai ya gyada
"Eh ama"
"Kana jinin gidan mayak'i?,jikan ABDU ME KANO?,ubangida fa aliyyu?" Ta kuma furtawa tana jinjina abun. Qasa yayi da kansa,yasan sarai dukka tambayoyinta abinda suke nufi,ya kuma san meye ya taba zuciyarta,to amma kuma shidin ya riga ya yiwa kansa alqawari ne,zaya dawo musu a cikakken mutum me dogaro da kansa,wanda yasan zafin nema da rashin,wanda bai dogara da kowa ba,wanda kuma bai aza nauyin rayuwarsa akan kowa ba.
"Allah ya bada sa'a" kawai tace dashi a taqaice
"Na gode" ya amsa mata yana miqewa dukka jikinsa a sanyaye. Ya sani don dai sunqi bashi cikakkiyar damar da yake da buqata ne,amma akwai abubuwa masu tarin yawa da suke buqatar su sanar da juna su kuma fahimtar da juna,saidai komai lokaci ne,yana sanya ran zuwa da wucewar komai a kurkusa.
A gaban benazeer da batoul ya tsugunna ya kama hannayensu ya sanya cikin nasa
"Ayima daddy Addu'a zaiyi tafiya" murmushi dukka sukayi,benazeer ta hade hannayenta waje daya ta fara karanto ire iren addu'o'in da ake koya musu. Murmushi ya dinga yi yana amsawa da ameen,har sai data gama suka shafa a tare,ya durqusa yayi kissing goshin kowaccensu sannan ya soma tafiya da baya da baya yana daga musu hannu suna maida masa,tamkar yasan idan yaje ya dawo din ba lallai ya taddasu,a haka ya fice a dakin.
Kamar zai wuce amma sai taji kaman ana jansa da magnet zuwa dakin nata,a nutse ya juya akalar tafiyar tasa zuwa dakin nata.
A tausashe ya murza handle din ya tura,tana tsaye gaban madubi da madaidaicin mug dauke coffee me dumi tana kurba a hankali. Har cikin jiki da zuciyarta taji shigowar tasa,amma wata zuciyar ta bata shawarar dakewa,don haka ta basar,tayi kaman bata ganshi ba tana ci gaba da kurbar coffe din nata da a yanzun taste dinsa ya sauya gaba daya a bakinta.
Maida qofar yayi ya rufe sannan ya murza key yana qarasowa cikin dakin hannayensa zube a aljihun wandon rigarsa.
Ta qasan idanu take satar kallonsa,zuciyarta taci gaba da harbawa tana qoqarin dannewa. Karon faro taji ya mata kwarjini sosai,shigar ta sake sakashi ya zama babban mutum kuma magidanci zam,taci gaba da dannewa cikin nuna dakiya da juriya,shi kuma yaci gaba da qarasowa,bai kuma tsaya ba har sai da yazo dab da bayanta. Cikin zafin nama taso zillewa,saidai ina ya fita ta wannan fannin,caraf ya riqota,ya kuma sanyata cikin jikinsa da kyau yana dora habarsa saman kafadarta,wannan ya bashi damar sakar mata numfashin da ya sanya dukkan wata tsiga ta jikinta tashi. Kici kicin qwacewa ta fara yi,ya mata namijin riqo muryarsa can qasa da wani irin laushi tamkar wanda ciwo ya yiwa sassan jikinsa illa yace
"Relax mana......zuwa nayi muyi sallama zan danyi tafiya,ayimin addu'a"
"Meye hadina da tafiyar ka?,wancan karon da zaka tafi din ka gayaminne?,yanzun ma Allah yasa kafi ruwa gudu" wata malalaciyar dariya ya saki wadda ta sanyashi sakinta yaja da baya qaramar dariyarshi nadan fidda sauti. Muddin a yadda yakeji a jikinsan nan yanzu da yadda lokaci ya qure musu yace zaya biye mata tafiyar ba zata yiwu ba,yana da burin ya jigatata ainun ta yadda zata rasa bakin maida masa martani
"Na fahimci tafiyata ta wancan lokacin ta miki zafi sosai......"
"Allah ya sawwaqe" ta maida masa a tsiwace. Murmushi ya sake qwace masa,shi daya yasan tanadin da yayi mata yana tarata ne kawai,sai ya kalli agogon hannunsa sannan ya maida dubansa tsakiyar fararen idanunta
"Idan ta miki idanma bata miki ba.....duk ba damuwa.....Allah ya dawo dani zan wanke kaina yadda ya dace" ya fadi yana dage mata girarsa guda daya. Kai ta dauke da sauri saboda wani nauyi da ya aje mata ta cikin idanunsa,ta soma nufar qofar toilet ba don tana da abunyi a can din ba
"Basai idan ka taras dani ba?" Har ya soma taku sai ya tsaya cak ya waiwayo a nutse yana dubanta,wani abu ya darsu a zuciyarsa,ya sauke numfashi sannan a nutse cikin jerarrun kalamansa da kuma wani yanayin sound dazai nuna maka da gasken gaske yake magana ya furta
"Idan kina ganin kin bacewa ganina a wancan karon......wannan lokacin kiyi gudu dukka iya yanda kike ganin zaki iyayi cikin fadin duniya.....ni aliyyu maina mayak'i ina me baki tabbacin zan taddoki na kuma zaquloki......i promise" ya furta yana daga yatsunsa. Da idanunta fes take kallonsa daga qofar bandaki,bai qara daga haka ba ya juya a dan gaggauce yana ficewa a dakin bayan ya aje mata wayarta saman sofa bed.
*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 77
Numfashi taja me qarfi matuqa daga hancinta zuwa cikinta sannan ta fesar,yanayin yadda yayi magana ya ratsata qwarai,har taji kowacce kalma na sauka a kowanne gaba na jikinta,ta dinga jin abinda ya fadi din kamar dahir ne,amma kuma wani sashe na zuciyarta sai taji ya kasa aminta da hakan. Ta ina zai zaqulota?,ta yaya zai taddota?,bayan inda zata shiga din zata guje masa ne da nisan tazarar tafiyar awanni da kwanaki ma?,ba zata taba bari ya zaqulota ba, tabbas!.....itama zata tabbatar ta cika wannan alwashin da taci. Da wannan tunanin ta fito daga bakin bandakin don dama bawai wani abu zatayi a ciki ba,mafaka kawai take nema,ta dawo cikin dakin jikinta na neman mutuwa amma ta bawa kanta qwarin gwiwa,ta sauke suit case dinta guda biyu,ta soma hada komai nata waje daya,tana ji a ranta da zuciyarta muddin yana nijer batasan ranar sake zuwanta ba.
Shi daya cikin mota suna a hanya amma dukka jikinsa ya mutu murus,irin qiyayya da tsanar da yake hanga cikin idanunta tana taba zuciyarsa sosai,baisan me take buqata daga gareshi ba wanda zai wanke dukka laifin da yayi mata. Kamar me magana a radio din yasan me yake tattaunawa cikin ransa ya soma magana kaman haka
_ba kowacce matsala ce tsakanin masoya sulhu ke maganceta ba,wani lokaci sai ayi fada,wani lokacin sai anyi qarfa qarfa an saka qarfin iko_ a nutse ya lumshe idanunsa yana digesting maganar a kwanyarsa,tsahon mintuna kusan talatin kafin wani murmushi ya subuce masa
"Na fahimta" ya furta can qasa yana jinjina kai.
"Me ka fahimta yallabai?" Suhail dake zaune gefansa yana duba newspaper da alama shidin makarancin labarai ne ya fadi yana duban maina. Juyowa yayi suka hada idanu dashi ta cikin eye glasses dinsa
"It's not your own business" idanu suhail din ya dan fiddo sai kuma ya maidasu yana rufe jaridan
"U right.....abinda yafi damuna rashin samun layin crush dina......kaine nake ganin zaka taimaka min kana neman watsa min qasa a idanu,ka qirqiri wasu labarai duk don ka nesantata dani......ni kuma nayi alqawarin bazan bar marad'i ba sai da soyayyarta" ya fadi yana dunqule hannunsa guri guda. Da qyar maina yawu ya wuce ta maqoshin maina,ya dauke kansa a hankali yana qoqarin tausar zuciyarsa kan kada ya yiwa suhail mugun bugu cikin motar,muddin yace zai daki suhail to saidai buzunsa,don ko a qirar jiki suhail din dan kalankashi ne me jikin fulani. Hannunsa ya tura cikin qaramar jakarsa ya fiddo headphones ya dora saman kansa ya toshe kunnuwansa,yayi connecting da wayarsa ya soma sauraren wani abu na daban,sai suhail yayi sak yana kallonsa kafin daga bisani ya dauke kallonsa yana girgiza kai.
**********Washegari sukayi sallama da dukkan wani family din MAYAK'I suka wuce airport suka bar al'ummar gidan cike da kewar iyalan ama musamman BB. Bibi harda qananun qwallar wucewar yaran
"An daukesu an dauke uwarsu" ta fadi cikin falon nata tana qananun qwalla. Kusan dariya ta bawa kowa,bibi din bata iya sabo da mutum ba idan ta tashi sabo dashi din,bare sultana da take tamkar wani bangare na jikinta,ga yaran suma sun dosano farinjininta da kuma soyayyar data samu din.
"Sai da nace ki shirya mu wuce tare bibi,yanzun a miki shiri ki biyo bayanmu?" Ama ta furta cikin lallashi. Kai bibi ta girgiza
"A'ah hamdiyya,barni a nan cikin ahalina,shekaruna turawa sukeyi,na gaji da yawo a qarfen nasara,irin haka ne mutuwa zata riskeka a qasar wasu azo ayita tiri tiri da gawarka,ko mutuwa ne gwara ka mutu cikin sutura a dakinka" maganar tata sai tadan taba zuciyar kowa amma sai suka bita da dariya,sultana tace
"Mutuwa bibi ba yanzu ba,Allah ya qara miki dogon kwana me amfani"
"Ameen" aba dake duqe shima a gabanta ya amsa. Nutsuwa sukayi bibi ta musu addu'o'i sosai sannan suka miqe,har sun fita ta sanya aka kira mata aba,ya dawo gabanta ya tsugunna
"Hamidou"
"Na'am bibi?"
"Rayuwa bata da tabbas,hakanan duk dan adam bai wuce kuskure ba,shine cikar dan adam din,abinda nakeso dakai don Allah ina roqonka ka sassautawa yaron nan koda a iya fuska ne,ya dawo da dukka qwarin gwiwarsa da kuma daidaita rayuwarsa,bai kamata mu rushe komai nasa ba akan kuskuren da ya riga ya afku,kuma Allah ya kawo yankewar komai ba tare da an samu mummunan sakamakon lalacewar rayuwar wani cikin su biyun ba" kai ya gyada a ladabce
"In sha Allah bibi"
"Allah ya albarkaci rayuwarku gaba daya" ya amsa da ameen.
Lokacin da jirginsu ya daidaita a sararin samaniya sai ta furta
"Alhamdulillah" cikin wata cikakkiyar nutsuwa,ta rufe idanunta tana jinta ta zama comfortable, murmushi ya kufce mata,can qasan maqoshinta ta fadi
"Naga ta inda zaka nemo ni" tayi maganar cikin mugunta da jin ta tsere masa har abada.
A nutse ama ta dauke dubanta daga fuskarta tana sauke tata ajiyar zuciyar,tun daxun ta fahimci yadda take cikin walwala da barowarsu nijer,ta sani koma meye zai sakata walwala baya rasa nasaba da gujewa maina,batasan yadda wannan qaddara ta samo asali ba,kuma Allah shine masanin lokacin qarewarta,bata taba ganin irin wannan mummunar rashin jituwar kamar tasu ba,tun abun be damunta har ya soma tabata,abu daya ya rage mata wannan addu'ar zata ci gaba dayi
"Allahumma khir li wakhtarli". Maida dubanta ta sakeyi ga benazeer da batoul,basuyi sallama da mahaifinsu ba don basusan inda zasu koma din wani guri ne da zasu jima basu ganshi ba,duka lissafinsu Nigeria zasu sake zuwa suyi wani hutun na kwana daya ko biyu kafin daddynsu shima ya dawo daga tafiya.
Iska ta kuma furzarwa,Allah ya sani taqi shaida masa ne saboda tana son ya sake sanin maqurar muhimmancin mace a wajen d'a namiji,tanason yasha wahalar samo kanta wadda bai sha ba sanda aka aura masa ita sama taka yana zaune cikin inuwa,tanason ya jigata yadda bazaiyi wasa da ita ba,bazai kuma yi wasa wajen nemo soyayyarta ba. Murmushi yadan qwace mata tana hangoshi sanda zai duba kaf gidan yaga ba ita ba benazeer ba batoul ba kuma sultana din. Ta tabbatar sai yayi musu qaramar hauka,to amma kuma tana dan shakkar anya zaya dauki lokaci mai tsaho me gano inda suke ba?. Ta sanshi farin sani tas ma kuwa,tunda dai ya fita daga jikinta ne,yana da naci da bin qwaqwafi akan dukkan abinda yakeson aiwatarwa ya kuma sanya a gaba,uwa uba ko da can yana da wata fikira da basirar saurin gano abu,to amma koda ya gano inda suke din,tasan bazai gano su a banza ba,dole energy da kudaden aljihunsa suyi aiki,idan yazo kuma ya kawo mata kanshi,don ba zata zake bari yayi aiki qarqashin wasu ba,bayan a abinda kakanninsa ita da aba suka tara masa yana da dukiyar zai dauki mutum Dari aiki a qarqashinsa da cikakken albashin da zai riqe kowanne ma'aikaci da iyalinsa.
Kwana daya rak suka daidaita cikin qasar France a garin paris. Ba wani dauda ko qura me yawa suka samu,don haka cikin awanni qalilan suka gyare komai,komai kuma ya koma kan muhallinsa,abu na gaba data fara shiri shine fara aikinta a sati na gaba a gidan tv ta qasar paris,wanda zata zama jagorar shirin daya shafi al'adun africa gaba daya. A satin suka tura mata kudade masu yawa daga gidan tv din na wardrobe allowance. Bata da buqata ba abinda kuma zatayi dasu,don suttura kam wata ma sai ta shekara biyu bata sakata ba. Ta bangaren aikinta da zata fara kuwa komai aba ya tanadar mata,ga ama itama a gefe data tsaya mata kan ta lissafa duk abinda take da buqata ko takeso,buqata kam saidai idan bata fadi wadda takeso ba,don haka hanakalinta kwance take shirye shiryen kama aikinta.
*_MAINA FA?_**_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 78
*ALIYYU MAINA*
Cikin qwazo da kuma qwarewa ya jagorancin aikin duba kamfanin da gabatar da abubuwan da suka zama dole a buqata a cikinsa don samun ingantattun abubuwa da zasu dinga fitarwa. Haka kawai ya samu hankalinsa da tunaninsa suna karkasuwa kashi kashi,wani a niamy wani a marad'i,duk bayan wasu lokuta sai benazeer da batoul sun fado masa a rai,ta wani gefen kuma sultanan ce gaba daya tayi masa tsaye a rai,yana tuna abubuwa masu yawa da suka faru a tsakaninsu,bama iya sultana kawai ba hatta da yaran,wani abun ya saki murmushi wani ya girgiza kai,daga qarshe yakai tafin hannunsa saman qur'aninsa saitin zuciyarsa ya dafe yana fidda wani sihirtaccen murmushi.
Ya yadda yayi imani sannan kuma ya tabbatar a yanzun sune rayuwarsa,sune Kuma duniyarsa gaba daya,bayajin zaya iya rayuwa ba tare dasu ba,haqurin da yayi na wancan shekarun,ya rayu babu su,a wannan karon baya jin zuciyarsa zata dauke wannan. Wannan tunanin ya sanyashi yin overwork a ranar,suhail nata mitar ya gaji,ba sauri sukeyi ba,me zaya hana su isa masauki su kwanta, gobe su qarasa zuwa jibi,ko gata ne sa koma marad'i din,ai suna da enough time.
Juyawa yayi kawai ya kalleshi,shi daya yasan me yakeji a zuciyarsa,yana ji kaman ya raba zuciyarsa ne gida biyu yabar rabi a marad'i,a wannin da yaketa spending a nan din yana ji kaman ya maidosu marad'i,bazai taba iya kaiwa jibi a niamy ba,yana buqatar komawa ya hada kan iyalinshi waje guda,ayi duk abinda za'a yi a gama,zai rungumi kowanne irin tsanani,don wannan karon bawi da wasa yakeson maidota cikin rayuwarsa ba.
"Ban hanaka zuwa ka kwanta ba......abinda na sani dai kawai shine,gobe in sha Allah a marad'i zan kwana,ko mun gama ko bamu gama ba,bare ma inda tabbacin na sanya dukkan effort dina,gobe azahar yayi yawa mun gama in sha Allah.....idan ka gaji kaje ka huta zan iya kammalawa" bai sake cewa komai ba ya maida kansa yaci gaba da magana da ma'aikatan.
Satar kallon maina din kawai yakeyi,he's so hardworking,tun farkon haduwarsu abinda yaja raayinsa game dashi kenan,bashi da wasa,ko meye ya saka a gabansa sai ya cimma nasararsa. Iya wannan daya tuna din,sai shima ya kakkabe dukkan wata guntuwar kasala ya miqe sosai suka ci gaba da aikin tare.
Kaman yadda ya yiwa kansa alqawari washegarin qarfe sha biyu na rana sun kammala komai,zuwa qarfe daya ya kammala rubutawa daddy report ya tura masa ya kuma turawa sardauna ragowar,kai tsaye suka koma masauki,ya koma toilet ya sake watsa ruwa,ya kuma shirya tsaf cikin wani lallausan farin yadi,saidai kuma dukka wannan gaggawar tashi dole ya jira akwai ragowar lokaci,don jirginsu sai qarfe hudu zai tashi,yana ji yana gani ya fita corridor din dake manne da dakinsu ya zauna samam couch yana duban suhail dake zaune d'ai d'ai abinsa ba alamun shiri tattare dashi.
Kanshi ya dauke yana zuqar numfashi,zayaso suhail din yayi zamansa a nan ba tare daya bishi marad'i din ba,duk da haka sai ya danne zuciyarsa ya tambayeshin yana duban wani guri na daban
"Hala ka dawo gida kenan?"
"Me ka gani?" Suhail dake shan yoghurt ya fadi
"Banga alamun tafiya tattare dakai ba,na dauka zaka kammala hutunka a nan,zamu hade kawai a France"
"Inaaaa" ya furta yana miqewa da hanzari kamar wanda aka mintsina,har sai da maina dole ya juyo ya kalleshi.
Fararen danunsa fes cikin na maina din yana kallonsa
"Banga ta zama ba,ka manta har yanxu ko cikakken magana bamuyi da crush dina ba?,yaya zan koma ban samu soyayyata ba?" Idanunsa ya mayar ya lumshe.
yanajin kamar suhail yana diga masa wani abu saman zuciyarsa,baisan me yasa ba,ba halin suhail bane qin fahimtar mutum da gangan ba,amma sai yaga kaman idanunsa ya rufe a wannan karon
"Idan ma akwai wanda ya sanyaka kakemin haka......ina me baka shawarar kabi a hankali,idan har ka bari na fusata zan manta da matsayinka a wajena,na gaya maka ina kuma sake gaya maka,sultana is my wife......" Yana kaiwa nan ya miqe a nutse yana bar masa wajen. Da kallo suhail ya bishi,shi fa har yanzu yana tantama akan hakan,ta yaya hakan zata kasance?,shekarunsu nawa dashi?,amma koda wasa bai taba zancan wata ba?,yaran da yake iqirarin nashin ne sau nawa suna zancan baisan yaran wanne qasa bane?. Kai ya girgiza,shi kam har yanzu bai