Showing 33001 words to 36000 words out of 294767 words
Chapter 12 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
umar da matansu. Batace komai ba ta budawa sultana bayan motar inda bibi ke zaune ta sakata
"Duk inda kikaji kin gaji ki samu waje ki zauna har sai jikinki da yanayinki ya daidaita" abinda ta cewa sultana kenan kawai ta juya tana barin wajen ba tare da tace da kowa komai ba,ba kuma tare da tayi tayin binsu din ba,saboda tasan yawo ne kawai zasuyi tare da batawa kansu lokaci.
Abu daya data sani shine,ko kadan a zuciyarta bataji tana qyamatar cikin da sultana ta samu ba,bata kuma ji baqinciki ba,kawai dai ta razana da jin sakamakon......tana kuma tsananin tausayin sultana da ciki a qarancin shekarunta.*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 17
Tunda ta koma ciki wayarta ke hannunta,sai tayi kaman zata kira bibi ko aba din sai ta fasa. Haka kawai takejin zafin yadda suka dauki abun da zafi suka girmameshi haka,a nata zaton yau ko fyaden da babu aure maina ya yiwa sultana,sannan har rabo ya shigo ciki,tayi zaton zasu karbi abun da sunan qaddara,su kuma rufa abun don yiwa juna halacci da kuma kyautata alaqar juna tare da girmama tsatso.
Daga qarshe data gaji da kai kawon da bashi da amfani sai kawai ta shiga kitchen da kanta. Dukka masu aikinta suna ciki,kowacce na hidimar da take alhakinta ce. Cikin girmama suka matsa suna bata hanya. Bilki ce ta fara tambayarta
"Ko akwai abinda kike buqata?" Kai ta girgiza
"Ba komai,zan dan gwada wasu qananun abinci ne ko za'a dace sultana ta samu wanda zata iya ci a ciki kafin su dawo" . Bata bawa kowa aiki ba,tace dai kowa yaci gaba da aikin dake gabansa.
Tana aikin amma sam ko qananun hirarrakin dasu bilki keyi a tsakaninsu bata iya tantancewa,saboda tsabar nisan da tunaninta yayi. INA MAINA YA TAFI?,wasa wasa kwanaki nisa suke suna kuma jirkicewa zuwa watanni,a ina yake?,ina yaje?. Ba qaramin damunta abun yakeyi ba cikin rai,a duk sanda ta sanya haqarqarinta a qasa zata kwanta maina dinne yake soma fado mata. Abinda ta lura ko sau daya aba bai taba tada maganarsa ba,sau biyu oncle umar da oncle bashar suna masa maganar sai yace dasu
"Ai ba yaro bane shi,ya fita sahun yara ko samari,magidanci ne yanzu,duk inda yaje ma zai dawo da qafafunsa,bani da lokacin bata lokaci wajen nemansa" itadinma ko sau dayan batayi gangancin masa maganar ba,tana iya nata qoqarinne kawai a bangarenta wajen samun koda labarin inda yake.
Shuru office din likita na uku da suka ziyarta a ranar yayi. Asibiti na qarshe da dukkansu sukayi yaqinin ba inda za'a gaya musu sama da abinda zasu gaya musun,saboda qwarewa da ingancin asibitin da har takai bayan ainihin asibitinsu Dr chafa'atou shine asibiti na biyu da ya samu lambar yabo daga qasar France,suke kuma da qwararrun likitoci da wasunsu 'yan asalin qasar France dinne.
Kanta na kwance saman kafadar bibi tana wani irin kuka kamar numfashinta zai dauke. Aba dake zaune ya gaza cewa komai,saidai dukka hankalinsa yana kan mahaifiyarsa saboda dimbin tashin hankalin da ya gani saman fuskarta. Shekarunta sun fara jaa,yana tsoron kada wani ciwon ya sarqafeta.
"Wannan kukan da takeyi yayi yawa,yanzu haka da na duba awon jininta,jininta ya hau daga qa'idar yadda ya kamata ya kasance,tana buqatar kulawa ta musamman,saboda shekarunta sunyi qanqanta qwarai da iya rainon juna biyu,muddin anason ta rayu lafiya ita da abinda yake cikinta dole a kula da damuwarta" kai bibi ta girgiza
"Ba zamu taba iya hanata wannan kukan ba.....mu dinma inda da hali barin namu idaniyar zamuyi ta zubda qwalla....... abu daya kawai na sani......bazan bari rayuwarta ta galabaita ba muddin ina numfashi" bibi ta fada da qwarin gwiwa.
"Yanzun zamu dan riqeta saboda tana da buqatar kulawar likita gaskiya qwarai da gaske,zamu sanya mata ruwa saboda jikinta babu isashen ruwa,sannan hawan da jininta yayi ma banajin yana da kyau a qyaleta ta tafi gida,akwai gwaje gwaje da dukka za'a yi mata a ajjiye koda buqatar gaggawa zata taso". Yana kaiwa nan nurse din ta shigo cikin harshen faransanci take gaya masa sun gama shirya komai
"Ku rakata dakin" ya fadi yana hada tarkacensa dake saman table din.
Tashin hankalin da takeji ya zarta duk yadda zata misalta. Sanda ta miqe nurse din ta kama hannunta sai taji ba zata iya sakin hannun bibi ba,a hankali taji idanunta sun soma rage kaifin ganinsu,wanda guda dayan da aka yi mata glasses saboda shi zuwa sannan ya sake samun raunin gani sosai sakamakon hawayen da take wuni ta kwana tana zubdawa. Babu wata ranar banza a gareta da zata fito har ta fadi hawaye basu fita daga idanunta ba.
"Muje ko?" Nurse din ta fadi cikin kwantar da murya. Qoqari take taga ta taka amma sai taji qafafunta kamar an riqesu,qirjinta kamar an aza masa wasu kaya masu nauyi,kanta kamar an daketa da wani qaqqarfan abu,duhu kuma ya soma mamaye hasken tarwai da office din yake dashi,ba tare data shirya ba hannayenta suka zame daga cikin na bibi,babu abinda taji sai salatin bibi da wani irin qaqqarfan sauti.
**********Tamkar wadda ake tasa daga bacci ta soma bude idanunta,wanda tun kafin takai ga gama bude idon gaba daya ta danji muryoyin qasa qasa. Sannu a hankali ta gama bude qwayoyin idanunta,fes suka sauka cikin dakin.
Mutum biyu ne zaune gaban kujeru ukun dake gaban gadon nata,sai kuma oncle umar da oncle bashar dake tsaye daga saman kanta. Saitin qafafunta kuma mamma kausara ce(qanwa ga mahaifinta hamani uwa daya uba daya).
Kusan kowa yunqurin mata sannu yakeyi,yayin da ama da mamma kausara suka matso suna qoqarin tadata zaune ganin tana mutsu mutsu
"Dole ki gaji,kwanciya ace tun jiya?" Ta danji mamaki cikin ranta,to amma kuma a yanzun ita duka ba wannan bane gabanta ba.
Duk sai da suka gama mata sannu da jiki sannan ama ta kawo ruwa ta bata. Tasha da yawa sosai,sannan ta kamata ta sauko da ita zuwa bandaki
"Kiyi wanka kizo ki rama sallolin da ake binki ko da a zaune ne" ama din ta fada.
Tayi wankan ta kuma rama kuma sallolin,saidai daga haka ba abinda ta iya qara yi,tana daga zaune saman abun sallar kawai. Ita ba tunani ba ita ba bacci ba, hakanan ita ba ido biyu ba,a haka 'yammatan gidan sa'anninta sukayi sallama suka shigo.
Aminata,yasmine,najma almu sai atta biye dasu. Sai da suka gama gaida iyayensun sannan suka qaraso inda take zaunen. Zagayeta sukayi kowa yana mata sannu cikin nuna kulawa da qauna ta 'yan uwantaka.
Banda kalmar DA SAUQI ba abinda ta iya sake furtawa. Da idanu kawai take binsu wani abu yana kai kawo cikin zuciyarta,sai kawai ta hade qaffaunta waje guda tana cusa kanta tsakanin cinyoyinta,don kuka take da buqatar ta sakeyi. Wannan kukan batasan yaushe zata daina yinsa ba tsayin rayuwarta,su aminata sha'awa suke bata,tana jin dama itace su,su dinma kamar haka rayuwarta take a baya ba?,tashi daya zallar zalunci irin na maina ya kutsa rayuwartata ya wargaza mata komai ds komai,ya rusa farincikinta da walwalarta,yayi rugu rugu da mafarkinta,a yanzun bata da wani sauran mafarki ko buri na rayuwa,tana jin rayuwarta dai dai take da fanko,tana kunyar kallon idanun su aminata su hanan da sauran qawayenta su ganta dauke da wani abu waishi CIKI!,cikin da suke gani jikin yayyensu?,cikin da suke ganin jikin iyayensu?. Batasan ya akayi sautin kukanta ya fita ba,saiji tayi su yasmine suna rungume da ita suna bata haquri,dukka muryoyinsu suma a karye,abinda ya sanya bibi miqewa kawai ta fice a dakin.
**********Dukkan iya abinda likitoci zasu yi mata na taimakon da ya dace sun bata,saidai kuma jigon samun sauqinta yadda ake da buqata yana hannunta.
Nutsuwa kwanciyar hankali da taqaita damuwa,abubuwa ne kuma da zasuyi wuyar gaske ace an samesu daga wajenta a yadda take ciki a wannan lokacin.
Wani irin matsanancin laulayi mai matuqar azabtar da ruhi da gangar jiki. Ta fita hayyacinta ainun,tayi wata irin rama da bata taba kwatankwacinta ba,har takai jallin da dukka suturunta sunyi mata yawa basa sanyuwa a jikinta. Bata iya cin komai,hakanan bata iya shan komai,kusan qarin ruwa shine abinda akafi yi mata duk bayan kwana biyu saboda samarwa jikinta abinci.
Wannan yanayin ya daga hankalin bibi matuqa,ta dinga jin kamar lokacin da zata rasa sultana ne yayi,kaman yadda ta rasa MOHMOUD ta rasa BINTOU ta kuma rasa NAFESSA. Wannan tunanin yayi matuqar razanata,ya kuma sanyata tattara dukka 'ya'yanta harma da ama da kuma mamma kausara ta shaida musu hukuncin da ta yanke ba kuma tare da neman shawararsu ba. Shawarar da take ganin ita daya ce MAFITA,ita kadai ce kuma hanya ta yankewa wannan AZABA da sultana ke sha, sa'annan qilan ta zama silar warwarewar bakin zaren komai.
*******A ranar data nemesun ta shaida zamanne bayan sallar isha'i. Cikin daya daga cikin falukanta masu kyau da tsari,wanda sam basu cika girma ba,sannan bata fiya wani zama cikinsu ba saboda ba falo bane dake a farko farkon sassanta ba.
Ama ce qarshen shigowa,sai data tsaya ta tabbatar abu me ruwa ruwa ya shiga cikin sultanan bayan wunin da tayi a wunin yau sur bata sanya komai a cikinta ba,sai uban amai da ya galabaitar da ita liqis. Duk sanda ta tashi da rikicewar yanayi irin hakan wuni ama din takeyi itama cikin tashin hankali. Tuntuni ta sauke dukka wasu harkokin business dinta ta damqawa wasu daga cikin mataimakanta,sai kuma saddi da yake yaayan atta da almu data dora masa wani nauyin shima,duk kuwa da cewa shekarunsa ba wasu masu yawa bane,duka duka sha bakwai yake amma lalura ta sanya dole ta fara dorashi bisa hanya.
Ta samu tasha oat da madara dan qaramin cup da baifi cup din yaro dan yaye ba,saidai duk da haka ama murna takeyi da ya zauna acikinta har ma bacci ya dauketa.
Tun jiya da bibi ta shigo wajen sultana,ta kuma buqaci ama ta basu waje zasuyi magana taji hankalinta bai kwanta ba. Duk wani kuka da damuwa da take ciki babu shi daga jiya zuwa yau din,sai laulayin kadai dake hanata sukuni. Maganar qarshe da taji bibi na fada bayan ta dawo canzawa sultana beadsheet ta tsaya mata a rai,ta kuma dinga juyata cikin ranta. Ta qure dukka maqurar tunaninta wajen son gano abinda maganar ke nufi,amma mahanga daya kwanyarta ke kaita,a ma'ana daya duk wani ma'aunin fassara yake zuwar mata,ma'anar da taqi gamsuwa da ita,zuciyarta taqi aminta da hakan.
"Karki damu,kwana uku kawai zakiji sauqi ki koma rayuwa kamar 'yan uwanki,duk wani ciwo zai wuce" to meye qarshen maganin laulayi haka da gaggawa?,laulayin da ba abu bane me yankewa yau ko gobe ba?,har sai sanda rabbi ya dauke maka,ko kuma zuwa sanda ka haife abinda yake cikinka?.
Da sallama ta shiga falon,sai taga kamar dukka idanu sunyo kanta. Bata wani bada muhimmanci ba ta qarasa daya daga cikin kujerun dake daura da aba,ta dauke filon kai ta zauna,ta kuma gyara zamanta sosai tana fuskantarsu
*_Tofa!,taron na meye?,me karatu muje zuwa,akwai sauran tirka tirka_*
*_wai ina Aliyyu haidar ya shiga ne?,ko team SULTANA NE SUKAYI MASA KURCIYA?_*🫣🫣🫣
*HUGUMA CE*
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
Book 02 page 18
"Tom,nasan dukkanku kuna mamakin abinda yasa na taraku a nan wajen?......a taqaice ba wani doguwar magana bace me tsaho,sannan kuma ba shawara na taraku nayi daku ba,na kiraku ne don na shaida muku,babu buqatar cikin dake jikin sultana a yanzu,saboda dukkaninmu munsan abinda likitoci suka fadi gami da hatsarurrukan dake tattare da lafiyarta,kuma ita din munfi buqatarta akan abinda take dauke dashi,saboda haka na yanke shawarar aje A CIRE CIKIN JIKINTA ma'ana A ZUBAR DASHI! don ta tsira da rayuwa da lafiyarta" Dif dakin ya sake yi,kowa ya zubawa bibi idanu sona son gano wasa takeyi musu?,ko tana fadin maganar ne da gaske.
Kaf dinsu babu wanda yaga digo ko alamun wasa tattare da bibi din, fuskarta ta sauya zuwa wani yanayi da yake sanya musu shakka a duk sanda wani ya yunqura zaiyi jayayya da umarninta. Ba wanda baiji saukar maganar har tsakiyar zuciyarsa ba. Kusan daqiqa uku kowa ya gaza tofa komai kafin daga bisani oncle oumar ya motsa yana matsowa gaba kadan daga kan kujerar da yake zaune
"Amma bibi......" Hannu ta daga masa tana cewa
"Dakata oumar,ya isa,bana buqatar qarin bayanin kowa,inajin dukkaninku ba wanda yasan ciwon sultana sama dani......."
"Sai kuma maina.....wanda shine yaci kashinta yaci fitsarinta,shine wankanta shine wankinta,tare suke jinya kukanta nashi ne damuwarta tashi ce....... shine cikinsa yake a jikinta a yanzu.....cikinsa na halak ba shege ba.....cikin da baya biya sadaki da albashinsa na dan makaranta.....shine cikin da ake cewa yanzu a cireshi?" Ta qarashe maganar tana jefawa bibi tambaya
"Hamdiyya...... meye haka?,kinsan a gaban wa kike a tsaye?,kisan me zaki fadi......"
"Me zan fada?,me zan fada ma?,to ban qarasa ba.......indai nice mahaifiyar Aliyyu,kuma akwai haqqinsa a wuyana,akwai kuma nawa haqqin a wuyansa.....ina fada da harshensa da nawa......ban yarda a fidda abinda yake tare da sultana ba,ban yarda ba har abada........!" Saita qarashe da wani kukan da bata shiryawa ba ya kufce mata,sai ta juya da gudu gudu sauri sauri tana fita daga falon,tana jin qirjinta yana mata nauyi,wani abu ya tokare mata qirjinta.
A gurguje a gurguje ta dinga ratsa farfajiyar gidan har ta isa sassanta. Can cikin dakinta ta yiwa kanta masauki,ta zube daga bakin gado a qasa kuka yana qwace mata.
Shin ta yaya?,ta yaya ma zata bari a zubda cikin aliyyu?,da wanne dalili zata bari hakan ta faru?,koda cikin shege bare na halak?,idan su dukka tunaninsu ya toshe hankalinsu ya gushe da soyayyar sultana don kawai su sama mata mafita to ita din tana a dai dai cikin hayyacinta.
Tayi kukan data jima batayi irinsa ba,ta kuma jima a nan zaune tana tunanin hanyar ra zata hana faruwar abinda bibi ta qudurta. Ta sani ta kuma yankewa ranta ko a mutu ko ayi rai,koda igiyar aurenta zata girgiza ba zata taba bari wannan abun ya faru ba.
Sanda ta kalli agogo sai ya nuna mata qarfe biyu da rabi na dare. Ta share sauran qwallar da suka rage mata cikin idanunta tana miqewa. Mafita guda daya ce yanzu tak ta rage mata ta amintar da sultana takuma sauketa daga doron amincewar da bibi ta sanyata tayi kan a zubda cikin.
Bandaki ta nufa ta daura alwala saboda ta samu sassaucin abinda takeji tsakiyar qirjinta,sannan ta fito ta dauki medium veil me santsi mahadin rigar jikinta ta yane kanta,ta jawo wayarta ta kunna data sannan ta nufi qofa ta buda a nutse ta fice a dakin.
Sau daya tak ta murda qofar dakin ta bude,saita tura a hankali tana shigewa. Fitilar gefan gado ne kawai a kunne,saman gadon kuma babu kowa alamun sultana din ta tashi,sai ta zauna saman sofa bed din dake daura da ita tana jiyo motsin ruwa a bandaki,sai ta tattara hankalinta akan wayar tana ci gaba da research kan abinda take da buqatar
A nutse ta kammala fitsarin tayi tsarki,saita matsa gaban wall mirror dake jikin bandakin,ta murda famfo ta wanke fuskarta da kyau,bayan ta gama taja qaramin towel ta soma goge fuskarta,a sannan ne idanunta suka fada kan fuskarta data fito tarwai ta cikin madubin kamar rana saboda wadatar haske da bandakin yake dashi.
A hankali take qarewa fuskartata kallo,fuskar da aqalla ta dauki watanni sama da uku rabon data kalleta. Lumshe idanunta tayi tana jin ciwon yadda dukka kamanninta suka canza,ta sanya hannu a hankali ta shafa gefan idonta da har yanzu akwai sauran tabo na bahagon marin da ya kaiwa fuskarta har ya zame ma idanunta illa. Janye hannun tayi tana jin wata irin mahaukaciyar tsanarsa tana ambaliya cikin zuciyarta,nau'in tsanar da