Showing 12001 words to 15000 words out of 294767 words
Chapter 5 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete
Washegari bayan mohmoud ya gama shirin fita wajen aiki ya zauna da bibi akan maganar, hamidou yana labe ya kasa zaune ya kasa tsaye yana jiran yaji me bibi ta yanke?. Mohmoud yasha fama da ita ba kadan ba kafin tayi amanna,tsananin murna ta sanya hamidou fitowa daga inda yake laben ba tare daya shirya ba. Da kallo galala bibi ta bishi
"Ja'iri dan nema,dama kana a wajen kenan" kunya ta kamashi,ya samu waje ya zauna yana sinne kai.
"In sha Allah bibi na miki alqawarin ba zakuyi nadamar shigowar hamdiyya cikinmu ba,hamdiyya bata da wani aibu ko makusa ta fannin tarbiyya,ni kaina inda nasan da matsala bibi wallahi bazan saki jiki da lamarin ba"
"Allah yayi zabin abinda yafi alkhairi"
"Yanzun abinda na yanke hamma ya samamin wani aikin da zan dinga yi,duk sanda bamu da lecture sai na fito nayi na koma makaranta" kai mohmoud ya girgiza yana murmushi,a duniya bashi da burin da ya wuce yaga farincikin 'yan uwansa
"Aiba wani lokaci za'a diba ba mallam,zaka tsaya tarin kudin aure kenan?,wannan yammatan yadda kuka mato akan juna banajin zata iya jiranka" kunya tadan kama hamidou amma kuma yana mamakin yadda za'a hada komai a qaramin lokaci,duk da abban yace baya buqatar komai daga wajensu face sadaki,amma ko bazai yadda ya auri hamdiyya baiyi komai cikin hidimar aurenta ba,ko yaya ne zaiyi daidai iya abinda Allah ya hore masa,a qalla dai da babu gwara ba dadi.
"Zakayi lefe kaman yadda kowanne namiji yakeyi in sha Allah,za kuma ka biya sadaki" abinda mohmoud ya fada kenan yana miqewa zai wuce wajen aiki.
Tunda yaji mohmoud ya fadi hakan yasan zai matsawa kansa ne,kuma sai yayi dukka abinda ya fada din,wannan ya sanya a sace shima ya soma 'yan buga bugarsa,abun kamar wani yayewar lullubi sai yayita samun ayyuka,abun ya dinga bashi mamaki,saidai yayi shuru bai gayawa bibi ko hamma mohmoud ba,saboda yasan yanzun zai hanashi yace karatu kawai zaiyi,shi dinne zaiyi komai. Cikin wata guda kacal ya samu 'yan kudadensa a hannu masu dan kauri,yanata mamakin yadda daga fara buga bugarsa qofofi suka dinga bude masa,aka dinga kiransa ayyuka daban daban da kuma kudi masu gwabi. Da yake su din damuwar danuwansu shine tasu,akwai asusu da yake yiwa oumar na jarabawar da zasuyi,wanda ya kallafawa kansa shine zai biya wannan karon hamma mohmoud ya huta shima,asusun ya bude,ga mamakinsa ya tara kudi ashe ba laifi ba kamar yadda yake tunanin bai wani tara abun arziqi ba,ya ware kudin jarrabawar oumar y dauki sauran ya hada da kudin hannunsa ya aje yana jiran dawowar hamma oumar.
A falo suke hira yana cin abinci,a kaikaicw hamidou ke kallon hamma mohmoud din saboda yadda gaba daya shekarunsa suka ninka akan nasa saboda da wahala da neman na abinci,har ya kammala mohmoud din ya kalleshi
"Ya kaketa kallo na ne kaman kaga hamdiyya?" Dariya dukka sukayi sai ya soma sude miyar hannunsa yana cewa
"Ka kwantar da hankalinka,lefenka ya gama haduwa,amma saidai su karba da haquri,akwati biyu ne" baki hamidou ya bude yana kallonsa,yayi imani ba wani lefe,lefensa ne da ya kusa shekara yana hadawa zai sadaukar masa,sai ya girgiza kai
"Aah hamma,ni bazan karba lefenka ba saboda na tabbatar shine,ni ina da kudadena da na tara"
"Kajimin yaro,yo kudadenka daka tara ai bance ba za'a karba ba,a ciki za'a fidda sadaki ka samu na dinkunan biki da dan abinda zaka bawa amarya ko bibi?" Ya fada yana maida dubansa ga bibi wadda ta kasa magana,wani irin abu me nauyi dake sauka zuciyar uwa akan danta ya tsaya mata iya wuyanta,zata iya cewa bata taba ganin mutum me tausayi da rahama ba irin mohmoud dinta,wanda ke maida matsalar wani tasa
"Haka ne,amma mohmoud kaine kafi cancanta da kakai lefen nan,ko ba komai kaine babba" murmushi yayi kawai yana nade hannun rigarshi
"Karki damu bibi,muddin kina mini addu'a tabbas zan hada wasu a kurkusa in sha Allah" daga bibi har hamidou ba wanda baiyi qwalla ba
"Yanzu gidan da zaka zauna nake qoqarin sama maka a biya haya kota shekara daya ce" mohmoud ya sake fada
"Wa?,ni?,ba inda zanje, gidanmu akwai wadatar sassa da babu kowa a ciki,a ciki zata zauna hamma ba inda zani na barku" hamidou ya fada da sauri.
Abinda suka kai sam hamdiyya ko mahaifanta basu raina ba,hakazalika ita da kanta ta qarfafi ta zauna dasu bibi din. Sashe daya cikin biyun dake cikin gidan aka bude aka yiwa dan kwaskwarima. Da yake gini ne dama asalam na masu kudin,rayuwace dai kawai data samesu sai wajen yayi kyau ya kuma dace da zaman rayuwarsu da tsarin kayan alatun da ake burin zubawa hamdiyya.
Sanda labarin aurensu ya fantsama dukka makaranta sai ta dauki dumi,saboda ba kowa keda masaniyar soyayyar dake tsakaninsu,don daga hamidou har hamdiyya kamammu ne,sun kame kansu sosai,basa wani abun da zai nuna ma akwai soyyaya tsakanin. Mazan da hamidou ya kasa suna da tarin yawa, cikin makaranta cikin nijer dama nigeria,sun kuma cizi yatsa ainun da ganin wanda hamdiyyan ta zaba ya kuma kasasu.
Biki akayi na hanakali, ba'a barnatar da dukiya ba,saidai duk abinda mohmoud ya tara saboda nashi auren ya narkar dashi gurin auren qaninsa hamidou,ya sadaukar da komai nasa ga hamidou din,ba abinda ya ragewa kansa,ya kuma tsaya ya zame masa makwafin uba mahaifi,duk abinda uba zaiyi shi yayi masa,hasalima shine alwalinsa,shi ya karba masa auren hamdiyya. Anyi biki lafiya an watse lafiya amarya kuma ta tare a dakinta.
To zamansun zama ne me dadi matuqa,duk yadda bibi da farko ta dinga dari dari da tsoron halin yaran masu wadata hamdiyya ta goge mata wannan,babu raini ko ganin ta fisu,ta sake sosai tamkar itama bibi dince mahaifiyarta. Biyayya takewa.bibi kaman yadda takewa hamidou, bashar oumar da auta dukkansu ta maidasu kaman jininta ne,ta zama dai 'yar gida sosai,ba zaka taba cewa surukar bibi bace.
Karatunta taci gaba dayi hankali kwance,don tare suke fita da hamidou a motarta da tuni ta mallaka masa ita,saidai yaqi sakin jiki ya karba din,har zuwa sanda ya gama nasa karatun ya zama ita ta rage amma shike kaita ya kuma koma ya dauko matarsa.
Duk wasu shares da dukiya ta hamdiyya mahaifinta ya tattaro ya damqa amanarwa hamidou saboda yadda da yayi da tarbiyyarsa. Bai boye komai ba yace ga amana nan. Qememe hamidou yaqi amsa,yace zaidai aje mata takardu da kayayyakinta. Wannan qin amsar shine karon farko da suka fara samun sabani shida hamdiyya,ta dinga fushi tana cewa ya qullaci wani abune akwai a ransa game da ita ko kuma bai aminta da ita da kuma soyyayar da take masa ba dari bisa dari, Sharia har gaban hamma mohmoud da bibi,suka rasa me zasu yanke saboda su kansu ba zasuso ya cusa kansa cikin dukiyar ta ba,ko a yanzun jigila da kuma hidima take masa da kudinta da jikinta,itace cefane itace siye siyen kayan more rayuwa cikin gidan,hakanan komai ta gani ya burgeta saita siya masa. Ba shiri ya dakatar da abun
"Munyi alqawarin zaki aureni ki zauna dani daidai qarfina,bamuyi dake zakina mun hidima ba" nan ma dai haushi taji,tilas amma ta rage wasu abubuwan saboda cika umarninsa. Wannan dalili ne ya sanyashi fara neman aiki ka'in da na'in. Allah kuma cikin hikimarsa sai gashi ya jefo masa da aiki da matsakaicin albashin da yasan zai iya riqeshi da yardar Allah.
Wani lokaci abba ya kawo musu ziyara,ya kuma samu hamidou ya soma aikin nasa. Sam aikin shi bai masa ba,saboda salary din da suke basun baifi albashin qaramin ma'aikaci a kamfanin hamdiyya ba. Wannan karon da kansa ya sake neman arziqin hamidou ya dawo aiki kamfanin hamdiyya kaman hakan zaifi dacewa,ya jima yana juya abin,ya kuma gayawa bibi tace ya nema zabin Allah,sannan uwa uba mutumin surukin arziqi ne,bai kamaci ace yanata neman alfarma kala kala daga garesu suna sullubewa ba,wannan shine silar da ya fara jagorantar dukiyar hamdiyya,saidai komai yana yine cikin takatsantsan da kiyayewa,albashinsa kuma ya yankewa kansa kamar na kowa,daga gefe guda kuma ya fara saving duk wani halalinsa da yake samu silar aikin da tunanin fara shima gina kansa,saboda bazaiyiwu ace zai dawwama yana qarqashin dukiyar matarsa ba. Duk da cewa wannan abun ba abinda ya qara face soyayya me qarfi da qarin girmamawa daga wajen hamdiyyan,iya tarbiyya ta sameta,sam batasan wulaqanta dan adam ba.
Rayuwa ta fara daidaita gidan marigayi mayak'i silar wanzuwar hamdiyya a cikinsu. Abu daya ne a yanzun ya fara musu cikas shine rashin samun haihuwa shekara ta biyu da aurensu. Tun bata damu ba duk da maitar son yara da Allah ya zuba mata,to amma saboda lokacin tana cikin kai kawon karatunta har hankalinta ya fara dawowa jikinta saboda a sannan karatu ya kammala sai business dinta da takeson kamawa.
Sannu a hankali ta fara tadawa hamidou hankali,har takai anje an gwadasu,an kuma tabbatar musu mahaifar hamdiyya ce take da dan rauni. Hankalinta yayi mugun tashi duk da yadda hamidou ya nuna shi hakan ba matsala bacea wajensa,ya dinga qoqarin kwatanta mata da kwantar mata da hankali amma ta birkice masa,sun dauki watanni a haka kafin ta dan sanyawa zuciyarta salama,sai kuma zancan auren mohmoud ya taso Gadan gadan.
Haka kawai shaidan ya sanyata ta dinga jin babu dadi cikin ranta,saita dinga tsarguwa kaman za'a qaro wata surukuwar ne cikin gidan don itadin bata haihu ba. Wannan dalilin ya sanya har akayi bikin aka qare aka kawo amaryar hamma mohmoud daya sashen a tsarge take,wannan ya sanya tayi bala'in kamewa daga shiga shirgin matar hamma mohmoud.
Bintou baiwar Allah,gwanar haquri da kawaici,kyakkyawar bafulatanar katsina,wadda tasha gwagwarmayar mayar rayuwa da wahalar riqo hannun kishiyar uwar da aka fita aka bar mata. Girmama hamdiyya takeyi duk da itace matar yaya,amma tana kallon cewa ta rigata shigowa gidan,bata da hayaniya bata da magana,shuru shuru da ita kullum. Yanayin rayuwar da bibi tasan tayi ya sanyata take yawan jan bintou jikinta don ta samu ta ware ta kuma dinga jinta mutum kamar kowa. Akwai banbancin rayuwa sosai tsakaninta da hamdiyya data taso cikin gata da soyayyar dangi gaba daya. Wannan abun sai ya dinga yiwa hamdiyya ciwo kadan kadan,duk da bata taba nunawa ba amma tana jin babu dadi a ranta,tanajin kamar Bibi nason wareta ne da nuna mata banbanci don bata haihu ba,wannan yayi mata tasirin data soma janye jiki daga al'amura da yawa na gidan,ta zama 'yar ba ruwana,dabi'ar miskilancintanan ya motsa,sai ayi abu cikin gidan ma bata sani ba,inda zakaji motsinta kawai ayi baqi yara ko ayi baqi da yara a cikinsu yanzunnan zakaga yadda zata sake jiki tayita hidimawa yaran,musamman idan akwai baby girls a ciki. Tanason 'yar yarinya mace sosai,takancewa hamidou tafison ta haifi mace akan namiji.
Tun bibi na qoqarin fahimtarta da son fahimtar meye ya sanyata sauyawa ta nuna babu komai,har bibi ta haqura ta barta da sabon halinta,tundai ba fada takeyi da kowa ba cikin gidan,tana kuma ci gana da girmama kowa kamar yadda takeyi a baya.
Ba jimawa kwatsam ciki ya bayyana jikin bintou,yadda gidan ya rude da murna kuma kowa hankalinsa ya koma kan cikin sai ya soki zuciyar hamdiyya sosai(kusan duk macen dake neman haihuwa bata samu ba tana da shigen wannan ciwon a ranta,ko hirar haihuwa akeyi saita tsargu taga kaman da ita ake bare ace wance ai ciki ne da ita,ba wanda zai fahimci hakan sai wanda ya taba tsintar kansa a irin situation din),wannan ya sanya ta sake kame kanta da zama a sassanta ita kadai. Sai taji bata sha'awar ta rabi kowa ko wani ya rabeta,to Allah baisa cikin yana da dogon zango bama bintou tayi barinsa. Sai kuma a sannan hamdiyya ta dinga jin ba dadi,ta kuma dinga tausayin bintou, hankalinta kuma yayi mummunan tashi sanda bintou ta dinga ciwe ciwe, daga bisani gwaji ya bada cikakken bayanin bintou sicklier ce.
*_KWANKWASON JIMINA_*
*_TSUTSAR NAMA_*
*_AMEENATOU_*
*_GUDUN KADDARA_*
_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*
LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200
_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_
6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank
_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_
09166221261
*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*
09134848107
*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*
09033181070
*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
BOOK 02 PAGE 07
Ta tsorata ainun hamdiyya a sannan,don mutum uku cikin familyn ummanta da taga yadda sukaci wuya da ciwon sicklier daga bisani kuma dukkansu suka rasu,wannan yayi sanadiyyar da tayi matuqar tsanar ciwon sicklier. Hatta da hamidou duk son da take masan sai da sukayi gwaji kafin aure.
Cikin hikima ta ubangiji a sannan din ashe tana maqale da cikin ALIYYU MAINA,wanda kwata kwata sam ko da alama bata sani ba bare kuma hamidou(aba). Bata tashi sanin da ciki a jikinta ba sai da yayi watanni hudu ya fara harbawa a mararta,ta tsorata dajin hakan ba shiri suka wuce asibiti. Bibi bata hanasu ba illa dariya da take musu qasan ranta, tasan yadda sukaje haka zasu dawo da borin kunyarsu.
Ilai kuwa sai gasu din,sun dawo mata shabe shabe da kukan murna da kuma kunya. Fadin yadda hamdiyya ke lele da qaunar cikin aliyyu ma kai tsaye za'a iya cewa bata baki ne, ba'a taba jarabtarta da wani abu da takeso sama da cikin ba baya ga mahaifin yaron. Motsi kadan kuma bini bini suna hanyar asibitin wai check-up a duba lafiyar yaronta,tun bibi na zuba musu idanu har ta gaji da gani ta tsawatar musu,sai suka koma fakar idanunta suna zuwa,sai kawai ta tarkatasu ta watsar.
Shirin haihuwa sukayi na garari,da ba'a qasar taso haihuwa bama amma ganin yadda bibi da bintou ke da kwadayin ganin yaron ya sanya ta haqura. Cikin aminci ta haifi aliyyu maina,sambalelen yaro da ya gaji kyau ta fannin uwa da uba da 'yan uwan uba dinma duka. Tun asali da farinjininsa maina yazo,uwa naso uba naso qannen uba naso,hamma mohmoud kuwa ba'a ma maganarsa,don yadda yakejin haidar din har cikin jininsa,yadda yake qaunarsa da qulafucinsa har yaso ma yafi mahaifinsa. Sannu sannu tun haidar na jaririnsa sai zamansa yaso yafi qarfin hannun hamdiyya,duk da mahaukacin son da take masa. Yadda sukeson janye haidar din sai yadan fara tabata,ganin kamar ganin yaron yanaso yafi qarfinta,shayarwa ce kawai ke dawo dashi wajenta.
Cikin ikon Allah watan haidar shida uku kacal Allah ya albarkaci bintou da wani cikin,tayi murna qwarai ita da hamma mohmoud sosai. Haidar maina nada shekara guda kacal bintou ta sambalo tata yarinyar da taci sunan NAFESSA.
Da nafessa da haidar kusan duka rainon bintou suka koma,saboda tun haidar nada watanni hudun yasan idan yana kuka aka ajjiye baby nafessa a gabansa watsal watsal dinta ya dauke masa hankali ya tsaida kukan da yakeyi. Sanda ya cika shekara ta biyu kuwa yasan ya kama hanya tiryan tiryan zuwa sassansu nafessa,duk kuwa da dan banzan qyuya da yake da ita. Ya kama sunan hamma mohmoud da suke kira da pappa da kuma sunan NAFESSA daram a bakinsa fiye da sunan kowa.
Wasa wasa wata irin mahaukaciyar shaquwa ce ta shiga tsakaninsu ta yadda bacci ne kadai ke rabasu,saidai idan sunyi baccin a dauke nafessa shima a daukeshi a maida sassansu.
Alaqar dake tsakaninsa da nafessa din ta nesanta shi da ama din,tun bai isa yaye ba,tun kuma bata saba ba har ta saba. Kusan duk yininsa yana wajen bintou ne,idan kima nafessa na sashen bibi shima yana can acan zasu wuni sur saidai ya leqota. Kishin hakanne ya fara kamata ganin sannu sannu yana barin sassanta da kuma raguwar shaquwar dake tsakaninsu duk da irin qulafucinta da yakeyi. Gashi daga itan har bintou daga kan yaran ba wadda ta sake samun wani cikin,gwara bintou dama an shawarcesu da daukan dogon hutu kafin ta sake samun wani cikin saboda yanayin lalurarta, hakanan ta sha wuya sosai wajen haihuwar nafessa,nisan kwana kadai ya kawota yau. Duk yadda zata ja maina a jiki abun ya faskara,ta kuma lura ita bibi hakan yana mata dadi qwarai,tana yawaita fadin Allah ya qara hada mata kansu shi da nafessa din.
Nafessa na da shekara hudu maina nada shekara biyar alamun ciwukan sicklier suka fara bayyana a jikinta,yau ciwo gobe lafiya,qwarai bintou taso aje ayi mata gwaji amma tsoron kada ya tabbata nafessa nada sicklier hamma mohmoud ya qiya,amma dole da gumu tayi gumu ya bari akaje aka