Showing 51001 words to 54000 words out of 294767 words

Chapter 18 - Gudun Kaddara Book 2 Hausa Novel Complete

miskilar qarfi da yaji da tayi ne duk ta koma haka,bata doguwar magana bare doguwar hira,dukka kalmominta taqaitatattu ne

"Baki shirya ba sultana,ya kamata muje mu dawo da wuri mu kwanta don mu samu gobe mu tashi da wuri,jirgi baya jira" ama ta fadi tana taje doguwar sumarta

"Ama na gaji,saikun dawo" waiwayawa tayi ta dubeta

"Ahaaa?......kina da tabbacin sake samun dama irin haka?,baki da tabbas zaki sake ratsa qasarnan,oya tashi ki shirya" ta fadi tana dan dakewa. Tsam sultana din ta tashi,ama ta bita da kallo har ta shige bandaki.

Sanda ta fito cikin ido sai ama taga tayi mata kyau ainun. Cikin doguwar rigar Dubai,tayi rolling kaman yadda ta saba shekarun baya. Ta cika tayi tsaf tamkar babu wani abu dake damunta.

Yawo sukayi sosai gidajen tarihin dake cairo,sannu a hankali sai ta dinga jin zuciyarta na sakewa,damuwarta dake cunkushe a qirjinta tana raguwa sosai. Saidai duk inda duka gifta sai an tanka benazeer da batoul,abinda ya sanya dole ama ta sake lullubesu da kyau.

Koda suka shiga daya bangaren na kayan tarihi sai ama ta miqawa sultana batoul. Waiwayawa tayi ta dubi ama din,sai kuma ta sanya hannunta ta karbi yarinyar ta rungumeta a kafada. Ajiyar zuciya ta saki a boye,wani abu taji ya zarta ta jininta sanda dumin jikin yarinyar dake cakude da daddadan qamshin turaren Dior ya sauka a hancinta. Sau tari cikin zuciyarta takanji yaran suna burgeta,irin burgewa da kake iyaji ga yaran da suke ba naka ba ko kake ganinsu daga nesa. Tun daga ranar da suka iso duniya cikin ado suke da kwalliya,koda a gida suke babu inda zasu fita to tabbas adonsu na dabanne,hatta kayan bacci idan ka gansu a cikinsu saisun dauki hankalinka.

A asirce tanja ta saki murmushi tana kauda kai,wato dai so sone amma son kai yafi. Tuni ta lura da abinda ya sanya ama ta maqalawa sultana batoul,idanuwa ne sukayi yawa akan sultanar,duk da cewa ba wani sakewa a tattare da yanayinta ko fuskarta,amma ta fuskanci tana ta fusgar hankulan mazaje dake wajen.

Duk inda ama taga wulgawar kayan yara saita saiwa su benazeer,kayan qyale qyale masu yawa,su kadai take tunawa,komai ta siya nasu ne.

Sai cikin dare suka koma gida a gajiye,duk da haka ama bata gaji ba sai sata wanke yaran tsaf,nan suka shiga baccin gajiya.


**********K'arfe daya na rana dai dai motar mallakin hajiya hamdiyya abdu me kano ke shiga makekiyar harabar gidanta dake garin abuja. Dukkansu ita da sultanan ba wanda bai saukar da boyayyar ajiyar zuciya ba.

Kafatanin masu aikinta maza da mata dukkansu suna tsaitsaye a harabar gidan domin yi mata barka da isowa. Sanda motar ta tsaya bakin motar sukayo,kowanne zuciyarsa fal farinciki da annashuwa,tsoro da fargabar data mamayesu na bacewarta tsahon watanni tuni suka bar zukatansu daga jiya data shaida musu isowarta,tare da isowar ma'aikata sukayi musayen furniture na gidan,suka kuma shirya lafiyayyen daki wa benazeer da batoul.

Bilki ce ta karbi batoul,uwa ta karbi benazeer kowa bakinsa fadi yake

"Masha Allahu,ma sha Allah,barka da arziqi sultana" a lokacin da sultanan ke fitowa daga motar cikin wata baqar doguwar riga me azabar sulbi da daukan idanu. Fatarta da jikinta dukka sunyi kyau,ta dan murje,saidai qiba ce har yanzu babu ita ba dalilinta,ta zama slimy.

A hankali idanun ama suka sauka kan baqin motoci da take gani a rumfar gidan,sai ta maida dubanta ga tasi'u

"Malam Tasiu wadannan motocin fa?" A ladabce ya rusuna yana cewa

"Yallabai ne suka zo shi da hajja bibi,yau kinsan ake bikin bude kamfaninsa na nan abuja" kai kawai ta gyada,ta san da company din,wanda ya dauki shekara da shekaru yana gininsa tare da tanadin ranar budesa,tabbatuwar kamfanin kuma zai iya sanyawa zamansu yafi yawa a Nigeria ne garin abuja saboda yawan hada hadar da a kullum aba din zai dinga gudanarwa.

Ciki dukkansu suka dunguma,tana jinsu bilki sun barke da hira da tanja hirar yaushe gamo?,sunata kwasar tanjar wai ta sauya quruciyarta ta dawo,itakam sai dariya kawai take musu.

Dukkan wani abu da zaiyi cikin watannin da sultana da ama sukayi baton dabo yana yinsu ne tuquru don wanke duk wani ciwo da radadi na batan sultana a zuciyar bibi. Ko a yanzun da duke dawowa su biyu rak cikin motar bayan ya karbi tuqin daga hannun driver dinsa ajiyar zuciya ta saki

"Har yanzu hamidou zuciyata ta kasa nutsuwa,har yanzu ina ganin cewa nice silar faruwar komai,inda nasan sultana na buqatar cikin,inda nasan da gaske hamdiyya take tana da buqatarsa itama,da na ajjiye nufi na,ba hamdiyya ba sultana..... shima maina tunda ya tafi....."

"Ki ajjiye batun maina,ba mune mukayi masa laifi ba,shi yayi mana laifi,sannan ya zabi tafiya ya barmu,koda kasheta yayi a yanayin da ya barta bashi da asara" ya furta maganar yana ciro wayarsa da yaji alamun kira ya shigo. Baikai ga daga wayar ba kiran ya katse,sai text din hamdiyya da ya shigo kusan awanni biyu baya,rububin taro ya sanya bai gani ba sai yanzun da ya samu ya sullubewa jama'a yayi bad da bami a mota daya ya taho gida kawo bibi ta hut sannan ya koma.

Hannunsa har rawa yake sanda ya karanta layi guda kacal na saqon,ita dai bibi batasan me yake faruwa ba,taga dai ya qarawa motar uban gudu bayan ya aje wayar da hanzari a gefensa

"Lafiya hamidou?" Bibi ta tambayeshi tana dubansa

"Hamdiyya ce ta dawo,ina kyautata zaton suna nan cikin abuja" ya bata amsa yana sake bakwa kwalta hankalinsa sosai. Idanu bibi ta fidda cikin wani mugun zumudi da ba zata

"Hamdiyya?,ita da sultanan?"

"Eh na tabbatar tare suke" ya amsa mata yana sake qara tsula gudu abinda sam ba al'adarsa ba

"Allahu qadiran Ala man yasha'u" bibin ta furta hankalinta yana daguwa,jinta takeyi kamar tayi tsuntsuwa ta isa gidan,sai kawai tayi luf jikin kujera tana kiran sunayen Allah a jejjere.


*_KWANKWASON JIMINA_*

*_TSUTSAR NAMA_*

*_AMEENATOU_*

*_GUDUN KADDARA_*

_DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_*

LITTAFI DAYA_400
BIYU_800
UKU_900
HUDU_1200

_IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_

6019473875
Musaa Abdullahi safiya
Keystone bank

_ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_

09166221261


*Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba*

09134848107

*Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin*

09033181070


*ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

BOOK 02 PAGE 27



"a hankali bibi" aba ya fada lokacin da yake tsaida motar tasa bibi na qoqarin budewa ta sauka. Ai bata saurareshi ba sai data tabbatar qafafunta sun taka qasa. Da sauri ya fita a motar yabi bayanta,yasan tana da ciwon qafafu,a yadda kuma take gaggawar kaiwa ga sultana yana gudun kada ta sarqe.

Dukka muryarta ta ware tana doka sallama kamar baquwar gidan,ta daburce gaba daya,saboda batasan ta inda zata fara ganin sultana ba.

Tana shirin shiga wanka taji kamar muryar bibinta,kamar muryar da kullum take mafarkin ji,sai kawai ta jawo babban mayafi ta yafa a kanta tana nufar qofar fita.

Qarar bude qofar ya sanya bibi maida kallonta gurin,sultanarta ce,itama sultanan bibin take kallo,kallo kallon suka hau yiwa juna kamar wasu baqin juna,sai kuma daga bisani sultana din ta nufo bibi cikin sassarfa tana kiran sunanta da rawar murya.

Jikin bibi ta fada bibi din ta maida hannayenta ta rufeta gam

"Sultana?" Itama bibin ta dinga maimaitawa tana jin wani irin abu cikin zuciyarta,abinda ya karyar da zuciyartata kenan hawaye masu sanyi suka saukar mata.

"Bibi" itama ta sake maimaitawa kowannensu hawaye yana fita a idanunsa. Da kyau bibi ta riqeta suka qarasa saman kujera,sai kawai sultana din ta kifa kanta saman kafadarta tana sakin sabon kukan.

Ya zata iya kwatantawa bibi abubuwan data fuskanta?,baki bazai iya bayyanawa ba, gwagwarmayar data ratsa har ta kawo yau din ita kadai tasan abinda taji,ba mahalukin da zai iya fuskantarta,wannan din wani abune da yake tsakanin zuciya ruhi da kuma gangar jiki ne kawai.

Kasa cewa komai da ita bibi tayi,sai sharar hawayen itama da takeyi aba yana tsaye a kansu yana basu baki,saidai fiye da rabin hankalinsa shima yana tsakanin falon da kuma qofofin da falon ke dauke dashi,yana son ganin ta inda ama zata bullo.

Dukkaninsu taga shigowarsu ta cctv camera din dake hade da system din gefan gadonta,amma bata motsa ba,sai data kammala shirya yaran tsaf bayan ta musu wanka,ta nadesu cikin overall set da wasu irin huluna masu kyau da suka boye tattausan sumarsu me azabar baqi da sulbi,fuskokinsu sun fita tarwai da wani irin haiba da annuri.

Nannadesu tayi cikin tausasan shawl sannna ta sanyasu a kafadarta hagu da dama,ta zura slippers dinta ta taka zuwa hanyar fita.

Duk da cewa takunta baya bada wani sauti amma sai fitowarta din taja hankalin bibi da aba tamkar wadanda aka jonawa mayen qarfe. Kasa miqewa bibi tayi,daga ita har aba bin ama sukayi da kallo har zuwa sanda ta qaraso ainihin cikin falon da sallama a bakinta.

Wuce aba tayi kaman ma bata ganshi ba,ta isa gaban bibi a nutse ta sauke yaran daga kafadarta tana kwantar dasu a gaban ama tana jeresu daya kusa da dayar,sannan ta miqa hannunta tana yaye shawls din da suka lullube fuskokinsu.

Dukkaninsu suka kai idanunsu kan yaran,tamkar an jona musu shock haka sukaji cikin jikinsu

"Subhanallahi wabi hamdihi, subhanallahil azeem" bakin aba ya furta yana tasowa da gaggawa daga tsaiwar da yayi daga jikin bango.

Gaban yaran ya qaraso ya zube,yasa hannu ya tallafawa bibi da hannuwanta ke rawa tana son karbar yaran,ya dauki benazeer ya dora mata ita saman cinyarta.

"Ya Allahu,ya assamadu" shine abinda take maimaitawa tana juya yaran qwalla na sauko mata

"Astagfirullah, astagfirullah....." Ta sake maimaitawa tana jin qirjinta na mata nauyi,har cikin jini da zuciyarta takejin wani irin nauyin ubangiji,har ruhinta takejin wata irin kunya tana saukar mata,yanzu wadannan halittun da taso a murqushe?, yanzu wadannan ruhin taso a niqeshi yabi rariya?.

"Allah na tuba,Allah ka yafemin,Allah kada ka barmu da soye soyen zukatanmu" ta dinga maimaitawa hawayenta yana qara yawa

Hannu ta miqa tana shafa fuskokin yaran,idanuwanta a kansu tana sake tsarkake girman zatin Allah.

"Ga jikokinku nan,kuma 'ya'yan jikoki,wadanda kukaso gushewar rayuwarsu kafin isowarsu duniya,nayi dukkan abinda nakega ya dace nayi,ga sultana nan na dawo muku da ita,yaran kuma zan riqesu,Allah ya rayaminsu" ama ta fadi hawaye yana cika idanunta taf ta sanya tafin hannunta tana sharewa

"Inaaa hamdiyya,kece kika cancanci mu bawa haquri,kece kika cancanci wannan yabon,abinda ya kamata tunaninmu yakai kai ya gaza kaiwa kece naki tunanin yakai,kika fiddamu daga halaka zuwa hanyar tsira,inda ace na aikata abinda son zuciyata ya gayamin a sannan tabbas da zuwa yanzu ina cikin fushin Allah,ku yafemin 'ya'yannan da naso kasheku tun baku shaqi iskar duniya ba" bibi ta fadi tana sake kuka.

Iya yadda bibi ta rame kadai ya isa ya gayama ama ba qaramin tashin hankali take ciki akan tafiyarsu ba. Cikin zuciyarta wani abu ya darsu me kama da tausayin bibi cikin ranta

"Zo nan hamdiyya,yaki" Bibi ta furta tana miqawa ama hannu. A nutse ta qarasa gaban bibin,ta tsugunna,har a yanzun tana jinta a matsayin suruka,kuma har yanzu babu abinda ya sauya. Ta sani dukkan wata zuciya cike take da son rai,saidai idan Allah ya baka ikon fin qarfin zuciyar taka.

"Allah yayi miki albarka,kiyi afuwa a gareni" bibi ta fadi tana dafa hannuwan ama. Qas tayi da kanta tana jin nauyin bibi din

"Ya wuce bibi,ya wuce har abada"

"Na gode hamdiyya" ta sake fadi tana sake duban fuskar yaran daya bayan daya,tare da tunanin da waye sukayi kama

"Wanne suna kika basu?" Bibi tayi tambayar sanda ama ke tashi ta zauna sosai saman kujera kamar yadda bibi ta buqata a tare da ita

"Nadeeya BENAZEER da Fatima BATOUL" a nutse aba ya daga kai ya dubeta karo na biyu yana jin kimarta na daduwa cikin ransa,yayi tsammanin zatayi zuciya ne,ta saka sunanta da kuma sunan duk wanda taga dama,sai gashi ta watsa komai a baya,ta sanya musu sunayen mutanen da suka kasance tsani na samuwarsu.

A hankali aba yakai bakinsa kunnen kowaccensu yayi mata addu'a,ya sauke batoul a nutse saman cinyar ama sanda ta fara mutsu mutsu yana miqewa idanunsa suna satar kallon ama. Ya sani akwai zantuka da yawa wadanda a yanzun ba zasu fadu ba,ba kuma zasu yiwu a tattauna ba,zai jira lokacin da ya dace.

Ta sani abinci suke da buqata a yanzun,don tunda suka taho daga Egypt bacci sukeyi abinsu basu buqaci madara ba,sai ama ta juya tana kallon tanja data rabe tana jin nauyi nauyin ama

"A sama musu ruwan zafi zan hada musu madara" dubanta bibi tayi

"Madara kaman yaya hamdiyya?,ko zasusha madara nono ai ya kamata a fara basu ko tukunna,idan basu qoshi ba saisu qara da madarar"

Ama bata dubi bibi ba tace

"Madarar sukesha,itace abincinsu" ta maidawa bibi amsa tana gyarawa benazeer kwanciya.

"Ina nonon uwarsu?" Maganar ta zowa sultana a bazata saboda ta tsammaci bibi zata bar maganar ne,sai gashi kuma ya jefo da wata tambayar.

Waiwayawa bibin tayi tana duban sultana,a hankali sultana din ta jawo gaban mayafin jikinta tana sake suturce qirjinta da bibi ke kalla

"Hamdiyya kada dai kicemin hanasu nono tayi" bibin ta fada da wani irin zafi a muryarta abun yana tabata. Kai ama ta girgiza

"A'ah,kawai dai bata taba gwadawa bane"

"To yau kuwa zata gwada yau dinnan" bibi ta furta da gaske tana zunkudawa gaba.

Dukka idanunta sultana ta fidda waje tana zarosu,nonon nata za'a zuqa kuma?,tashin hankali.

"Aje a nemo min wannan maganin duk inda yake a garin abuja,a fiddo da dukka bournvita din dake gidan nan da madara,daga yau zuwa safiya nakeso ruwan nono yazo yara su kama abinsu" sosai sultana ta sake gwalalo ido gabanta yana faduwa

"Da kin bari bibi,tunda sun riga sun saba da wannan ai..... Bakiga kuma yadda ya karbesu ba?" Ama fada tana tana fuskar bintou

"Kinga hamdiyya ki daina bata bakinki,darajar nonon uwa daban da madarar bature,kinsan Allah?, billahillazi daga yau su da madara saidai a matsayin ciko" kuka sultana ta saki tsoro yana kamata,yanzun ace nononta zasu tsotsa?, fisabilillahi har mutum biyu?,ta ina?.

"Don Allah bibi kiyi haquri"

"Yo ai bansan baki da imani ba,haba sultana,kece za'a ce kiyi haquri dai,don nono kaman sun shashi sun gama" idanu sultanan ta wuwwulga a falon,ba wani sauran me cetonta,aba ne ya rage dama,shi kuma tunda aka fara batun shayarwar ya fice.

Duk irin kukan da sultana keyi saboda tsananin tsoron shayarwar bai damu bibi ba,nan ta gwaggwafe hada wannan tsuma wancan,zuwa safiya sai ga nono yazo.

Bibi da kanta ta taka ta amso benazeer da batoul daga wajen ama,wadda tuni tayi musu wanka ta shiryasu tsaf sunata tashin qamshi sai tsotsar baki suke,da alama dama a yunwace suke. Qin bin bibi ama tayi kada tausayin sultana ya mata tasiri ta hana abinda ita kanta tasan shine dai dai,abinda ya sanya bata taba tilastata ta basu din ba alqawarin hakan ta yiwa kanta,kuma bata fatan hakan ya haifar mata da wani raunin cikin zuciya,ko taga kaman aman tana biyewa soye soyen zuciyarta ne tunda ita din bataso,biyayya kawai takeyi.*_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

Book 02 page 28


Idanunta fal ruwan hawaye take kallon bibi sanda ta fara aza mata benazeer akan cinya

"Don Allah bibi,wallahi zafi zanji na sani,bazan iya basu ba"

"Zaki koya ne,kowa ma ai da haka yake koya" bibin ta fadi tana hade rai babu alamun wasa saman fuskarta

"Yalla, fito dashi ki basu ko nazo da kaina na basu,an baki shine don kiyi ado dashi a qirjinki dama?,fito dashi" bibin ta fada cikin fada da tsawa. Hannu ta saka tanason cirosu,amma rashin sabo ma ya sanya ta kasa yadda zata fiddosu din

"Bari dai kiga" bibi tace tana motsawa kusa da ita. Kuka ta saki sanda benazeer ta cafki maman ta fara tsotso kaman dama ta saba. Idanun yarinyar qur kan fuskar sultana kaman tasan ba da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login