Showing 27001 words to 30000 words out of 304445 words
sonshi yana son yan uwansa ko sauran na gidan auren indai zai shigo zata tambaye ta babu abinda suke bukata musamman matan auren. A hankali Ilham din ta fara ci tana jin kewar Mai Martaba, a hankali ta fara kuka. "Ya Faris ina kewar Abbanmu." Duk sai ta basu tausayi, domin ita ce karama kuma mahaifiyarta tana tare da mai martaba ɗin.." ya isa idan kina son zuwa sai ki shirya Faruq zai zo ya miki kome sai Mai Bauchi ya kai ki." "Da gaske!" Gyada mata kai yayi yana murmushi, kafin ya ajiye mata ruwa ya ce mata. "And ina son na ja hankalinki akan abinda ya faru." Ya fada yana nazarta yadda take cikin abincin a nutse. Wannan shine tarbiyyar rayuwar gidansu, hatta cin abinci an nuna musu yadda zasu ci, tauna abincin ma a ladabce take ci. "Bayin nan ba bayi ba ne har abada, ki dauki kanki idan kace a matsayinsu." Da sauri ta d'ago kai jinjina mata kai yayi yana murmushi. "Idan kece a matsayin Iyami zaki ji dadi jikarki ta miki haka? An haife ni a gaban Iyaami, ita kanta Mai Babbar daki tazo gidan nan ta samu Iyami,she is my Nanny naji babu dad'i da kika musu haka." Kallonta yayi kafin ya dauko goran ruwan ya kara zuba mata a cup din. "Duk da kasancewarsu haka, Allah yana sonsu yana kaunarsu. sai su fimu kusanci da Allah mu bamu da ita. Sai ki ga sun shiga aljanna ba tare da wani dogon hisabi ba. Mu an samu matsala a namu sakamakon. Idan da manya a wuri ba a hukunta su har haka. Su manya ake gayawa abinda ya faru. Da kin gayawa Mai Babbar daki da haka bai faru ba, kada ki sake jin ji." A hankali take kuka hadiye lomar bakinta tayi sannan ta ce mishi. "Ba zan kara ba in sha Allah!" Murmushi yayi yana faɗin. "Is ok!"
***
Alhaji Nafi'u
Penthouse
Cikin gidan a resident din Alhaji Nafi'u yake, babban gida ne mai duhu domin babu haske ko kadan a gidan, a yadda yake takawa zaka san ya san cikin gidan ciki da waje. Tsayawa yayi ya kwabe kayan jikinshi yayi tsirara haihuwar uwarsa da Ubansa ya kunna wuta a jikin wani itacce, take wutar ta haska ko ina, sannan ya ajiye itacce ya kama tafiya haka har cikin gidan, wata kofa ya bude wanda ya kai shi dokan daji. Ya fita daga duniyar mutane ya nufi underworld, wata duniya ce me cike da duhu me cike da ban tsoro, tafiya yake amma ba a kasa yake tafiya ba sannan ba a sama yake tafiya ba, yadda yake tafiyar zai baka mamaki domin bakiɗaya iska ce take kadaiwa da shi. Cikin ɗan kankanin lokaci ya isa gaban wasu mutane wanda dukkansu tube suke tsirara. Kansa a sunkuye, wuta ce take ciki kamar zata laso sama. Saboda karfin cinta kowa yana cike da tsoro. "Gwaska dakare ya kusan fitowa, kun san yadda muke rayuwa a cikin duhu. Don haka ku san yadda zaku yi ku kawo mana mafita kafin ya iso." Inji wata murya me amo, wanda ya cika ko'ina. A can lungu da yake gefen wutar muryan yake fitowa, dan turo kai mai maganar yayi, wutar ce ta mutu murus a hankali ya janyo jikinsa. Wanda rabi mutum ne rabi kuma ta mage ce bakiririn. "Nafi'u ina jinin da kai yi alkawarin za a zubar?" Zubewa yayi a gaban dodon yana kerma. "Ban san waye ya shiga tsakaninsu ba, amma tabbas mun shirya za a zubar da jinin mutane." Dariya abun yayi kafin ya ce mishi. "Ka cika min muradina?" A hankali ya d'aga hannu sama sai ga kwarya cike da jajjayen kyalle. Murmushi yayi ya kalli kwaryan ya tawowa tayi gabanshi. "Idan ma haka bai samu ba ina bukatar jini, Nafi'u saboda kai ne na samu rauni Yaron nan ya lalata min jikina. Rilwanu!" Fitowa yayi da sauri yana zubewa a gaban mutanen "me yasa bai mutu ba?" "Tuba nake ban san me ya faru ba! Amma ya dawo da wata yarinyar da take bashi kariya?" Girgiza kai magen dodo ya ce. "Aiki ne a gabanka sosai!" Ya fada yana girgiza jikinshi. "Dole na sha jini, dole ayi wani abu domin ina son jini!" Ya faɗa yana lashe jikinshi. Hannu Alhaji Nafi'u ya d'aga sama yana wasu irin surutai, ya dauki kimanin minti goma kafin ya sauke hannun, sai ga kunshi abu a cikin zani yana faduwa daga sama wasu ka jikin bakin leda, wasu a jikin audigar mata, suka cika gabansu. Wasu karfafan maza ne suka fito. Daga wata kofa, sannan suka nufi kunshin cikin tsumar suka fara fito da jarirai. Sai kuka suke wasu yan mata kusan goma sha biyar suka fito da kwarya tare da wata ƙatuwar daro, aka shiga yanka jariran nan ana tara jininsu a kwarya, suna jurewa a daron, sai kwarya ya cika ake zuwa a juye a daron, sauran wanda aka samu na jikin audigar mata, aka jika a cikin jinin ana mikawa sauran mutanen suna tsotsa, a hankali yanayin halittarsu ta fara sauyawa, amma ban da mage dodo da Alhaji Nafi'u, idanunsa ne suka kad'a jajjur. " Har yau baka samu jinin ba ko? Ga zahiri ya nuna ba zaka tab'a rikid'ewa zuwa wata halitta, ba sai ka kwanta da me dauke da wancan nau'in jinin, ko kuma Yarka ta cikinka." Hankalinsa ne yayi Bala'in tashi ke nan ba ita ba ce wacece ko yar wurin Alhaji Saddam ce?.....
Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book.
https://wa.link/qhi0wb
*Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu ƙayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:*
*MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya haɗa da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.*
*AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen ɗin Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen*
*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
*POSTING*
*Ɗaya: 500*
*Biyu: 1000*
*Uku: 1500*
*DOCUMENT (da zaran an gama posting zai koma)*
*Ɗaya: 1k*
*Biyu: 2k*
*Uku: 3k*
domin tura shaidar biya ko Ƙarin bayani, ku tuntuɓi:
*08130269641*
Ko
*08137311900*
Ko kuma
*09063467258*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: ROYAL POLITICS 🔥
_An yanka ta tashi_
Ramlat A Manga
Mai_Dambu
TOP-NOTCH SEASON 4
Sadaukarwa ga Auntyna RUKAYYA GOMBE 🥰 🤩 😍
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HYpizDjKAkJB4QClSeLTvw
*Hajiata indai kinsan kina Neman jaka da takalmi na fita kunya na alfarma na shiga taro na zuwa villa,to gaskiya kawata karki wuce group dinnan domin kuwa akwai luxury bag's unique shoe's jewelries iya ganinki,hmm baa cewa komai dai ki shiga idonki ya gane Miki yar uwa*
09
Yadda ya ware idanu cikin kaduwa da tsoro yasa Dodo mage ya ce mishi. "Kai har yanzu da sauran lokaci, ba haka ba ne jininka me karfi ne don haka kada ka damu akan abin da zaka gani ko zaka rasa."
Ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin. "Na razana ne!" Kallon yayi duk jama'ar sun koma halittar da suke so. "Yaku waɗanda suka koma kalar da suke so, ku sani wannan abinda kuka samu kamar kyauta ce daga gare ni, amma ku sani dole ku kawo min tukwaici." Gurnani suka fara yi suna ihu. Sannan ya juya ya koma raminsa, kafin aka juye musu jinin bakiɗaya, wanka suka shiga yi da shi tare da ihu.
Sai goshin asuba suka fara barin wurin,har da Alhaji Nafi'u da Rilwanu Abubakar Yayari. Har zasu tafi Mage ya kara kiransu, juyawa suka yi sannan suka koma gare shi. Zubewa suka yi a gabashi. "Jinin yarinyar nan bai ishe ni ba Nafi'u, ina son jini Rilwanu daga cikin gidanku, akwai wani abu a cikin jinin gidanku. Ina so babba ko yaro, jinjiri ko dan tayi." Shiru yayi kafin ya ce mishi. "An gama!" Alhaji Nafi'u ya sake murmushi ya ce mishi. "Jini zaka same shi, amma Shugaba ya batun bude boyayyen masana'anta na ne?" "Ka kawo min jinin budurwa a kawai da shi zamu ga abinda ya dace da masana'antarka." "An gama!" Mikewa suka yi ya koma raminsa ya boya. Sannan suka bar underworld din. "Rilwanu Abubakar Yayari yanzu ya zaka yi?" "Amaryata tana da tsohon ciki, dan zan bada dama na aureta ne na sadaukar da duk abinda zata dauka ban aureta don tayi ta haihuwa ba." Rabuwa suka yi kowa ya kama hanyar kofarshi, yana isowa penthouse din wutar ya kama wani daki ya nufa yayi wanka. Sannan ya dauki kayansa ya saka, wayarshi ya lallubo ya kira wata number.
"Ina son budurwa mara galihu, a tafi gidan Marayu da F&F a dauko min ita kada na ji kada na gani." Daga can aka ce mishi. "Yallabai duk marayun suna da registrater sannan kullum Malam Junaid yana zuwa ya karya da su, gaskiya a duba wani abu." Shiru yayi yana ji kamar ya ganshi gaban Junaid ya shake mishi wuya,.tashi yayi ya nufi wurin kofar underworld ta bude mishi, tube kayan jikinshi yayi yana nufar can inda suke meeting. "Na dawo gare ka akan lamarin Junaidu!" "Na gaya maka babu abinda zaka iya mishi, kuna dayawa da kuke son ganin bayansa, amma ku sani shi din prey din Gwaska dakare ne matukar kuka tab'a shi zaku yi danasanin haka. Ka je akwai lokaci da zasu ribanci hakurinku. Wata nasara tana biye da kai."
Juyawa yayi yana me barin wurin, yana isa penthouse din wayarshi yana kara. Dauka yayi yana faɗin. "Ya dai?" "Alhaji wani abu ne ya faru na kira na gaya maka, wata yarinya aka kawo ba lafiya amma likitoci sun tabbatar da kodanta ne ya lalace, ko zaka yi wani abu a kai a mata dashen koda haka zai taimaka maka wurin fitar da makomanka" murmushi yayi ya ce PA dinsa. "Ayi kome sannan a tabbatar yan jarida an gaya musu, sannan a gayawa Yaranmu masu aikin nan su fitar da kome."
***
Ikhlas
Fushi nayi da kowa na gidan,.don haka ko Maluma fushi nake da ita, dani sai Hajja. "Takwara ayi haka ki ce ba zaki ci abinci ba, tsoro nake kada yunwa su karar da ke, zama gaki abu ba abu ba munafuki yaso tsegumi!" "Na koshi Hajja." Ganin naki kulata ta sake cewa. "Wai takwara bana ganin Irak ina take ne?" "Tana bangarensu." Na bata amsa ina jin kamar na kurma ihu, yunwa nake ji amma bakin halina ya hana ni tashi na je. Ganin bata gane min yasa ta mike tare da barin dakin. Ina jiyo ta tana faɗin. "Ban da mugun hali irin naku, yau kwana biyu kenan babu wanda ya ce takwara ta zo taci abinci, har da kai junaidu kamar baka san Allah ba, haba Junaidu tow wallhi ba zan yarda ba, dama ka saka mata sunana ne don ka azabarta da ita da yunwa? Maza a zuba min abinci na kai mata." Yadda take masifa zaka rantse da Allah ina kwance ne cikin mugun yanayi, nan kuwa dama bana rabuwa abin kwadayi. Kuma su nake ci idan na shiga banɗaki, naci na koshi idan na fito na koma narkewa a idanun Hajja. Ita kuma da bata da hakuri da jure ganina cikin wannan yanayin tayi ta damuwa kenan da damun kanta. Shi yasa nake bala'in son Hajja don tana taya ni abinda nake so.
Shigowa da tire Abba yayi Hajja tana bayanshi, ina ganin Abba ban san lokacin da mike tare da cewa. "Abba!" Yadda na kira sunanshi cikin shagwab'a da rikicin dole yasa shi zuwa min idanu, "Gashi nan!" Ya fada yana mika min, kuka na saka ina faɗin. "Abba kayi hakuri." "Shi kenan, ki shirya zaku tafi jibi!" Dangwara tiren nayi ina faɗin. "Real?" Gyada kai nayi, rungume shi nayi ina ihu "Abba na gode sosai!" Ma faɗa bayan na sake shi, fita yayi can sai gashi dauke da wata gora. Mikawa Hajja yayi ya ce mata. "Maganin baki da farin jini don takwaranki bakin jini ne da ita babu mashinshini!" "Abba ina da saurayi Uwais!" "Kul na sake jin sunanshi a bakinki!" Inji Hajja, kafin ta ce mishi. "Batun auren Irak ba zai yiwu ba, tun bayan ba nake son gaya maka." "Abba ki kyale Baba Malam Umaru ko wancan satin ya gaya min amma abinda zai yiwu nake fatan haka, ita me martaba ya bukata ba wata ba." Murmushi tayi ta ce mishi. "Tunda nake a rayuwata Dan uwana bai tab'a fada min abu bai faru ba, don haka mu barwa Allah ikonsa!"
Kallona yayi ya ce min, "Zaki tafi amma akan one condition!" Kallonshi nayi nace mishi. "Abba one condition?" "Eh ai ke ba yarinya ba ce duk abinda ya faru ki gaya min kin ji ko!" Murmushi nayi nace mishi. "Ok Abba in sha Allah za ayi haka!" Na faɗa ina barinsu dakin na wuce part din Mommy Turai, ina zuwa na ga kofar a rufe, kwankwasawa nayi Tauhid ya bude min, da sauri na shiga dakin da Iram na same ta tana kuka. "Baby Abba ya amince mu tafi?" "Da gaske?" Naji Muryar Mommy Turai, juyawa nayi ina murmushi na ce mata. "Eh! Amma Mommy me ya same ta?" "Akan Abbanku ya ce ba zaki bi mu ba ne!" "Tow ai ya amince, sai ki daina kuka gani nan na gaya miki zan je."
Dakyar Iram ta daina kuka tuni ta ware muka shiga tsara inda za muje. Domin daga Dubai Bangkok zamu tafi na Thailand ta ce Mommy tana da wani abin da zata yi na kasuwanci, sai China inda take odar kayan daki da na kitchen, musamman wanda take sayarwa da kuma na auren Iram din, daga nan sai mu dawo Nigeria.
Hajiya Turai na fita ta nufi daya dakin ta kira Hajiya Layla. Bugu daya tayi ta ɗauka. "Ke dai wallahi baki da mutunci, ina tsaka da jin dadi zaki kira ni." Tsaki tayi ta ce mata. "Banza zamu tawo Dubai don haka ki saka hoton da zan turo miki a kan Apps ko zamu kwashi dami akala."
"Ke wacce kenan?" "Tow!" Ta fada bayan ta kashe wayar ta tura mata hotonan Ikhlas guda biyu.
****
Wherehouse
Gida ne falle can dokar dajin domin ba zaka tab'a tunanin wannan dangun dajin zai samu irin wannan gidan ba, amma son zuciya irin na mutane gandun daji ce dajin Allah aka ware fili aka zuba gida me Bala'in kyau da girma kana aka ware wani shashi na musamman ana aikin sarrafa jikin bil'adama ana fita da su ana sayarwa, musamman koda da zuciya an fi sayansu sama da kome.
Yan mata biyar aka kamo suna ihu suna kome aka wuce da su cikin bangaren nan, aka zubar da su a kasa. Ƙatuwar sufanan babbar motar wani karjejen kato ya makawa daya daga cikin Yan mata ta fadi tana wani irin fisga domin ya same ta ne a tsakiyar kanta. Sauran yan mata hudu tuni tsoro ya kama su. Shigowar wata ƙatuwar Nissan versa 10 2024, baki wulik ta yi parking a daidai kofar mahautar bil adam,wata hamshaqiyar mace ce ta fito daga cikin motar idanunta sanye da tabarau baki, murmushi take ta na faɗin. "A fito da sauran yan matan su dauki darasi akan wanda ya bijire mana."
"Tow Hajiya Layla ikon Allah!" Inji daya daga cikin mutanen, fita suka yi can sai ga yan mata a kiyasti sun kai kusan dari, suka fito aka jera su, suna kallon yar uwarsu aka saka adda aka datse kanta. Jinin ya zuba a jikin kowa a wurin har da Hajiya Layla wacce ta saka hannuna ta laso jinin ya saka a bakinta. "Idan kun gadama ga kofa can a buɗe ku fita daga yau kada a kara rufe kofar gidan nan ko dare ko rana duk wanda yaso ya fita shi ya san yadda zai amshi sakamakon. Ina bata tab'a mu'amala da kowa ba, saka wancan kwaryan ka tari jinin, sannan a ware min Yan mata, kamar shida a musu passport, na Bangkok akwai wasu yan siyasa da suke da wani taro na musamman a can a kai yan matan bangaren yar Chadi a gyara musu jiki. Sannan a kwai wani abu daya a ware min dakin na musamman da alamu zamu yi bakuwa nan da sati biyu anan zata zauna."
Ta fada tana murmushi, kafin ta daura da cewa. "A bani yan mata biyu su min tausa." Ta wuce tana me nufar cikin gidan yan matan suka bita, wayarta ce tayi ƙara bodyguard dinta wata karffafiyar mace ta mika mata. "Allah ya taimaki Madam zaki shigo? Tow Alhamdulillahi bari na saka a zab'a miki yan mata na musamman ina godiya!" Can ta kuma cewa. "A'a ni zan saka a zab'a miki ai nasan baki son ragowar kowa sai naki na ji yanzu haka za ayi!"
A cikin yan mata shida da zasu tafi Bangkok aka kara ware yan mata uku, aka fara musu wanka da kayan kamshi wankar a aka musu na karshe dafaffiyar madara ce aka zuba mata kayan kamshi suka shiga cikin suka zauna sai da suka jima a cikin sannan saka fito aka basu wani irin ruwa suka yi wanka wanda saboda kamshin ruwan sannan suka fito aka shiga goge musu jiki da wani audiga daga yadda ake gyara musu jiki kowacce ta sha jinin jikinta bakuwar su mai muhimmanci ne, bayan sun gama aka kai su dakin, wurin karfe biyar na yamma aka ce bakuwar tazo. Amma da tazo meeting dinsu suka shiga yi, basu fito ba sai karfe goma. Jagora Hajiya Layla ta mata sannan ta rufe kofar, tana shiga yan matan da dama sun san aikinsu suka rufe ta tare da taimaka mata ta cire kaya, sannan suka rufe hannunta zuwa ban daki suna masu riketa har ta shiga wanka, suna taimaka mata har ta fito sannan suka daura mata towel suka riko hannunta,