Showing 87001 words to 90000 words out of 304445 words

Chapter 30 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

111

addu'a, sai dai ina fara karatu na ji jiri ya dame ni, dole na koma na kwanta, tea ya haɗa min na sha. Wayar shi ce tayi ƙara ya dauka. "Muna VIP 28 room!" Kashe wayar yayi sannan ya cigaba da bani tea din ina sha. Turo kofar da aka yi yasa muka kalli kofar. Abba da Umma ne sai Hajja. Bai daina bani tea din ba duk yadda naso na noke amma haka ya cigaba da bani ina shanyewa ya mike yana gaishe su. "Ina ka baro Matarka ka kare a jikin takwara." Murmushi yayi yana faɗin. "Haba Matar sona, na ji tausayinta ne kada kishinki ya motsa yasa nazo na zauna da ita." Ya fada yana mata murmushi, ya haɗa kayanshi da yake dakin Laptop, abin sallah, Alqur'ani, ya saka a wani bag me kyau, ya tako gabana. "Princess bakya bukatar wani abu?" Bariki na fada ina kallonshi yake nayi mishi na ce mishi. "Babu abinda nake bukata!" "Ok!" Ya fada yana leka gefen fuskana da ya ɗan kumbura. "Jiya kafin ki dawo kin bude kofar ki ne?" Shafa wurin nayi hawaye ya zo min ajiye jakar yayi ya ce min. "Gaya min me ya same ki?" "Babu kome?" " Ba zaki gaya min me ya same ki ba?" Ya kuma maimaitawa a dan zafaffe, "Takwara me ya same ki?" "Hajja Iram ce da wasu kawayenta suka dauke ni a makaranta, na gaya mata bani da lafiya amma haka suka dauke ni zuwa wani wuri, ban sani ba sai da na farka na ganni gefen fuskana a dan kumbure, ban san me suka shaka min ba, ina dawowa gida na shaki kamshim turaren wuta, wallahi ban san iya abinda suka min ba amma ta ce sun dauki kome a wayarsu ni don Allah Abba ka ce kada ta min haka!" Kuma abinda ya faru kenan shekaranjiya da na fita makaranta ban shiga makarantar ba suka min wannan aikin. "
A hankali ya dauki jakar ya nufi kofar fita, "at least kome aka miki ki gaya min, bayan ni sai Abba muke da ikon yaki akanki! Am sorry Mallam Junaid ba zan bari a cu zarafin matata ba." "Go ahead?" Abba ya fada mishi. Ban gayawa musu kome ba, amma lokacin da na farka abinda na ga suna yi ya girgiza, ashe irin rayuwar da suke kenan, dariya suka kayi ta min suna nuna ni. "Gara ki farka domin mun gama abinda zamu yi da ke!" Kuka na cigaba da yi Abba da Umma tare da Hajja suna rarrsshina
*
Karfe uku yana zaune Faruq ya kawo mishi Iram, wacce ta sha mari a wurin Faruq. Tsoro yasa ta yin kasa da kai. "Me na gaya miki kwanaki?" "Wallahi ban mata kome ba razanata nayi kawai." Shiru yayi kafin ya ce cewa Faruq. "Daure ta ina ga tana buƙatar alluran Mahaukata ne. " "Gaskiya Sir gwara a mata ko zata yi hankali bayan ta ware." "Wallahi ban mata kome ba, kawai abu na shaka mata yadda zata suma amma na rantse da Allah ba zan iya cutar da ita har haka ba, na san bamu kyauta ba amma ban yi yadda xan cutar da ita ba." "Amma nasan kin yi video kome?" "Wallahi babu abinda nayi na rantse da Allah!" "Bayan wanda kika yi?" "Allah da gaske ban mata kome ba!" "Ajiyeta akan kujeran lantarkin nan ko sumar da ita mu yi sau uku!" Kuka take tana bashi hakuri haka yasa mata lantarki ai ta suma ya kai sau goma duk da abinda ake mata a cikin sakon daya zuwa biyu amma ji take kamar ana zare ranta, tun da ta ga mutuwa ya kuma yi mishi alƙawarin ba zata kuma shiga harkan Ikhlas ba, ya saka Faruq ya dauke ta ya kai ta gida. Sauran yan matan da ta lissafo sai da aka ci Ubansu suka gane bafa kowacce yarinyar ake tab'awa ba.

**
Alhaji Nafi'u da Rilwanu sun hade kai sosai, sannan goyan bayan da Alhaji Rilwanu yake basu yasa ya zama kamar. Sannan a cikin Masarautar akwai akwai wasu mata biyu da suke aiki da Rilwanu Abubakar Yayari, sai bangaren bayi suma akwai munafukai sosai a cikinsu waɗanda suke aikata kome don biyan buƙatarshi.
Yanzu abin harinsu Ikhlas ce kota halin kaka, don haka suke farautarta dare da rana domin ta haka ne kawai zasu cimma shirinsu.
Da zai tafi ya zo yayi min sallama, wurin karfe sha biyu na dare ya turo min sako ya isa lafiya. *Ya jikinki? Da fatan kina lafiya?* Daga haka bai kara turo min sako ba,
Kwanaki goma nayi aka sallame ni, Cikin gida Umma ta mai dani, a wurin Mai Babbar daki. Kamar yadda ya ce amma Umma tana tafiya ta ce Iyaami ta mai da ni gidana,.kuma nima na ji a raina nafi son can din. Lokacin da na dawo na wuce bangarena, key dama yana wurina gyara wurina nayi na shiga nayi wanka na gyara bangarena tas, sannan na fita nayi girki na ci. Sau biyu Mr Brandy yana tambaya ta ko ina bukatar wani abu na gaya mishi ai nima zan yi ba sai ya samu kanshi ba.

Abinda na fara fuskanta shine wani irin rashin lafiya, bana barci idan xan yi barcin kuwa tow sai goshin asuba, domin wasu irin suratai nake ji ana yi a kunnena, haka yasa na koma kwanciya da karatun Alqur'ani, Alhamdulillahi ina samun barci. Haka ina sallah dare da karatun ne ma da na fara xan fara jin jiri da ciwon kai idanuna yayi ya zubar da hawaye ko kuma hancina yayi ya zubar da jini. Kusan sati daya ina haka, na kira Abba ashe yayi tafiya zuwa Sudan, na kira Maluma na gaya mata abinda ta ce min shine. "Karya kike baki son zaman aurenki na san halinki ne!" Kai karewa na tafi har gidan ranar naki dawowa domin anan na kusan kwana. Haka Maluma tayi ta min fada haka na dawo gida ina kuka, a firgice nake kome ya tsaya min, makaranta da muke dab da fara exam don ma an d'aga.
A hankali na shiga dakina, ka kwanta na rufe kofar dakina na kwanta, ji nayi alamar aka gudu a saman kwano dakina, na kunna wayata na saka karatu, dakyar na iya barci karshe wayar ce aka doka da kasa sai da ya mutu, duk addu'ar da tazo bakina yin shi nake, cikin dare kamar mahaukaciya haka na bar gidan na nufi waje, wanda na ga kofar a buɗe. Allah kaɗai ya kai ni bangaren Mai Babbar daki, domin ina tafiya gani nake kamar wasu halittu suna bina, abu daya ya kwace ni ba su kama ambaton Allah da nake da karfi da karfi, har na isa kofar gabas wanda na gani a bude,.sai dai ina isa kofar Mai Babbar daki na ganshi a rufe kuka nake ina kiranta bata bude ba, wani abu me kama da kare ko mage ne ya biyo ni da gudu. Na fasa wani irin ihu da yasa gidan yasa bakiɗaya wanda yayi sanadin faduwana a wurin sumammiya.

Haka yasa kowani bangaren aka fito duba lafiya. "Innalillahi wainnalihir rajoun! Zainab!" Mai Babbar daki ta kira sunana amma ina, shiga dani aka yi ciki. Wanda aka yi ta fama da ni har gari ya waye, aka kira yan gidanmu suka zo Maluma a gaban jama'a ta tsinka ni ta ce musu. "Auren ne bata so, kuma wallahi kika kashe aurenki babu ni babu ke!" Maluma bata fahimci halin da nake ciki ba, haka nayi ta jinya a wurin Mai Babbar daki, wanda a wannan lokacin na hango tausayina a cikin idanunta, sai dai kuma dab da zai dawo kamar wacce aka tsikara ta fara min wasu irin halayya, ranar ina kwance ta kira abokin aikinsa wai ya duba ni, a gaban mutanen gidan aka yi ta min rashin mutunci, duk da abu daya ne yake faɗa mahaifiyarki ma taki kula da ke sai ni, wannan yasa nayi hakuri haka ya bani maganin barci, ya tafi Ilham da Ijlal suka saka ni a gaba suna min dariya, a lokacin shiga daki nake ina kuka mai matukar ciwo.
Ranar da ya dawo da wuri na koma gidanshi, na gyara ko ina sai dai ina bude wardrobe zan dauki kayana na ga wasu irin rubutu, haka yasa na rufe da sauri. Ina zaune a dakin kamar mayya don bana son magana.

Shigowa yayi ya same ni zaune a tsakiyar gadon ya dunkule wuri guda, sannan wani abu da yake faruwa shine bana iya magana sai In-in-ina ya shiga maganar na kasa fadar meke faruwa, haka yasa bana magana. Bude labulen dakin yayi, ya hango ni zaune na cusa kaina a tsakanin cinyoyina. "Lafiya?" D'ago kai nayi ina kallonshi, na kara kifa kaina ina jin hawaye na zuba min. Na cigaba da zama haka fita yayi ya nufi bangaren Nady ya tambaye ta ko tasan meke faruwa ta ce bata sani ba, haka ya tambayi Ijlal ya ce bata sani ba, dawowa dakina yayi ya same ni, hannunshi ya kai da niyyar ya tab'a ni na fasa wani irin ihu tare da dira a gadon xan gudu. Da sauri ya riko ni.....
*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: Rirrike shi nake kara yi a matuƙar rikice wanda tunda nake a rayuwata ban tab'ayiwa wani mahaluki ba, jikina kuwa wani irin rawa yake da kyarma wanda ya saka ni sake fitsari a jikina wanda ban san lokacin da ya fita ba, saboda tsananin bala'in tsoro da tashin hankalin. Zufa ke karyowa a ilahirin jikina cikin wani hargitsatten kuka nake kara damke shi zuciyata kamar zata buga. Shi kanshi a matukar rikice yake ya rasa yadda zai yi da ni. Mutum ne a tun zuwana gidan bamu tab'a haka ba, balle kuma har wannan yanayin ya zo mana, rike ni yayi yana faɗin. "Ikhlas!!!" Abinda yake faɗa kenan amma ina na firgita na gigice na razana iya razana. Ya rasa yadda zai yi da ni bai san lokacin da ya buɗe muryanshi ya daka min wata irin tsawar da ya sani maza na daura kaina a kirjinshi tare da k'amkame shi da dukka hannu bibbiyu. Ina sake wata marayan kuka. "I say enough! Nace ya isa haka!" Sai yau na ji asalin fusatacciyar muryanshi. D'agowa nayi na kalli fuskarsa. Wannan hargitsatten kwayar idanunsa wacce baka tab'a fahimtar me ye a cikinta, na ga ya zuba min idanun idan ban yi karya ba, wani irin mai ce ko kwalla ce a kasar idanu, ga wani ja da idanun yayi kamar jini. A matukar tsorace na mishi kallon minti ɗaya da dakika arba'in da biyar, na maida kaina jikinsa. Yadda jikina yake rawa kaɗan kaɗan yana shafa min bayana yasa na fara samun nutsuwa, ajiyar zuciya na fara saukewa. A hankali yake hura min iskar bakinshi har sai da ji shi a tsakiyar kaina. Riko hannuna yayi ya raba ni da jikinshi sannan ya kawo ni bakin kofar ban dakin. D'ago kaina yayi da yatsar hannunsa yana me lumshe idanunshi ya bude a hankali ya nuna min kofar ban dakin yana me cire hannunshi a habb'ana, sannan ya juya zai fita da sauri na rike shi, cikin girgiza kai bakina yana rawa na fara ƙoƙarin mishi magana amma ina In-in-ina ya hanani magana. "Kada na fita?" Ya tambaye ni a matuƙar sanyayye? Hawaye ne ya zubo min na gyada mishi kai nayi ina zare idanu. Hawaye na zuba min shar-shar. Kamar yadda yake shafa magenshi haka na ga yana shafa kaina. "I'm here for you!" A hankali na sake hannunshi na juya zuwa ban dakin. Ina shiga na rufe kofar, a hankali na fara cire kayana, har na gama ban san lokacin da wani irin kuka ya zo min ba, a kasa da wata shida kenan da wannan ƙaddararren auren, ni kaɗai nasan yadda nake ji, babu wanda zai san yadda nake cutuwa, hakazalika ilahirin zuriar gidan Yayari babu wanda ya damu da halin da nake ciki, shima kaɗai yake kula da ni, saboda kuskuren da ba ni nayi ba, saboda laifin da san na aikata domin na rabu da aurenshi sai kuma zargin Abbana da aikata kisan aminsa, duk sauran Mate dina suna lafiya da iyayensu sannan babu wacce zata auri mai mata, sai ni. A hankali nake kuka mara sauti, tare da sakewa kaina ruwan sanyi domin ta haka ne zan ji sassaucin halin da nake ciki. Babu wanda ya yarda da ni, babu wanda ya amince da abinda nake gani. Na fadawa Malama amma bata yarda ba, na fadawa Umma amma bata yarda ba, Ya Abid na gaya mishi yaki yarda. Abba kaɗai zai yarda da ni amma baya kasan nasan da yana nan da zai iya taimakawa har na samu lafiya Maluma saboda halina ta juya min baya a gaban jama'a ta nuna karya nake , sai Ya Yunus lokacin da na fara jin abin ya yarda ya kuma ya bani addu'ar da xan yi amma tunda na dawo gidan na zama kamar wata mayya ban iya kome kamar ba mahaddaciyar Alqur'ani ba, na zama wata iriyar matsoraciya. Ko ƙarar abu naji zan firgita ina ji kamar wani yana farautar rayuwata. A hankali na cire pant din tare da bra, kamar jira ake nayi haka naga wutar dakin ya fara blanking ya dauke ya kawo da sauri na janyo towel na daura tare da kokarin fara bude kofar dakin amma kamar an datse shi, wani irin shafa bayana aka yi tare da kartan bayan kamar farce ne, ban san lokacin da na tsandara kara ba, tare da durkusawa a wurin ina ihu tare da buga kaina a kofar ban dakin saboda tsoro, gashi ina jin kamar abu yana tsaye a bayana. Jikina wani irin rawa ya dauka ina kokarin kiran sunan Allah amma kamar an danne min harshena da zuciyata. Bangaje kofar ban dakin yayi da karfin tsiya na zube can kasa, da wani irin karfi na mike towel din yana kokarin faduwa, hanya nake nima na falla da gudu yayi maza ya damke ni, na fara ihu da razana kamar na dazun, wani irin matse ni yayi tare da fita dani ya haɗa ni da bangon dakin wanda ya bashi damar damke ni da kyau, ya fara da Bismillah kafin ya haɗa da kabbaratul hajja, sannan ya haɗa da salati Ibrahimi.. kafin ya bude cool voice dinsa ya fara karanto ayoyi a cikin Alqur'ani mai girma, yadda yake karantawa a sanyi-sanyi zafi-zafi, ya kuma matse ni da kyau. Yana farawa duk wannan fisgar da nake yi sai na fara laushi, ina me jin bugun zuciyarshi da nawa lokaci guda, yadda na mai da kaina kirjinshi dai-dai kan zuciyarsa yasa shi cigaba da karatun har na wani lokaci, kafin ya janyo hannuna zuwa bakin gadon, muka zauna ya cigaba da karatun,.karshe kunna wayarshi yayi yana karatun yana me rubutu, can kamar minti goma ya mike tare da bude wardrobe dina ya ga na mike tare da kokarin dauran hanyar fita kallona yayi. Ya fasa, sai ya dawo ya rike hannuna, cire rigar jikinshi yayi ya saka min, sannan ya janyo ni tare da kifa kaina a kirjinshi yadda na bawa wardrobe din baya. Ya bude a hankali, wasu irin zane ya gani wanda bai san yadda zai iya fassara su ba, abu daya ya fahimta shine an rubuta *SAI KIN BAR MIN MIJINA* A hankali ya dauko min abaya, sannan ya rufe wardrobe din. "When haka ya fara miki?" Ya tambaye ni, bayan ya cire min rigarshi ya daura min abayata yana kallon yadda nake share kwalla. A hankali na dauko jotter na da pen na rubuta mishi. *Sati biyu* kallona yayi, abin ya bashi mamaki tun tafiyar shi kenan . "Waye kika gayawa?" Na kara rubuta mishi. *Kowa na gayawa ba a yarda ba! Last week Mai babban daki ta kira likitan Psychiatric ya duba ni* "a gidan?" Hawaye ne ya zuba min, gyada kai nayi tare da rike hannunsa. Alamar kada yayi magana kowa. "A gaban su waye haka yi haka?" *Every body!* "A gaban kowa na gidan Yayari" rubutawa nayi da sauri. *Babu kome kada ka fadawa kowa fa!* "Ok!" Ya fada yana mikewa, mayafin yafa min, wani zogi da naji yasani ajiye littafin xan tab'a wurin yayi maza ya rike hannuna. "Na gani kada ki tab'a!" A hankali na sauke hannuna, ya kwashe min littafin da pen din, muka fito ya duba min takalmina, a hankali muka ratsa cikin parlourna har zuwa Main parlour, tana zaune ita da jigajigan kawayenta feminist. Kallo daya tayi mana ba tare da ta fahimci haka ba, da sauri ta kara mana kallon gaskiya ganin yadda ya riko hannuna dauke da littafin rubutuna. "Baby ina zaka da wannan Psycho din?" Yadda yayi mata wata irin banzan kallo yasa ta shiga hankalinta. "Please ina zaka da ita? I hate na ganka da ita! Ga kawayena da business partners dina. Bai kula ta ba ya bar parlourn, parlourn shi ya kai ni,muna shiga Chef Jamimi ya ce mishi. "Barka sir! Everything is ready!" Jinjina kai yayi yana mai nufar parlourn shi da ni, a hankali ya nuna min wuri na zauna sannan ya mika min wayarshi. "Zaki iya jirana?" A hankali na kalli ko ina kafin na bude bakina zan yi magana ta shigo dakin kamar daga sama. "Prince!" Juyawa yayi ya kalleta. "Zaki iya jirana?" D'aga mishi kai nayi, "Prince!" Juyawa yayi ya rab'a gefenta zai wuce ta rike hannunsa. "Wannan yarinyar kowa yasan wacece ita? Mahaukaciya ce sakamakon zunubin Ubanta ya shafe ta, after all kai kasan ba ita zaka aura ba, yar Uwarta kuma Iram ce, sannan ba ita kaɗai ba ce a gidan muma matanka ne da yake munafu...." "Kin gama?" Ya datse sauran kalamanta da basu da dad'i ga a gare ni. "Please list to me! Yarinyar nan tana da hatsari." Fita yayi ya bar mu tare, ko babu kome yasan zata tsaya tayi ta jidali har ya dawo sannan ya san Ijlal


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login