Showing 102001 words to 105000 words out of 304445 words

Chapter 35 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

53

hira suka yi a wajen kafin su shigo, a hankali kamshi da hayakin yake tashi, wanda yayi daidai da shigowarsu, "sannunku da zuwa!" Na faɗa ina nufar window ina d'aga labulen don ni kaina nasan na kwafsa. "Kuyi hakuri" na fara ina kara sanyin Ac din parlourn yadda zai dauke kamshin turaren wutar. "Ikhlas Junaid Gobir ko?" Kallon Mr Faris nayi naga shima yana kallona, fuskarshi kawai zaka kalla kasan yana cikin farin ciki. "Waw! Walid M.A yayari! Mariano! Paul!" Ta fada tana wani abu kamar yarinya karama, ta karasa wurin Mr Faris ta wani jingina a jikinshi tana dariyar farin ciki. Buga bayanta yayi yana faɗin. "Kina farin ciki ko?" Gyada kai tayi tana faɗin. "Ban kawo da gaske kake ba! Muje table!" Ta nuna musu wanda yake waje, wurin suka nufa takowa yayi ya nufi inda nake ya riko hannuna ya kawo ni inda suke ya ce musu. "My second wife!" Dariya suka mishi da yake turawa ne Paul da Mariano suka ce mishi. "Bayan ita akwai Ijlal." Murmushi yayi ya yana faɗin. "Kira ta Zainab!" Tashi nayi na nufi wurinta na buga mata kofa, sake buga kofar nayi ta bude tana kallona cike da mamaki don tasan ni dai ba zan tab'a mata magana ko zuwa inda take ba.
"Mijinki yana kiranki!" Na juyawa zan tafi ta riko rigana ta baya, juyawa nayi na kalleta. Yadda na zuba mata idanu yasa ta sake ni, tana mai juyawa ɗakinta. Nima wucewa wurinsu nayi, na zauna can kuwa sai gata sanye da doguwar riga sai mayafi, ta zauna suka gaisa, sannan ta zauna daya daga cikin abokansa ya ce mishi. "Prince a ina kuka samo mata haka masu kyau kamar Barbie doll?" Murmushi yayi yana me min alama na fara saka musu abinci, nan suka ajiye maganar suka dauko wata, ina zuba musu abincin har ita Ijlal ɗin, bayan na gama na kome na zauna ni ban iya cin abinci a gaban wasu ba, musamman da ban sani ba, yana wahala na ci abinci a gabansu. Ganin naki cin abincin ya kalle ni. "Me yasa ba zaki ci ba?" "Murmushi nayi ina faɗin. "Ba kome!" Nayi mamakin yadda suke cin abincin musamman tuwon dawa basu wani ci na semo kamar yadda suka ci na dawan ba, sai da suka tab'a kome, sannan suka tashi hatta Ijlal sai da ta ci tana yatsina fuska.

"An cika gishiri da yaji!" Daga ni har shi babu wanda ya kulata musamman shi Walid cewa yake. "Zan dawo gida a cikin watan Ramadan dole na kawo Madam a koya mata aikin gargajiya!" Murmushi nayi suka dawo parlourn shi aka baza hira, ni kan da na haɗa kayan dakina na wuce, ban kara bin kansu ba, sai da zafi tafi ne kasancewar turawan sun zo mishi gaisuwa ne sai Walid wanda zai wuce jibi,

Bayan tafiyarsu na samu cin abincina, sannan na wanke kayan baki daya.
--
"Amma yadda na ganta kamar ba zata yi tashin hankali ba, ko dai kai ma kana mata wani abu ne?" Walid ya tambaye shi, bayan sun kai su Paul da Mariano airport, har sai da jirgi su ya tashi, sannan suka dauki hanya. "Hmm! Haka take kamar mai hankali an jima zata fara halinta?" Murmushi Walid yayi ya ce mishi. "Kuma ita ce macen da zuciyarka take so ba?" Kallon hanyar yayi tare da gyara glass din ya ce mishi. "Kusan haka,amma bana jin zamu zauna for long time!" "Me yasa ka ce haka?" Walid ya tambaye shi, cizon lips dinsa yayi alamar yana jin ba dad'i. "A rayuwata da nayi a baya kalilan cikin mutane suke sona, bayan kai da Faruq bana jin akwai mutanen da zasu kaunace ni, har su nuna min hanyar gida, a hankali ya gangara gefen hanya tare da dafe kirjinshi. "Walid kasan waye ni?" A hankali yake sauke numfashi. "Ka samu mutanen da suka sace ka?" Juyawa yayi ya kalli Walid a tsanake. Sannan ya girgixa mishi kai yana mai lumshe idanu. "Ji nake kamar ina cikin wannan dajin, gani nake kamar koda yaushe zasu farauce ni su kama ni, a da can baya naki dawowa gida ne saboda kada su cutar da kowa, amma a yanzu bayan rasuwar Mai Martaba na fahimci kome ya kare, sai dai kuma shigar Gwamnati al'amarin Fada ya sani jin wani irin tsoro kada akwai mutanen da suke goyan bayan gwamnati a cikin fada. Idan haka ya faru tow rayuwar kowa na cikin fada is not safe, a koda yaushe wanda ya sace ni zai cigaba da farautar rayuwata, har sai na kara gudu da kafana." Ya fada yana cire madubin idanunsa. Shiru Walid yayi kafin ya ce mishi. "Idan na gaya maka wani magana zaka yarda?" Tadda da motar yayi suka cigaba da tafiya. "Na ajiye aiki, na Haima ne sai watan gobe zata ajiye ta dawo nan mu cigaba, don kai na dawo domin Baba ya fara gaya min wani magana ya ce kana bukatar wani a gefenka." Cike da mamaki Faris ya ce mishi. "Akwai hatsari shiga rigima ta". Murmushi yayi yana faɗin. "Amma kasan kodan mahaifina dole na dawo ko?" Murmushi yayi ya cigaba da tuki. "Abu biyu ne a gabanka, abu biyu nake tsoron rasawa Mai Babbar daki da wancan Yarinyar da ka kasa boyewa kana tare da ita ka san sau nawa su Paul suka tab'a ni domin yadda kake kallonta lokaci zuwa lokaci idanunka yana kanta, rayuwarka tana zagaye da ita ne tsoro kake kada wani abu ya same ta?" Dariya yayi daidai suna isa kofar gidansu Walid din, aka wangale musu kofar suka shiga bakiɗaya. "Kana nufin don kada a cutar da Zainab nake tsoro? Tab aukuwa da na tabbata malalaci, ka manta ina raye aka tab'a mai martaba sai sune ba za a tab'a su ba? Allah ya kyauta kawai amma ai mafaraucina yana sane da inda nake raye, sannan yana tare da ni kamar inuwata ne, shi yasa ba zan tab'a yarda nayi wani kuskuren da zai shiga rayuwata ba." Yayi parking a cikin harabar gidan. Daga can kudu na cikin gidan, Alhaji Mamman Abba yayari da Alhaji Kabiru Hamud Yayari, sai Alhaji Nuru Yayari, rasawa suka yi tare da gaishe su, sannan suka mike zasu nufi cikin gidan, Alhaji Mamman Abba yayari ya ce musu. "Faris ka shiga ka fito muna jiranka." Gyada kai yayi yana faɗin. "Tow!" Suka shiga cikin gidan, sun samu Mahaifiyar Walid kasancewar shine da na biyu a gidan, "Gaishe ta suka yi." Cikin kulawa take kallon Faris ta ce mishi. "Ikon Allah rabonka da gidan ranka shi dade tun kafin ka bar gida, yau gaka a cikin gidan nan. Masha Allah" ta fada tana murmushi, gyada kai yayi yana faɗin. "Eh Umma!" Kasancewar tun suna Yara haka ake kiranta. "Allah sarki ya mai babbar daki?" "Tana lafiya!" Ya fada a hankali, sun jima har aka kawo musu abin tab'awa, sama sama ya tab'a sannan ya mike. "Zan tafi, Walid sai mun hadu." Mikewa yayi ya rako shi har waje ya ce mishi. "Faris jikina yana bani wani abu, ka taimaka min na taya ka aiki!" Murmushi yayi ya ce mishi. "Ni fa ba zan yi wani aiki don rayuwata ba, ciwon da aka ji min a baya ma ya isa, motsina kaɗan ake jira zaka ga mutanen nan sun fara bayyana asalin true colour dinsu, ni kuma nayi alƙawarin ba zan yi wani motsin da zai cutar da mutanen kirkin da suke zagaye da ni ba." "Idan sun kuma basu fahimci yarenka ba fa?" "Haka zan yi hakuri domin idan basu fahimci yarena ba, haka zan yi hakuri idan ta kama su kashe ni ma, ba laifi su yi duk yadda suke so. Tunda suka iya kashe duk wanda ya shiga musu gaba gaya min who am i da ba zasu kashe ni ba? Yayari house yana bukatar zaman lafiya mai daurewa, idan ta kama na bada rayuwata domin zaman lafiya me kake tunanin idan haka zai samar da zaman lafiya. Itama Zainab na ajiye abinda nake ji a tare da ita zan sallame ta domin ta haka ne kawai zan samu zaman lafiya ba tare da wani ya cutar da ita ba." Ya fada yana cigaba da tafiya a hankali. "Faris kana magana kamar baka yarda da kowa ba." Nuna kanshi yayi kafin ya ce mishi. "Ni? A'a na yarda da kowa domin da idanun basira nake kallon kowa ba da wata manufa ba, sannan kada a haka ya tab'a ranka." Suka saka dariya, yana son Faris saboda kirki adalci da hakuri. Shi tunda yake ba zai ce ga yaushe ya ga fushinsa ba, asalima mutum ne da ya san yadda yake rayuwa da mutane sannan baya rena hanyar saka wasu farin ciki. Haka yasa yake bada lokacinsa akan majinyata sa. Idan da zaka ka ga yadda yake tara Mahaukata yana basu labari suna kuka suna dariya sai ka ɗauka an halicce shi ne domin wadannan Mutanen.

A hankali ya isa wurin yan uwan Babansa, kuma manya daga cikin fada. Zama yayi yana kara gaishe su. Shiru yayi kafin ya ce musu. "Gani nan!" Ajiyar zuciya Alhaji Mamman Abba yayari ya sauke kafin ya ce mishi. "Ni da Kabiru Hamud Yayari, muna tare da kai, sannan muna da yakinin zaka zama sarki wata rana, shi yasa muke son mu gaya maka wani abinda yake shirin faruwa." Ya saka aya a wurin, kafin Alhaji Kabir Hammud Yayari ya ce mishi. "Nuruddeen Yayari, shima ya shigo cikin tafiyar tare da niman goyan bayanka bayan hukuncin da Mai Babbar daki ta dauka." Ya fada yana kallon Faris duk sai ya shiga rud'ani, yana son sanin me Mai Babbar daki ta saka yi. "Kwantar da hankalinka mai babbar daki bata yi wani abu ba." Inji Alhaji Nuru Yayari!" Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon ƙasa. Kafin ya ce musu. "Ina jinku!" "Dama Mai Babbar daki ta ce a fitar da wanda zai tsaya takarar gwamna ne, nan da shekara biyu." Wani irin abu yaji ya dake shi, ya d'ago kai fuskarshi bata wani nuna alamar mamaki ko shakku ba, asalima fuskar ta tafi daidai da yadda yake tun dazun ne, murmushi yayi yana kallonsu.."Shi kenan duk abinda ta ce ayi kawai ba mamaki akwai abinda take hangowa da yafi lissafin kowa ne, shi kenan ko akwai wani abu?" "Eh akwai abu kai idan har ana niman wanda zai tsaya takarar shine muke ganin da mu bari waje, mai zai hana mu nimo daya daga cikin mu Nuru Yayari, shi zai fi kowa wannan aikin sannan zai iya kome domin kuwa."
"Allah yasa mu dace sannan sai ayi yadda ta ce." Ya fada ya kuma ki yarda ya kara wani abu akan haka, abin ya matuƙar basu mamaki yadda yaki magana akan shirin Mai Babbar daki, ganin ba zai kara cewa kome ba, sai suka sallame shi suka kira Walid tare da tambayoyi akan meye matsala Faris me yake so me yake bukata? Murmushi yayi sannan ya ce. "Da farko dai shi likitan ƙwaƙwalwa ne, sannan kuma likitan Mahaukata ne idan har zaku shekara kuna son magana mai tsawo a tare da shi ku kai mishi mahaukaci ko mai cutar ƙwaƙwalwa zai muku bayani akan shi." Shiru suka yi baki daya kafin suka ce mishi. "Yana son mulki ko baya so?" Lashe bakinsa yayi kafin ya ce mishi. "Baya son mulki a yadda na bincika zamansa a Amurka, an bashi matsayin shugaban asibitin ƙwaƙwalwa da yake Machigan amma bai amsa ba, an bashi matsayin da dama bai amsa ba. Abu daya yake faɗa shi ba a halicce shi don mulki ba, an halicce shi don ya fada soyayya da ƙwaƙwalwar mutane ne, kasan wannan matakin? Idan har mutum ya isa wannan matakin kada ka ce zaka tab'a mishi aikinsa da lissafinsa, a takaice duk wanda suke tare da shi ba sonsu yake ba domin yana zaune da sune domin haka suke son.ya zauna da su. Sai dai abu daya da na fahimta a rayuwarsa na yanxu da ta baya." Ya fada yana cizon lips dinsa a hankali kafin ya d'ago kai ya kalle su. "Mai Babbar daki da Matarsa wacce na rasa gane kansa amma cikin mata ukun nan akwai wacce matukar ka tab'a zaka iya mutuwa." Gyara zama suka yi tare da cewa. "Wacce a cikinsu?" Musamman Alhaji Mamman Abba yayari, yadda yayo maganar a zabure, "ko yar wajen Junaidu?" "Ba ita ce ba ce," "baturiyar?" Girgiza kai yayi. "Yar wurin Mardiya?" "Baffa ni ban san wacce yaƙe lissafi akanta ba, amma tabbas yar wajen Junaidu zai sake ta." "Tow dole mu san abin yi ba zai ja mana abin kunya ba, don sake yar gidan Junaid kamar sabawa Marigayi ne bayan ransa." Inji Mamman Abba yayari. "Ina ruwanka idan ya so ya sake ta, amma maganar gaskiya shine kawai ya saka baki na tsaya a takarar gwamna." Inji Alhaji Nuru Yayari. Nisa Alhaji Kabir Hammud Yayari yayi yana faɗin. "Ni kuwa sai nake ganin dole a binciko matar da yake so,.sannan dole idan har zai sake Yar Junaid. Ba haka kawai Attahiru Shehu Yayari zai saka ya auri yar Junaid ba. Zan binciko idan na su abinda yasa Junaid da Attahiru suka hada auren ba makawa Abba yayari zaka tsaya almana a madadinka na ubansa ya rabu da ita." "Kamar ya?" Inji Walid, gyara zama Alhaji Mamman Abba yayari yayi ya ce mishi. "Walid listn to me, Malam Junaid Gobir ana zargin yana da hannu a kisan Attahiru Shehu Yayari da Saddam Tanimu Jatau, kafin rasuwarsu Attahiru Shehu Yayari ya tabbatar min da Junaid zai bada yarshi ga Faris don Allah na saka a idanu akanshi." Mikewa Alhaji Kabiru Hamud Yayari yayi tare da Alhaji Nuru Yayari suka bar gidan suna masu ce mishi Allah ya bashi sa'a.
*
Shiru yayi yana sauraren Mai Babbar daki, ya rasa meke mishi dadi. Ya d'ago kai a hankali ya zuba mata idanun. "Ba don na isa ba, ba don na kai ba. Ki janye bukatarki na bada goyan baya ga siyasar nan don Allah ki min wannan Adalcin ki cire kanki!" Dariya tayi tana kallonshi tare da duba littafin da yake gabanta ta ce mishi. "Kasan me yasa na shiga?" Girgixa kai yayi yana gabanta yana kallon yadda take murmushi. "don kai na yi shi, domin ka ni na baka kalamai na na kuma gaya maka sai kayi nasara koda shine abinda zai kawo karshen rayuwata matukar zaka zama sarkin zanzibara dole na bada rayuwata." Taya zai gaya mata gundarin hatsarin da yake tattare da hukuncinta? Murmushin bakin ciki yayi ya ce mata. "Muna kuskure amma bama gane inda muka kuskuren sai dai wannan hukuncin ba shine daidai ba, kiyi nazari da kyau ki yi hangen nesa, You don't need to fight for me, ni ba yaron da aka sace ba ne, don Allah kada ki saka hayakin da zai fitar da na rami waje." Ya fada yana mai.......
08130269641
*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500N
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 33
Mikewa, ya nufi waje, juyawa yayi yana kallonta. "Ummina akwai hanyar da zamu iya tsallake shi, amma a wannan takin kowa niman wancan karagar yake, Rilwanu karami ne a cikin gidan Yayari, bana son na rasa ki kamar yadda na rasa Abbana." Ya fada yana barin parlourn, shiru tayi amma ina zuciyarta ta zarme da son yayi mulkin kuma ko yayya ne ba zata tab'a barin wani ya amshi kujeran danta. Kujeransa ne kuma zata bada dukkanin kome har da rayuwarta zata bada don ya rayu a ka.
***
Saimah Shaiba.

Kallon Iram take da take kwance cikin ruwa ta lumshe idanunta. "Wai meye matsalarki? Kin san ba zaki iya min kome ba, me yasa kika zo? Haka don Allah kin wani zo kin b'ata min rai. Beauty!" Turo kofar yarinyar tayi, daga ita sai bikini tare da wani mayafi da ta daura a kugunta. "Mommyna!" Mika mata hannu tayi ta sumbaci hannun, sannan ta zauna a gefenta tana sumbatar wuyarta zuwa fuskarta. "Beauty baki yi fushi ba?" Murmushi tayi ta ce mata. "Mommy kana fushi ne da abinda ba naka ba? Kana fushi da abinda yake mallakarka, ke kin sani fushina akanki ƙalilan ne!" Ta fada tana sumbatar bakinta zuwa goshinta. "Beauty!" "Mommy bari na nuna miki sabon idea din da na samu!" Tashi tayi ta fita can sai gata dauke da nutella, ta isa gaban Saimah, ta janye rigar wanka da ta saka ta fara shafa mata tana goga mata a jikinta har inda lissafin mai karatu zai tsaya, sannan ta koma ta ajiye kwalbar kafin ta fara bin ko ina tana lashewa kamar ta samu alewa, lumshe idanun tayi domin yarinyar ta kurewa kome nata lissafin, haka suka fada duniyar kazamai, tashi Iram tayi a buge ta bar dakin kayanta ta saka tana me barin gidan bakiɗaya.

Tuki take har ta isa, wani wawan horn tayi tare da tura kan motar cikin gidan bayan an wangale mata gate din ta shiga, kifa kanta tayi tasan Abbansu baya gari shi yasa take yin yadda take so, da yana gari ba bata isa ba. Sannan Abid da Nawwas da Yunus ko Nuraim suna tsoron Uwarta ba wai tsoron wani abu ba, yadda zata saka iyayensu mata a gaba yasa suke share batunta. Haka ta nufi cikin tana tangadi. Kallo daya Maluma ta mata da take tsakar gidan tana shan iska, ta kirata. Ba musu ta isa gaban Maluma kamar zata fada kanta ta ce mata. "Maluma kirana kike?" Wani irin d'aci ne ya ziyarci makoshin Maluma ta ce mata. "Iram!" Juyawa idanunta tayi ta ce mata. "Na'am." "Me yasa kika zabi wannan hanyar? Kin ga Yan uwanki maza na yin haka ne?" Lumshe idanunta tayi ta ce mata. "Basu yi saboda kina musu addu'a, ni kuma bani da mai min addu'a idan ba Abba ba ko kema Ikhlas kikewa Addu'a." Ta wuce tana faɗin. "Kowani tsuntsu kukan gidansu yake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login