Showing 96001 words to 99000 words out of 304445 words
ne, don har na haddace number shi, ina zaune ya kara kira amma baki dauka, bayan kamar minti goma sai ga Mai babbar daki, kuna wuta tayi ta ganni cikin bargo a dunkule. "Zainab!" D'ago kai nayi ina kallonta. "Tashi mu je can ki kwanta!" "Zan iya kwana a nan!" Na faɗa ina lumshe idanuna. "Tashi Yarana basu min musu, basu tab'a min ba!" Haka na mike, hular kaina ne ya zame ta kalli yadda na daure kalabar din kaina sai daya da na bari a gaban goshin yana reto. Wanda aka yi shi a gaban kaina. "Gobe mai kitso da lalle zata zo ta miki kina so?" Ta tambaye ni, sunkuyar da kai nayi ina bin bayanta. "Eh!" Dakinta muka wuce, ta nuna min babban royal bed dinta, a hankali na zauna fita tayi can sai gata dauke da tea mai zafi da sauran cake din da na bar mata. "Sha fushin ya isa haka!" Ta fada tana mai kwanciya a wani ƙaramin gadon, a hankali na karba ina sha ina jin kuka na zuwa min, duk yadda nake jin haushinta Matar nan tana kulawa da ni jin yadda nake shashekar kuka. "Idan kin gama kukan ki kira shi don yana can ya zama tazuje!" Share kwalla nayi na cigaba da shan tea din. Can naji tana sauke numfashi, kafin na duba wayar ina tunanin yadda zan kira shi sai ga kiranshi nan ya shigo min. Dauka nayi a hankali. "Kin ci wani abu?" "Eh na ci!" Ina jin yadda ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi kafin ya ce min. "Alhamdulillahi da akwai wani abu ne?" Girgixa kai nayi ina faɗin. "A'a!" "Kin yi kuka ne?" "Eh!" Yar dariya yayi a wayar ya ce min. "Baki iya karya ba ne don kare yawa?" "Ban iya ba!" Na faɗa ina kallon window dakin da muke ciki a hankali na mike n a kashe wutar dakin giftawar mutum na gani,a hankali na ce mishi. "Wani abu na gani." " Ina?" "Bayan window Mai Babbar daki!" "Da gaske?" "Zan maka karya ne?" "No ai nasan ba halinki ba ne, kawai ina mamakin yadda kika ga wani ne." "Shii!" Na ce mishi, saboda yadda na ga kamar mace ce tsirara haihuwar uwarta da ubanta. A hankali na isa wurin mai babbar daki na tashe ta, ina me saka hannu a bakina na nuna mata window dakinta. Kallona tayi ta rike hannuna a hankali ta kai ni bakin gadonta ta zauna da sannan ta min alama da na kwanta, ban daki ta wuce tawo alola sannan ta dauki abin sallah ta fara sallah, ta jima tana ibada kafin ta dauki Kur'anin tana karantawa, ai kasa barci nayi na sauka zuwa ban daki nayi alola nima, na haɗe da ita muka fara sallah, har wurin karfe uku saura ni kan tunda na kai wurin karfe biyu saura barci ya fara cin karfina, amma naki tashi, janyo pillow tayi ta ajiye min tare da min alamar na kwanta, haka na kwanta na cigaba da barcina, har wurin karfe hudu ta tashe ni muka yi raka'atul feejir sannan bayan mun idar muka ayi sallah asuba, sai da gari ya fara haske sannan na kwanta ita kan ban san kwanciyarta ba, amma ban farka ba sai karfe daya na rana, na bude idanuna ina kallon dakin. Mika nayi na sauka gadon na gyara sannan na shiga share ban dakin, sannan na wuce ban dakin na wanke, kafin ka fito na dauki wayata na nufi dakina, tana parlournta, zubewa nayi a hanya ina sosa kai. "Ba dai kina da kwarkwarah ba ki zuba min a daki." "Ni bani da kome!" "Who might know!" Ta fada tana karanta wani littafi, wayata ce ta sake kara na ɗauka. "Amma yau kin manta da kina da class ne?" "Wayyo Allah na, gani nan zuwa!" Na mike da gudu zuwa dakin wanka nayi na fito tare da saka kaya sama sama na shirya sannan na saka Jalbab na fito da sauri. "Zo ki karya." Ta nuna min abin karyawa zama nayi ina duba waya ina shan tea a gurguje, amsar wayar na ji anyi na duba Abdulhafiz. Zama yayi cikin girmamawa ya gaida Mai Babbar daki, ya ajiye wayar. "Ya Faris ya ce na zo na kaita makaranta." Ya kifa min wayar yana kallon inda nake ya ce min.."idan ana cin abinci, shi ɗaya za a ci don tsari ne na gidan nan." Sannan ya cigaba da tattaunawa da Mai Babbar daki, yana bata labarin abubuwan da suke faruwa. Tashi nayi na kwashe kayan na nufi kitchen domin na lura da kamar ranta ya b'aci sosai. Abinda ya gaya mata shine za a kwashe bayin da suke cikin bangaren za a mai da su can bangaren Rilwanu Yayari, cizon bakinta tai koda na fito, na samu ta saka medical glass dinta ne tana rubutu da Ajami, sannan ta ce mishi. "Ba zai yiwu ba, Salman kaɗai yake da hurumin sallamar kowa, don haka idan ka fita ka min magana da Salama ya zo ina son ganinsa, ka gaya mishi inji ni Mai Babbar daki!" Yadda ta fada da isa da kasaita, kawai sai na ji ta burge ni na kara kallon yadda take magana babu wasa a cikin lamarin. Fitowa nayi na durkusa a gabanta. "Na gama Ummi!" Jakanta da yake wurin ta nuna min da pen dinta ta ce min. "Dauki abinda zai miki!" Ya cigaba da abinda take, budewa nayi ma dauki dubu biyu!" Juyawa tai ta ga abinda ma dauka. "Ki kara!" A yadda take maganar yasa ni kara ɗaukar dubu ɗaya. "Hafiz zo ka ɗauka mata goma ka bata." Ba musu ya taso ya dauka ya mika min, kallon kudin nayi ya ce min. "Ki yi godiya ki tashi muje!" Yadda yayi maganar yasa ni, mata godiya sannan na bi bayanshi ina mata sallama.
Bayan fitarmu Salama ya zo ya amshi sakon da ta bashi, a yadda ya fita zaka gane Mai Babbar daki ta wanke shi sosai, karfe biyar na yamma na dawo, lokacin na fahimci mulki a jikin Mai Babbar daki yake, domin duk wasu manya fada sun taru a parlournta, lokacin da nayi sallama tana kishimgid'e, ita ta amsa min. "Kin dawo!" Gyada mata kai nayi ina me fadin. "Afwa Umminmu, ban san da baki ba." Hade rai tayi lokaci guda ta ce min. "Ki tafi bangaren Zainab kome naki yana can!" "Allah ya baki nasara! Wannan ba Yar gidan Junaid ba ce?" D'aga mishi hannu tayi idanunta yana kaina, "wuce!" Ta kara fada a hankali, da sauri na fita kamar zan fadi. Har na fita idanunta yana kan kofar ya ce mishi. "Sa'i Matar Salmanu Faris ce! Ba kodayaushe zata zama yar gidan Junaid Gobir ba, she's my daughter -inlaw." Shiru yayi yana faɗin.."Gaskiya ne!" "Allah ya baki lafiya da nisan kwana. Muna magana akan yarjejeniyar bayi!" Daukar kofin ruwa tayi ta sha a hankali, ta ce mishi. "Wanbai Abubakar Yayari bai tab'a zama sarki ba, Rilwanu bai da iko akan bayin gidan nan domin na Salmanu Faris ne." "Amma!" A hankali ta ciro wasu takardun ta ajiye musu tana faɗin.."Wannan document din ina da gomansu fiye da haka ma, sannan ina da su sun kai dubu a hannun lawyers dina zuwa kan wasu masu alaka da gwamnatin tarayya." Ta fada tana mai tab'a su tana bubuga takardun. "Amma Mai Babbar daki. Idan muka amince aka tabbatar da Salman a matsayin sabon Sarki kina ganin ba zai dawo ya tsige mu ba!" Gyara zama tayi tana faɗin. "Har yanzu ina nan a matsayin na magajiyar gidan nan. Domin domin na haifi Salmanu Faris, Abdullahi, Sulaimanu, sai me?" Babu suka yi kasa da kai. "Ai wato inda matsalar take shi ne, su Rilwanu suna tare da gwamnati, ita kuma gwamnati al'umma ce take zaɓenta saidai yanzu gwamnati bata dawo da abinda al'umma ta suke ba,.idan muka yi la'akari da yadda Marigayi suka so kafa gwamnati daga can gefe bayan suna rike da sarauta, haka kaɗai zai kauda Rilwanu Yayari."
Murmushi tayi tana kallon fuskarsu. "Tow a nime wani ya tsaya a jami'ar Saddam mana yadda zamu dawo da martabar gidan!" Duk suka zuba mata idanu murmushi tayi mai sanyi kafin ta ce. "Idan masu gaskiya dubu zasu mutum domin tabbatar da gaskiyar nan ba. Ba laifi bane don mun kashe marasa hujja domin kafa gaskiya a yi kome a tsanake" sosa giranta tayi tana mai kallonsu, fuskarta dauke da wani bahagon murmushi ta ce musu. "Idan ma fahimci wannan yar maganar ta fita. jingina tayi kafin ta sake murmushi ta ce musu. "Wani manomi yana da gona, amma sai aka yi rashin dace, sai aka samu wani ja'irin bera ya gayyato da sauran kananun dabbobin suna mishi barna, don haka ya rasa hanyar da zai bi domin.kare gonansa, sai ya zuba guba domin wadancan dabbobin, ai kuwa suna ci suka mutu, washi gari da manomi ya zo gona ya ga duk wasu masu mishi barna son mutu sai yayi hamdala, ya cigaba da nomarshi, har lokacin girbi yayi ya kwashe abincin." "In sha Allah ba zamu kasance bera ba, zamu kasance masu amana da nagarta!". Suka fada, murmushi tayi tana mai girgiza kai. "Ba barazana ba ce na gaya muku labarin ne don abinda xan iya aikatawa." A hankali suka fita, zama tayi ya daura daya akan daya,.har suka gama fita sannan ta zubawa kofar idanu, bayan kamar awa daya sai Rilwanu Yayari, wato Mai Babbar daki ta tsokano shi ne,.tana zaune kwanta kan daya tana kallonshi fuskarta dauke da murmushi. "Me kike nufi Maryam?" Yana bakin kofar parlourn amma don Bala'i faɗa yaƙe kamar zai shigo ya dake ta. "Kai daina haushi kamar ƙare!" Cak yayi shiru shigowa yayi ya tsaya a gabanta. "Me kike nufi?" "Ka sauka ka bar kujeran domin ba naka bane!" "Wallahi karya kike Maryamu!" Murmushi tayi tana faɗin. "Zaka sauka idan lokaci yayi, zaka sauka naka shiryawa kanka ba!" "Idan naki fa?" "Shi kenan! Sai na zama manomi da ja'irin bera!" "Ki yi a hankali da ni!" "Nima baka san wacece ni ba kayi a hankali da ni!" Ya juya fita a fusace, ajiyar zuciya ta sauke tana jin wani irin a ranta, ita fa bata jin a ranta tayi kuskure ko ɗaya.
Tunda na shiga bangarensu Ilham, nake zaune a parlourn duk da Mamanta ta ce na shiga ɗakinta na sauya kaya, yarinyar nan ta yi kici-kici ta hana ni, nima ban damu ba ana Magariba sai ga Sailuba da Wildat, "Barka da dawowa, ki zo inji mai babbar daki!" Mikewa nayi don ko abincin da aka kawo naki ci, haka muka fito zuwa bangaren Mai Babbar daki, a parlourn na same ta, tana sallah nima daki na wuce nayi wanka na sauya kaya sanan nayi sallah, abinci na ci ina kallon wayata. "Assalamualaikum! Ki zo inji mai babbar daki!" "Amin waalaikumunsalam, tow!" Na faɗa mata ina me fitowa zuwa parlourn, zama nayi a can gefe.."kin ci abinci?" "Eh!" Ta mai da hankalinta kan tv, "Mijinki ya kira ki?" "A'a ma fada mata ina kallon kasa kafin ta ce cigaba da cewa. "Gobe za a zo a miki lalle da kitso zaki koma dakinki." Ban ce mata kome ba, ta cigaba da cewa. "Idan kuma bakya son kitson sai a kai ki matan alfarma a miki gyaran gashi da jiki." Gabana ne ya fadi na ce mata.."A'a kawai ayi min kitson anan da lallen!" Na faɗa ina kallon kasa. " Ya karatun?" "Alhamdulillahi!" "Allah ya taimaka!" "Amin Ya Allah!"
Daga haka muka yi shiru, na gaji don haka na fara jin barci. Kwanciya nayi a parlourn, har wurin karfe tara da wayata ta fara ringing, idanuna cike da magagin barci n a dauka ina faɗin. "Waye?" "Mutum ne!" Komawa xan yi na kwanta, na ce. "Tow sannu!" Na kwanta ina kara jin barci. "Barci kike ne?" "Eh!" Na faɗa, "A ina ?" "A parlourn" "ina Ummina!" "Gata nan!" "Mh!" "Shi kenan." Ya fada tare da cewa. "Baki bukatar wani abu?" "A'a na fada ina yada wayar domin barci nake ji, magana ya cigaba da yi ina amsa mishi sama-sama, karshe Mai Babbar daki ta, taso tare da ɗaukar wayar ta ce mishi. "Kayi focus abinda yake gabanka, na gaya maka wallahi ba zaka janyo min biyu babu ba." Ta fada tana kashe wayar, yadda na cigaba da barci a parlourn itama a nan ta zauna tare da saka Sailuba ta kwaso mata wasu takardun da ta cigaba da aiki. Ban farka ba sai wurin karfe uku na dare shima fitsari ya tashe ni, na ganta zaune tana duba wasu takardun ga abin sallah nan a gefenta. Lumshe idanuna nayi na nufi ban daki nayi fitsari na fito na kwanta, washi gari babu makaranta kawai na tsafe kaina kenan sai ga Hajiya Mardiya, tunda ta ganni, ta hade rai ni kuwa na dauke kai a kanta can mun fara lallen sai ga Ijlal lokacin ita Hajiya Mardiya tana dakin mai babbar daki suna magana, wanda ban san me suke yi ba. Tana shigowa kuwa ta ganni ana min lallen, daya na min kitso. "Shishigi." Murmushi nayi nace mata. "Haka dai kika gani amma ni ai Uwar miji ta gama min kome, babu wacce zata samu irin gatar da na samu." Ai kuwa ta shiga zagina tare da d'aga murya, kin kulata nayi Hajiya Mardiya suka fito da mai babbar daki, ganin yadda Ijlal take zagina ban tanka mata ba, Hajiya Mardiya ta ce mata. "Ke bana son shirme me ya haɗa ku?" "Kawai ban kulata ba ta zage ni." Inji ta wai na zage ta. Mai lallen da mai kitson basu san alakarmu ba amma suka ce mata. "Kai baiwar Allah ki ji tsoron Allah, ke kike fara da fada mata shishigi ita ma kuma ta rama." "To amma ai Ikhlas kece Babba bai dace ki rama ba?" "Akan me ba zata rama ba? Itama Ijlal me yasa bata zauna a matsayinta na karama ba? Mardiya kin san abinda yake gabana ko? Tow idan wani abu ya zo mara daɗi dukkanmu zamu ji a jikinmu. Ke Ikhlas ba sa'arki ba ce, ke kuma Ikhlas ki yi hakuri da rayuwa." Inji Mai Babbar daki, ganin yadda mai babbar daki bata goyi bayansu ba, sai Ijlal ta shiga fushi da wani kunkuni, wata Uwar tsawa Mai babbar daki ta daka mata sai da muka razana........ *Maneji Please 🥺*
08130269641
*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500N
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: "Me kika ce?" Girgiza kai tayi, ni da nake zaune sai da na fara ƙoƙarin mikewa domin Mai Babbar daki tana iya sakaka fitsari baka sani ba, "koma ki zauna ba dake nake ba." Ta fada min zama nayi, itama Ijlal ɗin dauke ta da mari Hajiya Mardiya tayi tana faɗin. "Hauka kike da zaki saka mai babbar daki d'aga murya? Maza durkusa ki bata hakuri." Ba musu haka ta bata hakuri, ta nuna mata ni. "Ko bata auren Faris ita ba sa'arki ba ce, Amrah ce sa'arta don har tabawa Amrah wata uku , don haka kada reni ya shiga tsakaninku, idan zaku yi kishinku. Kuyi a can ba a gabana ba." Ta fada tana barin parlourn, haka suka bita dakinta.
"Kin yi sa'a Uwar miji tana sonki!" Yake nayi ina kallon lallena. Sai karfe daya aka gama kitson uku da arba'in na cire lallen muka yi sallah da cin abinci,.sannan na wuce na zauna suka zana min bakin lalle mai kyau, lokacin da mai babbar daki ta fito da Hajiya Mardiya, kallona tayi sau daya ta cewa Hajiya Mardiya. "Bata son Faris amma duk da haka bata barshi ya tafi can Abuja haka ba, sai da ta nima mishi abinda zai ci kafin ya karya ita, Nady bata da wannan lissafin amma ita Ijlal da take nawa me yasa bata nima mishi abinda zai ci ba? Kishin miji ba a baki ba ne, a aikace ake yi haka kiyayyar juna ba a idanun da baki bane abu ne da suke aiki da zuciya da ƙwaƙwalwa." Sannan ta koma daki bata kuma fitowa ba. Masu min lallen da gulma sai kallon Ijlal da suka yi mutuwar tsaye suka yi a wurin, ni dai kunya ta kama ni, haka kawai sai nake jin kamar ban kyauta ba yadda nayi ta cewa bana sonshi. Eh bana sonshi amma kuma sai yau naji kamar nayi kuskure, fadar bana sonshi? Haka yasa na ki yarda na kalle su. Har suka fita Ijlal ta ce. "Malaman addinin sun koma malaman tsubu!" Uwar goyanta ta ce mata. "Ko yawo suke tsirara sai ta bar miki Faris damu kuke!" Duk muna jinsu. Babu wanda ya tanka musu. "Allah ya kyauta gaskiya ya kamata ki so mijin nan, yadda na ga yarinyar nan da Uwarta ba zasu zauna a haka ba. Kuma ya dace iyayenmu su tashi akanki." Murmushi nayi nace mata. "Allah yana kaina babu me iya cutar dani!"
Haka suka gama lalle mai babbar daki ta basu kudi me yawa, nima saboda lallen ya min kyau na tura musu kudi ta account, bayan sallah isha ina cin dankalin turawa, ta ce sailuba ta kira ni. Haka ta tashi na nufi wurinta, sai da na kai flat kitchen sannan na wanke hannuna, na tafi wurinta. Zama nayi a gabanta ina wasa da yatsuna. "Babu inda yake miki ciwo?" Gyada kai nayi, "Good!" Tayi shiru kafin ta ce min. "Zaki koma dakinki ne, amma ina da sharadi!" D'ago kai nayi na kalleta. Gyara zaman glass dinta tayi tana kallona ta ciki. "Bakya son zama da shi ko?" Da sauri na d'ago kai. Gabana yana faduwa ba dai zata ce ya sake ni ba ne? Sake kallonta nayi jiki a mace. "Ban yarda ki yi fada da kowacce mace ta gidan ba, idan aka kawo min karar kun yi fada