Showing 117001 words to 120000 words out of 304445 words
"Sai dai ki rena iyayenki, na san darajar iyayena!" Wani irin abu naji ya tsaya min a rai, sannan na zare hannuna cikin nashi. "Na gode! Ba zan rena su ba, kuma na zan yarda ka ci zarafinsu ba,na godewa Allah da bana jin kome akanka balle haka ya dame ni." Na juya na barshi a nan, har dare bai ci kome ba, ina kitchen ya shigo ya samu na dafa indomie, dauka yayi nayi maza na zubar da shi a kasa. Sannan na bi ta kai na wuce. Mikewa yayi ya zuba min idanu. "Abinci kika wulakanta?" Ai shiru ma magana ce kwashe abincin nayi na azuba a bola, sannan na dauki kayan kwadayi a firji na barshi a nan tsaye, shi kuma ya kunna gas yayi girki yana ganin kiwuya ce, dawowa daki nayi na ci na kwana, washi gari sai ga Ya Nuraim da kayan abinci, daidai zai fita suka hadu suka kuwa gaisa sannan ya fita. Ni kuwa don murna na rasa in zan saka shi, ruwa ya sha ya bar gidan. Wurin karfe biyu na rana sai ga cefane, kwandon timatur uku, haka buhun tattasai da atttarabu uku uku sai albasa kai hatta ledar daure tuwo sai da ya saya ban da doya da dankalin, madara da cadbury kowa kantan kantan Nadiya aka fara kira ta dauka sannan aka kirani da Ijlal muka dauka, a hankali na kalli kayan nace mishi. "Allah ya kara budi ya rufa asiri duniya da lahira, Ubangiji ya jikan magabata, ya karawa Mai Babbar daki lafiya da nisan kwana. Mun gode sosai Allah ya kara budi" Yadda ya sake baki yana kallona ba iya shi ba hatta matansa sai na wuce abina Ai kuwa Ijlal ta ce min. "Munafuncin wannan ai hakkinmu ne kuma dole ya bamu uwar niman suna," Faruq ya saka ya kai mana kowa kitchen ina jinta bani da lokacinta a kitchen Faruq ya ce min. "Kiyi hakuri wallahi Oga yana ganin girmanki da na iyayenki balle kuma yau kin mishi addu'a koyi hakuri da shi don Allah!" Yana fadar haka ya bar kitchen din, wato kowa yana fahimtar wani abu idan nayi mishi . karfe bakwai na dare aka shigo da namar saniya da rago, kowacce an yanka mata yadda zata yi amfani da shi aka ajiye mana, ni aka fara kira na dauka yana saurare na ce mishi. "Allah ya biya da gidan Aljanna, Ubangiji ya kara maka lafiya da nisan kwana, mun gode da ciyar damu da kake Allah ya albarkaci nimanka da samunka ya raba ka da Haram kome girmansa." "Amin Ya Allah!" Ya fada yana kallon yadda nake kokarin daukar nawa, shi ya mike ya daukar min ya kai kitchen, sannan ya saka aka kira sauran matan. "Kuna da bukatar kifi ne?" "Ni ina da shi, Abba ya kawo min sai dai su." "Eh ina bukata!" Inji Ijlal, "Nady!" "Ban ciki da munafunci, nan aka kawo kaya dazun baka daukawa kowa ba amma ita ka ɗauka mata har zuwa kitchen dinta don ka saka munafunci a ranka, sannan akwai wacce Chef da na dauka zata na zuwa tana min girkin bude baki da na sadaka. " "Hmm!" Ya ce Ijlal ma ta ce mishi. "Nima za a kawo min masu taya aiki har mutum biyu." Kallona yayi, "Ke fa?" "Ka tambayi Mai Babbar daki duk abinda ta ce shi kenan!" Na faɗa mishi ina mai kokarin barin parlourn, kamar yana son na zauna ganin xan wuce ya ce min. "Ki dawo muyi magana bakiɗaya." Komawa nayi na zauna, shiru nayi ina jin shi, can ya ce mana. "Ina son nayi rabon azumi tuntuni naso haka don har mun gama da Mai Babbar daki, amma ta ce na tuntube ku! Ya kuka ni?" Kallonshi nayi ina jiran su fadi abinda ya dace. "Ina ga ka bawa kowa ta kai family dinta tunda suna da mabukata!" Inji Nady,
"Ni kudin nake so a bani zan raba musu!" Inji Ijlal!, zuba min idanu yayi kafin ya ce min. "Zainab me kika ce?" Gyara zama nayi, na ce mishi. "Kafin mu mika ga danginmu, mu fara duba na kusa da mu. Akwai nayi da suke gidan nan bakiɗaya, maza da mata wasu basu cikin gidan nan, a raba musu, har na wajen raba musu, sannan a dauki mota a bi kowani massalaci idan an idar da sallah a rabawa mabukata, akwai makota a bayan fada a raba musu, sannan sai a dawo kan dangi, akwai dangin mai Babbar daki a Maiduguri da garin Farar kasa, a tura musu, akwai yan uwan Baba marigayi a bisu." "Ai suna da kudi karawa mai karfi karfi ne. "Ba dake take ba, da ni take." "Yawwa idan aka bawa dangi da makota mabukata, sai a bi kowa a bata abinda take buƙata."
Gyada kai yayi ya ce min. "Kina ganin idan aka saka like 10k a cikin kowani abu ya wadatar?" "Ba iya wadatarwa ba, hatta adalci kayiwa talakawan da suke tare da Baba lokacin yana raye. Sannan kayi musu abinda baa tab'ayi ba." "Duk da lokaci ya kure kina ganin gobe ya dace a fara kome?" "A niman lahira ba a tab'a lokaci,sai dai a jima ba akai ba." "Shi kenan akwai kaji daga gidan gona za a kawo muku gobe, ya batun abincin sadaka ina son na daurawa mutum daya ce." Mikewa nayi zan bar parlour ya ce min. "Dawo bamu gama ba." "Amma ka shirya cutarmu ne tunda gashi nan kana kokarin bawa mutum daya abincin sadaka." Kallon Ijlal yayi da tayi maganar, ya juya ga Nadiya. "Eh gaskiya ne, idan adalci ne a bawa kowacce ranar girkinta." Ina jin su, ya ce musu. "Shi kenan ranar da kowacce take da girki zata yi na kwana biyu, sannan ba zan dauki kuskure da batun lokaci ya kure, akwai babban kitchen wanda kofarshi yake ta wancan koridon," wato koridona da Nady, sannan ya kara da cewa. "Zaku iya aikin sadakar a can don kitchen ne na aikin haɗaka!" Ya fada yana kallonmu bakiɗaya. "Zan tafi na kwanta" na fada mishi ina kokarin barin parlourn. "Shi kenan!" Ya ce min, da sauri na barsu suna ta mota. Kitchen na nufa na bude namar na shiga kulawa a leda, ina kirga na wata gudu, domin a yanayin namar na fahimci har da na sadaka, sai ma ware na ragon. "Kizo yana kiranki!" Inji Ijlal, tashi nayi na tsaya a bayan kujera. "Gani nan!" "Dama akan abincin da za'a na kaiwa cikin gida ne! Shima zaku saka a cikin girkin ne?" "Duk yadda kace!" Na faɗa ina jiran Ansar shi. "Kina ganin haka babu takura don sun ce aiki zai masu yawa?" "Ba kome zan gwada!" Na faɗa ina me barin parlourn sannan na koma na zuba kome namar ragon na jera a firji na daban. Haka saniyar na sakata, sannan na dauko takarda da biro na rubuta kowanne." Kayan miyar ma a daren na baza wasu. Shigowa yayi ya ga ina juye timatur din a buhu ga tattasai ma haka, juyewa yayi yana mai cewa. "Ba wani sauran abinci ne?" Kallonshi nayi don yana bani mamaki. "Akwai!" Na ce ina mai nufar kan gas din, tuwon da nayi jiya ita na ciro a firji na dumama mishi ya zauna a kujeran parlourn yaci har yana niman kari na jure mishi sauran." "Me zaki yi mana, na sahur." "Sakwara miyar ridi!" Na cigaba da aikina. "Har dani!" "Eh!"
*Account Details:*
*08130269641"
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500N
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 38
Na bashi amsa sannan na cigaba da aikina, "Ni dai Allah sai ya saka min cin amanar da ake min!" Inji Nady da take tsaye, tana ganinshi yana cin abincin. "Ikhlas wallahi ki fita idanuna!" "Abinci da yazo ya ci!" Kuma sai na hana shi ai haka ba adalci ba ne shi yasa na bashi amma kiyi hakuri na miki kuskure don Allah ki yi hakuri." Na faɗa ina cigaba da aikina, shima gulmammen sai da ya cinye abincin tas ya koma dakinta, ban san me ya faru ba sai dai ta dawo ta samu na rufe kofar kitchen din ina dakina sallama tayi na amsa mata ina mai fitowa parlourn. "Dama maganar nan ne na dawo mu, Babankin ya dawo?" "Eh ya dawo! Zauna mana!" Na nuna mata wuri ta zauna. "Ikhlas na je asibiti, sun gaya min bai zama dole na samu haihuwa ba, chance din da nake da shi bai wuce only 1% ba, shine nake son ya zo muje ayi mana dabarar da ake yi mutumin nan yaki ko zaki hada ni da Babanki ne ya taimaka min?". Shiru nayi tabbas bani mantawa akwai wata Aunty Hawwa'u a maradi da ta tab'a zuwa tana kuka ta gayawa Abba rashin mutuncin da ake mata saboda rashin haihuwa dariya ya mata, ya fara bata rubutun tsawon wata uku, da wani itacce sai gashi ko wata biyi bata yi ba, sai ga ciki, tana haihuwa aka samu namiji shine aka saka sunan Abba, suna kiranshi Imam. "Baki ce kome ba, ki yi hakuri zan gaya mishi sai naji me zai ce." Daga haka ta mike tana faɗin. "Na gode sosai! Sai da safe." "Allah ya tashe mu lafiya!" Tana fita na yi shiru me yasa take son haihuwa da shi ne haka? Tab'e bakina nayi, na shiga daki na kira Abba na gaya mishi, ya ce ba zai yiwu daga baya ace an mata asiri ko wani abu ba, ya ce idan tana bukatar taimakon shi ta gaya Mijinta, kuma sai naga wautar amsa mata, na kwanta da karfe uku na tashi na daura abincin sahur, da yake ina da abin sakwara shi na daka mana, ina gamawa na malmala, jin ana buga kofar gidan parlourn har na ji motsinsa yasa ma cigaba da aiki maybe Faruq. Haka kuwa aka yi Faruq ne ya zo amsar abinci ina ga shi ya kira shi, ina gamawa na fito mishi da nashi, na mikawa mishi sannan na wuce na ajiye nashi a dinner room, sannan na wuce kitchen na hada tea nazo na wuce, ina ga shi da Nady ne domin ina jin maganarta sama-sama, kuma kamar fada suke. Abincin nake ci har aka kusan kiran sallah, sai gata nan ta shigo shima kamar ya biyo bayanta ne, don yana tare ta tana fisga ta shigo min. "Ikhlas na ci mutuncinki don Allah? Ba niman taimako nazo ba?" Yadda yake janta tana faɗin. "Na ce kazo muje asibiti ka ce ba zaka ba, Salmanu Faris dama Wannan shine kyautatawarka a gare ni kenan?" Saka hannu tayi ta rufe fuskarta, tare da fashewa da kuka, ba karamin tausayi ta bani ba. "Idan ya amince gobe sai na ajiye ki a gidan na wuce school!" Janta yayi ya rungume ta, sai kuka take tana yi tana karawa. Dai suka bar min parlourn, bayan sun narkan min da zuciya da tausayinta. Washi gari na shirya da zan fita ita ta dauke ni a motarta don daga yadda ta zo ta zauna jirana na fahimci har an shirya kuma tayi shigar arziki babu gashi a waje, tun kafin mu iso na kira Abba na gaya mishi, haka na kaita har cikin parlourn Umma sannan na kaita na Maluma, ganin gidanmu yasa tayi ta mamaki ashe nima dai Iyayena a tsaye suke da kafaffunsu, ba kwadayi yasa na auri Mijinta ba, don ko motocin gidan da ta gani sai tayi shiru, motar Mommy Turai ta gani ta ce min. "Wannan motar gidanku ce?" "Eh!" Bata ce kome ba, ta bi bayana na kaita cikin gidan, sannan na kuma kaita wurin Maluma, suka gaisa. Shiga bangaren Mommy Turai nayi na gaishe ta alamar zata fita kenan, Tauhid na gani yana game da sassafe nace mishi. "Zo kayi dropping dina makaranta?" "Zaki bani 20k!" "Mayen kuɗi!" "Na ji!" Haka kuwa muka fita da shi ya ajiye ni a school, ita kan ban san yadda suka kare ba, ina makaranta mun fito exam Umma ta kira ni take gaya min ai shima ya zo, da kayan azumi. Bayan tafiyar Matarshi. Shiru nayi na rasa ta cewa.
Karfe daya muka taso, Faruq na gani na zata shi ɗaya ne na shiga nufi motar a matuƙar gajiye. "Sannu ya exam?" "Alhamdulillahi!" Na faɗa ina shiga motar ganinsa zaune ya sani kamewa, muka bar makarantar, koda muka isa gidan aiki na kama ba wasa, sallah nayi na ga ya kawo kaji, rabawa nayi na zuba kowane daban-daban sannan na shiga aikina. Lissafina gobe zai bar dakin Nady Allah yasa ba dakina zai ce zai dawo ba, ni dai ban shirya karban shi ba wallahi.
Da la'asar me aikin Nadiya tazo suka fara aiki, duk da ita Uwar matan tana kwance, a harabar kitchen din da babbar taburma, matan tana da masu aiki har uku sune suke kaiwa da komowa. Kafin karfe shida sun gama kome har an fitar da na sadaka, sannan aka kawo gidan bakiɗaya, bayan an sha ruwa muka yi bude baki gaba daya a wurin, wani ikon Allah girkin yayi dad'i yayi kyau don matar ta san hannunta, sannan irin wannan lokacin koya ake ba zama ake ba duk wani abin da bai min ba, sai ta koya daga birnin farko na Nady, an kaiwa Mai Babbar daki, bayan isha nake gayawa Yeemar me ya dace nayiwa Mai Babbar daki. Turo min bayani tayi ce mata nawa zai isa? Ta ce min dubu dari biyu yayi, na tura mata har yau wancan Dracula bai daina turo min kudi ba, haka yasa Nima nake tab'awa last sakonshi ya ce min. _Ki ci abinda na turo miki! Halak Malak din ce kin cancanci sama da haka! Flower_ haka yasa na hadawa Mai Babbar daki kayan shan ruwa.
Ko shi ban gaya mishi ba, sannan ta kara kirana ta ce na tura mata wasu kudin na tura mata, Yeemar akwai taya bera barna. Bayan sallah tarawee sai gashi ya shigo min, yana kallona ganin na dauke kai ya ce min. "Gobe zaki karbi girkin ne?" Kallonshi nayi na kauda kai nace in sha Allah. Gyada kai yayi ya ce min. "Sailuba da Wildat zasu zo da sassafe na gaya mata kina exam ne." "Allah ya kai mu!" Na faɗa ina cigaba da aiki chat. Har zai fita na ce mishi. "Allah ya kara budi! Nagode" "Amin Ya Allah!" Sannan ya fita, yadda yayi min bazata shima haka xan mishi bazata. Ai kuwa a daren muka gama kome da Yeemar, da sassafe bayan an fita massalaci sai gasu Sailuba da Wildat, suka taya ni aikin gidan muka fitar da aikin doya suka gyara, aka dafa aka kwaso zuwa kitchen anan kafin na yi wanka sun gyara min kayan miya an zuba wasu a firji an gyara na markade, Sailuba ta dauka ta fita da shi waje na bata key mota ta saka min, sannan ta dawo na cire Nama kala uku daya ba miya daya na abinci, sai kaza kayan cikin saniya da zan yi farfesunsa. Sannan muka gyara kome, na saka turaren wuta a parlourn. Muka rufe ko ina muka fita, sai da na ajiye ta a cikin gida sannan na bata dubu kudin markade nace mata. "Idan na dawo zan shigo!" "Tow ki dawo lafiya, zan tafasa miki kafin ki dawo!" "Na gode sosai kin rage mana aiki!" Na mika musu key idan na wuce karfe daya ku tafi ku yanka doyar kawai ina zuwa sai suya." "Tow shi kenan!" Suna fita na ja motata, tana shiga ta ajiye sakon ta gaida Mai Babbar daki ta gaya mata aikin da suka yi. "Kin ga wani abu sabo a tattare da ita?" "A'a Mai Babbar daki, bata yi kome ba tana da kirki!" Yanayin fuskarta ya amshi yabon amma bata irin nuna ya burge ta ba. A injin din cikin gidan aka yi markade.
Wani ikon Allah yau karfe daya saura muka fito, sallah nayi na samu Yeemar tana faɗin. "Ga sakonki a muje na saka miki a motarki!" "Muje!" Ina zuwa wurin motar na samu a dankare da kaya har da turmin atamfa lafayya, lace, "Yeemar wannan kayan fa?" "Kin huta sayan kayan sallah Ramadan basket kenan." Ajiyar zuciya na sauke ina kallonta, sannan ta saka min a cikin motar, kome anyi parking dinsa a basket. "Na gode Bestie! Allah ya nuna min bikinki da Yazid naci Uwar sabada!" "Shegiya kamar da gaske don wallahi cashewa zamu yi!" "Sosai biki zamu yi!" "Yawwa a cikin azumin nan zasu tambaya fa!" "Don Allah?" Na tambaye ta, "Allah da gaske! Na gama shiri tsaf ni mijina ba zan d'ago mishi kafa ba a daren farko!" "An shiga uku muna azumi Yeemar sai an jima!" Rike hannuna tayi tana faɗin. "Ba dai har yanzu babu wani abu a tsakaninki da Prince ba?" "Yeemar ki bar maganar nan ba zai yiwu ba," "akan me? Ikhlas Allah yana ganinki fa!" Shiru nayi kawai ina jinta. "Matansa babu abinda basu iya na karuwanci ba. Me zan yi mishi sabo da zai burge shi? Kawai mu bar zancen." "Ikhlas kika kishin Mijinki ne?" Ware nayi ina rufe kofar motar. "A ina kika ga kishinshi?" "Wallahi kina kishi kalamanki yayi kama da mai kishi, idan Matanshi suna mishi ke ya miki mana, ki cire son rai ki bawa Mijinki damar baje soyayyar shi da ke." Shiga motata nayi ina faɗin. "Daga yau sai bayan sallah in sha Allah!" Na ja motatta zan tafi nace mata. "Zan gayawa Abba maganar saka ranar." "Ba shi nake magana ba, rayuwarki nake magana ai!" "Ke kauce!" Na ja motar a guje, sai da shiga gidan mai ina bin layi ashe a ganana motar Uwais ne, sai da na tashi biyan kudin akace an biya min da mamaki na ja motana, zan tafi na hango yana tsayar da ni. Tsayawa nayi ya zo muka gaisa n ace mishi.."ba dai kai ka biya kudin man nan ba?" Murmushi yayi ya