Showing 72001 words to 75000 words out of 304445 words

Chapter 25 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

41

na fito daure da towel. Hango ledar pad din nayi ina mamakin yadda aka yi ya kwaso min kayan abu kamar na matan duniyar nan aka daura min. Nasan wannan ba aika na bane......
*Wash......*
*ina mata yan gayu ina mata yan yayi! Tow ku matso nesa ta zo kusa collaboration Tangaza_Perfume tare da Anum∆Luxury Perfume sun zo muku da kayan kamshi gida da na jiki kai ba iya nan ba hatta turaren kaya irinsu.*
Mamoul all colors are back in stock. Mamoul turaren turara kaya. Ga kamshi ga kama kaya da gida. Available in;
MAMAOUL MADINA,
MAMAOUL MARYAM,
MAMOUL BADAR &
MAMAOUL SABAYA. Each one 3500

*New Drop!*
*Nassem Oil – 100ml*
Rich, elegant & long-lasting.
This premium fragrance oil is everything your collection needs — and it’s only *₦9000!*

*Luxury in a bottle.*
| Own Your Scent, Own the Room*

*Mosuf 50ml Body Spray*
Smooth. Fresh. Long-lasting.
Only *₦5000!*
✨💥
Smell amazing, every single day.
*DM to order!*

*Storm for Him & Her – ₦4,500* each
Fresh, fierce, and made to turn heads.
Whether it’s *Storm for Him* or *Storm for Her*, you’re getting bold confidence in a bottle — just *₦4,500!*

A perfect 50ml to carry your essence wherever you go. Subtle. Powerful. Unforgettable.
Now available: ₦2,300 per piece | ₦27,600 per dozen.
Available Just DM
08130269641

Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book.


*Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu ƙayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:*


*MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya haɗa da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.*

*AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen ɗin Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen*

*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*

*POSTING*
*Ɗaya: 500*
*Biyu: 1000*
*Uku: 1500*

*DOCUMENT (da zaran an gama posting zai koma)*
*Ɗaya: 1k*
*Biyu: 2k*
*Uku: 3k*

domin tura shaidar biya ko Ƙarin bayani, ku tuntuɓi:
*08130269641*
Ko
*08137311900*
Ko kuma
*09063467258*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: Bayan na gyara jikina, kaya mara nauyi na saka ina kallon kaina a gaban madubi duk nayi wani zuru -zuru, sai dan karan hancina da ya fito idanuna sun dan fada. A hankali na tashi na nufi wurin wayata na ɗauka tare da kunnata nayi, ina jin bakina babu dad'i, layin Abba na kira. Sai da ya kusan tsinkewa ya ɗauka. "Ina jin ki!" Jan hanci na fara kamar zan yi kuka. "Abba ba ni da lafiya?" Ina jin ƙaran taka birkinsa kafin ya ce min. "Ya Salam, ciwon cikin ko? Yaushe kika fara ko yanzu ne? Ina Yarima Faris yake?" Iyayena sun san wahalar da nake sha, wani lokaci amma kuma idan aka min allura bai zama dole wani lokacin na sake ciwon ba. Kamar yana gabana na gyad'a kai ina shashekar kuka, ina son na wanke wancan laifin ne. "Abba ka ce ya kawo ni gida!" Na faɗa ina kara fashe da kuka. "Amma kin san haka ba mai yiwuwa ba ne, Allah ya baki lafiya." Daga haka ya kashe wayar da alamu har yanzu yana fushi da ni ne, sai da nayi kuka me isata sannan na mike na nufi waje, a hankali nake takawa domin har lokacin ban daina jin ciwon cikin ba, yadda nake tafiya yasa ban san da mutum a parlourn ba, "Barkanki Gimbiya Zainab!" Ji nayi kamar zuciyata zata fado nayi da baya tare da riko kirjina. "Kin bani tsoro! Wace ce ke?" Na tambaye ta ina yin baya. "An turo ni ne na tayaki aiki, baki da lafiya." Shiru nayi kafin na juya ina kallon parlourn da yake wani irin karni karni,.ina ga aman da nayi ne duk da ta share ta goge. "Na gode sosai! Amma ki koma xan iya kome da kaina." Na faɗa ina jiranta tafi, fitowa tayi ta tsaya a kofar parlourn ni kuma na shiga kitchen, Daura ruwa nayi a gas na dauki bokitin mopping stick na zuba ruwa na dauka tare da zuba guntun omo, na fita da shi parlourn ban dakina, na nufa na dauko dettol na zo na zuba sannan na fara goge parlourn har zuwa dakina, ina gamawa na koma kitchen na yi na nan ma, kafin na dawo na saka turaren wuta, da roomfresh, sannan na koma kitchen har lokacin tana tsaye a bakin kofar, tea na dafa na zuba a flask, sai kwai da na soya da vegetables na juye sannan na nufi parlourna, kallon yarinyar nayi. Ajiye kayan nayi na koma na nimo cup, na kawo zan zuba mata. Sai gashi ya shigo da ita a bayanshi. Yadda yake kallona yasa na haɗe rai, na zuba mata tea din na yanka mata soyayyen kwai din nace mata. "Babu inda ake sayar da bread anan kusa ne?" Ina kallonta. "A'a gimbiya sai dai a siyo miki!" Ta fada min tare da zama kamar wata me rokon gafara. "Dama kece zaki ci da shi, na kawo miki kudi ki sayo!" "Allah ya taimake ki kamar yadda kike taimakon na kasa dake, gaba da fada ne zan sayo miki ko da ba zan shaki kamshinsa ba." "Kin ga tashi, ni bana son irin wannan abin Allah ake yiwa biyayya ba mutum irina ba, kin ji kada ki kara min irin wannan zaman." "Allah ya jikanki ba don kin mutu ba, haka a haife ni domin nayi miki biyayya." Wucewa daki nayi na dauko duhu daya na mika mata. "Ta dubu daya zata ishe ki?" "Allah ya baki nasara tayiwa baiwa irina yawa."
"Ki sayi na yadda zai miki, sai ki rike canjin." Na fada mata ina komawa na zauna na fara karyawa, duk abinda muke yana jin mu. Juyawar da zan yi na ga cup din tea a hannunsa. Kamar zan yi kuka ya fara kurba. "Ni dai a daina tab'a min abina!" Na faɗa ina hararanshi tare da tura baki. Wayarshi ce tayi ƙara. Dauka yayi ya saka a kunne. "Eh gata nan!" Ya ajiye min wayar akan cinyata. "Malam Junaid!" Na gani. Ina dauka nace "Abbana!" "Ya jikinki? Ya ce ya miki allura?" "Kambu!" Na furta ina kallonshi sai kuma na tuna da Abba nake waya. "Me kika ce?" Rufe bakina nayi nace mishi"wayyo abu na bari akan gas ya fara konewa ina zuwa Abba!" Na shiga bubuga plat din gabana. Kafin na ce mishi. "Abba!" "Na'am kin kashe gas din?" Murmushi nayi nace mishi. "Eh Abba, dama maganar makaranta na ne yaushe zan koma? Ana ta karatu an bar ni a baya."
Shiru yayi kafin ya ce min. "Kin ga baki da lafiya, sannan bani zaki tambaya ba Mijinki zaki tambaya Allah ya sawwaka." "Abba tow idan ya ce ba zan koma ba fa?" "Ki roke shi, zai barki." "Abba roko kuma?" Na faɗa ina kunkuni tare da faɗin. "Sai kace mabaraciya!" "Me kika ce?" "Shi kenan zan roke shi." Na faɗa ina jin.kamar zan yi kuka na kashe wayar ina tura mishi wayar.."sai dai ka hakura da karatun kawai! Akan me a same ka da abinka a ce za ayi maka mulkin mallaka, don an ga bani da gata." Na faɗa ina sake zuba ruwan tea din ashe jira yake na zuba ya dauko wuf. Hawaye ne ya cika idanuna.."sai ka cinye sai ka haɗa ka cinye ai." Na tashi na barshi a wurin. Shi kan cinyewa yayi abinsa, haka na zauna cikin haushi da takaici har yarinyar ta dawo ta karya, ta iso bakin kofar dakina tana mai bugawa ina budewa ta mika min, yawu ne ya taru a bakina, juyawa nayi na zubar a ban daki, na ce mata. "Lafiya baki tafi ba ne?" Don bana son magana. "Dama mai martaba sarkin gobe ne ya sa na mika miki wannan!" Amsa nayi, tab'e baki nayi na duba rubutun yayi kyau, hade rai nayi ka karanta abinda ya rubuta.
*Zaki iya komawa idan kin so!* Murmushi baki nayi ina hararan takardan. Sallamarta nayi na ce mata. "Ba sai kin kara zuwa ba! Na gode sosai!" Na duba dakin babu kome sai kayan kwalliya da wata hijab dina,.shi na hada na bata da dubu biyu. Zubewa tayi kasa kamar zata yi kuka ta ce min. "Allah ya baki nasara ni fa an turo ni na miki leken asiri ne, sannan idan na tafi ban san waye za a kuma turo shi ba, kyautatta min da kika yi yasa ba zan iya cutar da ke ba, sannan mai martaba sarkin gobe ya gano cewa nima turo ni aka yi don Allah kada ki sallame ni haka. Domin akwai dubannina da zasu zo su yi aikin nan." Wani irin tsoro ne ya kama ni. "Wallahi ba zan iya cutar dake ba, kaf zuriar masarautar nan kece kika bani abinci me kyau kika kula da abinda xan ci me kyau. Bayan sai anci an jagwalgwla ake bamu muci, gaya min me zan miki don na wanke laifina!" Hawaye ne ya zubo min, na ce mata.."ya Sunanki?" "Wildat!" "Suna mai dad'i! Ina Mamanki?" "Tana can bata gani makauniya ce." "Haka aka haife ta ko daga baya ta samu?" "Daga sama ta samu tunda tayi fama da hawan jini shine wani abu ya rufe mata idanu." "Tana nan?" "Eh tana nan!" Gyada kai nayi, "Allah ya bata lafiya, amma baku nima mata na asibiti ba?" "Wa zai bawa shege rogo, tunda Ubansa bai noma ba. Ai asibiti na dan gata ne mai dangi da yanci!" Sai naji abin sam bai min ba, taya za ayi ace da bayi masu yawan gaske sannan ace babu wata yar primary health a cikin community din. Shiru nayi na wani lokaci yanzu ya zan yi? "Shi kenan ki tafi, idan zan tafi makaranta zan kira ki sai ki zo muje asibiti da ita." "Ranki shi dade, dawainiyyar fa." "Gaskiyarki ce ta sa na ji haka a raina zan iya miki kome, don haka kada ki damu da cewa an saka ki leken asiri, ki cigaba da gaya musu kome, idan baki yi haka ba zasu iya cutar dake." "Tow Mamana fa?" "Yarima zaki ce ya taimaka mata!" Ina fadar haka na sallame ta, wai me ake nufi da ni a gidan nan? Haka ya tafi amma zuciyata cike yake da tsoron me zasu min idan suka hana yarinyar zuwa.

Ruwan tea nayi ta sha, har zuwa yamma na kara wanka sannan na shiga kitchen na dafa abinci shinkafa da miya, sai pepper chicken da nayi, na gyara kitchen din, sauran abincin na zuba a firji nasan zata zo gobe sai mu karya da safe, dauka nayi na kai daki. Na dawo na kara dafa shayi. Wancan dan renin hankalin ashe ina magana ajiye abincina ya zo ya zauna yaci son ranshi, sai da na gama na shigo parlourn na ga yadda yake cin abincin a nutse ba tare da fargaba ko shakka zan ganshi. Bude kular nayi naga da sauran abincin dauka nayi na wuce dakina da su. Na gaji da yin girki yana cinye min. Tunda bai da ta ido haka na cinye abincina, takaici ya hana ni cin abincin ma sai da na ta jin haushinsa ina jin haushin kaina, da ban gaya mishi magana yadda zai gane Allah da girma yaƙe ba.
Haka na ci kaɗan na bar sauran, sannan na fito da sauran yana zaune a parlourn kamar ba shi. Da gayya na dauki remot din na shiga sauya tv. Irin ai tv na ne, tashi yayi ya fita a parlourn na raka shi da harara. Haushin da yake bani Allah kaɗai ya sani, kamar na kama shi nayi ta bugunsa. Bayan sallah isha ina kwance ya shigo da alamar fita zai yi ya ce min. "Ina jiranki a waje!" Kallonshi nayi tare da nuna kaina, sannan na ce mishi."dani kake?" "A'a da wata, ina jiranki." Ya fita waje. Ina kunkuni haka na fito, shi ko irin Haushin nan baya ji, ni fa bana sonshi. Ina fita na ga ashe har da Matarshi, kamar ba zan isa wurin motar Ba na isa na bude na shiga ina me rufewa da kanshi yake tuki, ashe ya iya tuki. Wayata na ɗauka na kira Yeemar. "Ke banza shine babu kira!" "Mtseew kin samu miji ina zan iya kiranki ina kema mantawa kika yi da makaranta kin samu wutsiya kin lumanci!" "Bura uban can, ke ni bana son iskanci ni ba yar iska ba ce, Au'zubullahi, shegiya yar iska Yeemar kin lalace irin wannan maganar zata fasa min dodon kunnen."
"Ina mijiriya dan ganta?" "Silver spoon, gashi can da jajja amare!" Na faɗa mata ina dariya. "Ki dai ajiye kiyayya kiyi facing reality dinki." "Ke kyale ni, kin san dai ina da gwani kuma har abada ba zan daina kewa." Wani taka birki yayi sai da kaina ya daku da motar. "Kashe mu zaka yi?" Matarshi ta tambaye shi, kallonta yayi a dan yana yin jin haushi ya juya yana kallona da na wani haɗe rai. "Parking yayi ya fito inda nake ya bude kallonshi nayi a dan razane. Fisge wayar yayi ya saka a cikin aljuhunsa. Yana rufe motar na bude nima na tsaya a gabanshi shi. "Wayata!" Na mika mishi hannu. "Na gaya maka ka bani wayata ko na koma gida!" "Ki nunawa kishiyarki tarbiyyar da Abba Junaidu da Maluma Hajara suka miki haka zai bata lasisin yadda take so!" Daga haka ya shiga motar, yadda take dariya ya yi Bala'in kullar dani. Kamar na rufe ta da duka, haka muka isa cikin gida wato fada. Kamar ba zan fito ba haka na fito ya ajiye min wayata yayi a saman motar suka wuce da Matarshi cikin, dauka nayi ina murguda baki, dauka nayi muka shiga cikin gidan, ina bayansu har parlourn Mai Babbar daki, gabana ne ya fadi, saboda irin kallon da take min, zama nayi ina kallon kasa muka gaisa, ta amsa ba ta amsa ba, ban sani ba abinda na sani kulawarta bakiɗaya akan Nady take ko waye, "Nadiyyah!" Ai ho sunanta kenan? Hmm lallai fa ina ruwan tow, muna zaune ya dauki wayarsa ya fita, kallona Mai Babbar daki tayi ta ce min. "Isashiya kece ba lafiya har da dauka miki mai aiki ko?" Gyada mata kai nayi ina narke mata na ce mata. "Mai Babbar daki, nifa yarki ce ko ba kome akalla kin nuna min kauna albarkancin Yaya Yarima, tunda yana sona!" "Hi bitch yaushe ya fara sonki!" Matsawa nayi gaban basket din gaban Mai Babbar daki na dauki apple asalin na gabanta. Na zauna ina kallon Apple din, kalaman Maluma ne ya dawo min inda take cewa. "Ikhlas ina jin tsoron zamanki a gidan Yayari, domin nasan halinki sarai shi kuma zaman gidan iya ruwa ne fidda kai." Murmushi nayi na ce mata. "Mai Babbar daki! Ina sha'awar fura da nono." Na faɗa a kunyance, duk bayin da suke parlourn suka sunkuyar da kai. "Ke baki da kunya ne!" Ta fada min, amma na wani narke na kalleta kamar xan yi kuka na ce mata. "Shi nake so!" Na faɗa ina kallon kyakkyawar kofin kwalbar da aka zuba fura da nonon yayi kyau. Mika min wata mata tayi da ta kira da Sailuba tayi, na amsa na koma na zauna a dan kusa da ita. Na gyara zama ina sha ina b'ata fuska. "Mai Babbar daki ya ba sugar?" Na d'ago fararen idanuna na zuba mata. Rintsa idanunta tayi ta bude a kaina takaici nake kunsa mata. "Sailuba a kawo sigar a saka mata!"
D'ago kai nayi ina kallon wani hoton da tayi da alamu nashi ne da ita, yana gefenta. Abinda na fahimta kamar irin na sunan nan ne. Sai daga baya wasu baya ciki, mikewa nayi na nufi hotonshi da kayan makaranta yana dariya. Kasan hoton na kalla kwanan wata da shekaru ne. "Wannan hoton yana elementary School aka yi shi ko?" D'ago kai tayi tana kallona cike da mamaki. Fuskarshi na kalla a cikin hoton na ce mata. "Shi din yanzu da na da, akwai banbanci. Na yanzu yana boye gazawarshi ne domin ya zama jarumi na da kuma jarumi ne zuryan.!" "Ke rufe mana baki." "Ba dake nake ba!" Na gayawa Nady. Murmushi nayi na koma na zauna bayan na dauki kofin furan na ce mata. "Ana iya sauya kome, Mai Babbar daki amma ba a soya ƙaddaran mutum ni na yarda da haka. " Murmushi nayi sannan na sha furan na ajiye kofin. Daga haka na tashi na fita waje, na sha iska domin na gaji da zaman dakin. Wucewar mutum na gani a cikin duhu, duk da babu duhu sosai. Haka na bi wurin, a hankali nake tafiya har na isa wani lungu ban sare ba na cigaba da bin lungu. Kunna torch din wayata nayi na cigaba da shiga lungun. Nishi da gurnanin na fara ji, duk da a tsora nake. A hankali na haska wayar wani abu na gani yafi girman dan akuya shi ba mage ba, shi ba kuma zaki ba, ihun da nayi ne yasa shi juyowa da gudu, ya biyo ni, ai ban tsaya ba na shiga gudu kamar xan tashi sama, sai ji nayi an fisgo ni tare da rufe min baki abin ya wuce mu da gudu. Inda aka shiga dani kamar daki ne, ban san waye ba amma yana shiga da ni dakin ya matse ni da bango. Bakinshi ya kawo kunnena "Ki manta abinda kika gani," an yi maganar da wata irin siririyar murya ce, haka yasa nayi luff a jikinshi, ina jin kamshin kamar na sanshi, abinda ya fado min a raina aurena. Da wani irin sauri na kwace ya kara mai da ni jikin bango. " Na gaya miki, ina tare da ke! Kuma zan kare ki daga abin cutarwa." A hankali na ji kamar ya tab'a min wani abu a dokin wuyata, a hankali ya fito da ita daga cikin duhun ya kawo ta haske ya ajiye ta, tare da saka mata wayarta a kan cikinta.

Ya koma cikin duhun ya b'ace kamar bai tab'a bayyana ba. Lungu ne ya kama da wuta. Wanda hayakin da aka gani


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login