Showing 12001 words to 15000 words out of 304445 words

Chapter 5 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

125

daya ya juya ga Faruq ya wani juya kai. "Ka saka bullet roof dinka?" Hadiye yawun tsoro Faruq yayi, yana girgiza kai. Lumshe idanu yayi kafin ya buɗe, yana me lashe lips dinsa a tsanake. Ya ce. "Hmm! Kada ka kara min haka." "Afwa, Allah ya huci zuciyarka."
Da sauri ya wuce study room ya kwaso mishi wasu littattafai ya ajiye mishi, sannan ya koma ya tsaya.

***
Khlas

After five days
Yadda Abba ya saka min idanu, zaka rantse da Allah ya hala ya samu labarin ina cikin b'arayin da suka yi satar Lu'lu'an khoonoor ne, saboda yadda ya saka min idanu. Ya kwanan na biyar ya saka Iram ta kira ni. Tunda na shiga na zauna kusa da ita, kare min kallo yayi ya ce min. "Yau zaki koma aiki ko?" "Eh Abba!" Na fada ina kallonshi.."Zan gaya miki wani abu, ita wannan rayuwar da muke doronta, tana bukatar sirri duk wanda kika ga yana dariya yana da sirrin da baya son duniya ta sani. Ban zab'a miki aikin jarida don ki zama fadi ba a tambaye ki ba, duk abinda kika gani a wannan yanayin da lokacin shiru yafi alkhairi ayi ta. Zainab kada na ji kada na gani kin gayawa Uwais kin san waye shi? Kin san matsayin da yake. Kome kankantar Evidance idan ya samu tow ba makawa babu me fitar da ke, sai Allah batun mutuwa Joy na rufe shi a parlourn. Iram kema idan na ji labarin nan a cikin gidan nan, ki sani kece kika fitar don haka ku ji kamar baku ji ba. Wani lokacin shiru yafi zama alkhairi da fadar shi." Ganin yadda muka yi shiru sannan ya ce mana. "Ku ji tsoron Allah, idan kuna tunanin baku ganin shi tow shi tow shi yana ganinku, ku ji tsoron Allah ku kaunaci junanku, ku rufawa junanku asiri ta haka ne kawai zaku ci nasara a rayuwarku. Don haka ku tashi ku tafi." Ni ce uwar baki kuma uwar iyayi ina tashi nace mishi. "Abba Allah ya baka lafiya da nisan kwana, ya rufa maka asiri duniya da lahira." "Amin Uwata!" Har zan fita na ce mishi. "Abba ba na ji Hajja zata zo ba?" Girgiza kai yayi ya ce min. "Matsalarki ce zata zo da ita kuma na gaya mata kin samu lafiya!" Dariya nayi nace mishi. "Tunda ta ce zata zo Allah zata zo, matar da idan jinin tashi muje mu ya motsa mata sai dai a ga tana hada shirgi ka sa idanun zuwa ga Hajja sai ta zo." Daga haka na fita ina murmushi, ajiyar zuciya ya sauke. Da sauri ya mike tare da kira na. "Na'am Abba!" Na dawo dakin na zauna tare da cewa "ga ni!" Shiru yayi yana kallona kafin ya ce min. "Uwais kada na kara ganinki da shi!" Kallonshi nayi kamar xan yi kuka. "Abba!" Na furta ina jin kwalla na cika min idanu. "Na ce kada na kara ganinki da shi." Ya kara furtawa yana mai bari na a parlourn, hawayen da nake ƙoƙarin dannewa ne yake zuwa kamar da bakin kwarya, kuka ma sake tare da barin parlourn. Yadda na shiga na samu Ya Yunus yana zaune tsaki yayi tare da hayayakon min kafin. "Wallahi sai na karya kafarki idan na ji muryanki, mara kunya kawai."
Masifaffe ne fa shima ga saurin hausa, shi yasa naji Maluma tana faɗin wai Soja zai tafi idan ya dawo Service. Gara ya tafi can ya je ko zai samu me koya mishi hankali. Na wuce dakina da gudu. Haka na shirya ko karyawa ban yi ba. Na fita jiki a mace. A mota na sami Iram, ina da wani dabi'a shine damuwata da fushina na wani lokaci ne ban iya rike damuwa ko b'acin rai ba, da zaran na ga fuskar da na sani take nake mantawa da ina fushi. Ina shiga motar na samu Malam Babangida ya kuna gidan Radio Z, murmushi nayi na zauna na ce mishi. "Nasan Anas Manga ne cikin dakin watsa labarai, yanzu zai saka wakar Wendy shey. Ban rufe baki ba kuwa ya saka wakar. Nima da yake ina son wakar tuni na amsa.
_You break my confidence everyday_

_And you never thought I will be okay_

_you lie!! You lie to me_

_You make me want to freeze_

_coming back on your knees oh no_

_See you no get again_

_boy you no go get again_

_make you no disturb me_
_cos I no dey mind you oh no_
_Is too late!! Is too late!!_
Daga Malam Babangida har Iram tsayawa suka yi suna kallona. Musamman inda ta zo asalin baitin wakar.
_Wo pressure be rise_
_Adwen no be thinking_
_Hee ba when see sexy body_
_See see_
"Malam Babangida kashe wakar nan yarinyar nan ban da shirgin Aljanu bata da aikin sai tara mana su." Inji Iram, tsaki nayi na kunna wayata na saka. Sakon Uwais na gani sai a lokacin na tuna da abinda ya faru, ai kuwa na sake komawa kalar tausayi. Har muka ajiye ta a wurin aikinta, Ni kuma ya wuce da ni wurin aikina. "Malam Babangida meye laifin alakata da Uwais!?" Murmushi yayi yana tuki. "Hadin zai bawa mutane damar fadar cewa Abban." Cizon lips dinsa yayi yana kallon hanya kafin ya kai ni kofar gidan rediyon. "Malam Babangida damar me zasu ce?" "Ikhlas ki yi hakuri, ki rabu da Uwais!" Daga haka bai kara magana ba, kura mishi idanun nayi kafin na juya zan fita ya ce min. "Zainab!" Ban tab'a jin ya kira sunana haka ba, kallonshi nayi na ce mishi. "Kirana kayi?" Idanunshi yayi jajjur ya ce min. "Ki rabu da shi, akwai masu kaunarki da dukkan zuciyarsu." Girgiza kai nayi tare da faɗin. "Tun ina karama na tashi da son shi." Na fada ina son yin kuka amma na danne haka.
Murmushi yayi wanda ake kira da yake, wanda yafi kuka ciwo. "Ok sai nazo daukarki."
Fita nayi daga motar na nufi cikin gidan Radion. Ina shiga Yeemar take cewa. "Ke yau zamu shiga kofar fada wani aiki don haka karfe daya zamu tafi ki shirya!"
Dole na sake amma ban ji dadin yadda Uwais yake kirana ban dauka ba. Haka na gabatar da rahotannin da aka bani, bayan na gama muka fita aiki tare da Anas Manga.
*
Fadan Daba.
"Goga!!!" Sake karfen da yake d'agawa yayi yana faɗin. "Sai fille kanka, dan me kartan hancin uwarka, yaya ne?" Ya fada da wata katuwar murya irin wacce shaye-shaye ta fasata. "Ga can Smolli ya shigo mana unguwa da wata yarinyar ya ajiye ta." "Kutumar Uba, yau sai dai uwarsa ta haifi wani maza ku dauko gariyo da burmi. Yau abokin gaba a cikin chakwalikwalinmu!" Suka fita da gudu, suna masu diban kayan aiki, irin su Adda me tsatsa. Burmi wata yar karamar wuka, kawo da zarto, suka fita da gudu. Rigima tsakanin unguwar Tabkin A da Tabkin B, ba sabon abu ba ne kowa ya sani. Kuma idan suka fara ba iya su kaɗai suke kashewa ba, sannan gwamnati tana sane da fadar daba. Bata da yadda zata yi domin fadar tana tafiya da wani abu na musamman.

Yadda suka fita da gudu kuwa haka suka same shi, yana niman Canji kamar an ce ya waiga ya hango su, wani irin tashin hankali ya ji ya doki zuciyarsa, ya saka gudu kamar zai tashi sama, su kuwa binsa suke kamar zasu kama shi. Gudun da yake ya wuce misali, domin daga unguwa zuwa kofar fada babu nisa. Koda ya iso ture mutanen da suka fito sallah azhar yake yana faduwa kasa, an kuwa suka rufa mishi. Ihu yake tare da faɗin. "Wayyo Allah ku taimake ni zasu kashe ni, wayyo Allah na wayyo Allah na!" Saranshi suke ta ko ina. Salmanun Faris da Faruq sun fito masallaci kenan, da sauri faruq ya ciro wata kamar bindiga ya sake ta a sama "tauuuu!" Karar harbin ce ta dakatar da su. "Kuna motsawa zan sake muku daya bayan daya domin harsashina yana da karfin gudun guguwa ce." Inji Faruq, yana kallonsu. "Ku ajiye makaman hannunku." Cikin wani irin taurin kai babban cikinsu yaki ajiye. Sake harbi Faruq yayi yana faɗin. "Na uku a goshinka zan sake!" Jin haka yasa ajiye addar hannunsa. Da yake abin ya faru a tsakanin wurin ajiye mota ne. Wasu yan mata ne a can gefe cikin tsoro. "Oga wannan fadar daba ce, kuma gwamnati ta san da zamanmu, don haka ka kyale mu shima haka ya kashe min dan uwana, kuma aka kyale shi ya rayu. Don haka idan ina numfashi sai na rama, don na rantse da mai rumfar ba gwafa." Ya fada yana kallon yan matan da wutsiyar idanunshi. Tabbas ya samu yadda zai tsira da yaranshi. "Wannan tsakaninku baka ga inda kake ba ne? Kana kofar fadar Zanzabira zaka zo kayi kisan kai?" Murmushi yayi ya ce. "Fadar tamu ce, an gaya mana ko ina muka so mu yi shikar da zata mana, don haka ba ruwanka da mu domin matukar zabo na yawo kare na yawo wata rana za a jame." Ya fada cikin wani irin tsalle ya dira gaban yan matan tare da fisgar daya daga cikinsu.

Ikhlas
Tsautsayi da ƙaddara suka fito damu bakin aiki, ban tab'a ganin sara suka ba sai a wannan lokacin akan idanuna ake sarar dan Adam kamar an samu rake yana ihu yana niman hanyar da zai rayu, yadda na girgiza da abin yasa ko motsin kirki na kasa daga ni har Yeemar wacce take makale tana daukar sautin abin da yake faruwa. Ihun Yeemar ya dawo dani daga dimuwar da na shiga. Domin ina d'ago kai na ga mutumin da yake sarar ya shake min wuya tare da saka min wata karamar wuka a wuyata..... Holala😳🙄 Me zai faru next page? Twisted fate ko RIP?
Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book.



*Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu ƙayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:*



*MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya haɗa da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.*

*AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen ɗin Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen*

*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*

*POSTING*
*Ɗaya: 500*
*Biyu: 1000*
*Uku: 1500*

*DOCUMENT (da zaran an gama posting zai koma)*
*Ɗaya: 1k*
*Biyu: 2k*
*Uku: 3k*

domin tura shaidar biya ko Ƙarin bayani, ku tuntuɓi:
*08130269641*
Ko
*08137311900*
Ko kuma
*09063467258*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: ROYAL POLITICS 🔥
_An yanka ta tashi_
Ramlat A Manga
Mai_Dambu
TOP-NOTCH SEASON 4
Sadaukarwa ga Auntyna RUKAYYA GOMBE 🥰 🤩 😍


Page..03
Blaming

Few hours
Before accident.

Malam Junaid Gobir.

"Mahaifinka ya bani kalamansa da kwarin gwiwarshi akanka, don haka na kira na gaya maka ne Alhaji Nafi'u yana nima na, duk yadda kaso kayi amma ka sani rayuwata da na ahalina tana hannun Allah tana gare ka. Idan na rayu gaskiya zata rayu idan na mutu gaskiya zata mutu kuma za a binneta ne a inda bai dace ba." Ya fada yana kallon wayar da ya maka ta a jikin motar. Duk da ga shi dai yana waya ce amma daga can bangaren babu alamar za a ce wani abu. Muryan Faruq ce ta ratsa wayar. "Malam In sha Allah babu abinda zai faru sai alkhairi." Daga haka ya kashe wayar yana sauke numfashi.

***
Ikhlas
Karar da nake ji daga can nesa ne yasa na bude idanuna da kyar, "Malam Babangida!" Shine abinda na iya furtawa na tabbatar yana nan ko wani abu. "Na'am Ikhlas!" Tunda na iya jin muryanshi can-can na fara ƙoƙarin buɗe idona amma na kasa saboda nauyin da kaina yayi min. Daga nan ba zan iya cewa ga abinda ya faru ba.

Ban zance na san me ya faru ba, amma koda na farka kwana biyu da faruwar lamarin a asibitin ya cika makil da yan uwana. Ina bude idanuna Abba na fara hangowa shi da wasu mutane daya ya juya baya zai fita, ba yana mishi magana. Fita suka yi Umma ta ce min. "Sannu kin ji ai kun auna arziki ke da Babangida, yana can shi bai wani ji ciwo sosai ba, saboda ya saka belt din motar kece kika bugu a kai." Lumshe idanuna nayi na kara bude shi a karo na biyu. "Umma ina Maluma?" "Tana can ta ce ba zata zo ba, domin ta ji labarin kece kika tsokano wata mata ta saka aka biyo ki!"
Kokarin tashi nake amma na kasa dole Umma ta taimaka min na mike,tare da shiga ban daki nayi wanka da alola, sannan na fito nayi sallolin da suke kaina. Ina idarwa Abba ya shigo ya zuba min idanu. "Wata mata ce kuka yi fada da ita an ki gaya min wacece ita?" Yadda na ga yayi maganar tare da tsare ni da idanu nasan cewa ba lokacin gardama ba ne don haka na ce mishi. "Matar dan Sarkin Zanzabira ko wacce ban sani ba." Kura min idanu yayi kafin ya ce min. "Bana ce ki daina takalar fada ba? Yaushe zaki girma ne? " "Assalamu alaikum!" Shigowa Uwais Saddam ya kwace ni a hannun Abba. "Barka Abba ya masu jikin?" "Alhamdulillahi Uwais!" Ya fada yana kallona. "Autar Maluma ya jikinki? Umma da Ikram suna gaishe ki!" "Ina amsawa." Na fada ina wasa da yatsuna. "Zainab!" Abba ya kira sunana. "Na'am Abba!" Na amsa ina kallonshi. Shiru yayi sai ya juya ya fita. "Ya Uwais yaushe ka dawo?" Zungure goshina yayi yana faɗin. "Bakya jin magana me yasa ba zaki daina jan magana ba." Tea Umma ta mika min na fara sha ina jin shi. "Ba fa wani abu ne ya hada mu bangaje juna muka yi. Ta hau Bala'i!"
"Sai ki bata hakuri!" Ya fada yana kallona,
"Gaskiya kawai don mun bangaje juna sai na bata hakuri ai bata yi yadda zan bata hakuri ba." Zuba min idanu yayi kafin ya ce min. "Ni da aka kashe min mahaifina daga gwamnatin jahata zuwa masarautar Zanzabira sun bani hakuri don haka ki yi hakuri ki daina fada wani lokaci ko da gaskiyarka ana iya take ta a ce baka da shi, don haka ki koya daga Abba." Ya fada yana mika min flat din abincin da Umma ta mika mishi. "Ni gaskiya ba zan iya irin hakurin shiga daki kayi kuka ba, a dake ka sannan a hana ka kuka ba." Dariya yayi yana kallon yadda nake mishi. Can na ce mishi. "Ya Uwais ka san yarinyar da ta mutu nan Joy Moses?" Shigowar Abba ne yasa ni shiru, "Asma'u ki hada kayan mu koma gida babu wani abu sun sallame ta."

Mikewa nayi Umma ta haɗa kayan, ina kallon yadda Abba yake zuba min harara tow meye nayi na kuskure? Har Umma ta gama hada kayan Ya Uwais ya fitar da su damke hannuna Abba yayi. "Kika sake wani abu ya fito bakin ki ba iya ke ba hatta shi Uwais din da mu kanmu mutuwa zamu yi!" Yadda ya fada din nasan ba zai yi karya ba, wani irin tsoro ne ya cika min rai na ce mishi. "Abba da gaske?" Fita yayi ya bar ni cikin tsoro dama Umma ta rigamu fita, a hankali nake takawa. Wani mutum na gani a kofar dakin dogo mai kaurin jiki. "Sunana Faruq muje na raka ki." "Waye ya kai?" "Muje!" Ya furta a hankali. Haka muka shiga takawa har wurin motar. Sai da na shiga motar sannan ya juya abinsa. Yan sanda suka raka mu har gida.
Da farko parlour Abba na wuce na zauna ina zare idanu. Uwais ya shigo ya mana sallama, yana fita Abba ya hau min faɗa. "Sa'arki ce Matar da kuka yi fada da ita? Shin bana hanaki rena na gaba dake bane? Ikhlas yaushe zaki yi hankali?" Yadda Abba yake faɗa zaka rantse da Allah mugun laifi nayi ya daura min blaming din bakiɗaya. Har sai da na ji nayi danasanin biye mata muka yi faɗa. Tsaki Mommy Turai tayi tana faɗin."abin kunya ai ba yau Ikhlas ta fara janyo maka ba? Gaba har cikin shege sai." "Turai!" Ya daka mata tsawa. "Karya nayi? Nace karya nayi? Haka kawai zata saka matar Babban mutum a garin nan ta mata rashin kunya? Har ana yad'a labarin a kafafen watsa labarai." Kukan da nake yi ne yasa shi komawa daki Maluma da take zaune kamar ruwa ya cinye ta. Ta sauke ajiyar zuciya ta ce min. "Tashi mu wuce wurina!" Haka na mike ina kuka. Tunda na shiga dakin da yake gefen nata na rufe kofar nake shashekar kuka. Malama bata duka bata zagin Yaro, amma tana iya zuba maka idanun ta fita harkanka, sai ka ji a jikinka. Kafin ta shiga lamarinka.

***
Alhaji Nafi'u

A daren jiya zuwa wayewar Yau kafafen watsa labarai na Zanzabira suka dauki labarin hatsarin da ya faru har da short videon fadar Ikhlas Junaid Gobir da Nadiyyah Jamil Chiroma, wannan abin ya zama kamar wani sabon al'amari da yake niman ya fisgi zuciyar mutane. "Musharraf ka fahimci dalilina na saka idanun akan Junaid da Salmanun Faris?" Duk da kasancewar shi gwamnar jaha guda amma a zaune yake a kasa Alhaji Nafi'u yana zaune a saman kujeransa na gwamna. Yana juya kanshi a kan kujerar, "Rilwanu Abubakar Yayari ya same ni da maganar, rikon kwarya ya muka yi da kai?" Cikin kaskantar da kai ya ce mishi. "Yallabai gani nayi kamar matsalar tasu ta cikin gida ne yasa ban gaya maka, kuma sun bada haɗin kai an bawa Alhaji Mamman Abba yayari rikon kwarya."
"Zancen banza kenan, ce maka nayi ban san yadda aka yi aka bawa Attahiru Shehu Yayari kujeran bane? Ko ka fini sanin ya kamata ne? Ka manta lokacin da muka yi ta rokonshi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login