Showing 36001 words to 39000 words out of 304445 words

Chapter 13 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

43

yadda ya iya.
Ajiyar zuciya ya ji an sauke cikin wani irin murya me nauyi aka ce mishi. "Zan zo!" hawaye ne ya kara zuba masa, domin tausayin dan uwansa yana kara cika mishi zuciya a kullum ya tuna mafarkin bayin Allah nan sai ya ji kome ya tsaya mishi.

***
F&F gold miners.

Yau kimanin shekaru biyu kenan da gwal yayi wani irin b'atar dabo, koda za a same shi sai anyi ta hako ana tafiya mai zurfi kafin a hako shi. Amma ba a samun shi ta sauki domin wahalar da ake sha. Alhaji Nafi'u ya kananaye kamfanin nasu bakiɗaya, don ya hamdame kome kuma baya jin zai kara barin wani daga cikin abokansa kuma abokan gabanshi su samu mafita. Sai dai an wayi gari kamfanin hako gwal din ta tsaya cak.

An rufeta ma bata da wani amfani, haka yasa wurin ya zama matattarar marasa jin magana, sai mutane tsiraru da suke bin dare suna hako kuza, wata dutse ce itama mai daraja, haka yasa ba a san me akayi a wurin ba tunda an rufe ta ya zama abandon company. Wasu yara ne su uku suka tsallaka katangar, bayan sun gama abinda za su na rashin ji da shaye-shaye, sai fada ya kaure a tsakaninsu. Haka yasa biyu suka rufawa dan domin shi bai sha kome ba, kuma akan gaskiya ya gaya musu abinda suke yi bai dace ba, shine suka rufa mishi da duka, tun yana kare kanshi daya Yaron mai suna Amir ya dauki wani karfe ya soka mishi a gefen wuyarshi haka jini yayi ta tirsuwa karshe Yaron nan ya mutu a wurin suka gudu suka bar shi, wannan yasa jinin yayi ta malala yana gangarawa can kududdufin da ake hako zinari.
----
Da dare masu hako kuza da suka shiga kamfanin basu san me ya faru ba, haka yasa bakiɗaya suka zurma ramin da ake hako kuzan, sai da suka fara aiki wani abin mamaki ya fara bayyana musu shine madadin kuza ba sai ga gold ba, a wannan daren suka dibi arziki, sannan suka fita a cikin mutane fada ta sake kaurewa da wasu aka kashe mutum biyu, abin da basu gane ba zinari shu'umi dukiya ce, matukar ba a nime tsarkake ta daga Ubangiji ba, tow fa tana iya bayyana amma sai dai idan za a zubar mata da jini, a lokacin da abokai hudu suke kusan kullum idan za'a tafi hako zinari sai an yi sauka tare da yanka shanu da awakai a bata jinin, amma a yau da ta amshi jinin bil adam sai ta yi, ta yad'o tana baza shu'umancinta. Sannan wani abun da mutane basu gane ba, ita kanta zinari tana haddasa wani irin yaki domin a zubar da jinin kowa ita haka take so, a cikin mutanen da suka yi wannan hakon daren mutum biyu suka tsira suma don daya ya yarda zai dauki mafi kankantar kaso ne, haka yasa ya tsira.

Bayan kwana uku da faruwan lamarin ne wurin ya kaure da wari da doyi, haka ya ja hankalin mutane wurin ai lokaci guda aka fara bibiyar kamfanin da wurin hakon zinarin aka ga gawarwaakin mutane kaca-kaca. Tuni Alhaji Nafi'u ya dirko wurin aka fara binciken gaske anan aka samu wasu duwatsun zinarin da suka zube tuni aka tattara gawarwaakin aka wuce da su asibiti sannan ba tare da b'ata lokaci ba Alhaji Nafi'u ya bada Umarnin. " A fara aikin hako zinari babu wasa an samu."

***
Yau Laraba.
Muka bar zanzabira zuwa lagos, a daren ranar muka bar Nigeria.
Mun isa Dubai da safiyar Alhamis don murna ko barci ban yi ba, sai da muka isa masauki barci ya kwashe ni. Barci sosai nayi sai da na farka ne na ga ba kowa a dakin, wurin karfe uku na rana Mommy suka dawo ita da Iram da na ganta magashiya kamar zata mutu. "Ikhlas taimaka mata ki kai ta ban daki, mu ga abinda hali zai yi." Haka na riketa zuwa ban daki, tana shiga ta kamkame ni jikinta yayi zafi. "Cire min kayan!" Haka na kwantar da ita a cikin abin wankan, "Cire min pant din don Allah!" Haka ya cire mata sai ga audiga hade da dunkulen jini ya zubo bakiɗaya. Ajiyar zuciya take tana me juya kanta. A hankali take nishi jini ne guda-guda suke zuba har sai da ya fita dayawa kafin ta ce min. "Ni kira min Mommy ta kwashe!" "Iram me ya same ki?" Domin zuciyata tana raya min abortion suka yi, kallonta nake yi na kasa motsi. "Ki kira ta Please!" Haka na fita da sauri, ina isa kofar dakinta na ji tana faɗin. "Kada ka damu Lucky kayi yadda nace maka." Buga kofar dakin nayi kasancewar na jima ina jin lucky a bakin Iram ta ce babba Yaron Mommy Turai ne na nan Dubai, yana kuma kula da kome nata. "Ikhlas ce?" Ya tambaya. "Mommy kizo ta ce!" Bude kofar tayi yadda na ganta ban tab'a ganinta haka ba, murmushi tayi min ta mika min wani container. "Akwai wani bakin gudan jini ki saka shi a nan sauran ki saka handglob ki kwace kizuna a kan pit din." "Tow!" Na amsa a hankali, hannunta ya shafi kan hannuna, ban kawo kome a raina ba na juya da sauri. Kamar yadda tace min haka nayi na kwashe tas na zuba tare da flushing dinsa, ta ce min. "Ki zuba min ruwa amma mai dumi!" Haka nayi kuwa kusan ni ce nake kula da ita har ta gama wanka, ta fito a lokacin aka kawo abinci me zafi ta sha farfesu sannan ta sha magani da Mommy Turai ta bata. Tuni barci yayi gaba da ita.
Wurin karfe shida na yamma ina zaune akan abin sallah Mommy Turai suka shigo da wata yarinya kyakyawa budurwa. "Mom Iram tun yaushe kuka iso ban sani ba?"yarinyar ta fada isowa wurinmu, murmushi Mommy Turai tayi tana faɗin. "Dazun da safe, da yake mun iso bata da lafiya ne shine muka isa asibiti, amma da sauki." Ta fada tana kallona, ina ga Mommy Turai ta manta ni dalibar jarida ce yasa take maganar da tasan kai tsaye xan ƙaryata. Amma ganin halin da Iram take ciki kuma da alamu anyi gudun kada a can kowa ya sani yasa ake zo nan, sai na bisu da idanu. Haka suka yi ta hira da Yarintarta har wurin karfe goma na dare ta ce zata tafi. Ta rakata, suna fita Iram na bude idanun. "Dama idanunki biyu ne?" "Eh taimaka min na shiga ban daki." Haka na rike ta, zuwa ban daki tayi wanka ta kuma sake zubar da jinin a wannan lokacin ko gabanta bata gani ta gaya min, haka na fita na kira Mommy Turai,aka sake ɗaukarta zuwa asibiti, an kashe kudi kan kamar ba a san darajarsu ba, kuma an mata karin jini, a daren muka dawo gida sai dai parlourn na ga wasu mutane maza da mata, tunda na gaishe su na wuce Mommy Turai ta tsaya, jikina ya bani ban yarda da su ba. Amma a haka na kwanta bayan na rufe dakin nayi addu'a.

Kusan kwana uku kenan da faruwan lamarin, aka sallamo iram ni da yarinyar nan Nadrah mune a tare da ita ana sallamarta muka bazama garin Abhu dabi da yawo, shopping kamar mune jikokin karuna, domin kudi muke kashewa kamar ba gobe, ranar da muka cika kwana biyar Mommy Turai ta wuce Bangkok, ta barmu a gidan Khalisah Shaibah.
Babbar ma'aikaciya ce a jami'ar Dubai, mace ce mai nutsuwa da kamala. Tunda ta ganni ta zuba min idanu. Bata yarda tayi min magana ba, sai da Iram suka fita da Lucky wanda yake zirga-zirga da mu, tana aiki a kitchen na shiga tayata ta ce min. "Me yasa kika biyo su?" Kallonta nayi ina murmushi n ace mata. "Iram ta gayyato ni!" "Da baki amshi gayyatar ba, akwai ƙaddaran da muke kai kan mu ga ita Akwai kaddaran da ita ke bibiyarmu. Kada ki yi wasa da addu'a ba a fushi da addu'a daga yau wannan ya zama izina a gare ki kada wani ya kara janki zuwa ga biyar bukatarshi." Gyada kai nayi muka cigaba da aiki.
***
A daren ranar muna zaune Iram ta shigo dakin taci kwalliya ta ce min. "Ki zo mu je party kawar Nadra tana birthday." "Barci nake ji fa!" "Please zo muje Lucky yana jiranmu!" Haka na mike na saka abaya kamar yadda ta saka muka fita, wani store muka shiga ya zab'a mana wasu kayan arna, eh kayan arna ta mika min na ce mata."ke Iram ina tsoron kada Abba ya gani ya ji babu dad'i." "Ai baya ganinmu!" "Allah yana ganinmu, gaskiya ba zan saka wannan kayan ba." "Shi kenan na gode sai ki koma gida amma ni da Lucky zamu wuce " ta fada tana wucewa da kayan, riko hannunta nayi na amshi kayan na saka. Rigar ce iya cinya, ta kamani sosai. Sai sama rigar bra dina sun fito tantsantsan, tun dama can ina da kayan marmari balle da na saka kayan sai na sake fitowa kamar irin kalangun nan, haka yasa Iram da Lucky suke ta kallona. Kare kirjina nayi, ina faɗin. "Meye haka?" "Abu na gani!" Inji Iram tana dariya. Komawa Lucky yayi ya dauko wata top jacket ya mika min yana taunar chew gum. Amsa nayi na saka sai na samu ya ɗan rufe min kirjina, na saka wata high heels red kalar kayan, sai bakin jacket din ya tafi dai-dai, sai yar karamar pose da na dauka muka tafi, koda muka isa get pass Lucky ya nuna mana, muka shiga cikin baka iya jin maganar kowa saboda kida kawai ana ta rawa ashe ni ce kawai nayi shigar mutunci kuma aka barmu muka shiga saboda get pass dinmu, wurin ya cakude baka jin kome sai tashin kida yake.

Wuri can na nima na zauna aka bani ruwa naki sha, ina zaune Iram da Nadra suka tawo da wasu kawayensu aka rufa anata shewa anan ne iram ta zuba min Chapman na sha, a hankali nake ganin wurin yana juya min ta kara zuba min domin har ita sha take yi, a hankali na daina fahimtar kome. Sai bayan kamar awa daya na bude idanuna, na ji ana faɗin.
"Na bada dalla miliyan goma!" Dan hasken da yake nuna allon aka haska an rubuta harufan Mr Knight, can wani daga can ya ce. "Dala miliyan talatin!" Shi kuma an rubuta Draculas! "Akwai me ja?" "Talatin da biyar?" "Ya kara fa akwai mai ja?" "Dalla biliyan goma!" "Draculas ya kara akwai mai ja?" Daga nan ba a kara magana ba, aka buga karfen da yake nuna alamar an sayar mishi. Wai ma tukun waye aka sayar? Nake tambayar kaina. Ina zaune a cikin kage aka zo aka bude ni, wani mutum mai sanye da mask ya zo ya fitar da ni, tare da daukata a kafad'arshi, a hankali yake fita har ya kai ni wani daki, wanda nake da yakinin a cikin hotel din da muka zo party ne.

Bayan an fitar da Ikhlas Hajiya Turai ta sauke ajiyar zuciya. "Tana faɗin. "Lucky ina nad'e videon abinda ya faru a club ko?" "Eh Hajiya!" "Alhamdulillahi zan wuce Bangkok a daren nan zuwa gobe ka tabbatar ka nuna tab'ata sauran kuma zan ji da shi. Murmushi Mommy Turai tayi tana faɗin. "Dole ka janye auren da zaka kakkabawa Iram Junaidu."
***
Tunda aka kai ni dakin aka watsa ni a gadon, nake barci sama sama. Har gari ya waye. Bude idanu nayi na ganni a cikin dakin babu kowa. Na kuma yi kokarin tuna abinda ya faru ban tuna ba, bargon da aka lullube ni da shi na yaye na a hankali nake bin kayan jikina da kallo ba kayan da naje Party da shi bane, normal rigar barci fari riga da wando, sai gashina da aka warware min shi da na tufke. A gefen gadon na ga wani takarda an rubuta. *Sayanki nayi don haka, ki tabbatar kin ajiye a ranki zan nimo ki a duk inda kike a duniya sannan ke amaryata ce kada ki sake ki hada shimfid'a da wani domin Zan hukunta duk wanda ya kalle ki, You Are my bride!*
#Draculas
A haukace na sako a gadon, tare da bude ban daki babu kowa kayana da na gani a kasa na dauka wani takarda ne ya fado. *Kin yi min kankanta da na ci moriyar kudina! Amma Boons dinki natural ne tare da skin dinki! Ki tafi ban daki ki duba kanki daga Boons dinki zuwa kirjinki na ajiye miki shaidar da ko mutuwa kika yi ni zan gane ki!*
Da sauri na shiga ban daki rigar na fara kwabewa rubutu ne aka yi. "Draculas bride aka rubuta, ihu na saka tare da kamkame jikina, me yasa na fada hannun yan shan jini ni abinda ya fara zuwa min kenan, da gudu na shirya kwashe kayana na fita da gudu, na nufi stair n a saka domin tsoron amfani da elevator nake, kuka ne kwace min a hanyar sauka ksa na bude pose dina, wayata na cire na kira Abba. Bugu daya ya dauka. "Abbana zan dawo gida?"
"Me aka miki?" "Ni gida kawai nake so!" Na fada daidai wutar stair din yana daukewa. Wani irin tsoro ya kamani, haka nayi ta sauka da gudu, kusan hawa ashirin da wani abu, sai da nazo kusan sauka na goma sha tara na fado, ihun da nayi ya janyo hankalin wasu ma'aikata suna iskancinsu. Aka kira motar asibiti. Suka tafi da ni.

----- A yadda Hajiya Turai taso sai abin ya zo da tangard'a domin domin kiran da Malam Junaid da Iram suke yiwa Ikhlas yasa aka samu labarinta, lokacin da Hajiya Turai labari ya je mata kamar zata yi hauka amma sai tai ta fada ta ce mishi. "Ya san yadda zai yi ya gama kome akan Nadra.

Ita kuwa Nadra kusan tare aka sayar da su da Ikhlas ita wani Balarabe ne ya saye ta, ya kai ta gidansa ba wai don kanshi ba sai don danta da yake da laluran hauka, sannan idan ciwon ya tashi haka zai ta kokarin hakewa mata masu aikin haka yasa likita ya bashi shawarar ko zai nimo mishi mace a ajiye ya domin biyar bukatar dansa shine ya samo Nadra kusan dala dubu dari tara ya saye ta, tunda ya wurgata dakin take ihu a zo fitar da ita amma ina, ihunta ne ya tashi Yaron ya zuba mata idanun. Domin babu kaya a jikinta. Kare kirjinta take tana faɗin. "Kada ka cutar da ni." Damke ta gayen yayi ya kira mata idanun. "Abie a ina ka samo min abu me kyau haka?"
Daga nan ya wullata gadon..

***
MATAN ALFARMAN.

A fusace Hajiya Layla take kallon Sam Suhaima ta ce mata..
"Idan har wani abu ya sami Nadra wallahi ba zan yafe ba kuma ba zan yard ba."
"Ki min shiru waye ya ce ki sayar da Iram? Wannan abun iya na waje muke tab'awa baki da hankali ne da zaki tab'a Iram? Ko ance miki ita Uwar Iram bata da hankali ne? Ba Iram ba ce Yarinyar da nace kada ku tafi da ita sai da kuka.tafi da ita ko? Ai naga kudinki ya shigo na kungiyar ya shigo ki sani ku san hanyar da zaku dakatar da tonuwar asirinmu yan iskan karuwan banza karuwan wofi, ki sayar da g***dn iram ta sayar da na Nadra sai ki gaya min da ke da ita waye ya fadi nan na gaya miki kada ki fara abinda ba zai bude miki ba, kika ce ana niman budurwa yar asalin gidan Malam Junaid kika ce Iram hmmm ki tanadi zaman lafiya domin Turai tafiki karfi na gaya miki babu yadda zaki iya rusata...

Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book.


*Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu ƙayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:*


*MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya haɗa da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.*

*AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen ɗin Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen*

*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*

*POSTING*
*Ɗaya: 500*
*Biyu: 1000*
*Uku: 1500*

*DOCUMENT (da zaran an gama posting zai koma)*
*Ɗaya: 1k*
*Biyu: 2k*
*Uku: 3k*

domin tura shaidar biya ko Ƙarin bayani, ku tuntuɓi:
*08130269641*
Ko
*08137311900*
Ko kuma
*09063467258*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: ROYAL POLITICS 🔥
_An yanka ta tashi_
Ramlat A Manga
Mai_Dambu
TOP-NOTCH SEASON 4
Sadaukarwa ga Auntyna RUKAYYA GOMBE 🥰🤩😍

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HYpizDjKAkJB4QClSeLTvw

Dakata hajia💃💃💃💃💃 kin Dade kina Neman inda Zaki sai amintattun jaka, da takalma, sarkoki,masu kyau da quality cikin farashi Mai sauki❓
Ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,wannan gidan na RUMIEE UNIQUE BAG'S GALLARY na budeshi ne saboda na Baku damar siyan jaka,da takalma na Yara Dana manya masu kyau da quality da Kuma saukin kudi cikin aminci daga wajena.masu siyan daya da masu sari duk Muna mataba daku
Muna Kano Muna Tura kaya kowanne state da makotan Nigeria cikin yardar allah



13
Victims
IKHLAS
Ko lokacin da na farka, Iram da Aunty Khalisah na gani, hannuna da ya min nauyi na kalli sai dayan da aka saka mishi ruwa, a hankali kome ya fara dawo min na rintsa idanuna. Tare da fashewa da kuka. "An gama da ni, me yasa na zo? Me nayi na cancanci wanann kyautar? Ni ban cutar da kowa ba me yasa?" Na cigaba da kukana, har nurse suka shigo aka cire min ruwan nayi na shiga ban daki nayi wanka tare da alola na gabatar da sallah da ake bina, lokacin da na idar Lucky ya shigo da ledojin abinci. Kura mishi idanu nayi, "wani abu ne?" Dafe kaina nayi da yake sara min hawaye ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login