Showing 219001 words to 222000 words out of 304445 words
a matsayin Allah ne ya gwada imaninta ya nuna mata muhimmancin abinda ta wulakanta. Haka muka dawo gida, a hankali rayuwar Nady a cikin abinda bai wuce wata guda ba ta sauya ta koma mai miƙa lamarinta ga Allah, wani irin nutsuwa da tsantsani ya shige ta. Bata iya dogon magana ko hayaniya ake zata rufe kofarta, haka da Ijlal ta gani ta cigaba da iskanci tayi ta ihu ta zata ko rashin haihuwar ce take damunta ma'ana rashin samun cikin, haka muka yi ta rufeta baibai, iyayenta suka zo kamar su goya ni. Mamanta da kakarta abu ba abu ba zasu tambaye ni mai yasa bata magana. Dariya nake musu na ce musu. "Prince baya son hayaniya ne!" Wayyo Allah na, bayin Allah nan kashe ni ne basu yi da arziki ba. Tun a lokacin ni kan na daina damuwa da kome na yarda wata daukakar bata zuwa maka sai ta sanadin wani, domin kuwa kakanta wani kamfanin jarida ya min hanya nayi aiki da su kafin mu bar garin, domin an yi sai cikin yayi kwari zamu bar garin. Har lokacin babu wanda ya sani musamman Mahaukaciyar matarshi da cikin ya kara haukatata, domin rashin mutunci take, iyayenta kwanansu goma suka koma, sai ga Mai babbar daki tazo, wani irin Ihu da nayi ma rungume ta, ina ta ihu girgixa kai tayi tana rike kunnena. "Yaushe zaki girma?" "Ummi Ni ce Autarku!" Haka muka shiga ganin Nady ta fito tana murmushi. Ta riko hannunta idanunsu cike da kwalla ta ce mata. "Allah ya raba lafiya!" Murmushi tayi a hankali take kome, ummi ta riketa ta zauna sannan itama ta zauna. "Sannunku!" Murmushi muka yi, na dauki kayanta na wuce da shi dakina, hararata yayi yana faɗin. "Da yake baki da imani sai ki kai kayan dakinki don Allah ya kike so nayi? Rabo na dake ki min adalci mana."
Rungume shi nayi na ce mishi.."An jima mu fita shan iska sai kayi kome, Bana son kana barin Nady ita ɗaya ne, idan da wani a gefenta zata kara jin dadi." Shafa fuskana yayi yana murmushi. "Yaushe zaki dauki naki cikin?" "Duk ranar da Allah ya nufa!" Na fada, domin a ranar da ta dace na bashi hadin kai, nayi bakon watana. Ba karamin wahala na sha ba, amma wannan karon bai wuce kwana uku ba ya tafi sai ga Iyayen Nady haka yasa muka kara hakura da juna, sannan nima nasan ina pushing dinsa, itama Ijlal bata iya kome sai hakuri kawai.
Bayan sallah isha ya ce musu. "Bari mu leka wani taro da za ayi a makaranta!" Ya riko hannuna , Ijlal da bata zata iya hakuri ba ta ce mishi. "Shine zaka tafi ba zaka gaya mana ba, da yake abin Munafunci ne har kun shirya kayanku sai da kuka fito da shiri zaku gaya mana, girgiza kai Nady tayi ta bar parlourn Mai Babbar daki ta zuba mata harara. Muna fita ta fashe da kuka tana bata labarin yadda ake zaluntarta.
" Kina tsammanin zan barki, ki cigaba da mishi rashin mutunci ne rabuwa da ke dai yi domin ba zaki kashe min shi ba!" Tana fadar haka ta bar ta a parlourn, ni da shi muka fita zuwa wani babban hotel anan Scotland, janyo ni yayi a cikin elevator ya fara kiss dina, tun ina ture shi, har na shiga biye mishi muka isa floor din da muka kama dadin, ajiyar zuciya ya sauke muka fito zuwa dakin. Tun a bakin kofar yake matse ni har muka shiga cikin dakin, cikin wani irin fitar hankali yake bina kamar zai cinye shi, ina bin shi from the beginning har muka isa tsakiyar dakin, hmm, wani shagalin sai Allah ya haɗa ka da namijin duniya, da yasan kanshi domin cikin kulawa da tsafta da kaunar mara iyaka yake cinye ni tare da zungure ni daga farko har karshe, wani irin zungura yake min mai saka mace manta wani damuwa da duniya, asalin idan kana niman wata kalma da ake kira hukuna matata, shine asalin yaren da Mai Martaba ya fi ganewa, iya zungura da rarruka na sha a hannunsa, ya zane ni da bulalarshi mai shiga jiki, ya shanye duk wata damuwar da take tare da ni ya kuma rungume ni yana min godiya mai tarin yawa, shafa kanshi nake a hankali yana sauke ajiyar zuciya ya ce min. "Maisha kin san ma'anar sunan nan?" Girgiza kai nayi. Ya ce min. "Rayuwata ce ke...........
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 72
Bude idanu nayi ina kallonshi da dukkan mamakin da yake lullube a fuskata na kalle shi. "Me yasa ni ce?" Tashi yayi tare da janyo ni ya rungume ni sosai. Kansa ya daura a kafadata. "Ina son sonki!" Ya fada yana sumbatar bayana. Sannan ya cigaba da cewa. "Tafiya ce bana kare ba, sai dai ina fatan ko zan mutu na mutu a hannunki, haka kaɗai zai wadatar da rayuwata." Ture kanshi nayi ina jin wani abu yana yawo a jikina gwala-gwalan kalamanshi kara kashe shi suke a duk kowani fitar harafi, sai naji kamar gatse yake min ko ba'a na kasa nutsuwa na kasa zama. Dole na gudu ban daki domin ta nan ne kawai zan samu sauki daga kalamansa. Boye ni ban dakin yayi muka yi wanka a tare muna cikin ruwan a kwance ina kirjinshi nayi lumo ya ce min. "Ina fatan kema kin dauki karatun da na daurawa Nady!" Share shi nayi domin na lura idan na biye shi ba karamin abu za ayi ba.
Ina fitowa shima ya fito, a tunanina gida zamu koma amma ina shi bai san wannan zance ba, wani abu ya tsira na aiki, zama nayi jiran shi domin daure yake da towel irin bai gama abinda yake ba, haka lokacin Sallah yayi muka yi tare na zata zai ce mu wuce sai naga ya cire kayan yasaka kayan barci, idanuna ne suka cika da kwalla, meye nufinshi? "Yaya Ba zamu koma gida ba ne?" "Anan zamu zauna na kwana biyu!" Allah na zata wasa yake sai da dare ya fara rabawa na ga ya saka an kawo mana abinci, haka na kwashe wayata. Da wayarshi ya kira Ummi da Nady ya gaya musu. Bai gayawa Ijlal ba domin yasan a mahaukatan da yake gani ita lamba daya ne, haka naci abinci sannan na sauya kaya zuwa na barci. Ina zan iya mishi. Ganin na koma gefe ya janyo ni jikinshi yana wasa da kitson kaina.
A hankali barci yayi gaba da ni, ban kuma sanin inda nake ba, sai da hasken waje ya ratsa jikin labulen ya shigo dakin yana haska fuskana shi kuma yana ta aikinsa. "Yaya ban yi sallah ba?" "Kin gaji ne tsawon kwanaki kina tsaye ba hutu ai kin tausayawa kanki da jikinki!" Murmushi nayi na tashi zuwa ban daki nayi alola da ruwan dumi nazo nayi sallah, ina idarwa ana kawo abin karyawa. Yana gamawa ya ce min. "Zan shiga wani meeting, idan kin gaji ga wannan ki shiga cikin hotel din akwai wuraren shakatawa da hutawa, ki duba floor da room number din kin ji!"
Gyada mishi kai nayi, na mike tare da share mishi fuska na dan sumbaci kumatunsa sannan na rako shi bakin kofar ina d'aga mishi hannu, bayan tafiyarsa na koma dakin na gaji, kwanciya nayi na fara barci ban yi wanka ba sai karfe daya na rana ma tashi nayi wanka na rasa yadda zan yi da kayan jikina. A hankali na nufi wurin drower din jakar kaya na gani na bude riga da wando ne na maza, sai gefen kayan mu na hausawa ne, riga da zani. Ya aka yi ya zo da kayan bai gaya min ba. Cire rigar nayi da zanin na daura sannan na dauki wata after dress na saka akai, a hankali na fito ina kallon yanayin hotel din. Yayi min kyau.
Kamar xan fita sai naji bana son fita don haka ana dawo dakin na tsaya a bayan yar wurin shan iska dakin, yanayin garin yayi kyau haka nayi ta daukar hoto kaca-kaca,sannan na dawo dakin na bukaci abincin rana aka kawo min, naci na koshi. Wurin karfe shida dai gashi nan ya dawo, ruwan wanka n a shiga na hada mishi mutumin nan ya biyo ni ciki ya jika ni, a hankali muka lalace daga ni har shi, waje muka dawo muka cigaba da cin uwar sabada, sai da muka wujija juna sannan na samu nutsuwa, ya sake sani wanka. Fita muka yi da shi cikin garin muna yawo bamu dawo ba sai karfe uku na dare, muna isowa gida hmm, mutumin nan lalata min tarbiyya yayi ya man da ni yar iska. Domin ko bayan sallah asuba wasu jahilan kaya ya dauko min yana faɗin. "Saka min na ganki a cikinsu!"haka na saka sannan na fito mika min hannu yayi na nufe shi. "Ina jin dadin ganinki a haka!" B agari ya waye ba meeting ya dace ya tafi amma mutumin nan kamar wanda yake da lafiyar injin musamman wanda aka sakawa Ammasco injin oil. Wayyo Allah na kasa motsi nayi saboda yadda jikina yayi laushi, wanka ya min da ruwan dumi muka koma gadon, kwantar da ni abu daya nasan na kai bakina hot chocolate daga nan barci yayi gaba da ni, karfe biyu na rana ya tashe nii muka ci abincin rana, sannan nayi wanka na kwanta barci yayi gaba da ni, yana dakin yanata aiki. Wayarshi da take gefen goden ya tashe mu ashe shima ya biyo ni muka rama barci. Dauka nayi na saka a kunne zan yi magana ta ce. "Allah yana ganinka, hakkina da kake dannewa, shine ya fitar da matsiyaciya yawon shakatawa, ni kuma ka barmu a gida shegiya mai zubin karuwa."
"Na gode sosai Allah ya kai ladan kabarin mahaifiyarki " ina gama kai aya na kashe, na barta da ihu, ba zan iya tashin hankali da ita ba. Don ba Sa'a ta ba ce.
Kwanaki biyar na kwashe ina hutawa kafin ranar na shida. Muka bar hotel din muka wuce gida. Lokacin da muka isa Ummi ta ce min. "Na zata zan biku da kayanku ne?" Murmushi nayi na ce mata. "Gamu nan Ummi!" Na faɗa ina zama a kusa da ita. Ji nayi an fisgo ni tare da rufe ni da duka, kamar Yarta. Ummi da abin ya ishe ta itama ta rufe ta da duka. Ta gaji a cikin kwanakin da suka yi da ita ta fahimci gidan ba zai zauna lafiya ba matukar Ijlal tana gidan. "Ummi kyaleta abokin Mutuwa take nima!" "Karya wallahi ta tab'a ki ja'ira mara kunya!" Haka ummi ta kyaleta bayan ta ci duka itama. "Ba zan barki, ba idan na barki zuciyarki akwai mugun abu zaki aikata kome jibi tare zamu bar kasar nan!"
"Wallahi duk ranar da kika haihu ki bawa wani labarin sai na rama na rantse ba zan kyale ki ba!" Haka na wuce dakin yayi ta bani hakuri Nady ma ta bani hakuri har tana cewa. "Baby ta ce ki yi hakuri!" Gyada kai nayi na share amma tabbas sai na rama. Haka muka zauna na tsawon wuni biyu bata san tayi kuskure ba, sai da ta ga Mai babbar daki ta shirya kayanta Itama ya ce ta shirya ya mata saya mata kayan haihuwa gijib ya turata da Ummi suka dawo, sai ranar na samu damar kuka sosai haka yayi ta bani hakuri, Ashe tun kafin ta isa labari ya bazu tayi min shegen duka. Aka yi ta jinjina mata da ciki ta dake ni. Amma an korota lokacin da Daulah da Aneesah, bilkis, Kubrah suka zo tarban mai babbar daki, suke jiran ta basu kanun labaran. Aikuwa ta shiga basu labarin iskancin da tayi min mai babbar daki tana sallah. Bata san lokacin da ta sallame ba ta ce mata. "Karya kike yi. Shammatarta kika yi muna gaisuwa suka rufe ta da duka, nima kuma ta rufe ki da duka, ina jiran Yaya Yarima da Mardiya ba zaki kashe kowa a gidan Salmanu Faris ba. Tunda kin ji kin gani hauka zaki yi gara ya cike sakin biyun da ya rage ki je can. Yarinyar nan kowa yasan bata son shi amma ta zauna da shi ita da ya da ce ace tayi yaji ke da yake jaka ce saki ya miki. Kuma wallahi ki koma gidan Ubanki ba gidan Yaya Yarima ba domin ba zan kyale ki a can ba!" Yadda Mai Babbar daki take shiga ba nan take fita ba. Sai bayan isha Hajiya Mardiya tazo, da bakinta tayi ta bada labarin abinda ta aikata. Haka yasa suka bata rashin gaskiya suka mata fata-fata musamman Ubanta da ya nuna bai da karfin riketa ai ita matar manya ce. Gara ta rufawa kanta asiri ta zauna. Hajiya Mardiya kallonta take cike da bakin ciki domin akan Yarinyar nan wani irin kashe kudi ne bata yi, musamman aikin da suka dauka na Ikhlas, bokan ya ce musu gaskiya aikin bai zama dole ya yi kyau ba, domin ita kanta kullum cikin tsare kanta da mijinta take, koda zai yi aikin sai wani ikon Allah. Haka yasa take ta kashe kudi karewa har mahaifar mace aka binne da mataccen jinjiri amma yarinayr nan take mata sanadin da zata rasa damar mulki da gidan Salmanu Faris, wannan abin ya mata ciwo kamar ta zubar da kwalla. Bata ce mata cikanki ba har suka dawo gida, ya washi gari Alhaji Yarima yana barin gida, Hajiya Mardiya ta rufe ta da mugun duka da wayar wuta kamar zata kashe ta don ma ta kiyayye cikin jikina, amma fuskartar da kafarta ya cu bugu. "Na gama daukar zunubi saboda ki zauna a gidan na kafa ki a zuciyar Uwarsa amma kika yi fatali da abinda nayi. Daga Ikhlas har Nadiyya babu wacce ta samu yardan Maryama kamar ke amma kika janyo ta ce sai ya sake ki, kin ji abinda Lalataccen Ubanki yake yi, ban da masifa da ciki zaki tari fada da Ikhlas idan ta ture ki rasa cikin jikinki waye kika yiwa asarar? Ke da ita kun zama daya tunda ita ba haihuwa zata yi ba, amma.da yake ke kin fi shaidan kina kishi mara aji, ki duba da kyau zaman da kika yi da su me sukewa junansu ? Sai dai a fadin sun yiwa juna Alkhairi ke da yake jaka ce kin je kina ta hauka har kina fitowa da kishinki waje kowa yasan zaki iya aikata wani abu. Ban tab'a ganin jaka mara lissafi irinki ba, sai ki zauna zaman jiranshi, yana can yana shekar soyayyarshi da matansa!" Kai Ijlal ta gama bala'i. "Ko Yarana ban kauce hanya akansu ba, amma ke da yake jaka ce kullum.abu daya na rasa yadda xan yi da ke,ke ba yar rufin asiri ba ce idan mutum ya sake zaki tona mishi asiri. Tow ki sani ko kin tona min asiri sai dai ki zauna a wuri guda Ni Yarana zasu rike ni."
Damar da take samu ta tsula tsiyarta Haniya Mardiya ta ce bata ji ba, bata gani ba abinda yan aiki suke ci shi take ciki wulakancin da take mata a gidan sai Allah ya ce mata. "Kina iya barin kasar waje kika zo nan don masifa ai karshen iskanci ya ƙare."
***
Tunda suka bar gidan sai na ji kamar an bude min kofar shan iska. Wani irin dad'i da nutsuwa ba damuwa ba tashin hankali. Ririta cikin Nadiya da yake samun kulawa daga ko ina, ita kanta har mantawa take da ta tab'a kunci akan rashin haihuwa. Sai gashi kowa yana sonta cikin jikinta. A hankali kome yake tafiya mana cikin yana cikin wata na biyu ta fara wani irin laulayi, ruwa take sha kamar ba gobe, bata cikin kome gara wani lokaci tana cewa zata cin alele da kunu, haka aka nimo alkama na jika shi na markade shi na tace shi, sai gyad'a markadadden na damma nayi mata kunu da alele, tana ci tana kuka. "Mamy kin ji yadda nake ji? Mamy Alhamdulillahi amma haihuwa ba sa'a Yaro ba ne!" "Allah ya baki lafiya!" Mu da iya kanmu wata uku ne sai gashi mun kai wata hudu, a lokacin aka ta kiranshi musamman Ijlal da haihuwar yaki zuwa, haka dai muka fara shiri, mun yi akan Nady zata zauna a wurin iyayenta har na tsawon wata uku idan cikin ya shiga wata bakwai za'a zo a dauke ta..
. Wannan abinda yayi mishi dad'i itama ta ji dadin at least zata nutsu zata samu kwanciyar hankali. Haka muka iso abuja gidan iyayenta, na samu Babanta tare da Yaya muka mishi bayani na bashi surrorin da za a nan rubuta mata. Ni da kaina nayi tawadar a gidan sannan na samu mai kula da gate din naga irin buzu nan ne, zama nayi da shi na bashi abinda nazo da shi. Dattijo ne yayi dariya. Ya ce min."akawali kin ki musaya. Ki yi hakuri da baƙin alkalami mai rubuta ƙaddara, zuciyarki da halayenki kaɗai zasu jagoranci ki da izinin Allah idan kin rasa haskinki, ki tuna akai wanda kika yi yaki kanshi. Allah zai bude miki haske a cikin duhun da yake gabanki, zaki ga rayuwa zaki yi kuka ke daya zaki yi dariya zaki yi ta fadi tashi. Amma ke dai ba dai mutum ba sai da ta Allah duk wanda ya nufe ki da sharri zai rayu kamar mahaukaci,amma a rike hirji ban da wasa kamar yadda kike, ayi ata addu'a ayi ta nima a wurin Allah ga haske da budi can da nasara amma duhun da yake kan hanyar cike yake da ƙayoyi masu matukar dafi. Akwai mafita daga rabbi, kada ki tsammanci halacci domin bai zama dole ba, ke dai wanke zuciyarki. Lu'ulu'u! Gaki ga Shagonki wannan karon Allah ya sa mu dace ya kawo mana