Showing 141001 words to 144000 words out of 304445 words
ce naji dadi ba amma shigowar da yaso yayi ya bani tsoro, kuka nake sharshar ina jin kamar na rufe shi da duka. Tashi yayi ya wuce ban dakin parlourn bayan ya shiga na sauka a hankali na lullube kayana na saka tare da rarrafawa na bar mishi parlourn, a hankali idanun kowa bayan ina jin Maluma da Umma suna parlourn Abba, na shige dakin Maluma na shige toilet ruwan zafin plast dinta na juye na shiga da sauri har ina sauke ajiyar zuciya, kwalla yana zubo min, sai da na wanke jikina na gyara jikina nayi tsarki har zuwa lokacin wurin bai daina ciwo ba, haka na sake zama cikin ruwan zafin ma fito. Ina ga ga idan ya shiga sai abin ya fito ta bakina, ina fitowa na kwanta barci domin kukan da nayi ya saka min ciwon kai da kuma kokuwar da muka yi yasa ina jin gajiya ga cinyoyina da suke min wani irin ciwo kadan-kadan , wannan bai shiga ba kenan idan kuma da ya shiga tow sai na kwanta a gadon asibiti. Lokacin da Maluma ta shigo ta samu ina barci bata tashe ni ba, amma ta ga yadda nake abu kamar bani da lafiya. Tashina tayi ta ce min ."zaki sha magani ne?" Girgiza mata kai nayi ina kawar da kaina, saboda bana jin dadin kome, kwanciya nayi ita ta zata wani abu ne can ya haɗa mu tunda tasan ni kunci.. bata kawo wani abu ya min ba sai ta share ni.
Lokacin da ya fito pant da bra din ya samu a parlour sai ya dauka ya saka a cikin aljuhun wandonsa ya bar gidan bayan ya sha tea din cikin nishadi yana jin ko yanzu ta same ta, sai ya sake turmushe ta zai yi ya sha shayinsa hankali kwance yana murmushi, Zeenah Sarkin tsoro da ta sake ya shiga cikin jikinta tabbas sai ya jikatatta da kyau ya mata bugun sakwaran hege, yadda zata daina kallon kwayar idanunsa tana mishi renin wayo. Yana gama sha ya cire kudi mai yawan gaske ya ajiye akan tiren da wani karamin box tun daga Saudiya ya zo da shi yar karamar takardan da yake amfani da ita tare da biro ya rubuta mata. *Thank you for everything! Sleep well and have a wonderful dreams!* Kafin ya tashi ya saka a kasar kudin da box din ya bar gidan. Yana tafiya yana murmushi yana kara jin shi a wata duniya na daban, Yes saura kiris ya karasa shiga jaharshi. Baya jin wani abu zai dakatar da shi. Har ya isa gida murmushi yake yana shiga yayi parking sannan ya rufe motar ya manta da wani wando a aljuhunsa. Dakin Nady ya shiga ya samu tana barci tunda aka mata aikin take barci a ka'idar aikin sai ta yi wata guda kafin ta karɓe shi, haka ya wuce bangaren shi ya sake wanka cikin nishadi sai ga Ijlal ta sha wanka itama tana wani warin turare, abinci ta kawo mishi ya ce ya koshi don ya sha tea da snacks kafin ya fito kuma dubi a ci tuwon dawa miyar danyen kuka wato yarbo, ga man shanu ga yajin daddawa mai kamshin nama.
Yana zaune ya kunna wayarshi yana dubawa ko zai ganta amma ina yasan tana barci, kallon Ijlal yayi da take can kamar mayya ya ce mata. "Ki kashe min wuta ki fita!" "Ni nazo kwana ne!" "Kina shan maganin da na ce Faruq ya baki?" Shiru tayi tana kallon ƙasa ita fa tunda ya bata maganin bata kuma sha ba wallahi. "Kina da infection, Kuma na dauka sannan nady ma ta dauka ki gyara jikinki kafin ki dawo domin ni ina da tsafta in ba haka ba zaki tafi gidanku bakiɗaya!" Ya mike ya barta a dakin tana zare idanu, tun daga yanayin case din Nady likita ya tabbatar akwai shigar infection jikinta bayan wancan case din, yasan Nady yar gayu ce amma abu daya ke hada shi da ita cream dinta da suke karni idan tayi amfani anfani da su, yanzu da aka fara magani duk ta watsar ta koma normal Vaseline wato blue sea. Haka yasa yake jin tausayinta domin lafiyarta hatta abinci sai da aka saka mata doka don a samu lafiyarta ko zata dauki ciki, shi yasa kafin su bar kasar ya bawa Ikhlas wannan da kome na jikinta kamshi yake yau ya kuma tabbatar da tana shan magani. Wasu ashar Ta sake a dakin ta fito kamar mahaukaciya. "Wannan ma waye?" Ta nuna mishi pant din Ikhlas, tasowa yayi ya kwace yana faɗin. "Nawa ne! Wani abu ne!" Wato da ta lallayo asharar ta buga ta ce mishi. "Yaushe na miji ya fara saka pant? Ni zaka renawa hankali? Idan na yarda Allah ya tsine min!" Ta fada da karfi tana ihu. Wuce ta yayi yana mai saka pant din akanta shi ya wuce abinshi daki ya kwanta yana mai saka wandon akan fuskarsa. Yadda take yi tana bala'i zaka ɗauka kama shi tayi da wata mace, nan kuwa kishi ne hayaniyarta ya tashi Nady ta fito tana me buga mishi kofa. Yana tashi ya bude mata kofa ta shiga. Rungume ta yayi yana faɗin. "Mun tashe ki ko?" "Meke faruwa ne?" "Pant din Zainab ta gani a cikin aljuhun wandona take ihu." Murmushi tayi duk itama maganar ya dake ta, ta kira mishi idanu. Kafin ta furta a hankali ta ce. "Ayya ai hakuri ake. " Ta fada a matuƙar sanyayye, kafin ta ce mishi. "But you love Zainab badly!" Rungume ta yayi yana daura kanshi a kadafarta. "Idan nace miki ina sonta it was like im lie, I don't know what I'm feeling about Zainab but she is special for me, idan nace miki ta dabance kada ki ji haushi amma ita gani take kamar sha'awaeta nake kuma gaskiya ne ina sha'awararta kamar na zaucce. Nady ina gaya miki gaskiya ne kada ki ga na fara hauka ki ce wani abu aka min son Yarinyar ce yake azabtar da ni, da ta gaya min ya kusan rungume ta sai da naji kamar zan mutu Nady a yanzu idan na ganta da wani ya tsaya da ita zan iya kashe su bakiɗaya ns huta." Hawaye ne yake zuba a idanunta domin ta fahimci already yayi found abinda yake so, Zainab yake so da dukkan zuciyarshi. "Am sorry ina sonki kema!" Girgixa kai tana murmushi ta ce mishi. "Idan Zainab Junaid kake so. Sai na kashe duk wani abinda na mallaka domin ta zauna da kai, ni ma zan zauna ina kallonku haka zai saka naji dad'i, koda baka soni ba zan ji a raina ka samu macen da kake so ko yaya ne baka wulakanta ni ba, aurenku ya sani kara samun ilimi akan iyaye na gari, duk da rashin kirkin da tayi A baya ta zauna don iyayenta, ta daina kome don iyayenta, da naje gidansu Babanta addu'a yake min yana bani hakuri akanta ya ce min bata ji amma da na zauna da ita sai na gano ba rashin ji ba ne irinta ƙalilan ne babu ruwansu da kowa, Iyayenta mutanen kirki ne masu kirki da mutunci. Kayi sa'a don ko Allah ya bani haihuwa zan yi fatan Zainab ta taya ni renon Yarana. Kukan da nake yi at least ka samu matar da kake so ka samu macen da ta dace da kai, sannan ina tausayin kaina ne kada ka juya min baya,sannan ina tsoron kada na rasaka sune kuka na, sune damuwata sune tashin hankali na,
#Goodnight
*Account Details:*
*08130269641"
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500₦
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 46
"Can I promise you, ba zan tab'a barin wani abu ya cutar da ke ba? Zan iya miki alkawarin har abada ba zan daina ganin girmanki ba? Nayi alƙawari da Ubangijina duk macen da take karkashina ba zan bari ko sauro ya mata kuka ba. Matukar ina da halin ƙare ta zan tabbatar na kare rayuwarta." Shiru yayi yana murza yatsunta kafin ya sumbaci goshinta,Nady mutum ce da ba zai iya wulakanta ta ba, ba zai iya cutar da ita ba. Ba zai ce baya son Nady ba, sannan ba zai ce asalin soyayya yake mata ba, amma yasan From beginning yana da interest akanta." In sha Allah zaki haihu zaki haifa min Yara masu blue eyes dinki, zaki haifa min Yara masu yawa masu albarka." Ya fada yana kara rungume ta.
*IRAM*
Maganar gaskiya idan wani zai gaya mata tana wani abu ba zaka yarda ba, domin ko a magana ko a idanun bata nuna ita din ta lalace ba, kasa hakuri tayi ganinsu sai da ta dawo window waje, ta bude tare da leka su har suka kashe wutar parlourn, duk abinda suke da sautinsu hatta fitar Salmanu Faris a gidan tana tsaye, yana barin gidan ta ga kuma kome a hankali ta bar gidan, tun a hanya take kuka har ta isa wurin Saimah Shaiba First.
Zubewa tayi tana kuka me cin rai. "Me aka miki?" "Aure nake so. Aure nake so nima na rama abinda Ikhlas ta min, Aunty Saimah aure nake so yi!" Zuba mata idanun Saimah tayi tana mamaki kafin ta zaunar da ita.."kina da saurayi ne?" Girgiza kai tayi tana kuka wiwi. "Baki da shi kike batun aure kike so? Shi kenan zan nima miki mijin aure amma ki sani sai kin shirya." A hankali ya shiga mata abinsu na yan bariki kafin ta fada komarta suka cigaba da kwakule juna, bata dawo gidan ba sai sha daya saura ta shiga tsohon dakinsu ta ga Ikhlas bata zo ba, wato tana dakin Maluma. Itama dakinsu ta wuce ta shiga ta kwanta. Tana kwance ta tuna ai Saimah ta bata vibrating tashi tayi rufe kofar kafin ta kunna shi, a hankali ta ke gogawa a gabanta har jikinta rawa yaƙe saboda karfinshi. Kafin wani lokaci ta jika zanin gadon domin har fitsari sai da ya sakata, haka yasa ta nutsuwa. Tana gamawa ta ajiye abin ya shiga ban daki tayi wanka, sannan ta gyara gadon ta kwanta, kasa barci tayi tana juyi nishin Prince yana yawo a kunnenta, kalmansa da yayi ta amfani da shi wurin Rarrashin Yar Uwarta ya tsaya a ranta, kasa magana tayi tana juyi tabbas dole tayi wani abu, dole ta nimawa kanta mafita.
*
Kiran sallah farko na farka, ban daki na shiga na kara gasa jikina sai naji dadin kasata, sannan na yi alola sako ya shigo wayata yayi hasken maza na duba. *Kin manta pant dinki a cikin aljuhuna thank you for the last night!* Gabana ne ya fadi da sauri na fita waje, ina jin motsin Maluma a kitchen, parlourn na koma na kunna wuta, a hankali nake raba idanu a cikin parlourn bra dina na hango da sauri na dauka ina jin kamar zuciyata zata fita, zama nayi a gaban tiren ina kallon abinda ya ajiye min, murmushi nayi a hankali, ina kallon yadda muka yi ta juyi a parlourn sai nake jin kamar a lokacin kome yake faruwa, kaina yayi wani irin girma, tashi nayi jin zaa shiga sallah. Na nufi cikin gidan da tiren a hankali nake typing, yadda kasan kwai ya fashe min. A hankali na shige parlourn Maluma na ganta akan abin sallah. Wucewa nayi daki bayan na ajiye tiren, nima nayi sallah ina idarwa na fara azkar, bayan na isar da azkar na koma na kwanta barci mai nauyi ya dauke ni,
Barcin safe yana da dadi. Amma a gare ni barcin bai da fa'idar yinsa, domin ban jima da fara barci ba, na ji an tashe ni. Bude idanun nayi na tsinci kaina a wani daki, kallon ko ina nayi Yes wannan dakina ne na gidan Salmanu Faris, amma yaushe na dawo. Yan mata ne a gabana suna durkushe sanye da wasu irin kaya kusan duk iri daya ne, kayan jikinsu sake kallonsu nayi na ga kamar har da Wildat da Sailuba, kallon. "Ranki shi dade, ki wanke fuskarki!" Kallon tasar zinarin da yake gabana nayi, suka matso min da shi, tare da d'aga min kallon fuskana nayi na ga ba fa ni ba ce, wacece ni? Na juya da sauri na kalli Madubin Allah ba ni bace, ina na ke? Na shiga shafa fuskana. "Ana sanar da Gimbiyar Zanzabira ga Magajiyar Zanzabira ta iso." Bakiɗaya yan matan suka durkusa cikin ladabi da biyayya. Bude mata kofar aka yi ta tsaya tana kallona. "Ni Aojana ba zan lamunci ganin Awatif ta zama da mijina ba, idan na kyale ki tabbas kece zaki haifi magajin Bokanya Ajuji bata yi karya ba, sai na kashe ki!" Ta nufe ni da wani wukar zinari, kare kaina nayi da dukkan hannuna. "Ke Aojanah!" Ya daka mata tsawa, tsayawa tayi sanye yake da kayan sarauta shima, kallonshi nayi Yarima Faris, rike bakina nayi ina kallonshi. "Taso Awatif ba zata iya kome ba, ina son Awatif ni nan....." Kafin ya karasa matar nan ta nufe mu da wuka ihun da na kwala a mafarkin ashe har a zahiri ma ihun nake. Rirrike ni Maluma tayi tana tofa min addu'a, yadda nake ihun ya matuƙar razanata, "yaushe kika fara kwanciya babu addu'a?" A matuƙar razane nake kallon Maluma, kallon yadda na birkice yasa ta kara tofa min addu'a, har na samu nutsuwa, ita kanta mamaki nake bata yadda na jingina da bangon ta kalle ni kafin ta mike tana faɗin. "Matuƙar kika ce ba zaki yi addu'a ba aiki ya same ki, gara ki saka Allah a cikin lamarinki, kisan inda kike rayuwa ba ko ina bane sai Masarautar Zanzabira. Barci babu addu'a ba naki ba ne ko wani bai neme ka ba, kai ya kamata ka tashi akan kafarka muna wata zamani da kana barci wani yana maka minshari, don haka Addu'a azkar da sadaka ya zama farilla akanki sama da kome, na sani baki wasa da sallah, amma kuma Wannan gabbar dole na tuna miki girman hakkin da yake kanki ko don abin cikinki dole ki kula da addu'a!" "Abin cikina kuma?" Na tambaye ta domin kuwa na san lafiya ta lau, a ina kuma wani abin ciki, harara ta tayi tana faɗin "an jima Mijinki zai zo ku koma gida ni ba zan iya wannan rashin kunyar ba, " ta fada tana barin dakin, wani abin mamaki na manta da irin mafarkin da nayi sai ma wucewa ban daki da nayi, ina fitowa ana kawo min abin karyawa, kallon yarinyar nayi da mamaki. "Yaushe kika zo? Wasu Maluma kike yiwa aiki?" Murmushi tayi ta ce min. "Baki gane ni ba ne? Kalle ni da kyau?" Kallo daya nayi mata, nayi ta tunanin inda na san fuskar, matar mafarkin da nayi ganta rike da wuka ita kuma dauke da ruwan zafin tea din da ta kawo min yana tururi zata watsa min, na rintsa idanuna da karfi, ina jiran saukar ruwan naji Maluma tana faɗin. "Lafiya Lami?" "Lafiya Malama na kawo mata abin karyawa naga tana kare kanta." "Ke Ikhlas bana son iskanci, meke damunki?" Zare idanu nayi ganin yarinyar rike da tiren abin karyawan. "Wani irin shegentaka ne haka? Lafiyarki kuwa?" "Lafiya lau Maluma kawai kaina yake ciwo!" Na faɗa kamar zan yi kuka, shafa kaina tayi tana faɗin. "Allah ya kyauta!" Sannan ta fita a hankali na sha tea, wayata ce tayi ƙara ina dubawa naga Yeemar, dauka nayi na saka a kunne. "Ke ya labarin Abba?" "Lafiyarshi lau an dawo da shi gida Beb kina ina?" Na tambaye ta, "Gani zan tawo wurinki ko Mijinki zai barki mu shiga kasuwa sayan anko?" Murmushi nayi na ce mata. "Shi kenan, bari na tura mishi sakon zamu fita!" Ganin haka muka yi sallah, tura mishi sakon nayi kamar haka. *Zan raka Yeemar kasuwa cire ankon bikinta please!* Nasan idan girmansa ya motsa sai ya ce ba zani ba, ni kuma naci alwashin bikin nan zan yi rawan jiki da na kafa tunda ba ayi a nawa ba, ai kuwa ina tura mishi sako ko minti biyar ba ayi ba sai ga kira. Dauka nayi ina haɗe rai. "Assalamualaikum!" "Amin waalaikumunsalam ya jikin naki?" "Ni na ce maka bani da lafiya ne?" Na tambaye shi, "hmm baki gaya min ba, amma kuma ai nasan bakiɗaya lafiya!" "Ni lafiyata lau!" Na faɗa ina haɗe rai. Duk da baya ganina murmushi yayi ya ce min. "Ni nasan baki da lafiya, amma da yake shanshani ce ke mai kafar yawo zaki shiga kasuwa da aurena kina tafiya kafarki a ware ko?" "Kambu!" Na faɗa ina hararan wayar kafin na bashi amsa ya ce min. "Bar cire wayar a kunne ko kin harare ni ba gani xan yi ba, gara ma ki sani ba zan amince shiga kasuwa ba." "Amma ai matanka suna abinda suke so me yasa ni idan nace zan yi abu zaka fara nuna min rashin adalci? Kafi kowa sanin ina da tawa rayuwar da zabina amma na zauna kake min yadda kaso, ban damu ba amma yanzu kace ba zan shiga kasuwa da Yeemar ba wannan shine adalcin da kake yi, fisabiilillahi na gaji wallahi kayi yadda kake so da Ni matanka su yi yadda suke amma saboda kai kana tsoronsu ba zaka iya gaya musu gaskiya ba sai idan abu ya zo ta kaina zaka fara iyayi da mita, ba zan yi ba baka amince ba. Bayan ni ba haka nake maka ba, Allah ya gani ana cutar da ni da wnada nake da burin aure ne ba zai min haka ba!" Na faɗa ina kokarin datse wayar cikin sanyi sanyin shi ya ce min. "Ni Salmanu Faris Attahiru Yayari na ce ban yarda Zainab ta fita ba idan kika fita kuma ki sani Allah yana ganinki, don shi ya ce muyi aure mu bauta mishi ta auren amma tunda kin kira ni da matsoraci zan cigaba da tsoronki." Ya katse wayar, nasan ranshi ya b'aci amma haka da nayi mishi shine kawai abinda xan yi na huce b'acin raina, sai dai kuma tunda nayi mishi haka sai