Showing 258001 words to 261000 words out of 304445 words

Chapter 87 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

84

iska mara kunya, shegiya lalataciyayya da me kike da shi da zaki hana shi isa ga iyalinsa bayan yana da lafiya kece jaka." Zagi cin mutuncin kai babu wanda bai mata ba, sannan aka kaita dakin masu aikin gidan ta zauna. Kayanta kuwa ya rabawa matanshi kaf, don ma ba duka aka kwaso ba. Duk wannan azabar da aka mata tana ji ranta duk ranar ta samu damar fita tayi ido hudu da Nadiyyah sai dai Uwarta ta haifi wani kada ma Ikhlas ta ji labarin.

Tunda b a sake ta yayi ba zata yi shiru, ita yanzu bata jin akwai wani magani ko boka da zai mata aiki, in sha Allah aikinta shine boye kishinta, ya bisu da makirci. Sai ta musu abinda ba tab'a ji ko gani ba, babu wacce zata haifi Dan da zai kwacewa Amirah soyayya ba, yadda ta hango Soyayyar Uban da y'a a cikin idanunsa bata jin zata bari Nadiya ta haifi cikin jikinta lafiya.

***
Jama'a na manta Iram, ashe Uwarta tana can yana ta nimanta da tashin hankali, Abba yana sane da kome bai gaya musu, haka ya share sai Tauhid ne ina hanya ya gaya min ana niman Iram na jajjanta mishi kamar ban san kome ba. Ni da Bestie muka dauki hanya zuwa camp amma kusan ina matar mai rawani ba zan zauna a camp ba ko? Haka yasa masarautar Gombe ta tura aka dauko mu ni da Bestie, aka kai mu bangaren Hajiya Nana Uwargidan sarkin Gombe, nan fa aka shiga hidima da mu, cikin girmamawa da dattako, yadda ake kaf-kaf damu kamar kwai take naji kamar nima ina da nasaba da ahalin sarauta ko don jinina da yake gauraye da na shine. Tunda na iso na kira shi muna ta ɗan hira yake gaya min ai ya tura Matarshi gidansu zai ja labarin na ce mish, Allah ya kyauta. Haka muka rabu ina bawa Yeemar labarin abin dariya tayi tana faɗin. "Kin san Allah, yarinayr nan ita ce ƙaddaranku, ki lura da zaran ta fara abu zaki ambaci Allah, zaki kasance kina yawan tuba, ba don kome ba sai don tashin hankali da kike shiga kin ga kenan ita din ta kara pushing dinku zuwa ga Allah." Wallahi sai na ga maganar tayi dai-dai, Addu'a nayi Allah ya saka mu dace kawai.
Haka tunda muka zo bamu zama, da safe nake kiranshi ko ya kirani, ranar da muka cika kwana hudu ya gaya min Nadiya ta farka, da yamma bayan mun dawo ya kirani video call, ina ganin Nadiyya fuskartar ya kumbura, abin tausayi, hira muka yi da ita wnada rabi zolaya ce da matan addu'a sosai, sannan muka rabu, tana faɗin. "Mammy yaushe zaki dawo baby tana kiranki fa!" "Yana kirana dai!" Murmushi tayi tace min. "Mammy mace ce tun a Abuja suka tabbatar da haka!" "Ubangiji ya kawo mana Sultanah lafiya!" Tun daga lokacin na saka mata Oum Sultanah, shi kuma na koma Abbyn Sultanah. Shi kasan yasan yadda nake son yarinyar tun ba a haife ta ba, a gaban iyayenta take gaya musu ita idan ta haihu yar wa Ikhlas zata bawa, Hajiya Altine tayi mata addu'a sosai da kuma idan tasan ba don Allah zata bada yar ba kada ayi nisa domin zata iya baro jos ta ci Ubanta, itama yar zafin kai ce.

Haka aka yi ta kula da Nadiyyah, Doctor Munirah tayi kokari kuma tana kan ƙoƙarin.

Ranar da muka cika sati daya ba sai ga Mutuminku ba, ranar juma'a mun dawo daga camp, ban san ya zo ba ina Issa bangaren Fulani Nana ta bani wasu kaya masu tsada da alamu sabo ne fil, ta haɗa min kayan na musamman na gyaran jiki, ina gamawa n a fito na samu mai musu kwalliya na sarautar, wai aka yi aka bar ni a baya ban sani ba, haka kada gyara min jiki nayi sallah da yake alola nayi kafin isha mu hadu har lalle ja da baki an zana min, ina ganin haka na sake murmushi, na kalleta na ce mata. "Aunty Fulani Mai Zanzabira yazo ko?" Bude wani drower tayi ta ciro wasu kofi masu kyau ta haɗa min gumba mai kyau na madara ta bani na fara ci sai wani ruwan zuma da wani madara ta bani na shiga sha, dama tunda na iso cimar da ake bani daban na Yeemar daban, ko yau da safe an bani wata farfesun kaza da hadin ridi da wasu gadali. Naci. Hak yasa n a fahimci matar tasan kan rayuwa, itama ta fahimci wani babu ne a yadda kullum sai ya kira mai Martaba Sarkin Gombe ya gaya mishi a kula mishi da Fulani Babba yana hanya, kai Salmamu Faris bai da kunya, yadda aka yi abinci aka jera yasa ni jin wani irin abu a raina na fahimci, Allah sarki bayan sun dawo Masallaci ta ce muje ashe har da mijin Yeemar. Ina ganin Mijina da sassarfa na rungume shi ina bubuga kafana a kasa ina faɗin. "Shine baka gaya min ba?" "Sorry Baby!" Ya fada yana kara rungume ni, mijin Yeemar jan Matarshi yayi suka bar mu anan can hotel ya kama musu, ni kuma ɓangaren baki aka bamu, dakyar ya nutsu ya ci abinci. Tun a parlourn aka fara cin uwar sabada, tun ina buge hannunshi har na kyale shi domin ba yadda na iya da jarumina kuma sahabina. Wato tunda muka shiga muke kashe juna da kauna, Ya ilahi, na rasa inda zan saka kaina don azabar kewarshi ni daya nasan yadda nake ji da kewarshi. Zama yayi na zauna akanshi tare da rungume juna, a wannan yanayin ni daya nasan yadda nake ji, ina rungume da shi, sai da muka gaji don kanmu, muka kwanta bayan mun fito wanka.
Kusan yadda ya bani labarin gida kamar na bi shi idan zai koma, haka na kara kwanciya a jikinshi. Har barci ya dauke ni, ina barci ya ce min. "Hukuncin da kike yiwa Iram ya isa haka!" Tashi zaune nayi na ce mish. "Waye ya gaya maka?" "Abba!" Ya janyo ni, hankalin Uwarta ya tashi don Allah ba don na isa ba a kyale ta haka!" "Zan duba lamarin!" Na kwanta ba tare da na kara magana ba. "Zainab duk wanda aka bawa hakuri an zalince shi ne ki yi hakuri na ce!"

"Shi kenan ai nace ya wuce!" Duk yadda yaso na sake naki, haka muka kwana raina ba dad'i, washi gari na kira Faruq bai biyo shi ba na gaya mishi a sake Iram. Haka kuwa yayi ya kaita asibiti, domin ina sane da yadda take bawa jikinta drugs yasa ta kamar zata yi hauka, haka yasa na kira Abba na gaya mishi, lokacin da ya ganta sai da yaji ya damu ya tambaye ni mai ya faru na gaya mishi abubuwan da take sha, haka ya sa ya dirka a Part din su ya saka aka bincika mishi gidan sai ga shi na fito drugs....
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 85
Kaduwar da Abba yayi ina ji sai da jininsa ya yi mugun hawa, haka Maluma da Umma suka gaya min yana asibiti, na ce matuƙar bai cire iram da Uwarta a lissafinsa ba jininsa zai ta hawa ba damuwarsu bane, washi gari haka na tashi suku-suku sai bina yana lallabani, kusan dukkanmu muna kewar juna amma abin jiya yasa na ji ya gundire ni sai na kasa sake jiki da shi ko ya fahimci haka ne sai ya shiga jana a jiki yana min hira da bani labarin abinda yake faruwa a fada, da yadda ake wasu abubuwan da bai sani ba.
"Yanzu damuwata shine na gano su waye suke sponsor wasu abubuwan a cikin fada, kaina ya rike wuta domin duk wanda
kika yi abin ya wuce haka, na samu izinin gwamnati amma ban samu izinin mutanen fada ba, kuma idan ba da izninsu ba ban isa nayi gaban kaina ba, haka yasa na ce bari na fara shawara da ke!" Lumshe idanuna nayi ina nazarin wannan al'amarin, da ni kaina ban san yadda zan ce mishi ba, dafa hannuna yai ya ce min. "Ko Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, ya yi shawara da matansa, don haka na zo da wannan shawarar ce gare ki, domin na hada da nawa lissafin ko zai bani dai-dai." Dafa hannunshi nayi na ce mishi. "Ka janye idanu akansu, sannan ka watsar da binciken da kake yi akan idanunsu, gefe guda ka gwada bincike akan kome a hankali, ban ce ka dauki shawarar da na baka ba, amma idan kana son ka san me ke faruwa dole sai ka step down, ka nuna musu ka gaza ba zaka iya ba. Sannan ka rufe duk wani binciken akan idanunsu. Ban ce dole ka dauki lissafina ba amma ka yi nazari akan bayanina idan ma ba zaka ɗauka ba, ka kauda hankalin mutane akanka yana zai baka damar cimma nasara, idan suka san lissafinka zasu ta rufe hanyar da zaka cimma, amma idan ka rufe lissafinsu zaka na zuwa musu da ba zata."

Janyo ni yayi jikinshi muka kara kwanciya, "yar jarida ce kuwa ke?" Kwantar da kai nayi ina faɗin. "Duk yadda ka ce haka zaa yi, bari na baka labarin wani gidan jarida a new york, a shekaru da dama da suka wuce akwai wani attajirin ba amurike da yake da gidan Jarida, a lokacin yana samun nasara amma babu masu son karanta jaridarshi, ana haka ya wayi gari ya mutu. Bayan ya mutu sai dansa ya gaje shi, bayan ya gaje shi sai ya fahimci har da durkushewan kamfanin su na jarida a mutuwar Babanshi don haka ya fara tunanin taya zai tafiyar da harkokin kamfaninsa, sai wani shawara ya zo mishi mai zai hana ya fara ɗaukar nauyin wasu miyagun laifuffukan da ta'addanci? A lokacin mutane nason jin labarin ta'addanci da wasu abubuwan da babu daɗin ji ko gani da haka ya sai ya kasance yana daukar nauyin da wasu miyagun laifuffukan yadda za a watsa kai tsaye ga gidan jaridarshi. Don haka muma yan jarida mun san yadda ake lalata doka a kafa wani abu na musamman ba don kome ba sai don gyara sunanmu da kuma cigabanmu! Sannan ko manyan kasashen duniya da wasu manya abubuwan irinsu NGO ka bincika da kyau zaka samu suna da hannu a cikin wasu abubuwan da suke faruwa ba na ce maka su ke aikatawa ba, amma maganar gaskiya da sahalewansu ake aikata wasu abubuwan."
"Me kike son na fahimta?" Gyara zama nayi na ce mishi. "Idan har kana son ka tafi da su yadda suke dole kai ma, ka tafi da halinka irin nasu ka mai da kanka irin." Kallon juna muka yi kafin ya ce min. "Alluran da aka yiwa Faruq, irin wanda aka samu a cikin jinin Abbanmu ne! Sannan har yau na kasa gano yadda aka yi Abba ya samu wannan alluran?"
"Me kake nufi?" "Ina nufin nazo nan ne domin mu tallafawa juna!" Kallonshi nayi idanun cikin idanu. "Ta wacce hanya?" "Ta kowacce hanya, a cikin Autopsy na Joy an samu alluran a jininta! Sannan na tura masu bincike na musamman a kamfanin Alhaji Nafi'u da Rilwanu Yayari babu wannan sinfurin!"
A rud'e na kalle shi ina kallon yadda yake magana. "Magana a cikin zanzabira ba zai yiwu ba! Anan ma sai da na binciko, ko akwai wani abu da aka saka min, Alhamdulillahi Masarautar Gombe akwai karamcin domin babu miyagu a tare da su, gaya min me kike tunani?" Kifa kaina nayi a kafad'arshi.."Mu bar maganan nan daga baya mun yi shi." Murmushi yayi ya ce min. "Matsoraciya!" Kwakwasa kofar aka yi na mike, bayi ne guda shida da abin karyawa haka na matsa suka shiga cikin parlourn suka jera kafin suka mana sallama. "Zo ki ciyar da ni!" Abinci na zuba mishi sannan na nufi wurinsa muka fara ci tare yana murmushi. Wunin ranar abinci ake kawo mana muna zaune a daki sai sallah ce take fitar da shi na kara gyara dakin na zauna ina nazari, sako ya turo min. *Ki shirya zamu ganin Khairat!* Murmushi nayi na ce mishi. _Ina jiranka_ kafin ya zo na gama shiryawa cikin wata lace, orange colour sai babban mayafi da na saka, sai nayi amfani da takalmi da jaka fari, ko da ya iso, kallo daya yayi min yana faɗin. ".ba zaki fita a haka ba wallahi." Kallon kaina nayi na kara juyawa na ce mishi. "Me ye laifin wannan kayan?" Bude jakarshi yayi ya ciro min wata abaya, sannan ya mika min yana faɗin. "Saka wannan!" Cire kayan nayi, ya tako bayana yana wasa da cikina zuwa cibiyata. Buge hannun nayi ya kara na juya a fusace, hade bakinmu yayi yadda ya hana masifa. Daga nan mu da zamu fita karfe hudu sai gamu, kwance muna sauke numfashi, wasa yake da gashin kaina. Dakyar ya bar ni muka yi wanka, sannan ya taso muka fita zuwa unguwar kakanin Khairat. Muna isa Yarinyar nan ta makale min ma Mammy ga Mammynta, haka na rungume ta kamar ba zan rabu da ita ba, wani irin kaunar Yar nake ji, kamar na mai da ta cikina. "Sannu da zuwa Fulani!" Murmushi nayi ina mai gaida Kakarta. "Yawwa Umma ya aka ji da dawainiyyar Khairat!" Murmushi tayi tana faɗin. "Alhamdulillahi! Yarki taki zuwa wurin kowa don tace bazata zauna a wurinsu ba, zaki zo ki dauke ta! Ina mai Martaba yake?" "Suna tare da Baba!" Mahaifin Jasrah, hira muka shiga yi aka fara kawo min abinci da na sha har suka iso shi da Baban Jasrah, nan suka yi ta hira ina rungume da Khairat. Duk abinda na ci xan bata don ma yarinyar ta san idanun bata karba sai ta kalli Kakanta. "In sha Allah idan na gama kwanakin da nazo yi zan dauke ta mu tafi Mai Babbar daki ma tana fama da kewarta!" Murmushi suka yi haka dai muka zauna sai bayan Isha muka bar gidan shima sai da na rungume ta tayi barci, akan zan tafi da ita kafin aka shigar da ita dakinta, haka muka bar gidan bayan ya sauke mata kayan wasa da na ciye-ciye. Lokacin da zan shiga mota Baban Jasrah yake faɗin. "Fulani ki tayani godiya. Allah yasaka da alkhairi!" Murmushi nayi nace mishi. "Ba kome Abba yiwa kai ne!" Bayan mun bar gidan yake gaya min abinda ya faru. "Kinsan a kasar nan sai ka san wani zai sanka, dan kasuwa ne kuma yana aikin kwangilar gine-gine, yana ta bin a bashi wani aikin hanya ne, sai wasa suke mishi da hankali. Shine na tuntubi Babban na hannun daman ministan tsara birane, na kasa shi kuma ya bani, kin tuna wani aiki da na tafi abuja? Tow wannan aikin yar ministan nayiwa aiki har tana yawo yanzu da kafarta. Shine ya ce min idan ina da bukata na kira kai tsaya P.A dinsa."
"Mr connection!" Na fada ina daura kaina a kafad'arshi. "Ba haka ba ne, idan muna.da hali mu taya na kusa samu kada mu so kanmu da zuciyarmu!" Kuma haka ne kana da halin taimakawa wani amma sai ka ga kana baya baya ko me ye ribar haka oho.
Kusan hutun karshen mako nan a tare muka yi shi, haka yasa Ranar Sunday da zai tafi muka makale juna kamar kada ya tafi. Har Yazid ya kawo Yeemar, bayan tafiyarsu na gyara Part din na maidawa Fulani Nana key ɗin ina ta godiya da alkhairin da ta yi min. Ranar Monday muka nufi wurin bautar kasarmu. Haka muka cigaba da hidimar kasa har na tsawon sati biyu. Ya rage saura sati daya mu dawo gida
***
Jikin Nadiyyah ba karamin sauki yayi ba a cikin sati biyu, haka yasa a cikin yan kwanaki Doctor Munirah ta fara nazarin turata gida. Sannan za a hada ta da nurse biyu. Duk da tana son ta ɗan kara kwanaki amma ta lura da yadda Nady take tambayarta yaushe zata sallame ta tana son kebewa da Mijinta, ita kuma tana nazarin lafiyarta da rayuwarta tare da dan cikinta, amma ja'ira damuwarta Mijinta, musamman da ta fahimci ya sulale ya tafi Gombe, ta kuma san halinsa sarai yanzu zai iya daukar kafa ya ce zai koma. Haka yasa ta dami Munirah itama da yake likitar zamani ce ta ce mata.."Na san matsalarki, amma rayuwarki da na abin cikinki ne a gabana. Zan sallame ki nan da wata sati Allah ya baki lafiya!" Ta fada tana murmushi, Musamman yadda Nadiyyah ta hade rai, ita bata ki yau ba amma haka Doctor Munirah ta mata bayani, fushi ta ɗauka Hajiya Altine tana ganinta bayan fitar Doctor Munirah ta rufe ta da fada tana faɗin. "A gidan uban waye zaki je da ciki haka? Kina tsammanin ban da yana da wata mace zai tsaya akanki ne ? Dukkanku wato kanku kuka sani idan har yadda nake jin labarin wancan yarinyar da haukar da tayi wallahi kika sake yasan kina fushi don ya je wurin Yarinyar nan zan kyale ki na koma inda na fito yau na ga iskanci, ban da abu me muhimmanci ya kai ta can idan da tana nan ai wallahi ke da Mijinki sai dai ya zo da safe ya zo da dare, a cikin kwanakin nan da ya je kwana biyu yayi ya dawo zaki daurawa kanki kishin masifa? Ina zaki kai namiji da cikinki nan da gaya son kwaranniya? Gara ki sake rai ki samu lafiya miji ai sai ya gundire ki!" Yadda ta mata tas yasa ta hakura da maganar sallama. Shi kuwa bawan Allah bai san me ya faru ba, dama last week bai je Gombe ba tun satin farko da ya je bai kara komawa ba,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login