Showing 270001 words to 273000 words out of 304445 words
biyu ban ce ci kanku ba, ya shigo ya koma wurin Ijlal itama ta rike shi, murmushi nayi ba ta hanyar da suka bi zan bi ba, zan rama kwanciyar mage mai ɗaukar rai zan musu.
Yana shigowa ya same ni, ina zaune Wildat da ta shigo kafin ya shigo tana ta aiki a kitchen, zuwa yayi ya rungume ni ta baya. "Bea!" D'ago kai nayi ina kallon yadda yake murmushi. Shafa kaina yayi yana faɗin."i miss you!" "Me too my King!" Ta shi nayi na rungume shi. "Ka ci abinci kuwa?" Girgiza kai yayi, tab'a cikinsa nayi na kara kallonshi. "Na hada mata tea?" "Ai ba girki ki bane Mammyn Amirah, kada mu yi haka da ke!" Murmushi nayi na ce mata. "Zolayarki nake! Don nasan kin biyo bayanshi!" "A'a na kawo mishi wayarshi da ya manta ne!" Ta mika mishi tana wayancewa, dariya nayi na ce mishi. "Zaka iya tafiya!" Na wuce na barsu a wurin nasan ranshi ya b'aci, yadda yake kallonta yasa ta saka kai ta fita, bayan isha ina zaune ya shigo tare da kwalin nan ya ajiye min dauka nayi na wuce dakina na je na ajiye shi, sannan na dawo na yafa mayafin abaya muka fita, a hankali yake tuki muna hira a hankali. Wani katafaren plaza ya kai ni ana kan aikin wurin an kusan gamawa. "Zaki iya kula da wurin kuwa?" Ya fada yana kallona, fitowa muka yi ya zago tare da rike hannuna, muka shiga cikin plaza din. Ina kallonshi "kalli gabanki!" Murmushi na maida mishi, haka ya ta zagawa da ni a cikin ginin yana min bayani. "Yaya why suddenly ka sauya ra'ayinka?" Murmushi yayi yana faɗin. " Lokacin da kika gaya min kina son yin wurin nan." Ya fada yana shafa bayana bayan ya janyo ni jikinshi. "A lokacin ina duba kayan da ake so ne shine Nadiyyah ta gani take tambayar me xan yi da shi, shi ne nace mata kece zaki bude wurin kwalliya da gyaran jiki. Na manta tana da nata kasuwancin, sai tace na bari tayi odar kayan ban kawo zata nuna sha'awarta akai ba sai da kayan suka dauko hanya ta ce tana so, sai ban hango kome ba, sai da na gayawa Mai Babbar daki yadda muka yi, shine ta dauki zafi da fada take gaya min ina zata kai sauran kasuwncinta, wallahi ban kawo .lpìn ba. Ta kuma ce min burge ta da kika ce kin hakura. Ina zan yi sake da uwar Yarana har uku da Allah ya nufa ai da gidana ya cika da yara har uku!" Murmushi nuna min kome yayi kafin ya kawo ni store yana kallon yadda tsarin kayan aikin. Kafin muka fito, tare da kai ni wani wurin shan iska da kwadayi, idanuna ne ya hango Iram da wasu kawayenta. Mamaki nayi yaushe ta samu lafiya? Asusun motar da yake gabana ya ciro wani leda face mask ne da T-cap, ya fita yana murmushi. A hankali yake tafiya har ya isa cikin wurin, Dole sai ya ɗan jira layi, kiran Iram nayi ina kallonta. Bata dauka ba, sake kiranta nayi bata ɗauka ba. A na ukun na tura mata sakon. *Ki dauki kirana ko na saka a miki daukar Amarya ina kallonki* juye-juye ta fara bata ganni ba, sake kiranta nayi sai gashi ta ɗauka. "Me kike so?" "Yanzu ke abinda kike yi ya dace? Ki saka kai ki bar wajen nan ko a ji mu dake!" Cikin masifa ta ce min. "Kin!" "Kin ji ko baki ji ba?" Jin yadda nayi maganar yasa ta mikewa ta bar wurin, da sauri na turawa Faruq sako na na gaya mishi inda muke, kafin can ina hangota ta shiga motarta. Nasan zai rakata har gida, sako ya turo min. _Ana bibiyarta yanzu_ *Na gode sosai kasa su bita har gida Please* haka ya turo min da Done.
Bude motar yayi yana faɗin. "Sorry na barki ke daya!" Ya saka sauran ledojin a bayan mota, muka bar wurin. Lokacin da da muka isa gida bam na can na jiranshi, amma ganin abinda Faruq ya shigo mata da shi sai ta hakura.
Ina shiga gidana na baje ina sauke ajiyar zuciya, kiran Umma nayi na tambaye ta ko Iram ta dawo. Ta ce ta ga wucewarta. "Shi kenan Umma, dama maganar da nake son yi dake Umma don Allah idan ana maka leke mai ya kamata nayi ne?" Dariya tayi irin nasu na manya sannan ta ce min. "Idan kin san tana muku leke abu biyu zuwa uku zaki yi, na farko shine ki gaya mishi, idan bai yarda ba ki kyale shi, na biyu ki ajiye ruwan sanyi ko na dumi ki kwara inda ake miki leken, na uku kuma shi ne Abu me wuyar cewa, ki san abinda zaki saka shi yayi miki wanda kin san sauran ba zai iya musu ba! Idan kika yi haka in sha Allah zata yi lissafin cewa ayi mata daga nan zai san tana bibiyarshi!"
"Yes Ummana ki gaida Aunty Sajidah!" Muka yi sallama, haka yasa nayi ta shirin na musamman, yana gama kwanakinsa a dakin Ijlal ya dawo, tunda ya dawo baya zama sosai. Idan ya dawo ya sauka a bangarenshi wani lokaci ba zai zo ba haka xan tafi wurinsa, sai Nadiyyah ta tsiro kiranshi Baby yana kaza Baby yana kasa, a yanzu da take da wata takwas, Munirah ta ce ba zata cire Babyn ba sai ta shiga wata tara. Shi yasa iskanci take min kala-kala. Da ya dawo kuma Ijlal ta daura da leke. Yan iska nima suke na haukace, ashe shima yana lura da abinda suke min. Bai magana ba ne. Yana shigowa yau nayi kwana ɗaya gobe xan fita ba, sai na tattaro kayan kwalliya ta na kawo bangarenshi. "Ki yi hakuri jiya na barki ke ɗaya!" Dariya nayi na cigaba da cewa. "Yau ai kwalliya saka min nima na maka!" Muka wuce dakinsa, na bar wutar dakin yadda zata gani. "Yaya yau zan maka kwalliya ka min rawa don Allah!" Janyo ni yayi yana faɗin. "Babu korafi babu mita babu an danne miki hakkinki, bakiɗaya kika hakura da kome don adalci, me zai hana na miki rawa." Haka kuwa aka yi na zauna na bata lokaci ina mishi kwalliya da gyaran zaman gashin kansa. Wani ikon Allah kuwa sai gata, wakar sudaness na saka mishi, yai ta rawa ina dauka a wayata ina dariya, kai namiji akan abinda yake so ba ruwansa, tana gani har ya gama na ce ya je wanke fuskarshi bayan na goge mishi. Kwanciya muka yi abinmu, muka shiga baza kafasiti.
Washi gari da na fita na, da yake jaka ce itama ta gama shirinta tsaf,.da ya koma wurinta sai gashi ta same shi wai ya tashi ya mata yadda ya min, zuba mata idanu yayi ya ce mata. "Ni zan miki rawa? Ni sa'anki ne?" Ya fada yana cire hannunsa a kan laptop din da yake fama da shi. "Ai Allah ya ce ku yi adalci akan matayenku?" Cak ya tsaya yana kallon yadda take magana kafin ya ce mata. "Ban gane ba?" Ya tambaye ta, nan ta fara kananun magana ita sai ya mata abinda ya mun ai ta gani waye ya mutu waye ya dawo abu dai babu dad'i, koran kare ya mata fata-fata bata yarda a gidan ya kore ta ba sai da ya ce mata kada ya dawo Fada ya ganta a cikin gidansa ta je duk inda zata ya gaji da halinta, sai lokacin hankalinta ya dawo jikinta ta fara kuka da roko, kai karshe ita kanta Nadiyyah sai da ta sha jinin jikinta. Haka ta nufi cikin gida tana kuka ya ce ta bar mishi gidansa fa, ai kuwa Mai Babbar daki ta ce sai tayi bayani, anan ta ke fadar ai ta ga yana min abu ne ta ce ya mata ya ce ba zai yi ba. "Kin gan shi da idanunki?" Sunkuyar da kai tayi kasa, "Allah ya huci zuciyarki ba xan kara ba!" "Kina musu leke kenan!" Nan tayi ta bada hakuri Mai Babbar daki ta ce ta fita ta bar mata gida ta je can da mugun nufinta.
Haka ta rasa inda zata cusa kanta sai ta wuce gidan Alhaji Mamman Abba yayari, shima ya ce sam ba ruwansa, ta je gidansu Ikhlas wurin Babanta ko zaa dace. Haka ta je can, tayi ta kuka tana fada mishi sharrin shaidan ne wallahi ba zata kara ba, a yadda take rokon Abba ya fito mata a sak mutum ya gaya mata abinda ko ita bata san yana sane da shi ba. "Na mai dake ki cigaba da yakin ganin bayan Y'ata ko? Bayan nasan kece kike bibiyarta da sharri, zan so ki koma domin lamarin ba zai yi dadi idan baki nan ba, zan kira shi ya mai dake amma ki sani, ina sane da kome daidai da motsi idan kika yi ina sane da ke, Uwarki da take baki goyan bayan shiga da fita ko gaya mata ta kara shiri da kyau ta daura dammara da kyau lokaci yayi da zata san wane ne Junaidu Gobir! Koma dakinki ai yaki babu abokin yi banza ne!" Haka ta mike tana ta godiya tsoron baban Ikhlas ya cika ta, mutumin nan kamar me gani da aljanu, tsaf ya hango kome.
Bayan isha ya je suka yi magana ya ce mishi. "Kara gogawa Zainab bakin jini kake ba soyayya ba ce haka da kayi ya nuna kasan me kake yi amma shiru a bar kowa yayi yadda yake so kuskure ne a cikinsu har da Zainab ɗin."
Haka ya bar gidan Ai ranar Ijlal ta ga masifa da tashin hankali, da kyar ya hakura ya kuma hana ta kwana bangaren shi.
Sati biyu kenan da faruwan lamarin gidan yayi kyau da dadi, ina wurin aiki, aka fara aikin hada harabana da na shi, nan Nadiyyah ta saka tashin hankali, yadda ya fara bai mata magana ba. Haka bai saurari maganarta ba. Ita ce har wurin Mai Babbar daki, ta kira shi tana tambayarshi. "Ummi ina son zan saka kiwo ne a bangaren Ikhlas shi yasa na zabi bangaren nata ya fi girma!" Lallai bawan Allah nan da ƙoƙari yake kusan Uwa kuma akan danta ba sai ta bi bayanshi ba har da goyan mishi baya da majanyi. Nadiyyah ta sakawa kanta tashin hankalin da ya janyo jininta ya hau, haka ta dawo gida, a parlournta ta zube aka kwashe ta raɓe-raɓe zuwa asibiti, aiki kawai aka shiga da ita. Ina wurin aiki ya gaya min, daga can asibitin aka kawo ni ya kuma kira Iyayenta aka gaya musu an shiga mata aiki....
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 89
Jinin gidan Yayari yana da karfi, kasancewarsu ruwa biyu wasu fulani was barebari da shuwa haka yasa suke kamaancecceniya da juna, iyayen Nadiyyah daga Jos jirgi Uwarta da Hajiya Altine suka biyo, a yadda suka zo suka ga Nadiyyah sun ji dadi domin aikin bai wani dauki wani lokaci, sai gashi dauke da Baby domin tare aka shiga da aikin, bai nufi kowa ba sai ni, na hango abubuwa guda daya daga idanunsa Yarda wata irin Yarda na hango a cikinta wanda babu karya a cikinta sai gaskiya da yardan. A hankali ya mika min Yarinayar cikin sanyin murya ya ce min. "It's yours!" Kallonshi nayi cikin idanu cike da mamaki. Bakina yana rawa haka nake kallonshi, hantar cikina yana wani irin kad'awa. "Dauke ta mana, ta ji duminki, kin manta cewa ta ce tana haifa naki ne!" Da sauri na mai da mishi rikon Yar, bakina yana rawa jikina yayi sanyi. Murmushi mai cike da kwalla nake mishi. A hankali na girgixa mishi kai na ce mishi. "Da can baya ne yanzu, tana da kawazuci akan yarta kada mu yi haka da kai. Ka bar mata Yarta!" A hankali na kai hannuna fuskar yarinyar na shafa kumatunta ina murmushi. "So Cute!" Na furta, "Me yasa ba zaki amshe ta ba!" "Mikawa iyayenta ni kan Alhamdulillahi!" A hankali ya janyo ni ya mika min yarinyar, amsa nayi ina kallon yadda take motsi. "Ki kai musu da kanki!" Ya furta tare da juyawa ya koma cikin dakin aikin a lokacin ana gyara Uwar, wurin Mahaifinta na nufa ina tofawa Yarinyar addu'a, sannan na mika mishi ita da Bismillah. Maganar da naji a bakin bayin Allah nan ya sani jin kamar ni kaɗai Allah ya yarda da ni. "Yarki ce fa, ki ji a ranki Allah ya kawo miki ita cikin amincinsa. Kome za'a fada ba zamu manta alkhairin iyayenki da ke kanki ba, a yau kece rike da Yar Nadiyyah, mai yafi haka dad'i? Allah ya miki albarka ya baki zuria na gari masu alkhairi masu albarka da jin kai. Ke mutum ce na fada a duniya!" A hankali nake kuka tare da kallon yadda bawan Allah nan yake min addu'a da fatan Alkhairi. A hankali suke yaba min da duk wani abin da nayi sai na rasa wani aji xan saka iyayen Nadiyyah da shi kanshi mijin, Hajiya Altine ta amshi yarinyar tayi ta mata addu'a kafin ta dawo min da ita, idan ba bude baki xan yi addu'a sai kuka ya zo min haka ina kuka ina mata addu'a, ina tofa mata. A hankali na sauke addu'ata ta karshe, wanda yayi daidai da fito da Uwar jinjiran, ana tura ta a gadon. A hankali na mike tare da nufar wurinsa da yake cire facemask din. Shafa fuskarshi nayi ina rab'a babyn a kafadata.."sannu Boy ka sha aiki!" "Ni nawa tsayawa ne, sauran aikin Munirah ce." Ya fada yana murmushi, mika mishi babyn nayi hannunshi daya riƙe da ita, daya hannun yana rike da ni. Dakin Muka shiga aka gyara mata kwanciya, sannan aka makala mata kome kafin suka fita daga dakin Iyayenta suka shigo, a hankali na janye hannuna cikin nashi sannan na tsaya ina mata addu'a da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya umarce mu, mu yiwa mara lafiya, sannan aka kawo gadon babyn aka kwantar da ita, Mai Babbar daki bata samu zuwa ba amma ta aiko har da abinci, kallona yayi yana faɗin.."kin ci abinci kuwa?" Girgiza kai nayi ya ce min. "Muje gida ki ci kin ji!" Ya fada yana gaba na biyo shi a baya. Office dinsa muka nufa, na ga kome kamar yana nan a har yanzu. "Kana aiki ne?" A hankali ya tako gabana yana mai sumbtar goshina ya ce min. "Bana aiki! Me yasa kika yi tambayar?" A hankali na janyo kujerar office din na zauna. "Na ga kome neat!" Bude wani wardrobe yayi yana cire kayanshi, sai da ya saka sannan ya juyo yana kallona kafin ya ce min.."Ina aiki amma sai ta kama dole!" Murmushi nayi na ce mishi. "Ok!" Knocking aka yi ya ce min." Ina saka kaya kada ki amsa!" Ban amsa ba, aka sake buga kofar har ya gama sannan ya yi gyaran murya. Da sallama Doctor Munirah ta shigo tana gaishe shi, sannan ta juya gare ni. "Sannu da aiki." "Yawwa Auta!" Murmushi nayi, ta ajiye mishi file din da ta kawo da report a cikinsa. "Doctor mun gama hada kome, saura Babyn ta rage na ce ita ko zuwa gobe sai na mikawa Doctor Nuhu file dinta, tunda bakiɗaya aikin zan tura neurologist department ne!" "Hmm yau nace!" Ya furta yana gyara collar dinsa, a jikin Madubi. "Doctor!" Juyawa yayi ya zuba mata idanun. "Yau na ce! Kin san wannan karon ba zan kira haka da mistake ba." "Tow shi kenan!" Haka ta dauki file din ta fita tana fita ya sake fuska yana min murmushi. "Sorry!" Ya furta yana kallona. Tashi nayi ya riko hannuna muka bar office din, muka nufi waje, cikin ikon Allah har an zazzo daga Fada, domin cikin Nadiyyah kowa yana sonshi. Lokacin da muka isa, Daulah ya ce min. "Mamman yan uku ashe kun samu karuwa?" "Gwaggon Yan uku eh!" "Kin ga bana son wulakanci, ta ina na zama Gwaggo sai kace wata tsohuwa!" Murmushi nayi, nan muka koma gefe kasa kasa ya ce min. "Kin san tafiya zamu yi!" Murmushi nayi ina kallon Daulah. "Mammyn Yan uku, me kuka shirya akan haihuwar?" Kallonta nayi kafin na ce mata. "Shi Yayanki me yasa ba zaki tambaye shi ba?" "Wannan yakusashen," murmushi nayi na ce mata. "Duk yadda aka yi zai miki magana!" Kun san wani ikon Allah shirin da muke da Daulah da Bilqis ya b'aci.."kin san mai gado tana Saudiyya Umara!" "Ta gaya min tun last week, Allah ya dawo da ita lafiya!" "Amin Ya Allah!" Jan hannuna yayi muka bar asibitin, shagon Mr Brandy ya kai ni, tun kafin mu isa aka gyara ko ina, inda aka yi wurin parking a cikin mall din ne a kasan mall din, haka yasa muka shiga shagon ta kofar baya, lokacin da muka isa abincin an shirya da zafinsa haka muka ci sannan muka fito Mr Brandy godiya yayi ta mana. Har muka fito, daga nan muka wuce gida, lokacin ana sallah a cikin gida ya bar ni ya wuce massalaci. A hankali nake tafiya, tsigar jikina ne ya mike nayi maza na kalli gabana. Wata mace na hango tsaye a lungun da bishiyar maina na gidan yake, tana kallona da idanunta da suka yi wani irin haske, kamar fitar burgu haka ta fito da wani irin gudu ta yo kaina a guje, rufe idanuna nayi tare da salati na dunkule wurin, wani irin iska mai sanyi na ji da wani irin ƙara, bude ido nayi na ga wurin yayi wani irin yanayi kamar guguwa daga sahara. Sake bude idanuna nayi naga wurin yayi wani irin dubu. Na shiga dube-dube kafin na ji an ce min. "Ikhlas lafiya?" Juyawa nayi naga Ilham ce a tsaye ta ci Uban ado alamar ta dawo ne. "Ba kome!" "Tow shine kika tsaya a wurin,ana sallah!" Da sauri na shige cikin parlourn Mai Babbar daki, na sauke ajiyar zuciya,