Showing 279001 words to 282000 words out of 304445 words
daɗinka!" Ya fada bayan ya mikawa Faruq wani allura ya mishi, bayan minti goma ya fara sauke ajiyar zuciya. Sannan ya mike yana tambayar shi ya ce." Kasan kasar da Gwaska take?" "Ban sani ba, ban san inda yake ba!" Juyawa suka yi suka fita da shi, sannan ya kalli, Commander din ya ce mishi. "Kayi hakuri ban san dan uwanka suka kashe ba!" Murmushi yayi ya ce mishi. "Ba kome ai aikinka ne kare rayuwarmu, mu kuma duty dinmu ne mu ceto rayuwar kowa!" Sannan suka bar barrack din.
Karfe daya na farka, abin karyawa nayi oda aka kawo. A hankali nake ci ina jin wani irin yanayi yana kara tab'a zuciyata abinda nayi mishi dazun sai nake jin kamar nayi kuskure yadda yake bani kulawa bai dace nayi haka ba, lokacin da na gama karyawa wanka nayi tare da gabatar da sallah, sannan na sauka spa na cikin hotel din, na yi ta zagawa da nazarin wurin da abubuwan aikin, wanke min kai suka yi bayan sun min tsifa sannan suka min gyaran kafa, sai gyara min fatar goshina da suka yi na biya kudi na fito, a hankali na fito sai a lokacin na lura inda muke ashe hotel din a bakin ruwa yake, gyara zaman mayafin abayana nayi na shiga taka har waje na fita bakin Beach din, a hankali nake takawa ina tafiya ina kallon ruwan yadda ake ta hidima a wurin, wani rumfa na nufa na zauna ina mai kallon ruwa ganin wannan tekun sai ya dauke min damuwata da bakin ciki nake ciki haka nayi ta kallon ruwan yara ne guda biyu suke wasa da wata na ukunsu ina ga wasan boya suke, daya Yaron yana zuwa ya ce min.."don Allah kada ki ce kin gani zan baki chocolate!" Ya shiga ya boya ina zaune a wurin suka zo niman shi, sai ya kalle ni ya saka hannu a lips dinsa. Kallon Yaran nake da suke ta nimanshi kafin suka juya a hankali suna faɗin. "Mommy bamu ga Ayyan ba?" Matar da suka kira da Mommy ta taso a hankali tana faɗin. "Ba zaku tab'a barin mutum yayi zanensa cikin natsuwa ba, haba don Allah? Ina ya shiga shima!" Kallonsh nayi nace mishi. "Mommynka da sibling dinka suna nimanka!" Tura baki yayi yana faɗin. "Hide and seek muke fa?" "Tow ka fito kada su fara nimanka!" Na fada ina murmushi. Fitowa yayi yana tura baki ya cewa Mamanshi. "Mommy gani nan!" Ya fada yana tura baki, juyowa suka yi ya kalle ni kamar zai yi kuka. Irin na saka shi ya fadi. Karasowa Mamansu tayi tana faɗin.."Barka dai kamar daga Arewa ko?" Murmushi nayi ina faɗin. "Barka dai!" "Suna Maamah Mrs Abhu Zari!" Ta shigo rumfar tana murmushi. "Ummina ki yiwa Ade magana a kawo mana abin sha!" "Ok Mommy!" Yarinyar ta tafi da gudu, murmushi tayi tana faɗin. "Ke daya ce?" Yadda na ga take da rawan kai sai naji bata min ba, amma wani abu da na fahimta da ita yarda kuma aka mutane je cewa ita Mai d'a wawa ne. "Na fito shan isa ne, na zo nan na zauna!" "Kina lekke hotel kenan!" Ban ce kome ba aka shiga kawo drinks da snacks. "Bismillah! Ni yar yola ce, koda yake a can aka haife ni Mahaifiyata yar Gombe ce daga cikin gidan Sarautar Gombe, Sai mijina dan rano ne!" Kallonta nayi dakyau tabbas jinin gidan ce domin ina ta kallonta kamar na san fuskar da yanayinta, murmushi nayi nace mata. "Amma baki zauna a gidan sarautar ba ko?" Murmushi tayi ta ce min. "Ba zan iya mugun hali ba, wannan shariyar da dauke kai ko da mutum yana jin dadin magana amma yayi ta share mutane no baya cikin agenda na!" "Cupcake!" Muka ji an kira sunan, juyawa tayi tana faɗin. "Sayyid sunan nan dai ya dace na girma da shi ko!" Ta nufe shi da sassarfa. Tare ta yayi yana faɗin. "Ana niman wata mata ne wai daga masarautar Zanzabira, ta fita shine nace bari na zo na ga kuna lafiya!" Murmushi tayi tana faɗin. "Ikon Allah a ina suka sauka?" "A lekke hotel!" Juyawa tayi ta kalli matar nan, "ba kuma wancan matar ba?" Ta tambaye shi, leko ta yayi, suka tawo a tare. "Assalamualaikum, baiwar Allah daga Lekke hotel kike?" "Eh!" "Kuna tare da Sarkin Zanzibara ne?" Bai rufe baki ba sai ga Faruq, kallonshi nayi kafin na samu damar magana sai ga shi ya iso. Yadda hankalinsa ya tashi, na hango ƙarara a fuskarshi. Sunkuyar da kai nayi ya d'agowwa Faruq hannu ya bar wurin. Mikawa Mijin Maama hannu yayi yana faɗin. Mijin Maama ya ce mishi. "Sorry Sir, ban san suna tare da Madam ba ne, ka yi hakuri!" Shiru yayi kafin ya ce mishi. "Ba kome!" "Uncle kai ma kun yi hide and seek din ne?" Ɗaukarshi yayi sama yana murmushi. "Yes bata gaya min yadda za ayi game din ba ta gudu gashi ta saka heart dina yana ta beating bum-bum I thought na rasa kenan, gaya min me xan mata!" Abinka da yaro ya ce mishi. "Yanzu tayi Cheating dina, ta saka na fito a daura ta akan doki kawai a rama min!" Murmushi nayi ban ce musu kome ba, haka suka yi ta lissafin yadda zasu min abinda xan ji haushi. A hankali kuma aka fara hira, har zuwa wani lokaci kuma aka yi musayar number, muka bar wurin a hankali muke tafiya a bakin ruwa, haka muka cigaba da tafiya babu magana kowa da abinda yake tunani, janyo ni yayi jikinshi ina kallon ruwa. Dawo da ni gabanshi yayi yana faɗin. "Kin saka ni jin tashin hankali, na zata kin tafi kin bar ni ne!" Murmushi nayi ban ce mishi kome ba, har dai ya gaji yana faɗin.."ki yi hakuri da abin da ya faru!" "Ba kome!"
Na fada don na gaji da maganar, haka muka koma ma sauki muka yi sallah azhar sai bayan mun idar ya ci abinci tuwon shinkafa da miyar egusi, a hankali na koma na kwanta. Kamar yasan mai nake so can sai gashi an kawo min smooth da burga da shawarma, a hankali na fara sha ina kallon smooth din. Ina gamawa na gyara wurin na koma baranda dakin na tsaya, jin shi nayi ya rungume ni yana sauke numfashi. "Sorry!" Murmushi nayi ina kallon yadda ruwa yake sama ya koma ya kwanta, hango yara nayi suna ta wasa, ban san a waje nake magana ba, na ce mishi. "Allah nasan kai ne Allah, Ubangiji ka bani nima Yaran nan!" Rufe bakina yayi yana mai juyo ni. "Idan kika yi hakuri Allah zai baki, kada ki yi fatan ya baki yaran nan ala dole domin zamu wahala, ki yi hakuri Allah ya bamu masu albarka." A hankali na ji zuciyata tayi wani irin cushewa, na kifa kaina a kirjinshi ina jin kamar zuciyata zata fashe. Shafa bayana yake yana faɗin. "Ki yi hakuri!" D'ago kai nayi ina kallonshi har cikin idanunsa. "Kiyi hakuri!" Ya kara furta min, "nasan irin bakin cikin da kike ji, amma ki yi hakuri." Kifa kaina nayi a kirjinshi, ina sauke ajiyar zuciya. "Ki yi hakuri kin ji!" Haka ya shafa baya har nayi shiru. Dakin muka dawo. Ya kira Faruq yana faɗin. "Kome is ready?" "Yes Sir!" Sai ya kashe wayar ya nufi wurin kayanmu ya haɗa yana faɗin. "Muje ki raka ni!" Saka takalmi nayi tare da gyara zaman mayafina, ya janyo jakarmu tare da rike hannuna muka fita. A waje muka samu Faruq amsar jakar yayi, muka wuce can waje, motar da zai kai mu airport. Sai da ya kai mu ya gama kome sannan ya mana sallama, kaina na kifa a kafad'arshi. Na rufe idanuna. Rayuwata kamar mafarki nake ganinta, tunda na hadu da shi a rayuwata ƙaddara ta soma bude littafinta, har yau da nake cikinta kowacce shafi ta bude sai nayi shi kamar na farko ba kome ba ne....... IKFAR💕Safe journey 👋🏿🕊️
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 92
Cairo Egypt
Karfe goma na safe agogon kasar wahda yayi daidai da karfe takwas agogon Nigeria, muka isa a daya daga cikin manyan hotel din ƙasar. A matukar gajiye da zaman jirgin muka isa dakin, alola muka fara yi ya fita Masallacin da yake hotel din ni kuma na yi sallah a dakin, sannan na kwanta don ko yunwa bana ji. Haka na kwanta barci yayi gaba da ni don barcin da nayi a jirgi rabi da rabi haka nayi barcin nan, lokacin da ya dawo ya shigo da madara mai dumi ban san inda ya samo ba, haka ya tashe ni.."Oya sha kada ki yi barci da empty stomach!" Ya saka dole na sha, sannan ya ɗan rike ni a jikinshi na cigaba da barci, kusan awa minti arba'in ina jikinshi a kwance. Kafin ya kwantar da ni, barci mai nauyi yayi gaba da ni. Wanka yayi ya zo ya kwanta a gefena tare da janyo ni jikinshi muka kwanta.
Karfe daya na rana kiran sallah ya tashe mu, haka muka kalli juna cikin kulawa ya shafa gefen fuskana. "Kyakyawata!" Lumshe idanuna nayi da suka yi lufu-lufu, a hankali na gyara gyara kwanciyata, ji nayi ya kara matse ni. "Ka sake ni zan yi wanka ne!" Na faɗa a shagwab'e, bude ido yayi yana kallon yadda nake tura baki. "Zan sake ki amma sai kin yi min kiss?" "Ban yi brush ba!" Na fada ina ƙoƙarin tashi daga jikinshi kara rungume ni yayi yana faɗin. "Ba zaki tashi ba" "don Allah!" Yadda nayi maganar yasa shi sake ni na sauko da kafana a kasa, a hankali na ji na tsaya akan kafana, zare dogowar rigar jikina nayi ya fadi a ƙasa, na shiga cire bra ɗin. Tasowa yayi da sauri ya nufo ni tare da rungume ni ta baya. "Ki yi hakuri muje na taya ki!" Haka nayi shiru ya dauki ni, zuwa ban daki wanka muka yi a cikin ruwan muka kwanta can ya mike tare da daura alola ya ja hancina. "Zaki ja min makara!" Ya fada da sauri yana barin ban dakin, zama nayi cikin ruwan nayi tsam cikin tunanin rayuwata da abinda nake ganin ya dace da nayi, ban san me yasa ya hana ni wuyata ba. Bayan na gama wanka na fito nayi sallah azhar ina idarwa yana shigowa, aka biyo shi da Abinci, haka na shafa muka fara cin abincin don yunwa nake ji. Sai da muka karya sannan ya mika min wayata. "Abbanki da yan gidanku sun damu fa!" Amsar wayar nayi na kunna a hankali na shiga wurin kiran, text message na ga ya shigo, a hankali na kira Abba. Dauka yayi yana faɗin. "Ka isa wurinta ne?" "Assalamualaikum! Abba ni ce." Ina jin ya sauke ajiyar zuciya ya ce min.."kin isa lafiya?" Kallonshi nayi ya lumshe idanu yayi sannan ya buɗe. "Alhamdulillahi mun sauka lafiya!" "Iyayenki mata suka damu da son jin yadda kike ance kun yi hijira ke da Mijinki!" Murmushi nayi nace mishi. "A'a rako shi nayi wani aiki!" "Haka kika ce ina yake shi din an kawo min karanku, ke da shi." "Abba mun yi wani abu me?" "Ba shi!" Mika mishi wayar nayi na zuba mishi idanu, ina ga fada Abba yake mishi, mikewa nayi na koma inda yake ya mike tsaye na haura gadon tare da dafa shi na saka kunnena matsawa yai na tafi zan fad'i yayi maza ya tare ni na fada jikinshi, ko ya manta wayar da yake ne ya ce min. "Baki jin magana idan kika faɗi fa? Ba ciwo zaki ji ba? Idan fadar da Abba yake ne bari na saka miki ji ai nayi mana record din!" "Ikon Allah ni ne ma nake ta ku, wato ba ta ni kuke ba Salmanun Faris na gaya maka gaskiya ka daina biyewa Zainaba tana saka ka yin wani abun haba don Allah ace ranar sunan yarka ta biyu ka bar kasar ka hana ta taron sunanta!"
"Allah ya baka hakuri Abba!" Ya fada yana kallon yadda nake kallonshi. "Abba zamu shiga meeting!" Ya kashe wayar yana kallon yadda nayi rau-rau da idanu. "Ki yi hakuri idan dai akan wannan maganar ne zasu yi su gaji! Shirya muna da masu jiranmu gobe zamu wuce Dubai!" Haka na shirya cikin doguwar riga, na yafa mayafi babba, sannan na saka takalmi mara nauyi, shima yana sanye da kananun kaya. Kamar ba sarki ba kallonshi nayi na ce mishi. "Me yasa muka zo nan?" "Muje dai!" Haka muka nufi waje, kusan yadda yake tattare ni kamar wata yar koyan zama, haka muka yi ya takawa har inda zamu yi taron, haka muka tattauna sosai sai lokacin na fahimci maganarshi akan mall din ne, wani abun da ya ya saka ni kuka bayan mun fito taron shine yadda ya min bayanin hannun da na saka ya ce min. "Wadanda mutanen da kika gana da su, manya yan kasuwa ne da suke shigar da kaya kowacce kusurwan duniya. Abinda ya sa na hada ki da su shine idan suka yi kaya kafin ya zaga duniya ke da Model dinki zaku fara gani haka suke yi idan har kayan ya iso tow sai dai ayi sari a hannunki kin zama agent dinsu kenan! Sai shi ɗaya dan kasuwan shi irin kayan Islamic medicine yake dasu kin ga irin su zaitun da sauransu idan aka tashi nima sai a mall dinki za a samu kin ga za ayi ta sari a hannunki!" A hankali na tsaya cak kafin na durkusa a wurin na fashe da kuka, d'ago ni yayi yana faɗin. "Shi ɗaya mutumin babba kamfani ne da su na kayan provisions, duk abinda kike so a a mall din sun san yadda za a kawo miki su kawai oda zaki yi" fika kaina nayi a kirjinshi ina kuka mai ban cin domin Yaya yana min adalci ya kyautata min nan gaba ko me zai yi min xan yi hakuri da shi!" Haka muka fito ya ce min. "Na baki aron kudi mu ga yadda zaki fara kasuwancin Allah yasa albarka!"
Haka muka koma daki, sai naji na kasa hakuri da abinda yake ta min na rike hannunshi.."Yaya sauran yan uwana fa?" Murmushi yayi ya zauna yana kallon yadda na damu. "Kina tsoron kada nayi rashin adalci ko?" Girgixa kai nayi ina rike hannunshi cikin nawa. "Kwantar da hankalinki, ba zan yi abinda zai wargaza zaman lafiyar gidana ba. Ijlal na bata kudi kin ga ni!" Ya bude min account din da kudin da ya tura mata, "Saboda haka na bude mata dollars account zuwan mu Scotland, kin ga abinda na bata dalla dubu dari uku, dai Nadiyyah itama dalla dubu uku, kace dai na baki daya miliyan daya abinda yasa nayi haka saboda na tallafa miki a kasuwancinki, dubu dari uku naki dubu dari bakwai aro ne!" Murmushi nayi nace mishi. "Allah yasa albarka a kasuwarmu na mai da maka kayanka wallahi bana son bashi! Don ina da kudi account dina na Nigeria na gaya maka ai!" "Wannan hakkinki ne ba nawa ba, wannan kuma hakkina ne na kula da ke!" Tura baki nayi na fara shirin mishi rigima. Lallubo ni yayi ya cilla ni gadon yayi muka shi gayawa juna gaskiya.
Sallah la'asar ce ta saka muka hakura da juna, sannan muka shiga wanka muna fitowa ya nufi massalaci ni kuma na yi sallah a gidan. A hankali nake addu'a, bayan na idar shima ya shigo muka fita bayan la'asar sayayya muka yi sannan muka dawo hotel din cike da kaya. Sannan ya kai ni wani wurin gyaran fata na ga wasu sabilai da skins types da suke dauka don haka na sara domin yana da kyau da yadda zan yi amfani da su. Haka muka hadu da wata mata take gaya min akwai yadda suke gyara jiki da irin sabulun da na saya, don haka ta nuna min yadda zan hada su da numbersu, haka na saya shima sannan ta ce min. "Na ga kamar baki ne ku, da zaki iya da kin samu lokaci kika yi nazari a wani makarantar koyar da gyaran fata yadda zaki kware da gyaran jiki da fata!" "Zan dawo in sha Allah, ki bani number idan na dawo sai na nime ki!" Takardan makarantar ta bani na mata godiya muka gama na dawo gida,.a hankali na gama hada kayan mu cif sannan na haɗa a cikin wata jaka da ya saya min, a daren ranar ya kira Ijlal nan tayi ta mishi karuwanci, ban zauna ba na lallaba na shige cikin duvet na kwanta abinda, da ya kira Nadiyyah kuwa fada da rigima suka yi kaca-kaca, sannan ya kashe wayar, abinda ya bashi haushi yadda tai ya gori da maganar haihuwa, da nunawa wai ana mata bakin ciki.
Haka ya zo ya kwanta a jikina, ja janyo shi na rungume shi dama abina ne. Sa safe muka tashi don mun so makara, haka muka shirya bayan mun yi sallah asuba, muka nufi airport. Karfe tara na safe muka bar garin zuwa Dubai. Shima ba laifi mun yi magana da manya kamfanin abaya da dogayen rigunan maza, sai turare da ya min magana da wata kamfani muka gama shima nayi idan kayan aka zuba a cargo. Lokacin da muka bar taron a gajiye na koma dakinmu muka ci abinci muka fita da dare, satin mu guda a cikin Dubai kafin muka kamo hanyar zanzabira lokacin da muka iso da yamma ne, hakan yasa muka sauka a wurin mai babbar daki. Yadda nayi kiba da kwanciyar hankali yasa take tsammanin ko ciki ne da ni, ni kuwa tun a cikin jirgi na ga bakona har yana min sannu domin wannan karon da ciwon ciki ya zo min,.sai da aka nima min allura a cikin jirgin wanda suke ajiyewa in case. Lokacin da aka bashi yayi min da suke tambayar shi dama likita ne, anan ya gaya musu shi matsayinsa, ba karamin murna suka yi ta yi ba, daya daga cikin masu kula da fasinjojin