Showing 303001 words to 304445 words out of 304445 words
tayi ta ce. "Nayi master a lokacin a London ni da Mai Martaba yana Phd haka yasa muka samu damar karatu a lokacin Mijinki yana shekaru tara a duniya!" "Lallai Yaya dama can ya rayu cikin aminci!" "Ai sosai ma!" Amsar yar nayi na mikawa Mai aikinta ta mikawa Uwar ta mike tana faɗin. "Mai Babbar daki zamu wuce!" "Allah ya kai ku lafiya!" "Amin Ya Allah!" Ta fada tana fita na zube a parlourn ina juyi. "Sannu kin ji! Jikin na ciwo ko?" Tashi nayi na ce mata. "Ummi bakiɗaya jikin kamar ba nawa ba." "Sannu!" Na koma na daura kaina a cinyarta, wurin karfe biyar ya shigo ya same ni kwance a cinyar tana karatun Alqur'ani, Wildat tana min tausa. Hawaye ne ya zubo min na tashi a hankali na wuce daki bina da idanu yayi. Amai nayi ta kokarin yi amma yaki fitowa haka na dawo dakin na kwanta ina kuka, jin shashekar kukan ysa suka shigo dakin. "Sannu!" Gyada kai nayi ina kara jin kamar zan mutu, dafa goshina yayi ya ji zafi rau. "Ummi tun yaushe bata da lafiya?" Share shi tayi ta ce min. "Bari Sadi ya zo ya kai mu asibiti kin ji!" "Ummi bari na kira Munirah!" "Bana bukatar" yadda ta fada yasa shiru, fita tayi ya zuba min idanun.
"Zainaba me ke damunki?" Ban amsa mishi ba, na cigaba da kukan can ta zo ta ɗaukar min mayafi ta d'aga ni muka fita, yana biyo mu ta ce mishi. "Idan kana son na dawo maka da ita kada ka sake ka bi mu, ko kasa a bi mu idan na samu haka zan raba abinda ya haɗa." Wannan iyakar yasa ya hakura haka muka tafi asibiti wnada kamar an san da zuwanmu, muna zuwa aka bani magani gado, cikin abin da bai wuce awa daya ba na sha ruwa da leda daya saura likitan ya hado mu da shi, koda muka isa gidan barci nake ji, a dakin na kwanta barci yayi gaba da ni, ko an gaya mishi mun dawo sai gashi ya zo mai babbar daki ta bashi drip din ta daura min, yayi ta tambayarta amma bata ce kome ba, haka ya zauna a daren yaki tafiya gidanshi. Cikin dare dama tasan ina farkawa niman abinci, ina farkawa na ga kunun gyad'a sai kamshin citta yake kamar me, a hankali na tashi zaune ya ce min. "Sannu!" Gyada kai nayi na dauki kunun da zafi haka nayi ta sha ina gyada kai, ina gamawa na shiga ban daki nayi fitsari da alola nazo nayi sallah Magariba da isha, bayan na gama na zo na kwanta ina azkar. Barci me nauyi ya dauke ni. Washi gari kuwa suka kawo ƙaranshi, irin ai dole su kureta. "Ku da kuke da miji ita Zainaba ina ruwanta? Ku dai ku je ku rike kayanku, ai ta bar muku ne mace idan ta isa mace mai da namiji take gefe tayi facing reality dinta, sai ku ga yana bin ta, ita ba zata bishi ba don ba zata daurawa kanta kishi da hassada ba!" Daga haka suka bar gidan suna ganin ita take daure min takalmin da nake taka su san raina.
Asalin yanzu nake laulayi mai irin azabar ciwon nan. Amai yawu da kasala ashe don ban sani ba ne, ranar wata juma'a Abba da Alhaji Mamman Abba yayari suka zo, aka yi ta bawa Mai Babbar daki hakuri akan ta bar ni na koma amma taki. Cewa uffan sai da Abba ya kira ni ya zuba min idanu ya ce min. "Mamana sai ki zo ki zauna anan? Kin manta hakkin da yake kanki ne?" "Kada ka lallabata wallahi ko shi ya ce miki kule ki ce mishi cas, tunda sun kai haka kuma ba zata koma ba!" Da gaske Ummi ta hana ni komawa haka yasa suka tafi ransu a b'ace, ranar Asabar sai ga Baffanta da kanshi ya saka ta haɗa min kayana ta mai da ni, a ranar sun jima suna hira yana bata hakuri da wani laifin da ya mata, kafin ta bar garin ta koma Faransa.
Da yamma na koma don haka aka gyara min ko ina, kwanciyata nayi don har zuwa lokacin jikina da kasala, saboda bana son hayaniya rufe kofar da za a shigo daga ɓangaren shi nayi na rufe duk wani abu da zai alakanta ni da kowa, na saka kaina a daki ina fama da kaina. Haka lokaci ya tafi shima yayi nacin yayi magiyar yana tab'a ni zan fara kuka da jin kamar zan mutu. Haka yasa ya kyale.
Ranar wata asabar Ilham suka zo ita da mijinta, tana gaya min na musu girki, sai da ta bi matan gidan ta gaisa da su, sannan ta shigo wurina. Ina zaune bayan na gama karatu. "Aunty Fulani kin yi kyau fa!" "Nagode Funmilayo!" Zama tayi muka yi ta hira, Ijlal ta shigo tana ta kallonta yadda ta nutsu ta kuma yi kyau abincin da take ci ta saka hannu a cikin ta ci, da yake bata da kunya ta dauki bowl karami ta zuba abincin ta fita da shi a raina na ce can mata, haka Ilham ta gama yace zasu tafi na shiga na hada mata tsaraba na bata, muka yi bankwana.
Wurin karfe bakwai na dare, ihun Nadiyyah ya cika mana gidan, ni dama ba fita nake ba, ina jinsu na zata ita da Mijinta ne, na gyara kwanciyata da kyau. Ihu da salatin ya kaure a gidan nasan an hana ni fita na ja na make. Jin shiga da fita yasa na leka ta window yadda ta daukota yasa gabana ya fadi, Ismaha na ga tayi wani irin doro da ta ga xan fita waje, ta kuma tsare hanyar fitar, tsoro ne ya kama ni bata taɓa yi min haka ba, sai yau maganar Ba Dattijo ya fado min, tuni na koma dakina na zauna, har gari ya wayo ban ji duriyar kowa ba, sai karfe biyu Faruq ya zo ya ce min na zo ana nima na. Haka na saka katon hijab dina na nufi bayanshi tare da Ismaha. Gabana sai faduwa yake, muka nufi parlourn Nadiyyah da iyayenta suna zaune sai kuka take kamar ranta zai fita. Zama nayi a hankali na gaisu babu wnada ya amsa sai mai babbar daki. Ta ce min. "Zainaba ke ce kika yi wannan girkin?" Kallon abincin nayi na d'aga bowl din na saka a hancina, "a'a ni abincin da nayi cennomin jollop rice nayi?" Tasss naji an wanke ni da mari sai da na daina ji da gani, ina d'ago kai Nadiyyah ce, wato ban san me ya faru ba sai ji nayi kamar iska yana tashi a kaina, Daga nan dai an bani labarin na karya hannun Nadiyyah kab'as na koma gefe inji Ummi wai ina huci. Kafin kuma na dafe goshina, ihun Nadiya ya cika parlourn haka yasa Mai babbar daki ta kamo hannuna ta ce min."ina kina lafiya? Kin san me kika yi? Karya mata hannu kika yi?" Fashe da kuka nayi a lokacin shi Takawan baya parlourn shigowar da yayi ya ji irin abinda na aikata a lokacin aka warware min abin da ya faru, kuka nake ina rantsuwa ga shaidar dai na aikata abubuwa da yawa domin na karya mata hannu, sai parlourn ya rikice iyayen Nadiyyah suna rantsuwa basu yarda ba, tsawa ya daka a parlourn yasa kowa ya shiga hankalinsa ya kalle ni ya ce min. "Kina yin abu ina hakuri amma wannan karon kin kai ni inda ban iya juyawa," ya kalli Ummi ya ce mata . "Ki yi hakuri na gaji da fitinar Zainab, na gaji da halinta abin nata ya koma kisan kai, wannan abincin da ta girka ta basu hatta Amiratul Zaitunah sai da ta bawa itama tana can a gadon asibiti ba lafiya ni Salmanu Faris Attahiru Shehu Yayari na sak......!
*Alhamdulillahi anan na kawo karshen book 1 wanda aka kwashi gwagwarmayar mayya mai matuƙar al'ajabi kai Jama'a nayi nawa na gama saura ku, yan group ku hada kanku da yan uwanku mu koma Telegram domin no document ba zan baku a wallahi kun ji abinda na fada ba zan baku ba na gaji na gaji na gaji Allah ya bamu ladar hakuri da juna da muka yi ina muku sallama irinta addinin Muslunci assalamualaikum EVERYONE.....*
_Book 1 ya zama compelet book 2&3 500₦ hajiyata babu yawa, ki shigo faka-faka ayi da ke! Inji Sa'adu bori ya ce mace kazama bata bori! Nima nace Yan ROYAL POLITICS addict's fans let me led you to Zanzabira..._
```5921536136 Ramlat Manga Moniepoint```
08130269641
500₦
Ramlat Abdulrahman Manga
Mai_Dambu CE