Showing 201001 words to 204000 words out of 304445 words

Chapter 68 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

60

salo. Idan ka isa ka kare abu masu muhimmanci a rayuwarka zan baka mamaki ni kuwa....
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 66
Murmushi yayi yana auna kalman, kafin ya kashe laptop din ya gyara kwanciyar. Bayan yayi addu'a, shi fa abinda ya sani babu wanda zai tab'a d'aga mishi hankali domin idan ya tashi ya san yadda zai ji da kowa so babu amfanin tashin hankali da hayagaga.
Washi gari koda ya isa masallacin domin yin sallah asuba an cika masallacin har kusan waje. jami'an tsaro sun saka shi a tsakiyar su aka fara matsawa ya samu shiga Masallacin, jami'in bayan liman ya samu, sai ga masu tsaronsa sun cike sahun bayansa, gefenshi Faruq ne a hannun damarsa, hannun hagunsa kuwa Mai Bauchi ne,.haka suka sa shi a tsakiyarsu. Wanda ya bawa kowa mamaki domin kuwa wajen Masallacin wasu jami'an tsaro ne sun yi wani irin shirin ko ta kwana. Bayan an idar da sallah, sai da ya jima, aka kaita gaishe shi yana amsawa. Kafin ya fito massalacin Alhaji Mamman Abba yayari suka hadu da shi, cikin girmamawa suka gaishe shi, ya amsa cikin farin ciki da nutsuwa.

Kafin suka wuce wurin motar da suka zo.da ita aka wuce da shi, kofar cikin gidan. Lokacin da ya isa Mai Babbar daki ce kaɗai a parlourn. Kamar tasan zai zo ta zauna a parlourn tana azkar sai da yaji wani iri a ransa ya zauna a gefenta, yana mai daura kanshi a kafad'arta. "Ummina, barka da asuba!" Juyawa tayi tana kallonshi fuskartar dauke da murmushi. Amma a kasar murmushin nan ciwo ne mara iyaka. Ciwo ne mai zafi da ba zata tab'a mantawa ba. "Ummi!" Yatsa ta saka mishi a bakinsa tana faɗin. "Shiii! Yanzu ba lokacin magana ba ne roko ake a wurin mai dukkan." Ta fada tana cigaba da addu'arta har ta gama suka shafa tare. "Ka kyauta abinda ka yi kenan?" Ware idanu yayi yana kallonta da mamaki akan fuskarta. "Ummi nayi wani abu ne?" "Mai yasa zaka bi mace da ƙarfi? Duk ka ji mata ciwo haka, an gaya maka hauka ce abin? Kada ka kara bin mace da ƙarfi domin ba shi ba ne cikar mazantaka, namiji tsayayye yana bin mace a ruwan sanyi ne har ya cimma abinda yake muradi, na maka nasiha da kada ka kara haka, babu girmamawa a cikinsa. Ka shiga ka dubata" ta fada tana barin parlourn, sai ya ji babu dad'i tow amma ita Zainab din ce ai bata din ce ta ki bari ayi kome cikin salama, a hankali ya nufi dakin. Bayan na idar da sallah na koma gadon na kwanta tun kiran sallah farko Mai Babbar daki ta kawo min madara na sha, sannan nayi sallah nafilla na koma na kwanta ban yi barci ba na cigaba da karatu don bana iya jin dadin zaman, sallah asuba ba tashi nayi ina idarwa na zauna akan gwiwata nayi addu'a, domin ta leko ta ce kada na kwanta nayi addu'a sosai, tow Ina idarwa na hau gadon ina karatu, ya shigo gabana ne ya fadi, take naji cikina yayi wani irin murd'awa, na tashi kamar xan dirka a gadon na fita domin wani irin tsoro ne da tashin hankali ya shige ni, wnada ya haifar min za zazzaɓi lokaci guda, hawaye ne ya zubo min wani na koran wani. Abin jiya ne ya dawo min bakiɗaya na firgita. "Ya jikinki?" A hankali na fara ƙoƙarin sauka a gadon ya tsaya daga bakin kofar, murmushi yayi ya ce min. "Koma ki kwanta!" "A'a fitsari nake ji!" Na faɗa ina tafiya a hankali, wanda kana lura zaka fahimci ina dingishi. Tunda na shiga nake kuka domin Allah ya gani tsoronshi nake ji, ina zaune a ban dakin da nayi fitsarin tsoron, sai da ya buga kofar sannan na fito, kaina a kasa ya ce min. "Zo ki kwanta zan miki allura ne!" "Ka barshi na warke!" Ledan da yake gefen gadon ya ɗauka, ya saka abin drip sannan ya ce min. "Kwanta!" Ba musu na kwanta, tare da rufe idanuna ya haɗa min karin ruwan, da allura. Zama yayi a gefena, bakiɗaya ni dai bani da nutsuwa, hannuna da ya saka min karin ruwan yake murzawa. "Sannu kin ji!" Ya fada a hankali cak kasar makoshinsa. "Kina cin abinci idan aka kawo miki kin ji!" D'aga mishi kai nayi ina mai rufe idanuna. Tab'a goshina yayi yaji har yanzu da zazzaɓin tsoron ya ce min. "Ki nutsu babu abinda zan miki." Gyada kai nayi har lokacin idanuna a rufe, hannunsa ya kai kan cikina, yana kallon yadda na bude idanuna ba shiri. Fuskata tana nuna alamar tsoro. "Ya dai? Tab'a Baby nake na ji ko yana lafiya don nasan jiya when I chop her Mama!" Rintsa idanuna nayi da karfi na fashe da kuka. "Don Allah ka yi hakuri barci nake ji!" Na faɗa ina kokarin tashi zaune amma kamar a cikin maganin da ya saka min akwai na mutuwar jiki, a hankali ya janye rigar har sama. Wani irin kuka nake a hankali kasa kasa na ce mishi. "Barci nake ji!" A hankali ya ja rigar ya gyara min, sannan ya mike a hankali ya zuba hannunsa dukka biyu a cikin aljuhunsa yana kallon yadda nake sauke numfashi a hankali, alamar barci yayi gaba da ni. Takowa yayi ya sumbaci kumatuna da goshina, sannan ya tsaya yana kallona yadda nake yatsina fuskana kamar zan yi kuka.
"Sorry baby girl!" Ya furta a hankali, yana mai jan mayafina ya rufe ni sannan ya bar dakin, gidanshi ya dawo ya kwanta. Da Nady tana nan ba sai ya sauke gajiyar shi a kanta ba, amma ta kama ta wani tafi ita gata nan mai kishi, wancan mai tulelen ciki ta can tana fama da kanta, shi gaskiya a bashi matarsa yayi jinyarta a gabanshi ko ba kome zai na rage zafi. Da haka barci ya kwashe shi, wurin karfe sha daya ya farka kiran Nady ce ta tashe shi tana mai fada mishi. "Yau ce ranar ka ta farko a fada, kana barci?" Ta tambaye shi, "hmm!" Ya ce mata, can ta ce mishi. "Kayi hakuri gani nan a hanya!" "Better!" "Am sorry My king I miss you!" "Haka kika ce!" Ya furta a hankali, "Allah gani nan ba zan kara barinka makara ba,!" Lumshe idanun yayi yana faɗin. "Are you sure?" Ya tambaye ta domin yasan ba abun mamaki bane ta ce tana zoyalarshi ce. "Gani a cikin gidan bari ka gani?" Ta turo kofar dakin juyawa yayi yana kallonta, ta shiga kwalliya cikin riga da zani, murmushi yayi ya bude mata hannu. Ba musu ta isa gare shi suka rungume juna. "Me yasa baka shirya ba?" "I'm hungry!" "My King kasan zaka tafi fada!" "Just 45 mins!" Jan hancinsa tayi tana faɗin. "As you wish!" A hankali ya zuge zip din gaban rigarta. Yayi gamo da kayan marmarinsa, kifa kansa yayi ya shiga sarrafa su san ranshi. Kafin wani lokaci Nady da shi sun cika dakin bakiɗaya da hayaniyar da suke saukewa juna farin ciki yasa gidan ya ɗauka. Ijlal da take barci ta farka, gabanta faduwa yayi domin ta tuno da yau zasu tafi wurin Malamin Hajiya Mardiya, akan Matan Faris din sai gashi tana jin ihun Nady dama ta saba jin ihunta sama sama idan suna tare da Mijinsu, wani irin bakin ciki ne ya cika mata zuciya. Kallon cikin jikinta take yi da wani irin takaici tana ganin kamar shine ya hanata rawan gaban Hantsi.

Tashi tayi ya nufi ban daki tayi wanka, sannan ta fito a lokacin ta daina jin ihunsu. Shiryawa tayi cikin wani simple dress irin bubun nan ta fito a hankali zuwa Parlournta ta samu Yar aikinta tana gaishe ta, d'aga mata hannu tayi tana faɗin.."ki zubo min abincin." Tasan itama ta ji ihunsu, wucewa tayi parlournshi cikin wani irin zafin rai take buga kofar. Can suka fito cikin huci da takaici ta ce musu. "Idan zaku yi karuwancinku da cin juna me zai saka sai ta biyo ka, me yasa ba zaka bita wurinta ba, don sanin ciwon kai har yar aikina tana jin ihunki koda yake dole ki yi haka tunda g***ndinki na cin namiji ne ba haihuwa ba." Idanun Nady ne ya cika da kwalla, bata ce kome ba shima kuma bai ce kome ba, duk sai ta ji ta muzanta. "Ke da Allah ya baki haihuwar kina da wani sanin cewa idan Allah yaso sai ya kashe abin cikin karshe ita ya bata haihuwar jaka wawuya gara ita sau dubu bata bi kowa da sharri ba kika kara zuwa min nan da haukarki har kika zagar min mata sai na sake ki. Yarinyar karama dake sai fitina da rashin kunya look at you." Ya fada yana jan hannun Nady suka shige cikin sannan suka buga mata kofar bamm a fuskarta. Wannan zagin da yayi mata da dukar kawo wuka yayi mata da yafi mata sauki akan yadda ya gasa mata magana.

Haka suka shirya ya fito ya sha kwalliya Nady itama ya rakata suka shirya tsaf ta rako shi har waje, a kofar gidan can kuwa masu busa algaita ne da kad'e kad'e, suka raka shi har Fada, wunin ranar tunda ya shiga fada sallah yake fitar da shi, a sai can bayan la'asar ya shiga cikin gidan. Ya gaida mutanen gidan. Duk da yana hango kiyayyarshi a idanunsa amma yasan ba abun me sauki ba ne su tunkaro shi gaba da gaba. Abdulhafiz da Salim tun jiya suka kebe da shi tare da mishi mubaya'a, sannan suka ce zasu bashi duk wani goyan bayan da zai bukata domin ciyar da Masarautar gaba. Haka kuma zasu kaucewa duk wani abu da zai kawo matsala a mulkinsa, sun sani ko suna so ko basu so dole su yi mubaya'a, sannan dole su girmama shi a matsayinshi na Ubansu. Basu da wani babban da ya wuce su duk da sun gama magana sai da Abdulhafiz ya tura mishi sakon cewa.
*Yaya Sarki ka kula da mutanen cikin Fada, akwai masu shirin dabb'a maka wuka ta baya, sannan im deeply sorry da abinda zai bayyana a gaba don ka saka ayi bincike har a cikin gida dangane da rasuwar Abdullahi da Abba, Yaya Sarki mu ma kanmu ana turo mana da sakon barazana idan bamu yi wani abu ba! Yaya Sarki Yarana da matata da yan uwana. Har da kai ka saka idanu akanmu hakika Abba yayi gaskiya ya ce bai zama dole ya kare mu ba, Allah zai kare mu garkuwarmu yana nan tafe Yaya Sarki kayi wani abu!*
Your blood brother!
AAS Yayari! Tun da ya ga sakon, ya turawa Faruq, faruq kuwa ya tura team dinsa da suke aiki ba dare ba rana. A ciki da wajen Masarautar Zanzabira, tura mishi sako Faruq yayi ya ce mishi. *Done Your highness!*
Ba iya Abdulhafiz ba duk wani dan gidan da yake amsa sunan Yayari an shiga cikin lamarinsa, hatta Alhaji Rilwanu Abubakar Yayari, an san inda yake kuma Idanun Faris yana kanshi, Asibitinsa da yake kauna, ganinsa yake kamar rayuwarsa idan wani abu ya tab'a asibitin nan zai iya aikata kome domin asibitin rayuwarsa ce. Don haka ko ina a kai idanunsa. Sannan daren jiya aka yi wani aiki na sirri a cikin gidan.
Parlourn Mai Babbar daki ya shiga da sallama, yana mai ware idanunshi akan Ijlal da Hajiya Mardiya da ta kawota. Sai kuka take tana yin abu kamar an zalince ta. "Yanzu don Allah Mai Babbar daki, saboda kaunar da kikawa Uwar Yarinyar nan, yasa na amince aka yi auren nan bata gama makaranta ba, ashe rabo ne gashi bai damu da cikin ba, sannan a matsayinshi na likita bai damu da halin da yake ciki ba, ace kuma yana gaya mata abinda ya so? Hawan jini ne da ita fa, idan ya ga wani zai cutar da ita shi mai tsaya mata ne ba ya kuma kara tunzira ta ba, idan wani abu ya same ta bai da asara tunda yana da wasu matan, amma ya ka mata ya tuna ita ce matar shi da take dauke da cikinsa abinda ya kamata ya gane kenna ko ba kome ya kamata ya bata daraja akan sauran matanshi,tunda ita wacce bata sonshi, ma sai yanzu ta bada kanta da karyan anyi wani abu mai muni kanta." Sai da ta gama maganar yana zaune a gefen Mai Babbar daki kanshi a kasa ta ce mata. "Shi kenan zan duba lamarin." Kallonshi Hajiya Mardiya tayi tana son cewa ga shi nan, kallonta Mai Babbar daki tayi ya ce mata ."kul da yake yarima, yanzu uban kasa ne shi girmamawa yake bukata ba janyo shi kasa ba, ita yarki ba haka Uwarta take ba idan ma kina zugata ne ki daina domin ba zan ɗauki reni ba, idan duniya zata haifa da shi ina son ki sani sune gaba da ita, batun karatu gata nan ke kika ce kina son ki aurar da ita kada ta lalace, domin ance abinda Ubanta yayi kada shafe ta tow me ye laifina anan? Mardiya domin dakatar da auren Zainab da Salmanu Faris na shigo da yarki, sannan lokaci ya wuce da zan na fada a gabanshi, idan tana son zaman lafiya da shi ta kula da aurenta idan bata so kuwa zata iya tafiya ga shi nan sai ya sawwake mata ai ba matsala!"
"A'a ni da bance haka ba, taya za a raba sunnah maa'ikin Allah, wai na ga abin ne sai a hankali itama bata jin magana, in sha Allah auren nan mutu karaba!" Daga haka suka yi sallama suka bar gidan. Juyawa tayi tana kanshi, cire rawaninsa. "Ya aka ji da jama'a?" "Alhamdulillahi, Ummi!" Amsa masa tayi tana kallonshi. "Akwai wani al'amari a fada! Ummi akwai wani abu a boye a tsakanin mutanen da suke kewaye da ni, Ummi akwai wani Files da faruq ya turo min jiya ta !" Shiru yayi yana kallon kofar dakin da ta fito sanye da Abaya peach colour, tayi rolling kanta da bakin mayafi, tana tafiya a hankali kamar bata da jini a jikinta. "Fulani Babba me kike so?" Bata so su san ta fito ba, amma yanayin yadda ta fito yasa hankalinsa ya tafi gare ta, haka yasa Mai babbar daki itama ta juya tana kallona. Murmushin yake nayi nace mata.."Zan kai abu ne kitchen!" "Sailuba!" Mai Babbar daki ta kirata, zuwa tayi ta zube a gabana tana faɗin. "Ki gafarce ni Fulani, kawo na kai kitchen." Mika mata nayi na juya dakin." "Ina jinka!" Ya fada tana murmushi, musamman yadda ya shagala da kallonta, ta cika mishi idanu, bakiɗaya wani irin yanayi yake ji da kaunarta. "Ummi yunwa nake ji!" Share shi tayi ta ce mishi. "Bari na duba kitchen din!" Ta mike tana mai nufar kitchen, ta bashi wuri ya ga Zainab din. Kamar jira yake yana shiga ya same ta zaune tana gyara pillow. "Baby I want to chop?" Ya fada min yana zama a gefena, matsawa nayi domin yau ina jin dadin wurin ya daina min ciwo, a hankali ya matso ni. "Please" na fada muryata tana rawa. "Me nayi miki? Abinci zan ci!" Hawaye ne sharr. A hankali ya zauna yana kallona yadda nake shashekar kuka. "Dama haka kike kyau idan kina kuka? Gaskiya ki yi wani abu kin yi min kyau!" Ya matso nima na matsa jikinki allon gadon. Shafa fuskana yayi ya ce min. "You look pale, yanzu kina jin ciwon kamar jiya?" Kaina a sunkuye na ce mishi a'a da kai. Jan kumatuna yayi ya ce min. "Na yi miss old Zainab, idan kika cika sati ki ce zaki dawo" duk kaudi da iyayi duk babu, yadda ya ce na ce zan dawo bai san yadda gabana ya fadi,, ni ce zan ce zan dawo lallai na dawo ya kashe ni da abinsa mai taurin kan nan, salon ya sake turawa min sai ya fito ta wuyana.

Wayata ce tayi ƙara, zan dauka ya rigani Bestie ya gani, yana dauka ya saka a kunnensa.."Yeemar ki kyale Fulani Babba ta huta!" Daga can bangaren ta ce mishi. "Tuba nake Mai Martaba, ina son na yi magana da Fulani Babba;" ya mika min wayar, a kunne na saka na ce mata."yaushe zaki zo?" Na faɗa ina shashekar kukana, "har yanzu ba ki daina ba Zainab, kin girma fa!" Ta fada tana murmushi, sai nake ji kamar zagina take yi. "Kin kira ki min dariya ne?" Na tambaye ta, "a'a dama wasu kayan gyara na saya miki a wurin Maman Hidaya and khairat." "Wallahi sai na zage ki!" "Allah ya baki hakuri, ni dai na saya mana idan kin so kada ki yi amfani da shi .!" "Oho na dai gaya miki kada ki fara kawo min!" Amsar wayar yayi ya saka a kunne daidai tana faɗin. "Aikin banza idan n a kawo ki zubar kayan gyaran jiki ne yar iska don an farke ki uban waye ya ce ki ta gudun miji kaya xan kawo kuma wallahi kila zubar sai na fashe kudina ki gyarawa Mai Martaba wurin zama yayi kodumo son ranshi Yar iska irinku ne kuka gane gardin harka ake shiga uku da ku!"
"Ku turo da account number zan tura miki kudin ai dole ma ta gyara jikinta!" Kit ta kashe wayar ya kalle ni yana d'aga min gira, "zan biyata domin na jima da sanin zan kwashe dad'i anan!" Ya matso kusa da kunnena. Abinda Ya gaya min ya sani fashewa da kuka, tare da ture shi ina ihu. Mai babbar daki da take parlourn ta ce mishi. "Fito ka bar mana gidan tunda baka da aiki sai saka mara lafiya a gaba!" "Gani nan!" Ya fada bayan ya sumbaci bakina


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login