Showing 192001 words to 195000 words out of 304445 words
zai mana kyau ba!" Na kashe wayar shigowar Iram dauke da wayarta tana dariya. "Ke mai miji, da wani dan iska can da ya kashe Lucky, ga abinda yake faruwa!" Ta wurga min wayar. Hoton bidiyon mu na lokacin da aka yi party nan ne har aka sace mu. "Wanann shine abin da kike ihu a kai?" "Ba shi bane kaɗai duba!" Ta nuna min wani videon idanuna ne suka cika da kwalla. "Me nayi miki da zafi zaki lalata min rayuwata?" Murmushi tayi ta ce min kiyi ƙoƙarin haduwa da Mijinki da alamun kome ya kwace mishi, kamar yadda nake zaune babu aure haka nake son ganinki mun lalace tare!" Wani mug na kwalba na dauka na rosa mata a bakinta sai ga jini na zuba, na rufe ta da dukar da ban san ina da karfin ba dukarta nake iyakar karfina ina kuka har ina jin kamar juwa na kamani, ihunta da Maluma ta ji yasa ta shigo da gudu. "Ba zan yi irin rayuwarki ba, zan wanke kaina a wurinsa ke datti ce mai gurbata muhalli da rayuwa tur da samun yar uwa irinki!" Kwace ta Umma tayi saboda dukar da nake mata. "Eh naji amma ko mahaukaci Abba ya haɗa ni aure da shi, zan sadaukar da kaina akanshi ke fa? Mijinki har yau bai san ki mace ba ko boyewa kike kin tab'a bin namiji!" Wani kukan kura da anyi na shaketa ina buga kanta da bango. Ina kuka kamar zan mutu, kwace ta Maluma tayi ta wanke ni da mari kafin ta ce min. "Da gaske ne babu abinda ya tab'a haɗaku?" Wani irin kunya da tashin hankali na ji ya cika ni. "A'a Maluma ba haka bane?" "Wallahi haka ne idan karya ne a kaita asibiti a duba ta." Hawaye ne ya zubowa Maluma ta ce min. "Ya kike ji a rayuwarki? Baki jin kunci da tashin hankali? Shima ya kyale ki har wannan lokacin, Tabbas kin yi abinda Abbanku ba zai yafe miki ba. Kada ki sake taka inda nake!" "Aikin banza idan kuka yi haka wani uwar ce zata faru? Baki ga ita karuwanci take a gaban Malam kin ga yayi mata wani abu ne? Wannan lamarin ba wani abu ba ne domin anyi auren mata dayawa kuma suna gudun mazajensu wasu angurya ce hala itama shine a gabanta idan kuwa shine dai dai su shekara dubu." Inji Umma ta juya ga Iram ta ce "Sharifa kenan, sai me don kin gaya mana bata tab'a haduwa da mijinta, sai me? Gara Ikhlas sau dubu da ke, ba yadda xan yi domin nima Uwa ce amma macen da ake kira mace take gudun miji ba fanko irinki ba, ki tuba kafin lokaci ya kure miki domin ba domin madigo ba riba ce da ita ba har gara karuwanci shi namiji na auren mace ke fa? Bayan mahaifa ya lalace ko?"
Fita suka yi daga dakin suka barta tana numfashi tare da zubar da hawaye ta ce min. "In sha Allah sai na hanaki jin daɗin aurenki!" "Aniyar ki zata bi ki jaka kazama matacciya!" Domin abinda ya dace da ita kenan sunan da ya dace da ita kenan, haka ta fita na cigaba da kuka gidan yayi wani irin tsit fita nayi sanye da Hijab har kasa, ban tsaya ko ina ba sai Fada anan aka gaya min suna Asibiti na wuce. Cirko-cirko suka yi a gaban emergency, manya da Yara, sai kuka suke domin wannan shine karon farko da aka kawo Mai Babbar daki asibiti. Idan ka kalle shi sai ka ɗauka babu jini a jikinshi ne. Shigowar matansa biyu yasa shi zuba musu idanu. Kafin suka iso gare shi.
Rab'ewa nayi gefe domin nasan ni ce mai laifin. Duk abinda ya same Mai Babbar daki ni ce. "Yaya Salman me tazo yi asibitin? Tazo ta kara kashe mana Uwa ne?" Kallon Aneesah yayi da idanu. Kafin ya juya kaina ya kalle ni. "Gaskiya ta bar asibitin nan ko mu dauki mataki a kanta." Yadda suke harzuke, ya sa shi takowa gabana ya ce min. "Ki koma gida!" "Ka.... Bar...ni na wanke kaina." "How?" Ya tambaye ni yana zare min idanu. "Da gaske ba hotona ba ne?" "Waye zai yarda? Bayan ni da nake Mijinki guduna kike?" Ya fada kasa kasa yadda babu me iya jin amon kalmar. Da sauri na d'ago kaina ina kallonshi. "Idan na yarda ka bincika zaka wanke ni?" Duk da halin da yake ciki sai da ya kara min kallon ban dariya. "Ikhlas a zahirin gaskiya kin bani kunya, ace kina wife of crown prince a ce har an fitar da nude dinki! Kuma Prince Salmanun haka zaka cigaba da kallonta a matsayin mace." Inji Iram wacce ta shigo asibitin ita da Mommy Turai. "Wallahi ba nawa ba ne?" "Ku fita kafin na dauki mataki akanku!"
Wani irin kuka ne ya zo min, taya xan iya cewa bani bane. Haka na juya a hankali ina tafiya. Na bar cikin asibitin karar horn naji na tsaya ashe Uwais ne.. "yan mata shigo na kai ki gida ai na gaya miki ba sonki suke ba."
Yana tsaye ya ga lokacin da ta shiga motar Uwais. "Na gaya maka yarinyar nan bata sonka, duk abinda ya faru amma zata bi wancan dan iskan gayen!" Murmushi yayi ya kalli Nadiyyah. "Ni kuwa sai nake ga kamar Nadiyyah Jamil Chiroma da na sani bata damu da rayuwar wasu ba, tafi damuwa da niman kuɗinta da duniyarta yaushe kika fara damuwa da kishiyarki? Ko akwai wani abu da yake fishy ne ban sani ba?" "A'a... A'a no never!" Ta fada da sauri. Shiru yayi yana kallon motar, wayar shi ce tayi ƙara ya ɗauka. "Kan san mai wannan wayar?" Gabanshi ne yayi mugun bugawa, a hankali ya ce. "Eh!" Yayi shiru kafin ya ce . "Kanina ne!" "Tow Allah ya musu rasuwa bakiɗaya suna asibitin kwararru na jahar Gombe!" "Innalillahi wainnalihir rajoun!" Ya fara wani irin haki, tare da dafe goshinsa, zuciyarshi tana wani irin bugawa. "Lafiya?" Nady ta tambaye shi, lumshe idanun yayi kafin ya bude a hankali ya danna wayarshi. Ya saka a kunne. "Ka nime mana iznin private jet to gombe!" "Lafiya Ya Salmanun?" "Abdullahi Passed away!" Ya iya furtawa, yanzu ya fahimci abinda ya tab'a Mai Babbar daki, ba videon ba ne, domin wayar tana hannunsa sannan koda Aneesah ta ce ga abinda ya faru, ya shiga ya ga bata bude videon ba, haka yana nufin ba shi ne ya sakata suma ba. Haka suka fito Faruq ya kira sauran mazan ya gaya musu suka nufi Gombe, domin sun bar garin zanzabira, sannan sun cigaba da tafiya ana binsu ana basu wahala, har suka yi tafiyar da ta kusan kai su Gombe, kafin aka aikata abinda ake so, lokacin da suka isa Gombe kai tsaye suka nufi asibitin bayan sun sauka a jirgin. Suna isa aka wuce da su inda gawar take, domin dakyar aka cire su a motar suna manne da juna, Jasrah Abdullahi da Babyn a tsakiyarsu, wannan shine horrible abinda ya tab'a gani da ba zai manta ba, sannan bayan an saka wuta a motar tura su rami aka yi motar ta kama da wuta sosai, jikinshi tsuma yake kamar zai ci babu, wani irin wuta yake ji na kama zuciyarshi, jikinshi rawa yake kamar ya tashi. "Sir an samu wani witness din din da ya ga faruwar lamarin!" Juyawa Faruq yayi ta samu mutumin suka fita. Wani dan Yaron Fulani ne, a hankali yake gayawa Faruq abinda ya gani yadda aka sakawa motarsu wuta tana binsu koda suka tsaya motar taki budewa sunyi kokarin fita amma taki, sai ga wata babbar mata tana zuwa wasu mutane suka sauka a cikin motar suka kara zubawa motar petir daga nesa sannan babbar motar nan ta tura tasu da take ciki da wuta a ramin, yace musu yaji lokacin da suke fadar sauran na biyo bayanshi, shima ya je dibar itacce ne, anan wallahi abinda ya sani kenan. "Kai ma da kai yi magana rayuwarka tana cikin hatsari daga yanzu zamu tafi da kai domin zasu kashe ka!" Faruq ya gaya mishi yana shiga cikin dakin, ganin Salmanu akan gawar yayi shiru kafin ya dafa kafad'arshi ya ce mishi.."Yallabai an fitar da sanarwar rasuwar, zamu tafi da gawar ne?" "Iyayen Jasrah ya kamata su sani!" Ya fada a hankali, ya juya ya fita daga dakin ajiyar gawar sannan ya fito waje, so yake ya fasa ihu ko zuciyarshi zata yi sanyi. Wannan aikin ban da Allah waye zai maka wannan jarabtar? Waye zai kawo fitanannun rayuwarka. Waye zai shiga rayuwarka har ya maka irin wannan barnan. Shiru yayi can sai ga motar Sarkin Gombe, domin Labarin har ya kai musu Kasancewa an sake labarin har BBC Hausa sun samu sai kiran members na familys din ake yi gidan jaridu. Wayarshi ce tayi ƙara ya dauka a hankali. "Mahaifiyarka da Matarka, ban san waye ka fi so ba, ita Mahaifiyarka ka saka masu tsaron kofarta, babu da muka iya ita Yarinyar fa?" Murmushi yayi wanda kana gani kasan na bakin ciki ne da ba yadda ya iya. Kiran Faruq yayi ya matso da shi daidai kunnen. "Koda yake shi yaron ya gama mana aiki yanzu sai ka ceto rayuwarsu kamar yadda dan uwanka yayi ta kiranka yana niman taimakon ka, baka nan balle ka iya taimakonsa ita kuma gata a kusa da gadar mata, wanda yake cike da ruwan dam za'a sake shi nan da minti goma kacal!" Dariya mutanen yayi ya ce mishi. "Abokina ya kamata ka tunani." "Matsafi dakare ba!" Ya bashi amsa yana murmushin gefen baki. A can gefen kuwa Faruq ne yake waya kafin ya katse kiran.
Komawa yayi wurin wakilan Sarkin Gombe da iyayen Jasrah sanan suka amince a kawo gawar Zanzabira ayi musu jana'iza. Zuwa gefenshi Faruq yayi ya ce mishi. "Yallabai team am sorry!" Ya fada a hankali. "Don't try Tell me that narasa ta?" Girgiza kai yayi cikin sanyi murya ya ce . "Sir! An yi kokarin dakatar shi amma ya fada cikin dam din!" Kifa kanshi yayi akan tafin hannuna. D'ago kai yayi ya ce. "Kallu Innalillahi wainnalihir rajoun." Yana shafa kirjinsa kafin ya mike yana mai cewa.."Zamu tafi da gawar domin karfe biyar ayi musu jana'iza!" "Shi kenan! Muma muna tafe da za'a mana lamuni ne ayi jana'izar gobe!" Shiru yayi kafin ya ce musu.."shi kenan!" Haka suka wuce da gawar a motar asibiti. Lokacin da suka isa sun samu an gama shirya tashin jirgin. Sannan suka wuce Zanzabira.
***
A lokacin da muka bar asibiti kuka nake ina rantsuwa, shima sai cewa yake. "Na yarda dake amma su fa? Ki amince min ba nuna miki abinda babu wanda ya isa nuna miki!" Kusan haka yayi ta rarrsshina wanda ban fahimci kome ba, har muka isa gadar mata, anan yake bani zaɓi. Ban san me yasa na kasa mishi musu ba, domin a gabansa Abba ya kirani ya ce kada na dawo mishi gida ya gode da abinda na aikata. Duk sai na rasa meke min dadi. Nayi ta kuka har na rasa inda xan saka kaina. Muna zaune a wurin Yeemar ta kira ni tana gaya min labarin rasuwar Abdullahi nan na rikice da kuka zan koma a lokacin wasu mutane suka zo inda muke tare da ciro bindiga shi kuma ya ji tsoro tare da tasar motar, a tunanina zai bar wurin ne ashe mutumin nan nashi abun ya shirya kawai ya sha kwana tare da juyawa ya kalli ta inda ruwan dam din yake kawai ya naushi katangar gadar ihun da na fasa tare da rike hannunsa sai ji nayi mun.fada ruwa tsundum. A gaskiya na yarda da Allah kuma na yarda da duk yadda kaga rayuwa kada ka rena shi, domin motar ta rufe kanta, haka yasa ruwa bai fara shiga akan lokaci ba. An kira Jami'an kwana kwana amma basu zo da wuri ba, haka yasa aka nimo masu kama kifi suka shiga niman motar domin ta nutse, An kira Iyayenta bakiɗaya hankalinsu a tashe yake, lokacin da suka iso suka samu ana ta niman shi kanshi Abba sai da yayi danasanin fushin da yayi da ita, cikin ikon Allah kuwa aka samo motar wanda dakyar aka safa glass din gabar motar aka ceto ta, domin ta sha ruwa ana zargin ta musu, shi kan ko ba a fada ba yadda ya tashi a cikin motar ita ce ma bata tashi ba, haka yasa suka fito da gawarshi, wato ana fito da ita tana shan iska ta ja wani irin numfashi, ai kuwa take aka shiga matse cikin ya sai ga ruwan da ta sha nan aka wuce da ita asibitin, shi ma aka kira Danginsa aka gaya masu mutuwar dan uwansu, Budar bakin Mamanshi ta ce musu. "A'a ba d'ana ba ne, ku kai shi inda za a mishi kuka ai na gaya mishi ya fita harkansu, don haka ku binne shi kamar kare ne ya mutu!" Daga haka ta katse kiran.
A lokacin da gawar Abdullahi ya iso ba asamu yi musu wanka ba sai yayyafa musu ruwa aka yi. Aka musu sutura, a lokacin Mai babbar daki ta farka domin sun yi fatan ta farka domin ta ga gawarshi, Khairat Yarshi tana kafadar Salmanu Faris. Inda ta kwanta tayi shiru. Har aka gama jana'izar, yana rungume da ita har makabarta. Ta ce mishi. "Daada anan ake binne mutane?" Gyada mata kai yayi, ta kuma ce mishi. "Nima anan zaa binne Ammy da Dady?" Gyada mata kai yayi, "Daada Dady ya ce ko baya nan kai zaka zama Daadana?" Gyada mata kai yayi yana jin wani irin kaunar Yarinyar a ransa. A ransa yayi alƙawarin yar Ikhlas ce. Haka aka binne Abdullahi shi ɗaya sannan aka binne Jasrah da danta sai da aka rufe shi ya samu damar zama a bakin kabarin yana kallon mutane suka watse, sai a lokacin ya fara kuka a hankali yana faɗin. "Me yasa ka bar min ita? Ashe ka san tafiyar ne ka ce ni da Mai Babbar daki ka bar mana aiki? Me yasa Abdullahi, ka tafi ka bar ni da rashin yarda da ban yi da ku ba!" Haka yayi kuka a wurin har Faruq ya dawo saboda Magariba tayi daukar Khairat yayi suka fita.
Sai da ya koma asibiti har lokacin Mai babbar daki bata hmm ko uhmm, tayi shiru sai dai tayi murmushin karfin hali, amsar Khairat tayi tana mai rungume ta, ta lumshe idanunta akan yarinyar wani irin kaunar yarinyar take ji, tana jin wata irin zafi da ciwo domin tayi imanin ba a tab'a mata irin wannan raunin ba, an mata raunin da na zata tab'a mantawa ba, wani irin ciwo take ji a ranta da zuciyarta ita kaɗai tasan yadda take ji, musamman da take jin yarinyar na ajiyar zuciya.
A asibitin suka kwana gabakidaya mazansu da matansu, the next day suka wuce Fada, ko ta kan Ikhlas babu wanda ya bi sai Yeemar da ta zo, ita ta samu har lokacin tana kwance a cikin wannan yanayin. Haka ta tafi gidansu babu wnada ya damu sai Umma da ita suka zo.
Abu kamar wasa domin a cikin kwanaki uku daga Ɓangaren Iyayenta zuwa Salmanun Faris babu wnada ya tako asibitin, sai ranar asabar da ddare ya shigo Umma da Yeemar wacce take fama da Laulayin cikinta ta mike tana faɗin. "Umma zan tafi." Ya nufi kanta ta ce mata. "Don Allah ki tashi haka?" Ko gaisawa basu yi ba domin tafi kowa daukar zafi a cikin kwanaki ukun kullum tazo zata tambaye ta ya zo ta ce a'a, amma sai yanzu ya zo yadda yaga Yeemar bata kula shi ba ya sha jinin jikinsa, ita ma Umma wani dauke kai take tana mai kiran Nuraim ya zo ya dauke ta suka nufi gida.
Sai da ya gama dube-dube, sannan ya buga gadon yadda yasata dole ya farka.
Bude idanun nayi da suka yi nauyi, na kalli dakin me dauke da haske sosai. Sannan na kara lumshe idanuna a karo na biyu na kara bude shi. Juyawa nayi na ganshi zaune harde da kafarshi wato yayi Crossing leg yana kallon wayarshi. "Kin gama gudun?" Tashi nake son nayi amma na kasa, "wannan wani irin mutum ne da bai san tausayawa ba, sai bakar magana." "If you like ki fadi kome!" Bude idanun nayi ina jin kwalla na cika min idanu. Mikewa yayi. " Ai nasan ke ba jahila ba ce, da aurena akanki zaki bi a wani namiji." Murmushin takaici yayi ya cigaba da cewa. "Shima sai mun haɗu a gaban Ubangiji, domin ba zan yafe masa yunkurin kashe min mata da yayi ba.......
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 64
Wani irin d'aci nake ji kamar yana watsa min ruwan zafi, lumshe idanun nayi na kara rudewa for each any single words da yake fita daga bakinsa jin sa nake kamar rayuwata ce ta zo karshe domin yaki faiimtatta. Sannan yaki gano mai yasa kome ke faruwa, abinda na fahimta rayuwata tana dauke da wata ƙaddara da take bibiyata, domin xan iya cewa baƙin alkalamin ƙaddarata, ta shata min zanen ƙaddara mai karfi a kaina da rayuwata. Domin bana jin ko wanda ba Musulmi ba yana fuskarta rayuwar da nake fuskanta. "Tunda baka bukata na a rayuwarka don Allah ka yanta ni daga kaddararren aurenka, maybe da Iram ka dace we are not match to each other." Wani kallon banza ya min ya ce min. "Kina bukatar yanci? Hmm da yake kina da." Shiru yayi ya ce min. "Think wisely!" "Ka samar min da yancin ta hanyar da ba zaka kara jin sunana ba!" Na faɗa ina kokarin sauka a gadon don na gama gajiya da kwanciyar asibiti gara na boya inda zan samu yanci matukar na cigaba da rayuwa da shi. "Bayan duniya tasan cewa ba iya abinda kika aikata? Malam Junaid ya bani zaɓi, domin kare mutuncina da na gidan Yayari zan rabu da ke amma sai bayan nadin Sarautar da za ayi!" Kwalla ne