Showing 246001 words to 249000 words out of 304445 words
musu filin. "Ke waye kike yiwa ihu!" Ya daka mata tsawa da sai da Babyn ta firgita ta fashe da kuka, ya daura ta a kafad'arshi. "Ni sa'anki ne?" Ya fada da wani irin karaji, "don ina aurenki zaki na min iskanci wani irin abu ne bakya yi don na kyale ki? Tow daga kada ko da wasa ki kira wayata don idan kika kira wallahi sai na sab'a miki sakarya wacce bata iya kishi ba sai hauka da jahilci, ki dube nayi kama da wnada zaki yiwa rashin kunya ne!" Yadda yake Bala'i yasa har yan gidan suka fito, ya kara mata da cewa. "Na rasa wani irin hauka kike yi ne? Ikhlas ta samu Nady basu yi jahilci da kike yi, kin zo lallai ke sai na nisanta kaina da ita, matata ce fa Umarnin Mahaifina ce ita, Da ita mahaifina ya rasu burinsa na aureta gaya min me mece ce a gare ni? Mahaifiyata da ta ce na aure ki ce min tayi idan ba zan iya ba na rabu da ke itama kenan ta gaji da halinki, Look na gaji idan zaki zauna ki zauna idan ba zaki zauna ba zan sallame ki, tausayinki nake yarinya karama dake kin lalace, Matata Virgin ce da bata tab'a bin wani namiji ba amma red hand na kamaki kina chat da yan iska! Gaya min wani namiji ne mai hankali zai zauna da ke? Na rufa miki asiri zaki raba ni matar rufin asiri? Wallahi ko Nadiya bata isa ya raba ni da Ikhlas ba, idan kika cika ni sake ki zan yi na bata yar ai na ji duk abinda kuke fada, Ikhlas ta jefi yar naji magana ya dawo min, tow ki sani abinda kike yi ne ya dawo kanki har y'a tab'a min, tun kafin Zuwan Yayari Zanzabira babu wnada ya isa ya shiga cikin masarautar da tsafi ko asiri ba tare da ya karye ba, magabatanmu sun shirya tubalin masarautar na gaya miki wallahi ki shiga hankalinki malamai da bokayen da kike bi kuɗin zasu ci baki isa kome ba, domin Allah muka saka a gaba idan akwai wanda yake raka ki ya cigaba da zuwa kasa dusa domin ba zai tsiro ba!" Daga haka ya ajiye yarinyar ya fita bai kara bin ta kanta yan gidan ba. Alhaji Yarima da yake tsaye bai ce kome ba. Ya kalli Hajiya Mardiya da ta gama kaduwa ya ce mata. "Ni ba kamar jinin Yayari ba ne. Asiri zai iya kamani, amma su jininsu Rantsatsiyar jini ce da babu mutum ko aljan da zai shiga da mugun nufi sai dai mugu ya tadda mugu amma baki isa ba wallahi, ku tattara ku bar min gidana na gaya muku domin nima na gaji da halinki da na yan uwanki ban da Maryamu macen kirki ce mai adalci, ina zata hada jini da Bala mutumin banza da yake bin mata da yara ƙanana, ke har kina da bakin da zaki masa rashin mutunci idan ya sake ki baki isa aure a cikin zanzabira ba wallahi!" A daren suka wuce gidan Iyayen Hajiya Mardiya, Allah yasa Hajiya Karima tana nan aka fadi abinda ya faru inda take shiga ba nan take fita ba, kai matar nan yar jidali ce ta ce mata. "Ai hakki ma baki fara gani ba!"
***
A mota sai huci yake, na shiga shafa hannunsa ina faɗin.."Ka je gidan surukai kanata fada bai da ce ba." "Cewa suka yi kin yiwa yarinyar asiri!!" Yayi shiru kamar har yanzu abin yana masa ciwo. Kwantar da kaina nayi a kafad'arshi na ce mishi. "And sai me? Kada ka damu wallahi ban yi ba kuma ban tab'a yi ba, akanka ba zan sabawa Allah ba!" Shafa kaina yayi yana faɗin.. "na gode!" Gidanmu muka wuce nan ma muka sha hira da Maluma ta bani ruwan rubutuna na sha, ina tawwasali da ayoyin Alkur'ani Ubangiji ya bani sa'a albarkacin suratul Fatiha! Haka na nutsu na sha hira kafin muka bar gidan muka shiga fada wurin mai babbar daki ta bani sakon Nadiya da yake zamu bi abuja, itama muka sha hira, har ya bude baki zai yi magana na dafe hannunsa ina girgiza masa kai ina murmushi. Kwafa yayi yana faɗin. " Na gaji;" "baka gaji ba Allah kada ya gajiyar da kai!" Murmushi tayi tana faɗin. "Wani abu aka yi?" "A'a ba ayi kome ba!" Haka nayi ta lallaba shi har muka bar gidan. Muna shiga parlourn ya zauna yana tsaki sai mita yake, kwana muka yi yana mita dariya ya bani da safe na sumbaci kumatunsa na wuce na cigaba da hidimar gidan, ya shiga fada da wuri ya dawo muka wuce Abuja, abinda na fahimta shi da faruq ba zasu tab'a nisa da juna ba, akwai Abu masu muhimmanci da Faruq yake mishi ne. Karfe shida muka isa gidansu Nady anan muka yi sallah isha cikinta ya turo kai fa, sai hotonta nake daukawa ina mata tsiya. Ganin Nady da ciki sai ya fara saka min nima kwadayin nayi cikin, haka suka rako mu har bakin gate muka yi masu sallama, airport din matarshi tayi ta turo mishi da sako, bai bude ba haka kawai na ga sakon ban hakuri dogo. Sai nayi kamar ban gani ba domin sulhu take nima da mijinta ni kuma na shiga na zama yar iya sama an saba cewa ni ke saka shi yin wasu abubuwan, nace ba dani ba, haka jirgin mu ya tashi muka isa kasa mai tsarki, cikin amincin Allah muka sauka a garin Madina, Allah na gode maka masallacin Annabi muka yi sallah asuba, sannan muka yi ziyarar da ya dace kafin muka dawo masauki muka kwanta, kallona yake a hankali yana lumshe idanun. "Ban san me Allah ya shirya a cikin alamarinmu ba, amma na rantse da Ubangiji wannan garin ban san kome akan jinyar da kazafin ba, lokacin da yarinyar ta fara rashin lafiya aka ce wai asiri ne amma babu wanda ya gaya min sau Bilqis ta gaya min, ana ne take gaya min tun ranar sunan abin ya faru da kika dauki yarinyar ashe shi yasa cikin dare da take kuka suka kira ni da naje suka bani ita duk ban san kome ba da nace zan kawota ta biyo ni wallahi ban san sau nawa yarinyar nan tayi amfani da ni, tayi amfani da Yarinyar tana ta saka ni ina shirme da girmana!"
"Allah ya kyauta yanzu meke damun yarinyar?
Rintsa idanunsa yayi cikin jin zafi da damuwa, idanunsa yayi Jajjur kamar zai fashe da kuka ya riƙo hannuna ya janyo ni jikinshi. A kunnena ya ce min. "Don Allah koda ciki kika yi ki kula da shi domin zamu wahala, Amiratul Zaitunah tana fama da cutar. CEREBRAL PALSY.....
08130269641
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 81
"CEREBRAL PALSY!" Na kara maimaita sunan ciwon,kafin na ce mishi. "Taya ake samun ciwon?" Lumshe idanun yayi for seconds kafin ya bude a kaina. "Ciwo ne da yaro yake samu tun a cikin mahaifiyarshi." Ban san a fili na fada ba, na kuma godewa Allah da ba wani abu na fada ba domin cewa nayi. "Na shiga uku na lalace shi kenan Ijlal zata ce ni dole ta ce ni ce da na sake na dake ta ranar da ta dake ni!" Rike hannuna yayi gam ya ce min. "A'a babu wanda ya isa ya ce kece!" Tashi zaune nayi na zauna daram na cusa hannu a cikin kaina. "Da a ranar nayi dukar nice domin har kabarina wannan abin zai tab'a Ni."
Janyo ni yayi kirjinsa yayi na fashe mishi da kuka, na rasa meke min dadi shafa buga bayana yake a hankali har nayi shiru ya rike hannuna ya cigaba da cewa. "Kiyi hakuri babu wanda ya isa ya daura miki abinda baki aikata ba, kwanaki da bana zaman gida can nake zuwa Zainaba ni nasan abinda nake yi ba haka kawai na tare a can ba, lokacin da ta gaya min Yarinyar tana kuka da an bata nono sai tayi ta amai, na tura Faruq ya kaita asibiti. Kin san abinda yake gabana kuwa? Wani gagarumin aiki ne na saka a gabana shi yasa ban je da kaina ba, faruq yana zuwa ya ga yarinyar ya turo min hotonta, saura kaɗan na tashi a taron da muke, saboda yadda yarinyar ta koma, haka yasa na tattara kome ya mai da hankalina kanta, Likitoci uku suka tsaya akanta domin daga yadda Uwar take fada wai tana yawan kuka ne sai ta fara ramewa, shi ne mai kula da ita ta ce tana tsammanin Fason kai ne. Zainab ni fa likitan ƙwaƙwalwa ne fa akan me ba za a gaya min ba aka kai min yarinya wai wurin wanzami ya cire mata fason kai fisabiilillahi a matsayina, na likita ban cancanci yarinyar nan ta gaya min ba? Ko a matsayina na Uban Amiratul ban isa ta gaya min idan ban fusata ba me zan yi? Sai na bawa kaina hakuri na ji daga likitocin da na musu magana, su duba min ita ina zaune ina jiran sakamakon Dr Bashir ya fara tura min sakamakon ban yarda ba, na ce Jacob ya duba shima abu daya ne, sai na ce karya suke, na saka Mu'azzam idan baki manta ba ranar bakiɗaya bani da nutsuwa ko abincin da kika ajiye min ban iya ci ba. Sai gashi sun turo min sakamakon binciken wai Amiratul tana dauke da ciwon ƙwaƙwalwa, Idan da ace wani ciwon ne ba zan damu ba amma kin san yadda cutar cerebral palsy yake kuwa? Kada ki yi fatan ko wanda bai san sallah Allah ya daura mishi wannan ciwon duk yadda xan gaya miki ba zaku fahimta ba, !" Yadda yake faɗar ciwon ban kawo masifar ta kai har haka ba sai da ya janyo wayarshi ya min browser din ciwon sai da na ji cikina ya tsirga, da sauri na sauka zuwa ban daki,na fito na zo na kara kwanciya a jikinshi, video yadda iyayen yaran suke cin wahala da dawainiyyar yaran ake nunawa har yadda ake fama da su. Wata mata a cikin iyayen yarinyar wata mai suna Katherina ta ce ban da ina son yarinyata, da babu dalilin da zai saka na cigaba da kula da ita ba tare da nayi ƙoƙarin kashe ta ba, domin azabar rayuwa, na gaji da har ta kai ina jin da zan samu inda xan ajiyeta na huta to da nayi tun tana wata shida da al'amar ciwon ya bayyana, amma nayi hakuri na sakawa raina dangana, haka yana nufin dole nayi faffutuka don ta rayu!.
Ajiye wayar yayi yana matse hannuna, na yi lumo a kirjinshi, ina wasa da gashin kirjinsa. "Hmm!" Na sauke ajiyar zuciya mai zafi tare da ƙarfi na ce mishi. "Ita uwar tasan da ciwon?" "An gaya mata na kuma bata magani da suka rubuta da allurai." Kai kaina nayi tsakiyar kirjinshi ina dan buga bayansa har barci ya dauke mu, karfe daya saura muka farka a gurguje muka ci abinci muka wuce massalaci sallah azhar, muna yin sallah muna dawo gida abinci muka ci domin wanda muka sha tea ne sai bread, muna dawowa muka tsaya muka ci abinci sannan muka dawo muka kwanta tare da bude wani shafin kauna. Da ya mantar damu kome, sannan muka yi wanka wurin karfe uku muka nufi massalaci, cikin wani irin shauki. Kwanan mu biyar muka dawo Makka anan muka rubbayan ibadarmu da gayawa Allah kukanmu, ibada sosai muke.
**
Ijlal
Matar tana zaune a gabansu, gashin kanta tayi wani irin cunko da shi yanayinta kamar Fulani kamar irin bakin hauro ko ace bororoji, a'a wannan sadaka yalla ce domin yanayinsu da Fulani ko bororoji da rata, amma yanayin shigarsu da bororoji da Fulani a bayyane take. Bude kwalbar turaren bintu sudan tayi ta shanye ta wani girgiza jikinta kamar kaza mai kwanci. Ta wani kalli Ijlal ta buga kanta da hannunta sosai sannan ta ce mata. "Mijinki ya dauki kishiyarki sun tafi kasa mai tsarki, yarinyar tana da Allah a tare da ita. Ko zaki ci nasara akanta sai ta baya amma ta gaba baki isa ba." Ta fada tana zare idanu kafin tayi wani gyatsa ta ce mata. "Kai ina ba sa'a ba zaki iya ba sai dai ki fadi abinda za ayi iya miki a yanzu amma yarinyar tana tare da Allah!"
"Ni kada ta haihu da shi ne!" Watsa wuri matar tayi ta d'ago kai tana kallon Ijlal ta fashe da dariya tana nuna ta da yatsa. "Haihuwa fa zata yi, sai tayi haihuwa sama da yadda Bera ko karnuka suke haihuwa. Kin san yadda karnuka ko beraye suke haihuwa?" Dafe kirji Hajiya Mardiya tayi tana faɗin. "Kina nufin haihuwa zata yi kamar masifa!"
"Haka na faɗa! Zata haihuwa fa!" Yadda ta fada da karfi tana kallon Ijlal. Wacce ta gigice tana faɗin. "Yanzu mai zan yi?" Dariya tayi tana faɗin. "Wannan layar a samu cikin bishiyar roba,a sare a cusa wannan kuma a barbad'e shi a inda take zama zaki sha mamaki!" "Ai ba shiga wurin juna suke ba." "Ni kuma bani da hanyar da zan muku aikin nan!" Daga nan ta mike tana faɗin. "Kuna da kwanaki talatin da tara aikin ya fara idan kuka sake aikin ya fara ba tare da anyi aikin ba zaku rasa damar ku, shi wannan toshe bakin mahaifar zai yi ba shi zai hana ta haihu ba, amma kafin nan ta rasa nutsuwa, wannan kuma yadda take juya mijinki haka itama zaki juyashi domin duk wani nutsuwarshi zai dawo kanki, amma ki sani yar malamai ce gaba da baya sannan Matsafa da suka fi ni iko da karfin tuwo sun kasa mata kome,, amma Iyayenta ba zasu zuba idanu su ganta cikin azaba da tashin hankali ba, da, sai ki yi amfani da wannan duk wnada ya zo gaishe ta ki tabbatar kina wurin ki saka a bakinki, ki danne da harshenki, yadda suka mata sannu babu me tab'a cewa ta nime mi maganin karya sihiri hatta kanta. Amma ki sani yarinyar da Mijinki aiki ba zaki tab'a iya raba su ba, soyayyarsu daddadiya ce mai dogon tarihi da dogon ƙarni sannan tubalin masarautar da jinin gidan Rantsatsiyar ce ba zaki taba yin aiki ya shiga cikin masarautar ya kai kwana arba'in ba tare da ya karye ba masarautar kafaffiya ce babu aikin da yake zama kome me, kin tab'a jin sarakunan masarautar sun musu ta hanyar tsafi? A'a ina kashe su ake da guba ba dai tsafi ba shi yasa ba a iya musu yarki kuwa ƙaddarr ce zaki fuskanta da kanku da zuciyaki idan har kika hakura ki huta da wani damuwa idan kuma kika ce ba zaki hakura ba kishi a tsakanin zubda jini zaki yi lallai aiki ba gabaki kamar na bakar inuwar bayanki, ki sani akwai bakar Inuwa a bayanki kada ki rasa damar da zata wuce baki amfana daga gare ta ba, Hajiya bani kudin aikina dubu dari biyu da hamsin!" Ba musu ta bata sannan ta juya zata tafi ta ce mata. "Idan kin shirya haduwa da bakar Inuwa, zan zo gare ki daga lokacin da kika ji a ranki kina so ki ambaci suna Angaza zan zo!" Sannan ta fita tana dariya, "Hajiya ya zan yi da wannan abin?" Ta nuna mata kayan murmushi tayi ta ce mata. "Zamu yi tafiya, muje a saka a can shi kuma wannan Iram zaki nima ku yi magana da ita, zata fiki sanin yadda zai shiga cikin gidan."
Haka kuwa ta kira Iram suka sha hira kafin ta roke ta bukatarta da take da shi, shiru tayi kafin ta ce mata. "Zan yi amma sai kin amince zamu kebe?" "Iram nayi mishi alƙawarin na daina don Allah kada ki saka ya gano muna tare yi!" "Tunda ba zaki amince ba shi kenan ki nime mai miki aikin nan, domin ba zan yi aiki kyauta ba!" Tana ƙoƙarin kashe wayar ta ce mata. " Ina zamu haɗu?"
"A inda muka saba haduwa mana!" Daga haka ta katse wayar don ma Hajiya Mardiya ta bar dakin ajiyar zuciya ta sauke, tana nazarin yadda zasu hadu da Iram. don haka ta shirya haduwarsu akan zata kai yarinyar riga-kafi.
A can suka hadu suka watse san ransu, sannan ta bawa Iram sakon, amsa Iram tayi tana faɗin. "Yar uwata ce fa? Nasan da ni ce a matsayinta ba zata yi tunanin min haka ba, amma kuma yadda Abba ya ke nuna ya fi sonta yake min ciwo ko ba kome itama ta ji yadda kowa yake ji." Ta fada tana jefawa a jakarta.
" Na zata zaki ce ba zaki yi bane bayan sadaukar miki da kome da nayi!" Inji Ijlal, tana shafa bayan Iram. "Eh to da wannan don wannan harkan bariki ne sai a hankali!" Ta fada tana murmushi kafin ta wuce ban daki tayi wanka sannan ta fito tana mata dariya ta ce mata. "Mijin da kike hakilo a kai bai damu da ke ba, which mean ya ajiye ki ne don kina haifa mishi Yara kyawawa irin gidansu!" Ta shafa kan Baby Amirah. Buge hannunta tayi tana faɗin. "Don't dare touch my angel da wannan kazamin hannunki! Yarinyata innocent soul ce!" Gyara tsayuwa Iram tayi tana faɗin. "Oh laala;" taba wani kyafta idanu ta ce mata. "Kika ce me? Kada kazamin hannuna ya tab'a yarki.!" Dariya tayi ta dauki yar tana juyata. "Iram ajiye min Y'ata!" Wani rike kafar yarinyar Iram tayi tana faɗin. "Kamar haka na sake ta!" Ta fada tana murmushin mugunta. Zubewa kasa Ijlal tayi ta fashe da kuka. "Am sorry nayi kuskure, don Allah kada ki min haka ita ɗaya ce makamin da nake amfani da Salmanu Faris!" Murmushin gefen baki tayi ya gyara yarinyar da ta fara kuka, ta kwantar da ita ta durkusa gaban Uwar.