Showing 45001 words to 48000 words out of 304445 words

Chapter 16 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

40

kyakkyawar fata da nasara a rayuwarsu. Bayan lokacin da Mai Martaba sarki Shehu Yayari, ya dauka yana jinya ya rasu daren Alhamis wayewan juma'a aka yi mishi jana'iza aka kai shi gidansa na gaskiya. A lokacin Kilishin wancan lokacin duk da ta tsufa ta fara maganar mulki ya dawo hannun jikanta Rilwanu, abin bai tsaya haka ba, sai da ta shiga ta fita ta sayi rabin dattawan fadan, Rilwanu abinda ya sa ba'a sonshi ba ma shi ba mahaifinsa Abubakar Yayari, mutumin banza ne domin a lokacin mahaifinsu an sha kawo karanshi ya haɗa kai anyi zamba cikin aminci, an cutar da wani. Ga niman mata kamar bunsuru domin idan ya ga mace sai ya bita ya latsata. Sai gashi dansa wanda kowa yasan ya zama wani iri, a lokacin Abba Yayari da Hamud sun gaya mata gaskiya su ba zasu goyi bayan Rilwanu ba domin kowa ya san yadda yake rashin ji, don haka suna nimawa al'umma sauki ne, ba tashin hankali ba. Koda tayi musu barazana sai suka mata dariya tare da cewa ta kare jikanta kada ta damu kanta Allah ya tsare musu rayuwarsu da imaninsu. Wannan yasa ta saka su a matsayin makiyanta.

Saddam da Junaid sune suka fara, bada dukiyarsu domin a zaɓi Attahiru Shehu Yayari, kuma suka bi talakawa da alkhairi su tafi fada su ce sun yi muba'aya, duk da haka kuskure ne amma kuma hakan da suka yi don zaban mutumin kirki ba kuskure ba ne, ganin talakawa sun goyi bayan Attahiru Shehu Yayari, sai Kilishi tayi step down akan kudirinta domin abun ya samo asali daga lokacin da talakawa suka zabi abinda suke so mutum yace bai ji ba be gani ba karshe mutuwa ce, haka yasa suka hakura, a lokacin Alhaji Nafi'u yayi na shi ƙoƙarinsa.

Nad'a Attahiru Shehu Yayari ya kawo wani irin cigaba, na farko kara dankon zumunci a tsakaninsu, a lokacin ba karamin dad'i kowa ya ji ba, sai ya kasance duk bayan shekaru goma suman meeting, shekarun gomar farko na kasuwanci ne, sun kulla yarjejeniyar kasuwanci da hako Ma'adinai, shekarun goma na biyu sun kara karfafa kansu sananna a lokacin aka kulla yarjejeniyar aure tsakanin Saddam da Nafi'u, Junaid da Mai Martaba, a lokacin anyi nasara an ci gaba, sai dai kwatsam Alhaji Saddam ya fara samun matsala da kasuwancinsa, bai yi kasa a gwiwa ba ya same Nafi'u, ai kuwa jikinsa na rawa ya taimaka mishi.

Bari na fito muku da asalin halayen abokai hudun nan,
*Alhaji Nafi'u* mutum ne mai izza, bai da kirki akan talakawa da dukiyarshi domin bai san asara ba, kaf duniya bayan abokansa bai yarda da kowa ba. Sannan mutum ne me daukar ƙananan magana duk abinda za a gaya mishi tow zai dauka babu ruwansa da gaskiya ko karya ne, yana da wani irin kauna da kudi domin yadda yake son kuɗi ya munana. Yana da wani irin hali na bin mata da Yara ƙanana amma mata. Da wannan suke yawan samun saɓa da abokansa.

*Alhaji Saddam* wani irin mutum ne mai tsananin hakuri da kawaici, mutum ne da yake da budadden hannu, yana da kirki mutum ne da duk yadda zaka fasalta shi sai ya kure tunaninka domin kirkinsa da adalcinsa. Bai damu da ace ko nace ba, saboda bai cika daukar maganar, yadda yake da wannan halin abokan suke ta bashi shawarar ya tsaya takara za a zame shi tunda ya bawa matasa aiki mai yawan gaske.

*Malma Junaid* idan aka zo fagen ilimi da abinda ya shafi rayuwar tow a rufe domin mutum ne da ya kere sa'i'insa haka yasa wasu malaman suke zaginsa da cin zarafinsa, Malam Junaid ba mabukaci bane domin yana tsaye akan kafarshi, ba iya kamfanonin da suke da shi na hadin gwiwa ba, shi din manomi ne da yake noma, sannan mutum ne da yake da wani irin juriya da hakuri sannan yana daga cikin mutane da suka tsaya a gefen Mai Martaba sarki Attahiru Shehu Yayari.

*Mai martaba Attahiru Shehu* Idan aka ce sadaukarwa ce tow wannan shine makura ya bada kome domin abokansa kuma ya toshe kunnensa akan abokansa, haka yasa aka rasa hanyar da za a karya shi. Sun buga sun buga sun rasa sai ya zamana ana tabin abokanshi ana ƙoƙarin a ga sun juya mishi baya yadda za samu matsala amma fir suka ki.

Halayen abokai hudu kenan.
Alhaji Nafi'u ya bawa Alhaji Saddam basu ba tare da an sani ba, da yake Allah gwanin hikima ne, sannan idan yana son fitar da wani abu daga cikin nagartattun mutane sai aka samu matsala dukiyar da Saddam ya amsa ya b'ata, abun da ya kawo asalin tashin hankalin farko, a cikin shekarun goman tsakiya, takanas Alhaji Saddam ya je gidan Alhaji Nafi'u ya gaya mishi ya kuma bashi hakuri domin ya kwashe kusan rabi da kwata na dukiyarshi ya zuba, da farko Alhaji Nafi'u ya nuna babu kome domin suna yiwa juna wannan Adalcin da alfarma idan a waje ma ya ciyo bashin shi zai iya biya mishi daga baya su warware, amma sai me? Bayan sun gama magana babu wanda ya kawo maganar bata kare ba, sai da aka kwana biyu Alhaji Nafi'u ya fara addabar Alhaji Saddam fitina rigima da tashin hankali, haka yasa Alhaji Saddam ya tafi har gidan Sarki ya gaya mishi abinda yake faruwa shi kuma ya kira Malam Junaid suka yi magana aka taru a yi sulhu Alhaji Nafi'u yaki, dole Malam Junaid da Mai Martaba suka biya kudin nan a lokacin ba tare da sun ja tashin hankali ba, kuma basu nuna ransu ya b'aci ba.

Bayan an yi haka ko shekara daya ba ayi ba sai aka samu bullowar wata kungiyar asiri Black cat, kungiyar asiri ce sai suka fara niman Alhaji Nafi'u, yadda suka kawata mishi sai ya amince ya fara niman Alhaji Saddam, ya ce ba zai shiga ba iya wanda yake da shi ya ishe shi. Wani abu da mutum zai fahimta duk da haka Alhaji Saddam bai gayawa kowa ba, sai Ya tuntubi Mai Martaba, anan aka fara jin kansu yayi mishi tas domin suna da hanyoyin samun kuɗi ba sai da kungiyar asiri ba, sannan ya ce maza maza a kori mutanen a garin, sai dai ko da aka je koransu sai abin ya kawo wani irin tashin hankali wanda ya janyo aka kashe wasu daga cikinsu, su ma suka kashe jami'an tsaro da dogarai, wannan dalilin ya kara haifar da wani irin tashin hankali amma Allah ya kawo saukin lamarin.

Bayan shekaru uku da faruwan lamarin, Salmanu Faris da su Abid da Uwas suka shiga daji irin dabi'a na Yara, harbo tsuntsaye suka shiga wanann daji, tunda suka shiga dajin Salmanu Faris ya nuna musu dajin is very strange, suka ce shiga, wani abu da Allah ya taimaka shine Malam Junaid yana kafe Yaransu, musamman Salmanu Faris da yake gidan sarauta duk da ya girmewa su Abid haka yasa suka shiga dajin, wannan dajin ana kiransa dajin fatake sannan dajin kamar ya mutu babu kome na tsuntsaye a cikinsa. Jin haka yasa shi ce musu. "Mu bar wurin nan akwai yanayi me ban tsoro." Juyawar da zasu yi suka gamu da katon muzuru wanda ya kai girman dan akuya, burin muzurun nan yayi kansu, shi kuma ya dauki danko yayi ta harbin muzurun nan, karshe sai ga Salmanu Faris da dambe da muzurun wanda yayi sanadin jiwa muzurun ciwo sosai, domin shi muzurun idan ya tab'a Salmanu Faris ji yake kamar wuta yake tab'awa, sanadin haka ya janyo jiki muzurun ya kone sosai.


Dakyar suka fita a dajin, duk wannan abin da ya faru a kan idanun shugaban ƙungiyar Black cat, yasa aka dauko mishi muzurun yayi jinyata, amma ba zata tab'a warkewa ba, sai an nimo jinin daya daga cikin Yaran abokai hudu mata.
Bayan an yi wannan ko sati daya ba ayi ba sai b'atar Salmanu Faris wanda aka nime shi aka rasa.
Sace Salmanu Faris ya janyo aka zargi wancan kungiyar asirin ce sai aka kama shugaban kungiyar aka rufe shi, amma idan akwai bakin cikin da ya kai wannan babu wanda yafi kowa ji kamar mai martaba,. kawai dariya yaƙe amma yaji ciwo don.sun dauki kwanaki uku suna cewa ya basu damar kafa ƙungiyar idan yana son danshi amma yaki haka suka salwantar da rayuwarshi.

***
A hankali kome yake tafiya kamar bai faru ba, wata rana Litinin sai ga Kayan Alhaji Saddam ya dawo haka yasa shi kara yiwa Ubangiji godiya ya kuma ta sadaka da kyauta domin a lokacin har hajji da Umara ya biya, cikin wannan yanayin Alhaji Saddam ya tsunduma siyasa kamar babu wani bayanshi tow yana da goyan bayan abokai biyu haka yasa koda ya samu damar sanata aka kuma zabe shi, ya shekara hudu ya kara wani shekaru hudu sai ya fito takarar gwamna.

A lokacin ne aka kama Khalifa da laifin yiwa wata Yarinya fyade wanda ya janyo ta rasu, duk da haka abokai hudu basu yarda abokinsu ba, sun tsaya mishi domin a lokacin duk da yana da dukiya bai da daraja a idanun jama'a, saboda abinda yayiwa Abokinsa abin ya shiga lungu da sako, an sassanta lamarin a cikin gida aka biya diyyar yarinyar, kafin daga baya kuma Alhaji Saddam ya janye maganar Auren Ikram da Khalifa, hauka ce kawai Alhaji Nafi'u bai yi, haka yayi ta bin abokan nan amma suka ce y'a ta Saddam ce kuma babu me mishi dole,.kuma hujjar da ya kawo ita ce gaskiya. Yace yarinyar kamar Ikram ba zata iya ji da rayuwar Khalifa ba, koda kuwa an ce din zata iya ba zata iya ba domin Khalifa ba zai biyo ta dad'i ba. Wannan yasa yake ganin kawai ya nimawa dansa abokiyar rayuwa, don yana ganin yadda Khalifa ya lalace. Sannan idan wani abu ne Malam Junaid ya bashi Iram tunda da Alhaji Nafi'u da Uwar Iram Turai uwa daya Uba daya ne, koda Turai ta ji tsalle tai ta ce ba dai iram ba itama tana da buri akan yarta.

Haka ayi fara hidimar zabe, ana kamfen Alhaji Nafi'u shima ya tsaya anan ne aka fara wani irin tashin.....
Mamoul all colors are back in stock. Mamoul turaren turara kaya. Ga kamshi ga kama kaya da gida. Available in;
MAMAOUL MADINA,
MAMAOUL MARYAM,
MAMOUL BADAR &
MAMAOUL SABAYA. Each one 3500

*New Drop!*
*Nassem Oil – 100ml*
Rich, elegant & long-lasting.
This premium fragrance oil is everything your collection needs — and it’s only *₦8,000!*

*Luxury in a bottle.*
| Own Your Scent, Own the Room*

*Mosuf 50ml Body Spray*
Smooth. Fresh. Long-lasting.
Only *₦5000!*
✨💥
Smell amazing, every single day.
*DM to order!*

*Storm for Him & Her – ₦4,500* each
Fresh, fierce, and made to turn heads.
Whether it’s *Storm for Him* or *Storm for Her*, you’re getting bold confidence in a bottle — just *₦4,500!*

A perfect 50ml to carry your essence wherever you go. Subtle. Powerful. Unforgettable.
Now available: ₦2,300 per piece | ₦27,600 per dozen.
Available Just DM
08130269641

Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book.


*Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu ƙayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:*


*MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya haɗa da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.*

*AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen ɗin Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen*

*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*

*POSTING*
*Ɗaya: 500*
*Biyu: 1000*
*Uku: 1500*

*DOCUMENT (da zaran an gama posting zai koma)*
*Ɗaya: 1k*
*Biyu: 2k*
*Uku: 3k*

domin tura shaidar biya ko Ƙarin bayani, ku tuntuɓi:
*08130269641*
Ko
*08137311900*
Ko kuma
*09063467258*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: ROYAL POLITICS 🔥
_An yanka ta tashi_
Ramlat A Manga
Mai_Dambu
TOP-NOTCH SEASON 4
Sadaukarwa ga Auntyna RUKAYYA GOMBE 🥰🤩😍

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HYpizDjKAkJB4QClSeLTvw

Dakata hajia💃💃💃💃💃 kin Dade kina Neman inda Zaki sai amintattun jaka, da takalma, sarkoki,masu kyau da quality cikin farashi Mai sauki❓
Ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,wannan gidan na RUMIEE UNIQUE BAG'S GALLARY na budeshi ne saboda na Baku damar siyan jaka,da takalma na Yara Dana manya masu kyau da quality da Kuma saukin kudi cikin aminci daga wajena.masu siyan daya da masu sari duk Muna mataba daku
Muna Kano Muna Tura kaya kowanne state da makotan Nigeria cikin yardar Allah

Last Free page

16

Alhaji Nafi'u ya je har Fada tare da niman goyan bayan Attahiru Shehu Yayari akan idan ya bashi goyan baya zai kara mishi karfi amma Attahiru ya tsaya akan ra'ayinsa tare da gaya mishi gaskiya ba za a zab'e shi ba, haka ya fita a cikin kunci da bakin ciki, sannan aka wayi gari an sauya dan takara daga shi zuwa kan Musharraf.
Haka ya tab'a zuciyar Alhaji Nafi'u, domin har wurin Malam Junaid ya je domin ya tsaya mishi, shima ya nuna ba zai iya ba, wannan lamarin yasa shi jin wani irin kunci da bakin ciki ya kuma jefa zuciyarshi cikin zargi mai mugun nufi,.kawai sai da ya rage kwana biyar zabe, a wani dare Alhaji Saddam da Malam Junaid sun hadu a fada suna tattaunawa, bayan sun gama a lokacin Mai Martaba ya gaya musu bayan zab'e zai tafi USA an gaya mishi an ga Salmanun Faris a can ne a matsayin likita suka goya mishi ba, har shi Alhaji Saddam yake cewa ya tafi ya bar zaɓen, ya ce A'a sai ya ga abinda zai faru tukun idan ya tafi zai bar baya da kura. Haka ya hakura bayansun gama suka watse, kafin Malam Junaid ya isa gida aka turo mishi sakon. *Ka kula da kanka wanda kuke dominshi na cikin tarkonmu* sai da motar ta kusan kwacewa a hannunsa koda ya isa gida, a daren Alhaji Saddam ya kira Malam Junaid duk da a lokacin kusan sha biyu saura ne haka ya je ya same shi a bakin hanya, fitowa suka yi suka yi ta hira kamar ba dazun suka rabu, a har kusan karfe daya saura kafin suka yi sallama, sun rabu dai kowa ya koma gida, sai dai wurin karfe shida na safe aka kira shi Alhaji Saddam ya rasu, kuma ba a ga al'amar wani abu ba, amma kuma tabbas an ce ya shigo gidansa hankali tashe, daga haka yayi ta faɗin. "Junaid Junaid Kai Junaid Junaid dai Junaidu nawa a'a ku bincika" kafin ya cika da kalmar da duk wani muslmin kwarai yake fatan cikawa da ita, da wanann aka daura zargin mutuwarsa akan Malam Junaid,kuma koda aka duba wayarshi last call dinsa Malam Junaid ne, haka yasa aka fara bincike dakyar Allah ya fitar da Malam Junaid.

Karshe zaben da aka yi sai mataimakinsa ne yayi nasara, ya kuma tabbatar da ya cika duk wani alƙawarin da Saddam din ya ɗauka, ko shi Alhaji Nafi'u ba zai boye ba ya ji mutuwar Saddam, haka ya sake busar mishi da zuciya, bayan Zabe gwamnatin tayi adalci inda ta bawa Uwais dama dayawa wanda har saka shi aka a cikin manyan lauyiyon jahar, sannan mai martaba da kanshi ya kai musu ziyara ya kuma yi kokarin fahimtar da su Junaid ba zai tab'a aikata wani abu ba.

Haka lokaci yayi ta tafiya, Mai Martaba ya tafi har USA, ya ga dansa ya kuma amince Jininsa ne amma abinda ya lura Salmanun baya son magana gida domin a fuskarshi kamar akwai labari amma bai bashi damar jin ta bakinsa ba, a lokacin da ya ga Nady a matsayin matar shi yayi bakin ciki da damuwa amma haka ya gaya mishi baya son aurenshi da Nady amma zai barshi da ita amma ya zaba mishi, wannan alƙawarin da ya mishi ya dawo gida, sannan ya saka Salmanun sai da ya zo sau biyu ya ga gida.
***
Bayan shekaru hudu wanda yayi daidai da shigarsu sabon kakar zabe, wannan lokacin har Fada Alhaji Nafi'u ya je gaban Attahiru yana rokonsa a gaban jama'a, amma ya juya mishi kai domin suna zarginsa da abubuwa dayawa amma sun ki nuna kishi. Kallon Attahiru Nafi'u yayi ya idanunsa cike da kwalla ya ce mishi. "Ni ban maka kome ba, amma ka tsane ni kasa Junaid ya tsane ni, na rantse da Allah yadda kuka min sai na muku? Kamar yadda kake murnan ka samo danka zai dawo cikin Zanzabira haka zan saka mishi kahon zuga Attahiru sai ka roki Allah ya kashe ka da ukubar da xan gana maka, shi kuma Junaid zan barshi a raye domin ya girbi abinda kuka min ka kuka da kanka da abinda kake ci domin nasan aikin gama ya gama."
Hawayen bakin ciki ne ya zubowa Attahiru ba mutuwar ba ce damuwarsa a'a alakarsu da ta lalace take ya tono baya da yadda suka gina kansu. Hawaye na zuba mishi.
*2004*
Ƙarƙashin sassanyar inuwar bishiyar mangoro da yake yalwacce a gidan gonar Sarki Attahiru Shehu Yayari, kishingiɗe yake yana hutawa tare da wasu daga cikin manyan hadimansa. Musamman Salama wanda kowa yasan amintaccen hadimin sarki ne, domin ana yawan faɗin. Kafin ka ga Attahiru II fara isar da sakonka ga salama. Wayar tafi da gidanka da yake aljuhun Salama ce tayi ƙara, ya kalli Mai Martaba cikin kulawa da niman izinin. Murmushi yayi cikin dattaku irinta manyan mutane ya ce mishi. "Har sau yaushe zaka fahimci girmanka Abdulfatihi?" Kasa da kai yayi cikin girmamawa ya ce mishi. "Lafiya toron giwa, lafiya Mazaje, Giwa mai tafiyar kasaita. Na gaida Angon Mai Babbar daki, Mijin kilishi, Mai dakin mai daki wato Fulani karama, Babba dan babba namiji Babban Salmanun Faris, Garnakaki Garko na Turaki! Gaba Salama baya salama mijin Maryamu Uban Maryam, Uban Fadimah, Angon Balkisu. Miji ga Khadija, Baban kubra, na gaida Mijin Zainab Abu Fulani karama baban AbdulHafiz!." Cikin murmushin da yalwatu a fuskarshi ya ce mishi. "Salama dauki wayarka!" "Na gode Salama yana godiya!" Ya mike da sauri ya matsa kaɗan ya amsa. "Alhamdulillahi, mai martaba yana nan lafiya, muna gidan gonarshi. Wanda yake wajen gari." Ya fada


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login