Showing 123001 words to 126000 words out of 304445 words
dako nayi yaron shago, kafin na fada hannun wani bawan Allah duk da ba musulmi ba ne, na taimake shi a lokacin da yake gab da mutuwa, na taimaka mishi lokacin ina da shekaru goma sha bakwai a duniya, shi din attajiri ne dan kasar Ethiopia sai dai yana auren wata baturiya wanda matar ta nime rayuwarshi tunda Allah bai bashi damar haihuwa ba, shine ta tura mutane su kashe shi na taimaka mishi lokacin da suka wurga shi cikin ruwa, Na tsamo shi na kai shi asibiti. Haka na zauna da shi har ya farka don asibitin sun ce ba zan tafi ba sai ya farka. Lokacin da ya farka yaji ni na taimaka mishi, sai ya fashe da kuka, yayi ta min godiya yace ma ni ne Almasihun da aka ce zai yi ceto don na dawo da shi bayan ya mutu." Murmushi yayi daga nan ya cigaba da cewa. "Na rayu amma rayuwata ji nake kamar ana farautarta, mutumin nan ya tambaye ni amma nace bani da kowa haka yasa yayi Adopted dina a wurinsa, ya kuma tsaya min na koma makaranta, ina da baiwa ilimi don haka na raba kaina ina zuwa academy class, na koma makarantar sakandare domin takarduna kasancewar nan kasar turawa suna da goyan kayi karatu. Sannan na gama a cikin shekaru biyu sai na tafi Jami'ar Harved da taimakon Uban rokona, na samu gurbin karatu. Haka na rayu ina mai karatu ba dare ba rana amma bana barci, karatu da niman ilimi yasani na zama kamar zararre, rashin barcina sai da ya janyo aka dakatar da ni daga karatu, a lokacin kuma Uban rikona ya rasu, abin sai ya tab'a sosai. Baki bana son shiga mutane bana son mu'amala da kowa, sannan kaf dukiyarshi sunana ne zan gaje shi, haka yasa na sake shiga wani irin kunci da damuwa, dakyar na koma karanta, ya zamana a rayuwata ina barci na tsawon awa uku cif shima Makarantar ce ta saka min doka. Shi yasa na mai da hankali na kammala degree na farko ban ji sha'awar aiki ba sai da na hada degree na biyu, sannan na fara aiki. Allah ya bani kome amma ya hanani nutsuwa. Ikhlas haduwata da Nady da aurenta yana cikin ƙaddarata, domin Nady ita ce ta fara koya min ilimin zaman aure. A hankali na zama likitan da babu irinsa a cikin Amurka a bangaren ƙwaƙwalwa, ganin haka na koma Phd yadda na kara sanin aikina. Lokacin ina phd din na fara aikin cire ƙarin ƙwaƙwalwa, daga nan na samu damar zama zaɓaɓɓen likitan da yafi kowa daukar kasada a aikin dashen ƙwaƙwalwa." Leka fuskata yayi ya ga idanuna biyu ina kallonshi yana kallona,, tashi nayi daga cinyarsa. Na zauna tare da rungume gwiwata da hannuna. "Na cigaba da aikina, kafin na hadu da Walid wanda shi a lokacin yazo wani aiki Sweden muka hadu ni naje bikin ƙwaƙwalwa ta duniya. Anan muka haɗu." "Taya kuka hadu da Faruq." "Abokin gwagwarmaya kenan, mun hadu da shi a wani gidan Abinci yana aikin karban oda, sai na yarda Wallet dina, tsawon kwana uku yana nima na, karshe a sanadin nima na ya aka kore shi a wurin aikinsa. Ya zo ya fara aiki duk da haka ana koranshi wata rana sai aka kawo min shi yayi hatsari ana kawo min shi na fahimci ta bugu akanshi, shine na mishi aiki na cire dattin. Daga nan da ya farka yake gaya min daga Nijeriya yake Iyayenshi yan Maiduguri ne, rikicin bokon haram ya sa a ka shigo da shi kasar Amurka, da na tambaye shi takardunsa ya kawo, na tambaye shi me yake so. Abu na farko da ya fara shine bani Wallet dina, daga nan ya ce rayuwarshi domin ni zai yi ta domin ni na dawo da shi bayan yana gab da mutuwa. Daga nan na samu dan uwa sannan na tura shi makarantar horan da yan sanda, tare da dabarun kare kai Yaron nan mahaukaci ne koda ya gama aka bashi aiki amma yaki yi, domin ya zaɓi ya zauna a tare da ni. Ya dauki kasada dayawa a kaina, sai biyu ina bude kan Faruq." Murmushi yayi ya ci gaba da cewa. "Don haka na zabi zama da shi a matsayin nawa, duk da ban san abinda yake ran kowa ba amma Faruq nawa ne ni daya daya na kuma ba zan tab'a barin wani ya cutar da shi ba. Gara na rasa kome akan na rashi."
"Tow Malam labarin yayi amma me yasa ka dawo?" "Mai martaba ya dawo dani, amma ban dawo ba sai da Baba Mamman da Malam Abba Junaidu ya tafi ya dawo da ni, taya mutum irinsa zai dawo da ni na ce ba zan dawo ba, ai na cika mara kunya da rashin mutunci wai fa tun kafin B'atana suka hada aurenmu, ni kuma nayi dacen kwaila mara kome a kirji."
"Ya labarin mutanen da suka dauke ka?" "Ke ba Fansa ya dawo da ni gida ba, zaman lafiya ya dawo da ni gida, gara na zauna lafiya amma ita yarinyar dole na nimo ta," ya fada yana mikewa. Ban daki na wuce na kama ruwa nayi alola na zo na kwanta, shima fita yayi don lokacin karfe daya saura. Da sauri na tashi na rufe kofana na bar key ɗin, yana zuwa naji yadda ya murda amma bai bude ba, ya juya abinsa, da asuba da wuri na tashi na mana dumame sannan na shiga rage aikina. Bayan sallah asuba da na kwanta barci karfe goma mai kitso ta zo ta min sai da na tsafe na wanke kan lokacin har su Sailuba da Wildat sun gama wanke wanke, kwanciya suka yi, muna hira har muka gama kitson ta min lalle tana cikin yi ya shigo wurin karfe sha biyu saura. Kallona yayi lokacin ana zanen lallen ya ce min. "Kada a cika yayi yawa kaɗan yayi!" Ya ajiye min kudi a gefena ya fita, "Thanks!" Yana fita ya nufi bangaren Nady itama ya bata, sannan ya bawa Ijlal itama, sannan ya fita. Ana gama min lalle wurin daya, wurin uku saura kwata na cire na shiga nayi wanka da alola na biya mai kitso kuɗi, ina sallah muka fada kitchen, kosai aka kai nika aka dawo, sannan aka buga na fere dankali turawa, kafin na daura abincin sadaka, Jollop din shinkafa da ya sha kayan kamshi domin tun kafin a fara min lalle ma basu kayan aikinsu suka cigaba da aiki in zuwa nayi paboil na shinkafar na zuba. Na cigaba da aikin gida, Shinkafar na karasa na kawo kosai aka saka kai da soyayyen nama, kunun da aka yi tun karfe uku aka zuba a gora sannan suka shiga park din abincin a takeaway. Ana gamawa Faruq yana zuwa wurin karfe biyar na da rabi ya fita dasu yana faɗin. "Madam an gama da wuri!" Na ce "eh wallahi!" Na faɗa ina tattara kayan wurin su kuma suka wanke tukwanan, sannan muka shigo cikin gidan muka sayo dankali hausa da guntun kullin kosai, nayi aka kaiwa Mai Babbar daki. Na ce musu. "Daga yau mun gama sai nan da kwana hudu zaku dawo!" "Wayyo Gimbiyar Zanzabira Allah zamu yi kewar girkin mai dadi haka Mai Babbar daki ma zata yi kewar girkin domin shi take fara ci kafin taci na gida." Murmushi nayi nace musu . "Kada ku damu, kuna zuwa amsar na sadaka Nady zata saka muku haka ma Ijlal!" Ji na kawai suka yi amma ransu bai basu , su zo din ba.
Bayan tafiyarsu na zauna gyara ko ina, haka baki suka zo suka cinye abincin. Sai na fahimci wani abu ni da Nady zai kawo mutane su ci a daɗin rai domin ita Matar da take girkin gwana ce. A daren da aka ci kowa ya ji dadi, amma Ijlal sai da ta ce girkin ba dad'i, tun a daren take niman fitina babu wanda ya kulata. Washi gari azumi ya kama hudu ita ce da girki, tun safe da aka yi baki masu taya ta, aikin suka shigo ake shewa koda yake ina dakina, haka Nady ta fita nata harkan bata.
*Account Details:*
*08130269641"
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500N
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 40
Bana ce nasan mai ya faru ba, ashe itama har da Lalle aka yi karfe uku na fito na nufi kitchen, yarinyar da na bala'in rena tsayuwar ta ce zan ci girkinta. Haka kuwa na shiga na fere doya na saya sannan nayi kifi banda, na wanke na zuba a firji shima. Ganin haka na dauko na yi miyata sai taliya da nayi na hada da miyar, sai kunun tsamiya da na dumama. Na kwashe zuwa dakina, ina gama na sake wanka wurin karfe biyar na yamma. Sai lokacin ake aikin bude baki. Ni shegiya inji dan daudu. Motsin Nady na ji a kitchen na fahimci itama ta barwa Mai gidan kayansa. A hankali na ji kamshin girkinta da alamu har da suya tayi. Wurin karfe shida ba a zo jera abinci ba, hmmm karshe sai ga shi an fara shigo da kulollin abinci, daya dai wani abincin turawa aka yi,.na yan gayu na biyu kuwa. Manya kular alfarma aka yi ta shigo mana dasu. Na sadaka kuwa an jibga taliya jollop ita kanta namar bata dahu ba, ga kunun da aka yi shi kamar talge kai mata suna ganin duniya. Haka aka kira Sarkin kofa ya zo ya kai na mai babbar daki. Ai tunda muka ga girki karfe biyar da rabi, na fahimci akwai matsala domin kuwa kowa ya sake ya zubawa cikinsa sai na lahira ya fishi gata. Haka aka gama bata yi wanka ba ta shigo dakin cin abincin. Kowacce tana dakinta har aka sha ruwa ita ta gama abinda zata yi sannan aka kira mu bayan ya shigo gidan. Zobon da tayi yayi bala'in jin yaji ga tsami. Tunda na shiga naji karnin kaza ya cika ko ina, na ce akwai case. Nan sai rawan jiki take tana zuwa mishi abincin. Kallon dankalin hausa da nadiya tayi yayi baki alamar ya sha wuta. "Prince ni fa ba zan ci wannan kazamin girkin ba, gara na tafi na ci wanda nayi!. Asha ruwa lafiya. "
Tsaki tayi tana faɗin. "Ke ki yi da kanki mana ina kema dauko yar aiki kika yi?" Ni dai tunda na zuba ruwan tea a cikin kofi naji yana hamami wani irin itacce na rike shi a hannuna na kasa sha. A hankali na ajiye kofin na ce mishi. "Am sorry nayi abincina." Na mike tare da bar musu wurin, kallonta yayi yana shan fruit wanda ya sha jagwale ba, bamu yarda da ita ba ne domin ranar da Nady ta fara bata zauna a dakin ba, muna jin ta shiga ta rufe can ta kara fita jin motsi yasa ta cewa waye, lokacin da ya zo tana dakin koda ya buga cewa tayi waye a firgice which mean ba zarginta muke ba amma bamu yarda da ita ba sam. Tunda mijinta ya sha kunun yaji shi kitikir kauri kamar an yi don yara yan wata shida. Ya ajiye kofin. Nan kuwa zuba mishi kome tana fadar abubuwan da ta haɗa a girkinta. Tunda ya kai farfesun kazar bakinshi ya ji wani amai ya zo mishi cire cokalin yayi ya ajiye yana kallonta. "Wani
irin girki ne haka?" Sake baki tayi tana kallonshi ya ce mata. "Look ba zan iya cin abincin nan ba nima min wani abu!" Ya fada yana barin dakin, bangaren Nady ya shiga ya tambayi abinci, ta ce iya cikinta ta dafa, ina tsaka da cin taliya na baza kifi a kai ga kunun tsamiya ina sha a hankali, saka hannu yayi ya dauke flat din gabana. Ya hau ci sai da ya cinye ya dauki kunun ya sha. Haka ya fita sallah tarawee.
Har karfe sha daya bai dawo ba, ashe Mai Babbar daki ta ci abincin ijlal yayi yaji shine ya tashi hankalin cikinta. Karshe ulcer da ciwon ciki nime kashe ta, shi ne ya kai ta Asibiti. Ina kwance ya buga min kofa bude idanun nayi da kyar na bude dakin. "Ko zaki min kunun madara, ban sani ba amma wata likita ta ce ayiwa Mai Babbar daki Please!" Yadda yayi maganar ya kashe min jiki, don haka na shiga kitchen ya zo ya zauna kusa da ni na fara aikin yana tambayata ko akwai abinda zai min na ce babu, shinkafa ce kuma na saka a pressure pot, na cigaba da aikina. Sai wurin karfe sha biyu da rabi na juyo ruwan shinkafar akan ruwan madaran da yake dafuwa, sannan na shiga juyawa ina gauraya shi kafin na fara zuba garin madara har ya kama jikinsa, dan tsimiya na dauko a firji zan zuba ya ce min. "Ulcer kada ki saka." Fuskata a sake nace mishi. "Ba mai yawa zan saka ba!" Na diga kuwa sai gashi yayi kauri me kyau. Na juye a wani flast karami. Na ce mishi. "Don Allah jira ni!" Na saka muka fita tare, ai kuwa mun samu ta farka an bata madara tana sha mai sanyi da yake dakin VIP ne babu abinda babu a dakin, ina mata sannu ta gyada min kai, zuba mata kunun yayi na amsa ina juyawa har ya yi sanyi na mika masa yaji, sannan ya zauna kusa da ita Abdullahi ya ce mana. "Amma girkin da kika ci bata Ikhlas ba ce ko?" Sai na ji gabana ya fadi. "Jiya ta fita yau kuma naci wahala!" Ta kurbi kunun madaran tana juya min kai. "Ulcer ta bai tab'a ta shi haka ba sai yau, haka ta sha rabin flast ɗin sannan muka dan yi hira kafin muka bar asibitin. Ni dai bakina Kanin kafana har muka iso gidan.
Kwanan mai babbar daki daya don har na kai mata abinci, ga Yaranta sun cika asibitin, irin kallon da suke min yasa na koma gefenta ina zuba mata jollop din cus-cus da yaji kifi da tattasai daya kawai nayi amfani sai kayan lambu, taci sosai anan na wuni sai dare na dawo ina dawowa na hada sauran abincin da na rage da kunun da na mata nayi dumame na ci, kusan ranar girkin Ijlal mun shan azaba na sadaka ma aka ce karshe mutane zubarwa suke. Karshe Almajirai marasa galihu suka karbi abincin. Washi gari Nady ta amsa kusan ma ba zo da abincin gidan ba don ina ganin a can aka yi don ba zata iya jure zaman leka ake akayi ba, abincin ba laifi na sadaka ma ya tafi yadda ya dace, don rashin mutunci sai ga Ijlal tazo cin abinci har da ci kamar hauka. Da yake sun kawo har da tuwon asuba, haka na amshi nawa ka kitchen, tun akan Ijlal muka dauki darasi, domin duk wanda ka ga yana dariya abin kuka bai kama shi bane.
Kafin na shiga girki na gama shirina tsaf, sannan na wanke gefen da aka surfa min na shiga tun a yammacin ranar na saka Faruq ya kaiwa Sailuba aka niko min ita da ruwanta da na shiga shan ruwa gidan Mai Babbar daki na dauko, naso na saka hannu na juya shi. Washi gari kafin na zuba mata kanwa kaɗan na rufe haka muka yi miyar ganye sannan na zuba sugar da kubewa busashe. Na rufe kafin na zuba gishiri da dan baking powder. Sannan na fara soya shi a non stick. Kafin kafin su gama abincin sadaka don don taliya da miyar kayan ciki nayi gida nayi masar gero sai tuwon dawa.
A bangaren Nady tana ta shan addu'ar da take amsa wurin Abba, sannan a cikin azumin zasu tafi da shi asibitin ko za a dace. Haka na gama kwanaki biyu babu matsala Madam na amsa don babu canji Shinkafar da tayi mana har da na sadaka ta dafa mana, tun kafin a sauke ake shewa girkin yayi kyau shi kuwa gwaska ya ce kada ta sake ta kaiwa Uwarsa ta ci haukarta ita ɗaya domin kuwa ya dauko abincin don mun ki zuwa ma yau ina gani nace mishi. "Kaci da hakuri ya jike tun akan wuta." Shiru yayi amma ya share ta fita haka muka tura kwanakin goman farko babu abinci me kyau a ta bangarenta.
Allah mai yadda yaso, inda muke fatan a samu abu sai bai zo ta nan ba domin mun yi buda bakin girkin Nadiya Ijlal ta fara amai kamar wasa mun dauka janyo shi take ashe ciki ne haka muka nufi asibiti, don ba karamin aikinsa ba ne ya ce bamu damu da ita ba, haka aka wuce da ita amai tana daga kwance yi take kai hankalin kowa a tashe, haka aka mata allura aka saka mata ruwa a daren aka bada test aka yi na jini da fitsari. Aka je aka yi can wurin karfe sha daya aka kawo Result. Duk mun kagu da muji ance guba ta ci, domin abinta take fada kenan an bata wani abu ta ci, ba sai ga shi likitan ya ce mishi. "Congratulations Prince ina tayaka muryan zuwa little prince ko princess!" Ba iya shi ya girgiza ba hatta ni na girgiza, domin Nady nayiwa fatan nasara sai gashi Ijlal ta samu. A sanyayye ya mike yana faɗin. "Thank!" Shima na fahimci bai yi na'am da babyn ba, ina kallon shi ya nad'e takardan ya saka a aljuhun wandonsa ya riko Nady ya ce mata. "Muje na kai ku gida don na ga yan gidansu sun zo!" Ban yi yunkurin shiga gaba ba, amma ta ce min. "Shiga Zainab kawai ina son zaman bayan!" Shiga nayi na yi shiru kamar ruwa ya cinye mu. "Congratulations Baby, Ubangiji ya a sauke ta lafiya!" Ya fada muryanta yana rawa. "Na gode! Na bar miki Babyn in sha Allah tana haifa zan baki dukka!" Kuka ne ya kwace