Showing 252001 words to 255000 words out of 304445 words
yi ne Ikhlas ta sha wahala! Waɗannan mutanen sun dake shi, sun azabtar da suka a cikin kwanaki shida kafin suka dauki number Salmanu Faris suka fito wajen gari suka gaya mishi sun yi garkuwa da Matarshi da yarsa da kuma Uwarta. Sannan suna ce kudin fasan miliyan dari da hamsin. Kafin suka kashe wayar.
***
Tashin hankalin da ya shiga lokacin da masu garkuwa suka kama Ijlal shi Yarshi ce ma damuwarsa idan ta ita ce ta kare a can bai damu ba, kasancewar lamarin babba ne kuma baya son a ja da nisa. Don haka ya bada waya da wanda suke ganin zai shiga lamarin a tsakiyarsu, ba tare da wani damuwa ba,aka fara ƙoƙarin basu kudin domin Dattawan fada da suka ji haka sun bada shawara kada ayi amfani da hukuma, ayi sulhu a basu abinda suke so ko don rayuwar Yarshi, sai da ya ji haushi ina ma da Ikhlas ce yasan da sau tayi aikinta na jarida, koda ya gayawa Mai Babbar daki abinda aka yanke ta ce mishi. " Ba mu da wata mafita ka amince a yi kome Allah ya kubutar da su." Maganar gaskiya an boye lamarin kamar yadda ake gudanar da shi a sirrance haka yasa aka tura musu kudi ta inda suka ce, sannan suma suka sake Ijlal da ta fita hayyacinta saboda zubar jini da tashin hankalin, asibiti aka wuce da su,lokacin da suka iso domin ita Hajiya Mardiya amai da guduwa tayi ta yi Ijlal kuwa ciwo sosai ta kwanta domin yadda tayi ta zama cikin kazanta ya haifar mata da wasu irin kuraje a gabanta suka cika kamar kudaddaji sun samu sabon bahaya, shi kan har ga Allah wani irin kishi da tsanar Ijlal, haka ya mai da hankali akan Yarshi da kulawarta. A lokacin da Mai Babbar daki ta zo ta ganshi tsaye a kan yarinayr da tayi fama da rashin kulawa itama jikinta yayi wasu irin kuraje, ga yunwa da ya ci jikin yarinyar, yarinyar da bata wuce sati biyar ba duk ta fita hayyacinta kamar wacce ta shekara da jinya. Dauriya ce da hakuri yasa yake tsaye amma da ya fadi akan Ijlal da Yar Uwarta. Haka yayi ta fama aka kika da yarinyar, kwanansu hudu ta wartsake kamar ba ita ba, sai rashin wayo da fama da ciwon madara yasa aka fara bata domin yana ganin haka shine mafita, duk wani gwajin da za ayi akan Ijlal an yi babu alamar wani ya tab'ata sai dai infection da take fama da shi kamar zai kashe ta. Haka ayi ta mata allurai kamar ba mutu ba.
***
A hankali nawa ciwon ya warke bakin ciwon ya motse tare da hadewa kamar bai tab'a wanzuwa ba, kafin wani lokaci lafiya ta samu, har ina kome da kaina. Kwana biyu ban ganshi ba ko text message baya turo min sai da nake gayawa Hajja ko yayi tafiya ne nan ta sake salati tana gaya min abinda ya faru, na ji tsoro a raina na razana da dukkan zuciyata, sannan nayi masu fatan sauki.
Na kira Nadiyya na jajjanta mata, itama ta ce a wurin mai babbar daki ta ji bai fada ba, sai naga rashin amfanin na mishi magana amma na tura mishi sakon da cewa.
*Hello saurayi kwana biyu da fatan kana lafiya i miss You!*
Sau ga kuwa kiranshi, nan muka yi ta hira duk yadda bakina yake son na tambaye shi ba.kasa sai nayi shiru na bar shi kawai. Satina biyu da kwana biyar Umma da Hajja suka mai da ni,bayan Maluma ta gyara min jikina ciki da waje, lokacin da muka isa Nady tana dakinta jin motsin ana bude kofar gidana yasa ta fito tana tambayar lafiya sai ta ganni. "Maman Anur shine zaki dawo babu notice?" "Ayi hakuri Nannynmu!" Haka ta shigo muka sha hira Umma da Hajja da Aunty Shukrah suka gyara min gidan, sai da Umma ta shiga toilet ta ga an sauya kome na ban dakin. Kirana tayi muka shiga na sake baki ina ganin bayin, Ashe dama da gaske zai sauya kayan ban dakin? Murmushi nayi na yi alola da na zo nayi sallah ina idarwa na shiga kitchen, na dafa wani abu. Nadiya take faɗin. "An daura abincin dare ba sai kin daura ba!"
Tow shi kenan!" Bayan fitarta Umma ta ce min.."na ga alama kin yarda da kowa, ban amince ki ci abincin kowa ba domin baka sanin waye yake nufarka da mugun nufi! Baka san waye mai kyakkyawar zuciya ya isa haka ki zauna idan an dafa a zuba mishi ke iya bakinki ya isa kin dai ji cewa kashe ki aka so Allah bai nufa ba, don haka kada na ji kada na gani." Umma dai umma dai, haka suka bar gidan suka bar ni.
Bayan isha na sha wanka cikin wata riga da zani na atamfar Vlisco pink. Ina zaune na kashe daurin dan kwalli ina kallon wa i Turkiyya series, ya shigo shi da Nady, mikewa nayi na shiga kitchen na kawo nishi ruwa da abin tabawa kafin ya kai hannu ita ta riga shi ba ruwanta, sai da ya gama hutawa ya ce mana. "Nasan zuwa yanzu kun fahimci halin da nake ciki, tow Ijlal zata dawo!" Mikewa Nadiyyah ta yi tana faɗin. "Gara ka bude idanunka, ba zaka dauko mata ragowar yan bindiga ka ce mu zauna da ita ba, wannan rashin adalci ne." Ta bar parlourn sai nayi shiru kafin na ce. "Idan ka tabbatar bata da matsalar kome ka dawo da matarka kada rashin Adalcin ya maka yawa, domin idan ka cigaba da nuna ko in kula zai haifar mata da babban tashin hankali da damuwa ita kuma Nady ka kyale ta matsalar gabanta ya ishe ya ita ba tashin hankali ta iya shiga ba balle har ta fara yanzu."
Nayi ta kwantar mishi da hankali da kyawawan kalamai...
08130269641
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 83
Bayan fitarshi na tab'e baki a raina na ce. "Hmm da wani ne a wannan halin ijlal sai ta kusan hauka." Koda yake Nady ta fimu gaskiya fa mace yan bindiga su tare da tare da rike ta na tsawon kwanaki sannan ya ce zai dawo da ita. Hmm Nadiya tayi gaskiya fa, amma idan na ce zan yi magana zafin zai mishi yawa sai na koma gefe ina kallon yadda kome yake tafiya domin idan na biyewa Nady sai ya ce min hade kai zamu hana shi zama da Matarshi. Aikuwa bangaren Nady ganin na bashi goyan baya itama ta fito tayi ta masifa tana faɗin mugun halin Ijlal, ban ce kome ba, nasan na sake nayi magana sai na nawa yafi na kowa muni, don haka na barwa Allah ikonsa, iskancin da tayi da Ba zata sake tayi yanzu ba domin kowa ya sha kunarta sai dai a kone bakiɗaya. Kwanaki uku a tsakanin ranar wata juma'a da yamma, muka ji dirin mota nasan ba mamaki ita ce tunda a can naji ƙarar. Ina kwance naji hayaniya da wasu maganganun alamar habaici da harbin iska, don ma Dogarai sun tsawatawa masu hayaniya sannan aka gaya musu ba a son tashin hankali. Idan ba zasu iya shiru ba su fita. Haka yasa suka yi shiru kuma da gaske ne cikin Nadiyyah sam bata son damuwa ko hayaniya yanzu sai kanta ya fara ciwo wnada haka yake haifar mata da hawan jini babu gaira babu dalili.
Haka suka gama hayaniyarsu aka barta ita da yarta da masu mata aiki, domin tun dawowana aka ware kowacce mun bayinta asalima akwai BQ a bayan part dinmu ma'ana a cikin gidan kowacce mace akwai bq haka yasa kowacce ta killace hadimanta sai ya kasance bayan gidanshi Jakadiya take zaune da wasu bayi da suke mishi hidima amma abinda ya shafi wanki da kome na shi Faruq ne guda kuwa waje ake kaiwa. Karfe takwas ya kira kowaccenmu zuwa parlournshi. Haka na shirya cikin doguwar riga mai kyau na nufi bangarensa, a hankali na samu Nadiyyah tana tafiya a hankali. Murmushi nayi na ce mata. "Maman Trip!" Hararata tayi muka shiga cikin parlourn da sallama, zama nayi a kujera ita yanzu tafi gane zaman kasa, tana isowa ya mike ya rikota. Sannan ya taimaka mata ta zauna, murmushi nayi ina kallon yadda take narkewa. *I can't wait to see,nima ranar da za a ce ina da cikin nan!* " Yan mata cikin ya baki sha'awa ne?" Murmushi nayi mai haɗe da dariya na ce mishi. "Ciki da ban sha'awa mana, kawai hakan ya burge ni ne.". Gyada kai yayi yana faɗin. "Lallai kuwa tow ki shirya na zuba miki yan biyar!" Hararanshi nayi daidai shigowar Ijlal dauke da yarta a kafad'arta, wani turus tayi ganin yadda yake daman matsewa Nadiya kafa, kamar zata sake yar hannunta.."Ciki kike da shi? Amma ba nashi ba ne ko?" Ta sake wannan maganar kamar an sake kashi, mahaukaci ya ce. "Abin ba dad'i!" Bayan ya ci kashin, shine wannan kalaman Ijlal. "Ke wawuyar ina ce? Cikin ba nawa ba uban waye ya mata idan ba ni ba? Kin zata je daya ce kike da ikon bude jiki ki haihu da ni, itama ciki da ita ke mutum bai ji zafin zama da ke ba sai kece zaki ga matata da ciki ki tambaye ta inda ta samo ko an gaya miki ban san abinda kike aikatawa ba ne!"
Da yake sulhu take nima, cikin sanyin murya ta ce mishi. "Allah ya huci zuciyarka ban san zaka fusata ba ne. Nadiya ki yi hakuri. Ikhlas ya gida ashe baki ji dadi ba!" Ya fada tana min wani irin kallo mai dauke da wani tsinannen murmushin da duk lokacin da tayi nasan akwai wani abu da ta shiryawa kanta, ban bi ta kanta ba domin ita ba ce matsalata, balle har ta zama topic of discussion da zan sakata a gaba..
Yadda ya taru magana yayi mana tare da ja mana kunne da mu kiyayye shiga hakkin juna, sannan ya kuma mana barazana idan wata ta kawo mishi fita zai rabu da ita, musamman ita ya nuna Ya ce kada ya ji kada ya gani idan ta sake aka kawo ƙararta wallahi zata fuskanci b'acin rai yasan sai ba shiga harkanta nake ba, haka yasa kowacce ta kama kanta, ta kuma rufawa kanta asiri ya kara jajjadawa ta raba girki kowacce tayi nata da bayinta, haka yasa kowa ya tsaya a inda yake amma a bangaren Ijlal cikin Nadiyyah yazo mata bazata ya aka yi bata sani ba, kasa motsi tayi har bayan sallamarsu da yayi sai da ya daka mata tsawa ta mike jiki a sanyayye, maganar gaskiya yana dan kyamarta, don haka ya ce mata. "Ki zauna ki kula da kanki da Yarinyar bana son na ga kara ganin kafarki anan idan kin samu lafiya sai a san yadda za ayi." Sunkuyar da kai tayi tana jin wani irin ciwo da zafi a ranta, Ikhlas ta fita da sauki abin amma yadda ya nuna mata a gaban Nadiya sai ta ji kamar muzantata yayi a gaban Matarshi, haka yasa ta fita tana mai nufar bangarenta, tun da ta shiga parlournta take wani irin kuka ba kukan abinda ya mata ba, kukan yadda ba zata kasance da shi ba ita babban burinta yanzu ta sake samun wani cikin da shi amma bakiɗaya ya hade yaki mai da hankali akanta.
Haka tayi ta nazarin yadda zata yi da cikin Nadiyyah, duk yadda taso ta kawo karshen tunaninta abin ya ci tura don haka, tunda tasan ba zai tab'a nimanta ba sai share su. Washi gari ta shirya tsaf mai kula da Amiratul Zaitunah ta mata wanka ta gyara yarinyar sannan aka kawo mata abin karyawa, har parlournta irin wannan rayuwar take so fa, Alhamdulillahi ta samu, mai kula da Amirah ta bata madara tasha dakyar, sannan ta sakata a kafada tana jijjigata har tayi barci, ita kuma Fulani karama Ijlal ta zauna tana karyawa sai kallon agogon bangon parlourn ta cewa mai kula da Amirah. "Ko dauko gadonta na hutawa ki saka kafin ya shigo ya ganta anan." "Allah ya baki nasara an gama!" Haka ta dauko tayi kome tare da kwantar da yarinyar ta cigaba da jijjiga gadon, har wurin sha daya saura sannan ya shigo parlourn, mikewa tayi tana gaishe shi. Da hannu ya amsa mata. Ya durkusa a gaban yarinyar yana shafa kanta yana jin wani irin nutsuwa a ranshi ko ba kome zai bude idanu ya ganta. Murmushi yayi ciro wayarshi ya dauke ta hoto sun kai kala goma, haka ya mike yana kallon bayin da suka zube ya ce musu. "Wacece cikinku take kula da ita?" "Allah ya baka lafiya da nisan kwana, ni ce takawarka lafiya jini da nasaba ta sarauta tana yawo a jikinka!" Kallon Ijlal yayi ya ce mata. "Kin bata maganin Amirah?" Shiru tayi ta manta ita fa har yau da tunanin cikin Nadiyyah ta tashi. "Ba magana nake ba!" Ya daka mata tsawa, a dan birkice ta ce mishi. "Na manta!" Tsayawa yayi yana kallon yadda take kokarin barin parlourn, takaici da bakin ciki kawai sun isa kashe bawa idan ya zauna da Ijlal. Kawo maganin tayi ta mikawa yarinyar. "Ki mata bayani yadda zata bata!" Daga haka ya juya ya fita, haka ta gayawa yarinyar yadda zata bata maganin, da sauran kulawar da ya dace. Gyara parlourn suka yi suka koma bakin kofa suka tsaya, kasa barci tayi tana nazarin yadda zata yi da cikin Nadiyyah Allah ya gani cikin Nadiyyah ya tsaya mata a rai, idan ta ce tana kaunar cikin tayi karya.
Sha daya da rabi ya shigo min, ina hada abin karyawa, ya shigo tsayawa yayi a bakin kofar kitchen din, cire alkyabbar shi yayi yana mai shigowa a hankali na ce mishi.."Nasan ka shigo fa!" Ya cigaba da aikina rungume ni yayi ta baya. "Ina kewarki!" "Nima haka!" Na fada ina wanke roban da na kwab'a fanke. "Abin karyawa kika mana?" Murmushi nayi ina faɗin. "Ka ci naka a wurin Giwar sarki kada ka saka rai a nawa don ba baka zan yi ba." Ba faɗa ina cire jikina daga gare shi. "Bakyau rowa dai!" Juye kunun gyad'a nayi a cikin wani glass jug, na saka a tire, yana ganin yadda nake haɗawa na dauka na kai parlour na dawo na kwashe kome na kai, sannan na goge kitchen din duk yana tsaye ni ban san me yake yi ba na dai ga kamar yana tauna, kamar ance na d'ago kai ashe fanke ne a hannunshi ya cika baki yana ci hankali kwance. Wani irin kallo nayi mishi irin ina wasa da kai waye ya baka? Ai kuwa na nufe shi da sauri ya fito waje da sassarfa ya saka alkyabbar shi zai fita na rike rigar. "Ka ga bana son haka bani abin karyawa na!" Tura na karshen yayi a baki gashi sun yi laushi gwanin dad'i, sai da naji haushi ya kama, haka na kyale shi sai da ya fita don daukar alhaki ya leko yana faɗin. "Sai ki yi hakuri!" Ya juya yana mai barin parlourn, haka na girgiza kai, zan rama wallahi.
Wurin karfe daya saura sai ga Iram, ta sake zuwa da niman fitina. Ina parlour ta shigo ina karatun Alqur'ani, tunda Wildat ta kawo mata ruwa ta zuba mata, take zaune bata ce min ba ban ce mata ba, karatuna nake har na kai aya kafin ta ce min. "Kin san abinda ya same ki nice na zo na zuba miki a ban dakinki yadda duk lokacin da kika buge gabanki zai lalace!" Na razana amma kuma wannan lamarin ba na razana bane sai na sake murmushi. "Allah ya baki ikon ne don ya jaraba imanina, kai ni ban yarda akan kece ba nafi yarda da cewa Allah ne ya aiko min jarabawa kuma Alhamdulillahi ba a wahala ba Allah ya kawo sauki!"
"Ai shine abin ya bani mamaki, me yasa ke baki tab'a wahala ne?" Ta tambaye ni tana mikewa, "Sarkin dogarai!" Na kira sunansa domin na ga tana shirin ciro abu a cikin jakarta bayan ta ja handglove din hannunta. Sai gashi kuwa ya shigo da zabgagge bulala a hannunsa. "Fulani Babba gani nan fada na cika!" "A bude jakarta, sannan a kira min Faruq!" Da yake ba shi daya ya shigo ba, ai kuwa sauran suka kira Faruq, wani hoda ce da wasu kwayoyi da allura, kai abubuwa dai ba kyan gani. Na cigaba da karatuna dariya tayi tana faɗin.."Ni zaki tozarta? Ni yar uwarki ce fa!" Zuga mata bulala yayi ta danna ihu. "Allah ya baki nasara me zamu mata?" "Jira Faruq!" Na cigaba da karatun, after wasu mintuna Faruq ya shigo, wayata da take gefena, na mika mishi yana gama ji ya mika min tare da cewa.."ranki shi dade mai ya da ce da ita!" Kasa yayi da kanshi daidai dan kusa da ni yayi magana maganar, nima haka na mishi bayanin yadda zai yi da ita"Ku manta da jinin da yake tsakaninmu, ta fada maka wanda ya saka ta aikin, sauran ka gaya min idan ta yi laushi kuma ya faɗa ku kaita inda kasan zata zauna na wani lokaci har ta biyo, kada ta rasa ci da sha kawai a boye ta wani lokaci wayarta da jakanta ga number Tauhid kasan yadda zaka bashi sauran kuma mu ga abinda zai faru." "An gama ranki ya dade!" Ya juya tare da kallonta bai mata magana ba, wani irin duka ya mata tuni ya yi kasa ya dauke ta ya saka ta a kafad'arshi ya bar parlourn da ita Sarkin dogarai ya juya zai fita na ce mishi. "Sarkin dogarai! A duniyar nan tana da fadi da girma, wannan maganar ya zama iya mune muka san da shi!" "Ranki ya dade ai ko kashe kaina kika ce nayi zan yi wannan