Showing 297001 words to 300000 words out of 304445 words

Chapter 100 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

35

sani ba don a wurinta yake, sai da Mai Babbar daki ta kira ni tana cewa. "Zainab ga yan uwanki anan Mijinku ba lafiya ke baki sani ba ne?" "Bai jima da barin nan ba, har sun tafi asibiti?" Driven cikin gidan yazo ya dauke ni, da kunun shinkafa da alkama da dabino sai aya da na saka, sannan na dan mishi light food na wuce asibitin. Ina zuwa na samu yana zaune ma, maltina yake sha na zuba mishi idanu. Murmushi yayi yana faɗin. "Ni nace kada a gaya miki!" "Amma ai zaka saka a dauka da gangan naki zuwa! Ajiye maltinan ka sha kunu!" A hankali na zuba mishi yana sha yana kallon kunun. Dawo da kofin yayi kamar zai yi amai. "Yaya ko a kira likita ne?" Girgixa kai yayi yana faɗin. "A'a!" Abincin na bude mishi ya girgiza min kai. Dariya Nadiyyah tayi tana faɗin. "Munafuncin banza." "Bani abincin!" Bata rufe baki ba ya amshi abincin ya fara ci, dan dandanon yajin abincin yasa shi ci sosai, sannan ya sauke ajiyar zuciya. Maltinan ya cigaba da kurba saboda dan dacinsa. Ai kuwa aka sallame shi haka muka dawo gidan, zai shiga wurinsa ya ce min. "Ina son biski da miyar yakuwa!" "Tow Yaya!" Na wuce kitchen daga nan, a daren na mishi biskin sai dai bani da miyar yakuwa na tuna na gani a cikin gidan wurin Mai Babbar daki, kiranta nayi na ce zan turo faruq ya amsa min, ta ce to.
Sai da nayi biskin gero wanda yafi na shinkafa ko.masara tashin kanshi. Na dauki faife na rufe shi kamshin ya zaga gidan, haka na gama na juye mishi, aka kawo miyar na dumama..na bawa Faruq ya kai mishi don ina tsoron fitina. "Ina Zainab din?" "Tace kayi hakuri sai gobe!" Haka Nadiya ta zuba mishi abincin. Ya ci sosai sannan ya cire hannunsa mayya ta cinye abincin..
Washi gari bayan ya dawo sallah asuba,nima zazzaɓin ne ya rufe ni da mura. Yana shigowa na tashi zaune. "Yaya ta jikin naka?" "Da sauki ko zan samu koko da kosai?" "Eh zaka samu Yaya!" Na mike, zai rungume ni na yi masa na gudu yana jin zafin jikina zai ce ya fasa parlourn ya dawo ya kwanta, na cigaba da sai wurin karfe takwas na gama na zuba mishi na kai parlourn. "Sannu Yaya;" "yawwa Zainab na ji mai babbar daki ta ce zata kawo miki Khairat shine nace ko zaki hada ki min wata alfarma" shiru nayi ina kallonshi a hankali kafin ya gyara zaman shi yayi yana nazarin yadda zai gaya min abinda yake nufi da kuma yadda zan fahimce shi ba tare da nace a'a ba, nima kuwa ina kara nazarin mai zai bukata haka idan dai wani abu ne mai sauki zan amince amma idan abin ba sauki Allah ba zan amince ba, sai dai duk abinda zai faru ya faru, wayata ce take kara na wuce dakin na ga kiran Yeemar dauka nayi a hankali na saka a kunne. Kukan da take yi yasa jikina ya dauki rawa. Ta ce min" Zainab Yazid babu sun kashe min Mijina!" "Innalillahi wainnalihir rajoun, Innalillahi wainnalihir rajoun!" Wani irin abu naji ya dauke min ji da ganina. Na zube a wurin a sume. Shiru bata fito ba ya shigo dakin ya ganta zube a kasa ɗaukarta yayi yana jijjiga ta, yadda jikinta ya dauki zafi, ya kwantar da ita ta dauko ruwan sanyi ya kurba sannan ya fesa mata. Wani irin ajiyar zuciya na ja da karfi....
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 97

Tare da kamkame shi na fada da wani irin kuka ina. Na rasa meke min dadi jiya nake bata labarin kudin nace xan turo mata nata kason, Mijinta sai dariya yake min wai ko me na samu Yeemar, da yarsu daya an kashe shi. "Mene ne? Dama baki da lafiya ne?" "Mijin Yeemar aka kashe!" Gabanshi ne yayi wani irin bugawa, ya rike ni tsam. "Mijin Yeemar Yazid?" "Shi fa kasan lauya ne mun bashi labarin mutuwar Joy!" Sake baki yayi ya rasa mai zai yi guda ɗaya. "Shirya Faruq ya kai ki! Za ayi jana'izar a fadar nan in sha Allah!" Haka ya fita tare da nufar waje, dakyar na shirya doguwar riga na saka, na fito ko kasa zama bana iyawa, muna isa gidan an cika wani irin karta cikina yayi na shiga ban dakin da yake dakinta nayi bayan gida kadan ne kuma da alamar atini ne, kafin wani lokaci dangin mijin da nata sun cika gidan. Kai Atinin nan ya saka ni a gaba tun ina iya zuwa karshe dai bayan anyi mishi sutura aka wuce da ni asibiti, domin kuwa Atinin da nake ya koma bana iya kome sai majina da jini, haka aka yi ta saka min drip.

Daga gida kuwa Rubutu Abba tayi ta min ana kawo min in sha. Domin suma Doctor Munirah sun kasa tsayar da Atinin, kafin wani lokaci na wani irin zabge kamar wacce nayi shekara ina jinya. Kowa ya ji irin yadda nake kwance sai ya zo ko daga gidansu Yeemar da Yazid din sun zo sosai, kwana biyar nayi aka sallame ni, bayan an samu ya tsaya anyi iya bincike babu kome lafiyar cikina da jikina lau. Haka yasa muka dawo gida, sai dai ba kwari jikina. Har lokacin ana saka min ruwa.. shima karfin hali ne amma bai da lafiya, haka yasa duk muka koma wasu rubabbun. Sai mita Nadiyyah take tana faɗin. "Na ga Romeo and Juliet karewar soyayya mutuwa suka yi lokaci guda." Ni kan ban da lafiya sallama musu mijin nayi don ba zan kashe kaina ba, akan namiji ba. Kwana biyu aka yi addu'ar bakwai naje gidan mun sha kuka, ta rike hannuna tana faɗin. "Mutuwar miji akwai ciwo, kada ki yi fatan ganin haka wallahi zaki zauce idan kika ga wannan ranar zuciyata kamar zata buga!" Ita kuka ni kuka haka muka yi ta kuka bayan addu'ar iyayenta suka tattara kayanta, domin tsira da rayuwarta, Nima haka ya zo ta dauke ni. Dafa goshina yayi yana faɗin. "Sannu kin ji!" "Gyada kai nayi, sannan muka dawo gidan mutuwar mijin Yeemar ya tab'a, kwana biyu na kara zuwa na ganta na kai mata kudin nan haka muka yi ta kuka, sannan muka rabu. Ranar da ta cika sati biyu bai gaya min ba ya haɗa mata kayan abinci da kudi ya bawa Faruq ya kai mata, ya ce idan tana da matsala ta yiwa Faruq magana, haka yanayin ya cigaba da tafiya a hankali na samu wani irin sauki amma fa duk wannan jikin babu shi na lalace tas.
Sai na danyi duhu na dishe, haka na cigaba da rayuwa, gida ba dad'i. Har zuwa ranar da Yazid ya cika kwanaki Arba'in, muka yi shi abincin sadaka, muka kai. Tunda muka je na ci fanke da su Maluma suka kawo, tun a hanya na cewa Faruq. "Don Allah kai ni wurin Maluma ta bani fanke!" Haka muka je gidan na samu wai ya ƙare. "Ko na Abba baku ajiye ba?" Yadda nayi tambayar a dame Umma ta ce min. "Akwai na shi bari na juyo miki!" Haka ta juye min, suna kallon juna ita da Maluma tas na cinye su na sha ruwa na ce mata. "Umma ke ce kika yi fanken?" "Eh ni nayi!" Ta bani amsa tana kallon Maluma hankalina yana kan waya, dauka nayi nace mishi. "Allah ya huci zuciyarka, gani nan abu nazo amsa!" Na mike ina sabar jakata na ce mata. "Umma ko zaki kara min ne! Idan akwai?" Na tambaye ta, "sai dai ayi miki Faruq ya zo ya amsa ko?" "Shi kenan don Allah ayi min taliyar murji da miyar attarubu,.yaji albasa yankanku kada a saka kome haka nake son shi danyen miya Umma kin ji!" "In sha Allah!" Na fada Rungume ta nayi.na rungume Maluma na fita da gudu, "Zainab ki kula ba kyau!" "Tow Ummana!" Tana fita Maluma ta yi sujadar godiya. Sannan suka rufe maganar, Babu wnada ya kara magana, da Abba ya dawo a rubuce suka gaya mishi, rubutu yayi ya saka aka wanke sannan da Faruq ya zo amsar amincin ya kawo mata.

A daren kuwa ina zaune aka kawo min, na zauna ina ci ina jan ya ji Umma har da miyar da taliyar ta hado min, wani ikon tas na cinye na tashi, dama haka kwana biyu nan yunwa ya gallabe ni, tun bayan rasuwar Yazid nake fama da yunwa, haka na cinye na kwanta yau yana ɓangaren Ijlal ne, rubutu na na shanye tas. Nayi alola nayi shafa'i da wutir na kwanta, washi gari na tashi da son soyeyyar dankalin hausa, da miyar sauce, irin wanda ake sayarwa a bakin hanya. Kiran Abba nayi kamar zan yi kuka domin jiya ya ce min duk abinda nake so na gaya mishi, kada na tambayi ko shi mijina yana da kyau na koyi shiru. Dariya nayi kawai. Na ce mishi. "Abba ina son cin dundun kolo, da doya soyayye ba irin na gida ba, na Umma da Maluma yana jan mai, ka saya min na Maman Ester." "Shi kenan da kaina zan kawo miki!" "Na gode Abba akwai kunun da take yi mai kauri nan ka haɗa min da shi!" "Shi kenan My Queen!". Ina zaune Wildat ta zo suka yi aiki ina ta jiran Abba na kira shi ya fi sau goma, can ya ce min. "Gani nan!" Ya buga kofa na tashi na bude mish da basket, amsa nayi na ce mishi. "Ka shigo!" "Tow!!" Ya shigo ya zauna kafin ya ce min. "Ina dakinki?" Nuna mishi nayi ya shiga can ta fito. Zama yayi ya ga yadda nake cin abincin kamar za a kwace gashi katon kula ce amma tas na cinye, ina faɗin. "Abba Allah ya maka albarka!" "Amin uwata!" Ya ajiye min goron rubutu na shanye shi tas, na ce mishi. "Abba kasan me? Na koshi da yake kai ne ka kawo min!" Gyara zama yayi ya ce min. "Na gaya miki babu kyau surutu ko? Idan kika ga abu kina so kada ki gayawa kowa let me know, ko ko gayawa Mai Babbar daki kin ji!" Gyada kai nayi nace mishi. "Tow Abba! Amma Abba kace zaka hada min maganin ciwon ciki baka hada min ba?" Zuba min idanun yayi ya ce min. "Yaushe zaki fara!" Kunya yasa na tura baki ina juya kaina. "Saura kwana biyu!" "Zan turo miki da shi!" Ya fada yana mikewa, lokacin da ya tafi Mai Babbar daki ta kira ni a waya take tambayar ko ina son wani abu na ce mata. "Ummi Abba ya kawo min abinci kuma na cinye tas!" "Tow Madalla Yar Abba da Mai Babbar daki!" Dariya nayi kawai, ranar wainar fulawa nayi irin na yan fashi da makami, domin na irin wancan local din nayi ba wannan kwai biyar na zuba tare da kazar da na nike shi na cinye tas, da dare ina kallon Afirkan magic na ga ana yin tuwon fufu miyar kubewa, ga nama da ganda gundun gundun, na zubawa tv idanu haka na kira Mai Babbar daki ina kuka. "Zainab lafiya?" "Ummi yanzu naga fufu miyar kubewa da ganda da kifi da nama Ina son irin nasu kuma.dare yayi!" Shiru tayi kafin ta ce min.."zaki ko?" "Eh Ummi idan ban samu ba zan sha miyar kuka na kwanta!" "Ki yi hakuri za a kawo miki!" Haka na zauna daram, har ya shigo ya same ni zaune, kai har ya shiga ciki ya dawo ina zaune ya ci abinci ina zaune ina yi.ina kallon wayata. Karfe daya saura na mike ina jin kamar xan mutu aka buga kofar. Faruq ne ya rakota, juyawa nayi naga Yaya ya bude kofar, Mai Babbar daki ce fa kanta. Kuka me ya zo min na nufe ta, ina shashekar kuka, "Ummi dama zaki zo?" Zama tayi ta bude min kayan abincin na zauna na fara hadiye yawun. kafin na zauna na fara ci yana min tsiya wai. "Allah ya kyauta kwadayi bai yi ba!" "Eh kasan yau nayi baki shine abincin ya saura na ce nasan itama zata so na kawo mata. Ni zan tafi!" Ya mike. "Ummi;" na kira sunanta sannan na mike na mata side hug, ina faɗin. "Allah ya baki lafiya da nisan kwana!" "Amin Ya Allah!" Ta fada tana min sai da safe, fufun nan guda biyar ne, dama ya tafi rakata. Kafin ya dawo wallahi billahi azim na cinye guda uku ina cin na huɗu har wani mulmula shi nake ina kara jin wani shegen dadi, ashe Malam Salamanun faransa sauri yake yazo ya ci amma ina yana shigowa ina kai lomar na biyar tas na cinye abincina nayi wani gyatsa bad manners dai ya fara bin jikina hararar da ya watsa min ya fi ban dariya har da zungure min goshi ji fa. Sauran miyar na kai firji, washi gari na kira Maluma na ce ina son Alelen gwangwani gani nan zuwa. Haka na fita bayan ya tafi fada, na je na zauna musu aka gama dama mace musu ina son mai kala biyu wnada cikin yake ruwan kumfa a kasar gwangwanin, wani shegen dadi ya kama ni, ina ci ina lumshe idanun, dama yasan bana gidan sai yamma na dawo na wuce wurin Mai Babbar daki, na zauna a yan kwanakin nan na lura har wani kiba na fara , sai na kara dishewa, ina nan Nadiyyah da Ijlal suka shigo. Muka gaisa sama sama, ba laifi cikinsu ya fito sosai. Shafa cikin suke yi na dauke kai ina shan fura da nono hankalina kwance, ban kara damuwa da su ba. "Wasu sai kiba suke tow ba ya shiga mahaifa sai dai ya bi jini dole ayi ta kiba kamar kudin cizo!"
Murmushi nayi na tuna wakar gwanja, inda yake faɗin. "Allah ke sonmu ba da ban ba da sai sun kar mu, mun ƙare layin makiya sai da ku ganmu, ba boka ba malam!" Na yi shiru saboda jin muryan Mai Babbar daki tana waya, narkewa nayi akan kujerar parlourn ina yin abu kamar xan yi kuka. "Me aka miki?" "Babu kome Ummi ki bani Khairat sai ja min rai kike!" "Allah Sarki zata zo Aneesah ce ta dauke ta!" Na ji haushi, ai tasan wurina zata zo ta wani dauke ta. "Ki yi hakuri zata kawo miki yarki!" "Ba kome!" Na fada ina kokarin mikewa. Zan tafi ta ce min. "An jima zaki raka ni unguwa!"
"To Allah ya kai mu!" Na fita daga gidan na wuce namu, na samu gidan tsaf kwanciya nayi, n huta sannan na daura faten wake da iya shi kadai, na bare ayaba, kafin waken ya nuna na soya ayabar amma na cinye tas a gindin murhu. Murmushi nayi ka zauna na jira wanken, bread din da na zo da shi daga gidanmu na ciro na yanka shi a tsakiya, na tsayayyenruwnq waken na.hada kayan miya, na zauna na mishi fate sama sama, na juye a cikin bread din kusan Allah lamarin nan babu wani boye-boye ina son wannan haɗin, haka nayi ta matse bread din sai da ya shanye faten na rike a hannuna kamar yadda na ga wasu anyi a lokacin da muka yi camp, ina gutsira special burger, Wai wai ashe haka wannan lamarin yake, Allah na tuba sai da naji kukan farin ciki ya zo min ina ci ina share kwalla, tas na cinye na sha ruwan rubutun nan. Yau ya kamata na ga period dina, wancan watan ban yi ba ni fa tunda nayi bari nake skipping wasu watani yanzu tun tafiyar shi LA nayi ban kara yi ba sai bikin ilham bayan sati da bikinta nayi na kwana uku, da na gayawa Munirah ta ce haka zai dawo normal ko kuma gajiyar biki musamman yadda Yaya ya dame ni a Abuja nan haka nayi na kwnan uku, ranar da ya zo min a haukace! Murmushi nayi saboda da tuna wannan ranar na kwana biyu da wanka na, yadda ya haukace min sai da tsigar jikina ya mike kamar nayi kuka sosai nake jin wannan ranar. "Farin cikin me ake?" Ya tambaye ni gyara tsayuwa nayi ina faɗin. "Ba kome My King!" Jan kujeran yayi ya zauna yana murmushi. Nima zama nayi ya sake murmushi ya ce min. "Dama tun kafin rasuwar Mijin Yeemar nake son na miki wata kyauta bayan Khairat." Zuba mishi idanu nayi na ce mishi. "Ina jinka!" A hankali ya shiga warware min bayanin da na ji kamar na rufe shi da duka, wato don bana haihuwa shine zai kwaso min Yarshi da Uwarta ma bata iya zaman jinyarta ba sai ni. "Shine nace tunda kin ga Uwar ja fama da kanta ko xan kawo miki Amiratul Zaitunah ne ki rike ta da Khairat.......
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 99

"Meramo ki hada mata inabi da dabino su zama abincinta saboda inganta lafiyar bayin Allan jikinta, sai madara safe da yamma!" Kafin ta riko hannuna muka fito, garin yayi wani irin kyau shakar iskar garin nayi na ga yayi matukar burge ni. Bude min motar Sadi yayi muka shiga a hankali, nake kallon ledar agwalimar da aka saya Min. "Sha!" Ba musu na dauki leda daya na bude na fara sha a hankali, ina wani lumshe idanuna. Yadda nake sha bana wani jin tsamin kawai zuciyata. Yayi nisan kaunar shan abin gajiya nayi na ajiye shi na dan mai da kaina baya, barci ne yayi gaba da ni. Ban kara farkawa ba sai bayan wasu yan mintina na ji Ummi tana faɗin. "Sannu tashi!" "Alhilal specializing na gani, fitowa nayi na shiga bin ta har cikin asibitin yadda babu wanda ya bi ta kanmu haka muka zauna can Sadi ya kawo mana kome da kome da Ummi ta bukata, muna zaune can aka kirani, kallon mai babbar daki nayi na ce mata. "Ni ai lafiyata lau!" Na fada rike hannuna tayi muka shiga cikin office din, zauna da ni tayi itama ta zauna tana kallon agogon bangon dakin. "Sannu Hajiya lafiya?"


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login