Showing 162001 words to 165000 words out of 304445 words

Chapter 55 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

70

da take ciki idan ka matsa kusa da ita zata bude abubuwa dayawa wannan rigimar da kuke har da rashin shakuwa mai kyau, ita mace tana bukatar lokaci ba wai kana nuna mata isa isa ba ne." A dazun da Uwais ya zo ba kai kara yayi ba amma yadda yake damuwa da Zainab din idan wani abu ya faru ta barinta yasa Mai babbar daki ta fahimci irin raunin da Danta yayi domin baya iya tabuka kome akan Zainab irin tashi rayuwar kenan, sannan bata jin zata iya sauya shi domin haka yake, sannan idan ta saka lallai yayi yadda yake so, zai iya raunata zuciyarta sannan yayiwa kanshi illar da ba zai tab'a recovery cikin sauki ba, tasan duk abinda yake faruwa, Salmanu Faris baya cikin mazan da suke iya niman soyayyar mace sai dai biyan buƙatarta kansu ita kuma Zainab tana ganin yadda ake bata dama a rayuwarta kamar gangnaci ne, ba wani ya gaya mata haka ba, takunsa da kuma takun Zainab din ta karanta ta gano kome tsaf da kuma yadda suka ɗauki zamansu. Mai Babbar daki tana sonshi da Zaianb amma tana son su samu kyakkyawar dangantaka wacce suka gina daga zuciyarsu da kansu.

A hankali yake shafa kanta yana shaƙar kamshin sabulun wankarta tare da shampoo din da tayi amfani da shi, a hankali barci yayi gaba da shi,
#GoodZeefaris
**
Alhaji Nafi'u
Yau kwana uku kenan ya gagara samun damar bude kofar underworld, zaga parlourn yake yana jin kamar yayi wani kuskuren da bai san yadda zai gyara ba. Kiran wayarshi aka yi kamar ba zai dauka ba, can ya dauka ya saka a kunne. "Khalifa ya dai?" "Dad yarinyar ta mutu ya zamu yi kenan? Dad mai yasa da zarar na!" " Ka fita a wurin za a gyara wurin! Ina fatan babu wanda ya wanda ya ganka ko?"
"Eh Dad!"
Kashe wayar yayi ya ki wani layi cikin minti goma aka kawo mishi Khalifa da yake buge, ba zai ce ga lokacin da khalifa ya zama Addict da bin mata da shaye-shaye ba, amma a duk lokacin da ya kalli Khalifa yana jin zafi sosai. Sannan ga Yaran Saddam, Attahiru, Junaid, kowannensu ya ginawa Yaranshi mafarkinsa sun yi gaba amma Khalifa kullum kara tsulla tsiya yake, yana jin kamar akwai abinda yayi yake fuskanta published ta sanadin Khalifa, haka yasa shi ganin dole akwai abinda yake faruwa ba haka kawai Khalifa ya lalace ba, domin ko Ahmad Rilwani Yayari yana da sana'arshi da iliminsa idan aka je fagen iskanci ne yaron ya jika Khalifa ya shanye amma me yasa na Khalifa yayi worst sama da na kowa? Mai yasa Khalifa yake wani abinda ya wuce na kowa? Ji yayi yana zargin akwai hannu akan Khalifa. Saimah dama tun farkon aurensu ta fito ta gaya mishi Mijinta sunan suna aure ne amma baya mata yadda take so, haka ya rarrashe ta, yasan tana zaune lafiya ne duk da damar da ta samu. Amma me yasa kome baya shiga cikin kan Khalifa a bakin Ahmad yake jin yana faɗin. "Ai Khalifa da dabbobi yanayinsu daya Gayen da idan ya fara kwanciya da mace kamar ya samu roba, baya jin ya gaji ko ya huta ai kome yana bukatar hutu da nutsuwa kome idan zai yi sai ya kwafsa domin yana abu kamar mai jin yunwa, wannan abin ya mishi ciwo, kallon Khalifa din yayi da yake kwance a wuri daga shi sai gajeren wando. Shi Alhaji Nafi'u ya manta abinda ya aikata idanunsa sun rufe da niman duniya yayi ninkaya cikin saɓon Allah....
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 53
Ashe da gaske aka ce wanzan bai san Jarfa, wato shi duk abinda yake har yanzu bai hango kuskurenshi ba, don haka ya cigaba da shirya yadda zai wargaza kowa, a cikinsu kuwa har da Uwais da ya janyo shi cikin al'amarin, yayi haka ne domin biyan buƙatarshi, domin ya cusawa Uwais wata muguwar bayani wanda yasa shi dole ya kalubalancin Faris duk yadda zai so ya mishi bayani domin ya mishi wankin ƙwaƙwalwa ne da bayani mara kan gado, kuma ya lura Uwais din ya ɗauka.

**
Da asuban fari.
Tunda na ji dadin jikinshi ba sai na kara nanike mishi ba, ga wani irin sanyin asuba da yake ratsa duk wani muslmin kwarai, dole wannan lokacin ya tashe shi, yadda nake kara nanike mishi yasa shi ture ni a hankali, ina tura baki kamar xan yi kuka na kara shige mishi har ina sauke ajiyar zuciya.
Ware idanun yayi lallai yarinyar nan ta gama rena shi, sake saka yatsarshi yayi ya ture kanta. Ta kara matse shi har da wani dan gunaguninta. Bude idanu yayi anya ba mafarki take ba? Don haka ya janye jikinshi da karfi ai kuwa ta ce mishi. "Meye haka?" A wani shagwab'e, tana kara lumshe idanu. Ban daki ya wuce yana ganin yadda abin sa ya cika wando Amma yarinyar nan tana tambayar shi meye haka, ruwan sanyi ya sakarwa kanshi yana jin wani irin yanayi na fisgarshi haka ya gama ya wuce part dinsa ya saka jallabiyarshi, da hular a sallami dan naci, ya nufi masallaci a waje ya samu Faruq yana jiranshi, murmushi ya sakarwa Faruq din ya ce mishi. "Barka da safiya!" Sosa kai yayi yana amsawa.budewa Salmanu Faris mota yayi ya shiga sannan ya koma gefe shima ya shiga ya tashi motar, a hankali suke tafiya babu wani hira ya mikawa Salmanu Faris wasu files, amsa yayi ya ce mishi. "Ka duba gefen can na ajiye maka abu ka buɗe!" Ba musu yana kallon hanya kafin a dauko wani kwali ya ajiyeta yayi bai ce kome. Har suka isa masallaci, kafin ya fito Salmanu ya rigashi suka shiga , don dole ya hakura ya mai da abin ya boye sannan ya fito daga motar ya rufe suka shiga cikin Masallacin. Bayan a idar da Sallah aka yi sanarwar rasuwar da aka yi, Na'ibin ya mike yana faɗin. "Ya kamata gwamnati da masu ruwa da tsaki a cikin wannan lamarin su tashi su san me ake ciki, yan daba sun fara cin gabala a kan al'umma, Yaron da aka kashe bakiɗaya shekarunsa tara ya tafi karbo wayar Iyayenshi a wurin charge yaran nan suka far mishi sai da suka kashe shi, don Allah masu ruwa da tsaki su shiga cikin al'amarin nan kafin lokaci ya kure!" Kallon juna suka yi shi da Faruq, kafin suka fita. "Allah ya taimake ka, wannan maganar yana cikin wancan file din fa!" Gyad'a kai yayi suka nufi wurin motar, suna shiga ya ce mishi. "Bude abinda na baka!" Ba musu ya bude kafin su bar harabar masallacin, mika mishi yayi ya bude a hankali, ya duba kome na abin kafin ya hada abin charging da motarsu, sannan ya kunna wani irin kara abin ya fara suka fita suna bin motar da kallo. "Koma ciki kawai!" Suka bar masallacin, har kofar gabas suka nufa anan ya kalli Faruq ya ce mishi. "Fito ka duba!" Ba musu ya fito suka duba a a hankali har suka samo abinda aka saka musu. A wurin tayar motar.
Amsa yayi ya kashe sannan ya saka a cikin aljuhunsa, suka koma motar ya ce mishi.
Wannan na'urar da ke hannunka ana kiranta da "Ghost Finder" ko "Pinhole Eavesdrop Jing Detector". A takaice, tana da amfani ne wajen gano abubuwa masu zuwa:
1. Gano kyamarori ɓoye (pinhole cameras) – Wannan na'ura tana taimakawa wajen gano ƙananan kyamarori da ake ɓoyewa domin yin leƙen asiri.
2. Gano na'urorin leƙen asiri (eavesdropping devices) – Idan wani ya saka na’urar leƙo asiri ko bugging device, wannan na’ura za ta iya gano su.
3. Ghost Finder (sunanta kawai) – Kalmar "Ghost Finder" ba ya nufin tana gano aljannu da gaske. Sau da yawa ana saka wannan suna ne don tallata ta, amma aikinta na gaskiya shi ne gano na'urori da ake ɓoye su don leƙen asiri
Ma'anar maballan:
A & B buttons: Wannan na iya zama maballin don canza yanayin aiki, misali daga gano kyamara zuwa gano bugging device.
M Light: Wataƙila tana nuna yanayin aiki ko yawan ƙarfin sigina.
Ƙarshe: Wannan na'ura tana da amfani musamman idan kana zargin ana saka kayan leƙen asiri ko kyamarori a wajen da kake (kamar otal, gida, ofis, da sauransu). Ajiyar zuciya Faruq ya sake yana faɗin. "Allah ya saka maka da alkhairi Yallabai."
Sannan Salmanu Faris ya sauka ya shiga cikin gidansu, A tsakar gida gida ya hadu da Fulani Balkisu, duk da matar mahaifinsa ce amma yadda suke yiwa juna kallon kurilla ya b'aci, dauke kai yayi ya ce mata. "Barka da asuba!" Ya wuce ta amsa bata amsa ba, ita ta sani amma har ya wuce bangaren Mai Babbar daki yana jin yadda take kallonshi. Wani strange feel ya ji daidai zai shiga kofar Mai Babbar daki, juyawa yayi suka yi ido hudu da ita, ta shige abinta shima ya shige. Bakinsa dauke da sallama ya shiga parlourn babu kowa sai Sailuba da take aiki a kitchen, ita ta amsa sallamar ya wuce dakin Mai Babbar daki ya same ta zaune akan abin sallah. Murmushi ta sakar mishi, sai da ya zauna a gabanta ya ce mata. "Ummi na kwanta akan cinyarki? sarauniyar Zanzabira!" Ya fada yana gyara kwanciyarshi akan cinyarta. Shafa kanshi tayi a hankali ta ce mishi. "Yanzu na fahimci dalilin saka maka suna Salmanu Faris bayan sunan da ya dace da kai Usman ne, ashe akwai buƙatar a sake samun jarumi kamar sarki Shago!" Bude idanu yayi ya ce mata. "Waye shi?" Murmushi tayi tana faɗin. "Wani sarki aka yi a wannan Kingdom din over 4yrs ago!" "Descendants dinku ne!" "Ummi manta da shi, ki saka ni a cikin addu'a!" Tattaro nutsuwarta tayi tana faɗin. "Wani abu ne?" Girgiza kai yayi yana lumshe idanunshi, anan ya fara magana a hankali. "Akwai wani yunkuri da nake son yi amma dole ina bukatar addu'arki ne." Daga haka ya cigaba da sauke numfashi a hankali. Kamar mai barci. "Yau Ijlal zata dawo!" Bude idanu yayi tar. "Hm" ya fada a hankali yana lumshe idanunshi. "Baka jin dadin zama da ita ko?" "Ya zan yi da ita tunda kin ce na zauna da ita, ko da tafi haka worse zan zauna da ita balle bata kai haka ba, tsakaninta da abokan zamanta ne!" Yadda yake gaya mata abinda ya shafe shi, yana mata dad'i. "Baka da abokai ne?" "Ummi dole kece ya dace na gayawa matsalata da damuwa ta sai kuma faruq wanda ya zame min nauyi akaina na kula da rayuwarsa." " A ina kuka hadu da shi ne?" "A can Amurka muka haɗu, amanarshi da nagartanshi ya sa nake tare da shi." "Ka yarda da shi kenan?" "Gaskiya sama da yadda na yarda da kaina, daga shi sai Zainab da Nady, waɗannan bayin Allah n yarda da su." Shafa kanshi tayi tana faɗin. "Allah ya maka albarka! Amma yan uwanka fa?" Tashi zaune yayi yana yar yaƙe, ya ce mata. "Zuciyata ta yarda da su yan uwana ne, bata yarda na bawa kowa Amanar kaina ba, haka yasa nake sonsu amma amanata iya Waɗannan mutanen ne sai ke Ummi kaf duniya kece ba zaki iya cin amanata cikin sauki ba, sai idan ya zama dole." Daga haka ya mike yana faɗin. "Zan tafi na shigo gaishe ki ne! Ummi ki kula da abinda kike ci, idan da hali Ikhlas zata na zuwa tana miki abinci."
"A'a ba sai ta zo ba, idan da ban koyi kare kaina ba ai da baka zo ka same ni ina raye ba, sannan kuma tun bayan rasuwar Mai Martaba, na koyawa kaina bin didigin motsin kowa don haka kwantar da hankalinki."
Fita yayi yana girmama jajjurcewa Umminsa, a kofar gidan ya samu Ahmad Rilwani Yayari da Walid Mamman Abba yayari, mika mishi hannu suka yi ya mai da hannunsa baya tare da cewa. "Lau!" Ya wuce wurin motarshi da Faruq yake tsaye. Tawowa Walid yayi ya ce mishi. "Man list to me!" Juyawa yayi yana murmushi. "Me kake son cewa?" "Yazo baka hakuri ne!" Shiru yayi kafin ya kalli Faruq ya ce mishi. "Muje!" Zai shiga motar Walid ya ce mishi. "Kana tsammanin haka zai saka wasu abubuwan su daina faruwa ne? Ya zo baka hakuri ne ba shi ya kawo shawarar abinda suka yiwa Matarka Ijlal ba, sannan ko da suka zo wurin Zainab basu mata kome ba." Takawa yayi gaban Walid yana wani irin daskararren murmushi. "Ban yi mamaki da jin kalmanka ba, but watch your words before let it out!" Daga haka ya juya zai shiga motar ya ce mishi. "Wani lokaci bai zama dole kowa ya zama kamar kowa ba. Amma domin samun wasu abubuwan dole sai anyi wanka da kazanta ka kiyaye kanka da hurumin sallamammu!" Daga haka ya shiga motar zuwa wurin glass din motar Walid yayi ya ce mishi. Kwankwasa mishi yana faɗin. "Kana ta wani famkama kamar wani abu ne kake da shi, kada ka manta Yaron nan Ubansa." Wani irin kallo yayiwa Walid din da bai samu damar karasa maganar bakinsa ba. "Ka manta waye ni kenan?" Mai da kai yayi ya kwanta yayi faruq ya rufe motar suka bar wurin. "Sir akwai wani abu ne?" "A'a kyale su!" "Sir kyale su yasa suke abinda yayi musu!" "Eh na sani amma rashin kyale su zai haifar da tab'a rayuwar wasu!" Daga haka suka cigaba da tafiya ba wanda yayi magana. Yana kawo shi ya sauka ya kalli Faruq kafin ya ce mishi. "Kada ka tafi ka jira ni!" "Ok Sir!" Daga haka ya shiga cikin gidan.

Ina barci na ji an yaye min bargo, "kin yi sallah kuwa?" Ware idanu nayi ina kallon silif din dakina a hankali na tuna ai fa a kasa na kwanta ba a sama ba, a wani speed na mike a gadon tare da dirka a gadon rigar barci jikina sai gajeren wando. "Waye ya mai dani gadon nan?" Dauko wayarshi yayi ya kunna sannan ya mika min, yadda nayi barci har da daura mishi kafa na wani tukwaikuye shi. "Lokacin da kika yi shirin yi min fyade ne Allah ya kwace ni baki lalata min samartakana ba." Wani harde hannu nayi a kirjina tare da yin baya ina faɗin. "Ni ce zan maka fyade? Ni?" Na kara nuna kaina ina yin baya, murmushi yayi ya ce "idan baki yarda ba bari na nuna miki wani abu." D'aga rigarshi yayi sama ya zamar da wandon. "Innalillahi wainnalihir rajoun!" Iya abinda na fada kenan da karfi na fada toilet na rufe kofar da ƙarfi, murmushi ya sake yana faɗin. "Yarinya baki ga kome ba, shi dai sau biyu yana kai miki ziyara!" Buga kofar yayi ya ce min. "Malama ki zo ki rarrashe shi sakamakon abinda kika mishi jiya yace ba zai yarda da ba sai an sammi shi wani abu." "Ni dai ba yar iska ba ce!" Na faɗa da ƙarfi, "ok shi kuma ɗan iska ne gara ki fito tun wuri kafin ya fasa kofar ya shigo!" "Wallahi zan maka ihu!" Na faɗa kamar xan fashe da kuka. "Babu me shigowa domin zaa ce ihun kauna ce babu me damuwa na zungure miki dadi yasa kika fasa ihu!" Rike kaina nayi dama haka ya ke da batsa? "Ni dai don Allah ka kyale ni!" "Idan na kyale ki waye zai bawa abina hakuri bayan kin fusata min shi!" "Sallah dai zan yi don Allah ka yi hakuri!" Na faɗa kamar xan fasa kuka, yar karamar dariyar nishadi yayi ya fita yana faɗin. "Gara ma ki fito ko bata hakuri!" Ya fada yana barin dakin wanka nayi na gyara jikina sannan na fito, na shirya cikin lace bubu, sai da nayi sallah sannan na kafa daurin Zahra buhari, ina mamakin yadda aka yi na makara, waje na fito na samu Nady tana shirin fita, ta ce min. "Yau na tambayi mijinki ya bani aronki mu fita!" "Ina fatan ba sayar da ni zaki yi ba?" "Wane ita!" Ya fada yana shiri shima. Dining table ta nuna mana muka nufi wurin karyawa muka yi sama -sama, ina son mata magana amma nayi shiru. Can dai ya kalle ni ya ce min. "Kamar bakinki nan yana da magana?" "Tun dazun na lura da haka!" Ta fada tana kallona. "Dama kin iya abinci haka?" Tab'e baki tayi tana faɗin. "Eh tow wani lokaci kana koyan abu don kare kanka ne, ke ce kika tuna min nima mace ce, bayan kin kori Brandy!" "Sorry!" "No more apology, domin kin nuna min girma da miji yake da shi a kasarku!" Murmushi nayi na ce mata. "You Are amazing chef wannan breakfast kamar. " "Malama kada ki zage!" Kwalla ce ya cika mishi idanu, dama haka mazan da suke da mata sama da daya suke ji idan aka samu zaman lafiya a tsakaninsu? Safe hannun Nady yayi ya ce mata.." You Are wonderful woman Nady! Ina ki haifa min Yara da zasu dauki halinki!" Tashi tayi ta sumbaci kumatunsa. "Kai na fara so, kuma zan yi farin ciki idan na mutu kai zaka fara saka ni a makwancina! Zainab ta bawa abinda na haifa tarbiyyar gidansu!" Ta fada tana kwashe kayan." Ta bar wurin, kallonshi nayi na ce mishi. "Ka bita mana!" "Kin bani izini!" Harde hannu nayi a kirjina na ce. "Malam jeka bana ciki da gulma!" Na faɗa ina kauda kai, zama ya gyara ya cigaba da shan tea, tashi nayi a hankali na bar shi a wurin, wani lokaci ana bukatar ka bawa mutum damar ya sake numfashi, haka da nayi kuwa ina ga ya haifar da kyakkyawar alaka na musamman. Tana kitchen tana wanke plat ne, amma kuma hawaye na zuba mata wanda ya hadu da murmushi, idan ta tuna sai ta sake murmushi, rungume ta yayi ta baya yana faɗin. "Thank you for choosing me, as your life partner!" Ya kifa kanshi a kafad'arta. "Thank you for everything!" Ya kara furta mata, yana kara jin wani irin tausayinta, "thank you


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login