Showing 255001 words to 258000 words out of 304445 words
yarinyar yar ta'addace!" "Yayata ce Ubanmu ɗaya!" "Allah mai iko,.Allah ya kyauta!" Ya fita, motar Iram da ta zo da shi haka aka fitar da shi daga cikin gidan tare da ita suka kai motar inda Tauhid yake suka bada sako a bashi, sannan ita kuma Faruq ya tafi da ita.
Turawa Abba sako nayi tare da cewa.
*Assalamualaikum Abbana ka gafarce ni sannan ka min uzuri nayi maka wani laifi na gaji da ganin hawaye na zuba daga idanunka yasa nayi haka ka min kyakkyawar fahimta! A matsayina na Fulani Babba daga masarautar Zanzabira na hukunta Iram da laifin yunkurin kashe ni. Ban saka a mata kome ba amma ka yi min uzuri na dauke ta daga cikin mutane da sauran al'umma idan lokaci yayi xan bayyanata Yarka Zainab Junaid Gobir! Wannan ya zama sirri a tsakaninmu*
Kirana yayi yana ta saka min albarka, ya ce min idan na samu lokaci yana son magana da ni, dama ya zuba min idanun ne ya ga zan iya handle wani case ko ina nan a yadda ya Sanni, sai gashi na gama kome cikin ruwan sanyi. Ban yarda na yi wasa da damata ba, na nutsu na zubawa kowa ya idanu.
A bangaren Ijlal dama ta kira Iram ce su san yadda zasu magance matsalolin da yake gabanta musamman na cikin Nadiyyah, sai gashi cikin wani irin yanayi Babu Iram babu dalilin. Don haka ta kira aunty Fa'iza ta gaya mata da yake basu da man kai, matar nan ta ce mata maza ta san yadda zata yi za'a kawo mata magani ta zubawa Nadiyyah a cikin abinci domin cikin ya zube, tsoro yasa ta kasa ai watar da kome, koda aka kawo mata magani kasa amfani da shi tayi to taya zata yi amfani da shi?
Da yamma na shiga bangaren Bayi na samu sun taru wuri guda suna ta aiki bakiɗayansu. Wildat tana rike da wayata na tsaya ina mai kallonsu yadda suka zube suna gaishe ni. Jakadiya tare da uwar tuwo suka fito suna cewa. "Barka da zuwa Fulani Babba, bari a kawo miki kujera!" "Barshi Jakadiya!" Na fada ina kallonsu. Kafin na ce musu. "Ban zo nan don na ganku ba, na zo ne domin na muku kashedi guda uku. Na farko babu ruwanku da shiga sabgar iyalin Mai Martaba abu daya kuke yi aikinku! Na biyu kada na ji ko na gani an zauna ana gulmar wata ko wani abu! Na uku kada na ji ko na gani wata an hada kai da ke an cutar da wata a cikinmu, Faruq ka musu magana da Hausa!"
"Duk wacce aka kama ta da laifin saka idanun a cikin gidan Mai Martaba hukuncinta shine bulala dari , na biyu kuka zauna kuka yi gulma za a kai mutum gidan Yari na tsawon wata shida da aiki me tsanani, na uku aka hada kai da ke aka yi wani abu tow hukumcin da zai biyo baya ba zai yiwu kowa dad'i ba." Sannan ya koma kan Jakadiya ya ce mata. "Jakadiya aikinki, shine ki yiwa Bayi jagora da isar da wasu abubuwan, Jakadiya idan wani abu ya fito har da ke a cikin hukuncin don haka ki gaya musu wannan sabon dokar Fulani Babba ce su kula da kansu da lafiyarsu.
Tabbas tsoro ya shige su ainun, tsoro na hango a cikin idanunsu. Shiru Ijlal da zuwa Iram ba ƙaramin hana ni barci yayi ba, don haka duk tsoro ya hana sakewa shi yasa na fara kashedi akansu. A hankali na koma bangarenmu, kowacce ta kama kanta a bangarena Wildat kaɗai na rike daya yarinyar ma na kyaleta nace iya Wildat nake bukata, haka yasa itama yarinyar ta zama kamar wata makusanciyata. Sannan na gaya mata idanuna na kanta da motsinta.
Cikin ikon Allah lokacin bautar kasarmu ya zo, don ma ana ta samun wasu matsalolin da yasa bamu tafi ba, a wannan lokacin Yeemar cikinta yayi kwari, ranar ta zo mana wuni, tana ganin nadiyya da ciki sai da ta kasa boye damuwarta, nayi ta dariya ina faɗin. "Ke bestie haihuwa ta Allah ce idan ta haihu kamar ni ce na haihu kada ki damu wallahi!" Haka tayi shiru bata ce min kome ba, amma ranta ya nuna min bata ji dadi ba, tow ya zamu yi ita ta yiwa Faruq bayani, da Yazid ya zo ɗaukarta nayi mishi godiya sannan suka tafi. Bana jin zan yi kuka da rashin haihuwa musamman yadda Nady take alakanta ni da Babyn sai.na ji ina son babyn har cikin raina. Amma ba yadda xan yi tunda dole sai Allah ya baka kafin ka same su.
Faruq ya gama min kome ya amso min kome ni da Yeemar aka tura mu Gombe, ba sai ga bawan Allah yana ya fushi ba shi fa bai ji a ransa na tafi na bar shi ba, haka shima ya haɗa wani tafiyarshi, wai zai je ziyarar gani da ido ga masarautar Gombe, a raina na ce wannan shine namamajon gaskiya,, sanin cewa Nadiyyah tana fama da kanta bata son hayaniya saboda yadda jininta yake hawa idan ta dan shiga damuwa haka yasa bakiɗaya muka tsani ko kara ne, abin mamaki ba sai ga masu algaita ba, sun shigo sun fara busa da kade-kade ina cikin hada kayana fa. Mamaki ya cika ni na leko ta window na ce.."Sarkin dogarai! Maza a sallame su ba a son kara da hayaniya!" Tasowa yayi da gudu yana faɗin. "Allah ya baki lafiya da nisan kwana ranki ya dade Fulani karama ta gayyato su!" Fitowa nayi waje cikin d'aga murya na ce. "Kaiiiii!" Zubewa suka yi akan gwiwarsu, "Allah ya huci zuciyarki!" "Ki fita daga cikin gidan nan kafin na saka ayi waje da ku!" "Babu inda zasu Hajiya mai gadara!" "Sarkin dogarai ayi waje da masu busa!" "Sarkin dogarai idan suka fita sai na hukuntaka!" Dariya nayi na ce da ƙarfi. "Securitys" ba musu suka iso inda nake. "Ayi waje da su kuma a hukunta su sakamakon kin bin umarnin Fulani Babba, na farko kenan, na biyu shigowa cikin harimen Mai Martaba ba tare da izinin Fulani Babba da Giwar sarki ba. Na uku a rufe su na tsawon wata uku saboda d'aga Giwar Sarki daga barci Bayan an hada ko karar mota ce a cikin gidan balle har ayi busan algaita da kakaki tare da ganguna! Wanna shine hukuncin da na zartar a cikin gidan nan matsayina na Fulani Babba!"
"Aikin banza aikin wofi sai dai a kare da mulki amma haihuwa sai dai a ga muna yi.....
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: *Assalamualaikum, ina ganin ra'ayinku sosai, sai dai ku sani wannan labarin ba just irin sauran labarai ba ne. Musamman role din Zainab da Ijlal and Nadiyyah! Duk yadda xan yi fashin baki matukar ban isa inda nake so ba zai bada ma'ana ba. Duk yadda kuka so ko na so dole labarin nan yana da karshe amma mafi muhimmanci a labarin sakon ya isa inda ake bukata, dayawanku kuna son Zainaba ta haihu, with time zata haihu amma babban damuwata shine mu isa inda ake bukata! Kuyi hakuri idan babu manta ba labaruna basu wuce 82 yau gani har 84 so don Allah ayi hakuri ina jin dadin comments din ku musamman yan comments section 😂🤣👍🏿Sai da ku fa wallahi. Allah ya saka da alkhairi na gode sosai da alkhairinku!*
Takawa nayi gabanta na wanke ta da mari, ta kara d'agowa na kara kifa mata mari. "Ki godewa Allah kina shayar da yarinyata, da sai na tsiyayyar miki da idanu. Kuma ki tattara kafarki, ki koma dakinki wallahi kika sake wani hauka sai na fasa miki baki!" "Mrs Yayari!" Na ji murya matar da take kula da Nadiyyah da sauri na juya gare ta ina tambayarta. "Lafiya Juliet?" "Madam Nadiyyah zo ki ganta!" Juyawa nayi na kalli Ijlal sannan na ce mata. "Sai ki san Yaren da zaki mishi, idan ya rasa matarshi da dansa!" Na juya na bar wurin raina a soshe don har ga Allah, maganar Ijlal da ta gaya min ya min ciwo amma kuma halin nady take ciki yafi d'aga min hankali, ina zuwa dakin na same ta cikin wani irin yanayi, ba zan iya ɗaukarta ba amma kuma zamu iya kamata, ganin mun yi ƙoƙarin haka abu ya citura kawai na kira shi. "Doctor kazo akwai matsala a gidan!" "Lafiya?" "Please ka zo!" Ina fadar haka na kashe wayar, tafiyar minti goma ya kawo su shi da faruq, zai shiga wurina Sarkin dogarai ya gaya mishi tana wurin Nadiyya gabanshi ne ya fadi, ya shigowa zai magana na ce. "Dauketa bamu da lokaci!" Haka ya dauke ta muka fita a wani irin yanayi, asibiti aka wuce kusan, Dr Munirah ita ce likitanmu bakiɗaya haka yasa muna zuwa ita ce a tsaye akanta ita da, gani har shi muna cikin tashin hankali. Kallon Juliet yayi ya tambaye ta ba'asi, dafe goshina nayi domin dai abinda ta sani ta faɗa, yadda na defe kaina da hannu bibbiyu yasa shi kiran Faruq ya bincika mishi me ya faru, to ya ce mishi ya fita can sai gashi ya sunkuya kasa yana mishi bayani mikewa yayi a fusace na rike hannunshi. "Sake min hannu!" Janyo shi nayi tare da zaunar da shi. "Kasan me yasa Allah ya ce ku maza ne a sama da mata? Saboda kaifin basirarku da tunaninku, ba irin namu ba ne, idan har ka ce zaka lankwasa Ijlal karyata zaka yi kuma ba zaka tab'a samun biyan bukata ba, me ye amfanin tursasawan? Tabbas abinda aka gaya maka gaskiya ne amma meye ribar da ka cimma akan abinda tayi?" Murmushi nayi na ce mishi.
"Rufe sirrinka hikima ce; amma tsammanin wasu su rufa maka shi, wauta ce. Fushinka ci bayya ne tsammanin wasu su tunzara ka kuskure ne, ka yi duk yadda ka zaka yi amma ka sani da zarar ka nunawa Ijlal Nadiya tana bukatar kwanciyar hankali kamar ka bata gudummawar izza wuta a cikin gidanka ne, tunda tayi zata yi tsammani zaka yi magana kayi magana ta maka rashin hankali kuskure ne babba gara ka hakura ka bita da idanu, ni da na mata iya abinda zan yi amma idan ka rena nawa ka yi naka hukuncin!" Na fada a sanyayye, janyo ni yayi yana shafa bayana. "Allah kada ya nuna min ranar da zan juya miki baya Nagode Zainab ke haske ce a rayuwata ki yi hakuri da halina!" Murmushi nayi na kwantar da kaina a kafad'arshi, haka suka kwashe kusan awa uku akanta kafin Doctor Munirah ta fito tana faɗin. "Sir gaskiya Nady ba zata iya rike cikin nan har 40 weeks ba, ina ga zamu mata CS a 37 to 38 ko kasa da haka, domin cikin yana girma yana kara mata hawan jinin ne, a yanzu zamu riketa na tsawon wata daya anan domin inda take babu tsaron da ya dace." "Shi kenan duk yadda kika ce!" Haka suka fito da ita zuwa can Amenity aka kwantar da ita. Wannan lamarin ya dame shi sosai, murmushi nayi lokacin da na ga fetur din yake juyawa a cikin cikin har kana iya hango yadda ya saka hannunsa da kafarsa ne, da sauri na dafa Uban ina nuna mishi, hada hannuna da nashi yayi muka tab'a wurin hawaye ya zubo, ko sai yaushe Allah zai nuna min wannan Dreamland din. Rungume ni yayi yana faɗin. "Idan da rai da rabo wata rana kema haka zamu ga naki!" Sumbatar kumatunsa. "Allah yasa!" Ya ce min Amin, haka muka zauna sai yamma can Mai Babbar daki da su Bilqis suka zo ban da Aneesah, ganin yadda muke nanike a jikin Nadiyyah kamar zamu shige cikin Mai Babbar daki tana zuwa ta rike kunnenmu daga ni har shi zata fito da mu waje nayi maza na ce mata.."Ummi takawa ne fa taimaka ko sake kunnensa kada al'umma Zanzabira su fuskanci fushinsa." Sakewa tayi tana zungure min goshi. "Kema ya mai da ke irinsa, yanzu haka kuka saka dan tayi a gaba kuna wasa da shi anya ba za a auna min kanku ba!" Ni da yake na mai ita rabi kaka rabi uwa nace mata. "Allah ya kawo mu zamani idan ban yi wasa da Babyn ba da wa zan yi? Tunda bani da abokin wasa sai baby!" "Allah yasa ki girma!" "Amin Ya Allah! Na zama katuwa!" Fitowa muka yi domin ta fara motsi. "Me ya faru ko dazun da safe ta kira ni mun yi waya fa!" "Inji kubra tana faɗa, don tana odar kayan jarirai daga China, kuma ko ni na saya a wurinta, tana ta min tsiya ko ina da ciki ne na fara tanadi dariya na tura mata na ce mata im still baby. "Wallahi ta sayi wasu kayan da aka shigo min da su, kawai ta ce min zata kwanta kanta na ciwo idan ta tashi zata turo min kudin, ashe abinda zai faru kenan" haka suka yi ta jajjen, jan Mahaifiyarshi gefe yayi ya gaya mata abinda ya faru, sai da ta mike ya ce mata. " Zauna Ummi, idan muka ce zamu yi kaf-kaf da Nadiyyah Ijlal ba zata daina ba, don haka muna kokarin ta kwana biyu a nan asibiti daga baya ta koma gida don sun ce wata takwas da sati biyu zasu mata aiki! Kasa motsi mai babbar daki tai haka suka bar maganar, amma kana ganin Mai babbar daki kasan a fusace take da zasu koma gida na bisu. Gaskiya ban damu da ya dawo gida ba, na bar shi ya zauna a can saboda yadda take din ya kula da ita. The next day kuwa da yake ya kwana a can na tafi bangarenta ni da Jakadiya muka tsaya aka kai musu abincin asibiti, a ranar iyayenta suka iso ni kuma daga asibiti na wuce gida nayi musu sallama na gaya musu halin da nadiya take ciki, anan aka tawo da Hajiya Altine Kanwar Baban Nadiyyah, mace mai addini da dattako domin a ranar da ta zo take gaya min ita fa tana azumi, ai kuwa ina komawa gida bangaren Nadiya na bada umarnin ayi mata abin buda baki a kai asibiti, sai ya zama da Hajiya Altine da Juliet suke kula da ita har lokacin barci take jinin kuma yana ta sauka, a kanta na fara ganin irin wannan cikin,a raina na ce Yaron cikin tun bai zo duniya ba yake gwada shi basarake ne.
Iyayen Nadiya suna nan da xan tafi Gombe na je nayi musu sallama har da ita Nadiyyah da take barci haka nayi ta kuka, tausayi take bani, ashe rashin kunyar karya Ijlal take ina nan bata yi wani motsi ba, sai da na bar garin ta shiga asibitin ta fara musu rashin kunya da hayaniya a bakin kofar Nadiyyah, Uban Nadiyyah bai san Ijlal ba ni ya sani ba sai ya kira Kwamishinan yan sanda ba aka zo aka kama Ijlal, wannan abin ya faru a ranar da na bar garin, mijinta yana fada aka kira shi aka gaya mishi, commissioner of police ya kira shi don suna mutunci sosai, domin a haka da yake sarki idan abu ya shafi na aikin ƙwaƙwalwa a cikin manyan mutanen yana iya ajiye aikinsa ya musu ba don kome ba, sai don ƙara ƙarfinsa ko yaya dole ka sadaukar da wani lokacinka, mafi yawan lokutan da yake aikin dare ne, ko kuma ya saka ayi aikin yana gani, haka ya sake kara mishi kusanci da mutane kai ta kai ko mutum ne dansa yana shaye-shaye idan ya haɗa shi da Salmanu Faris sai ka ga an dace. Wannan yasa kafa kanshi a gwamnatin kasar. Yau ko Fada bai je ba yana can yana mitan zainab tafi ta barshi aka kira shi. Yarinyar nan sai ta zubar mishi da kima hankalinta zai kwanta, haka.yasa shi kiran Zainab ya gaya mata, hakuri ta bashi tana kuma nuna mishi muhimmancin hakuri, taya zata so ya sake matarshi ita bata yi alkawarin ɗaukar Yarinyar ba har ga Allah, haka yayi ta fada yayi ta fada tana bashi hakuri ya rasa gane yadda zai rabu da ita ko don rayuwar Amirah ya dace ta kula da kanta, shawarar da Mai Babbar ta bashi shine ya ji ya mishi daga nan bai zame ko ina ba sai headquarters na police, aka gama kome bai ce mata cikanta ba, sannan Mahaifin Nadiyyah ya saka hannu ta saka hannu, haka mahaifinta yasa hannu. Da zasu fito zata bi Salamanu ya nuna mata babanta. "Mun gama magana da shi." Dama Amirah madara take sha ya dauki Yarshi suka bar ta nan ba fada ba zagi, suka dawo yarinyar da bata cika wata biyu ba amma tana ganin rayuwa, haka Mai Babbar daki ya dauki yarinyar tana jin tausayinta. Ita kuwa Uwar Ubanta yayi gaba da ita yana kaita gidanshi, ya tara Matanshi da Yayunta suka mata shegen duka, sannan ya ce musu. "Kada naji kada na gani wani ya bata abinci a free sai tayi aiki ku san mata kamar yadda zaku bawa almajiri, ina son almajiri yafita daraja a idanunku, yarinyar ki ci ki sha ki saka suturan arziki, amma ki ce ba zaki zauna lafiya ba karya kike, na gaji da lalata min rayuwa da Mardiya take yi idan da tana son ahalin masarautar Zanzabira me yasa ta ki biyayya ga Mahaifinta ta ce Attahiru bai da arzikin da zai riketa ba zata aure shi ba tunda ko ta aure shi bai da arzikin da zai rike ta, yanzu don ta cusawa Maryamu haushi shine zata fake da ke tana lalata miki sauran kimarki, shegiya ke idan da Uwarki tana raye zai duniya ta ji kansu da Mardiya. Duk abinda nake Uwarki hakuri tayi da ni, don ubanki na bi mata na sha giya na dake ta, bata taɓa hanani yadda ke so ba, mata nawa na aura akanta amma dai-dai da rana daya bata ta tab'a cewa kada na kwana a dakinsu ba, sai ke yar