Showing 75001 words to 78000 words out of 304445 words
daga can wajen masarautar aka gano wuta ne ya kama a cikin gidan aka yi cikin gidan aka niman a gaji, sai dai abin mamaki duk wanda ya zo wurin ganin Ikhlas zai tsaya dole aka shiga niman a gaji, lokacin da Faruq da Salman din suka iso sun same tana a yadda mutumin ya ajiye ta, daukarta yayi cak ya kaita parlourn mai babbar daki, aka shiga bata a gajin gaggawa. Sai da aka fitar da ita daga gidan zuwa asibiti, sannan aka samu ta farfaɗo, sannan aka mata alluran barci ta koma.
A can gidan an kashe wutar, sannan aka samu aka ga wurin dai yayi kama da ana wani mugun abun wurin a hankali aka fara samun takalmar Yara da kayan Yara kananu musamman Yaran bayin da suke b'ata a cikin gidan, ba karamin tashin hankali aka shiga ba domin lungu yana cikin gadon Alhaji Rilwanu Abubakar Yayari. Kafin zuwa gobe da safe kamar an rufewa mutane baki dole suka Manta da abinda ya faru.
Washi gari
Ni bana ce na tuna abinda ya faru ba, sai dai zuciyata tana cikin wani irin tsoro. Domin kuwa abin da na gani ya tsaya a raina da kaina. "Me kika gani a wurin?" Abba ya tambaye ni. "Abba bana ce ba, amma na manta fa." Na faɗa ina zare idanu. Shigowar shi yasa Abba ya mike, suka kara gaisawa. "Ya ake ciki?" "Muje waje!" Suka fita, kallonshi Malam Junaid yayi ya ce mishi. "Ya ake ciki?" "Ana zargin Ikhlas ne da saka wutar!"Faruq ya fada mishi yana kallon dakin Ikhlas din. "Kana nufin bayan ta saka ta suma?" "Shine abinda har yanzu muka kasa fahimta, amma kuma a rahoton Autopsy dinta ya gwada ta suma sanadin ganin wani abun tsoro ne, "Me ta gani to?" Abba ya tambaya a hankali. "In sha Allah, haka ba zai kuma faruwa ba." Faris ya fada a hankali, yana kallon window dakin, haka kawai sai yake blaming kanshi.
Nady
"Ni dai ayi kome amma kada sunana ya fito, yarinyar nan daga zuwa zata fara min iyayi... (Ayi min hakuri uzuri ya sha kaina)
*My Book isn't Free 500₦*
Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: Kwana ɗaya nayi aka sallame ni, wanda a gida na cigaba da dama da ciwon kai da jiri,har zuwa lokacin da na warware bakiɗaya, ina lura da irin kallon da yake min, ko kallon tuhuma ce ko zargi ne ni dai ban sani ba, sai dai nayi ƙoƙarin share batunsa. Ranar Monday ina kwance a kan abin sallah bayan sallah asuba, ina jan casbi ya shigo kallo daya nayi mishi na lumshe idanuna. Yana tsaye a bakin kofar can dai da ya ga ba kula shi zan yi ba ya ce min. "Faruq zai sauke ki a school!" Daga haka ya juya wannan mutumin da jin kai yake, murgud'a bakina nayi ina me gyara kwanciyata. Karfe tara na shirya sannan na fito na nufi waje, daidai matarsa tana fitowa itama zata fita, kusan ina gaba tana baya ina jin tana faɗin. "Mace sai dai ta zama hoto a gidana." Juyawa nayi ina kallonta murmushi nayi mata ban kulata ba, n a shiga motar da aka bude min ba zan iya kulata ba. Ganin Faruq ya buɗe min kofar kuma na shiga, kallonta nayi na mata wani alama da hannuna.(🖕🏻) Yadda na mata yasa ta sake wani irin ihu, nima na rama ta ji yadda kowa yake ji, haka na tafi ya ajiye ni, karfe hudu ya zo ya dauke ni.
Sai dai me? Muna komawa bangarensu Mai Babbar daki ya kai, ban tab'a jin labarin ko gani yadda ake cin zarafin mutum kamar yadda yau Mai Babbar daki tayi min, ina durkushe a gabanta ita da Yaranta suka gama min diban albarka, hawaye ke zuba min, cikin kuka nake faɗin. "Ni ban ce ina son zama da shi ba, shi ya zabe zama da ni, asalima ni ina da wanda nake so." Daidai shigowarshi, "Ni na gaya mishi gaskiya bana sonshi ya kyale ni nayi rayuwata, amma haka bai saka ku gane cewa ni bana sonshi. Gashi nan ya zo ki tambaye shi idan wani abu ya tab'a hadi ni da shi, yana can da Matarshi ina wurina, sai da soyayya ake rayuwa idan babu soyayya tow meye ribar zama inuwar wanda baka so, nima fa Y'a batun makaranta da abuna ya ganni idan aka hana ni zan hakura amma ace za a soke min niman ilimina, zalunc..." Tass na ji ya dauke ni da mari. "Watch your words!" Tunda ya danna min mari na rike fuskana, ina kallonshi. "Me nayi da zafi kaza mare ni?" Na faɗa hawaye na zuba min. "Me nayi maka zaka mare ni?? Don ina da bakin kwatarwa kaina yanci sai na zama abin wulakantawa? Akwai Allah kuma yana magadakata!" Na suri jakata na barsu nan zaune. Abinda yayi min yasa Mai Babbar daki jin gamsuwa don haka ta dauke kai tana faɗin. "Ban ga amfanin zama da ita ba, tunda bata sonka kuma kai ma kasani gara a rabu kada ta cutar da kai!" Juyawa yayi ya kalli Nady da take zaune tana murmushi. "Yarinyar bata da kunya, idanunta ya bude sosai rashin tarbiyyarta yana kara samun haɓaka ne saboda My Babe yana kulata." Mikewa yayi ya bar su anan sai da ya isa bakin kofar ya cewa Nady. "Matata ce, ban mare ta don ta ce bata so ba ne, na mare ta rashin kunyar da take yiwa Mai Babbar daki yasa na mare ta, and daga yau kada na kara jin kin shi rigimarmu da ita."
Fita yayi tare da Faruq, suka biyo bayana ni daya kamar mayya haka nake tafiya ina kuka. Shan gabana suka yi ya fito da wani irin sauri. Ya zo ya fisgo ni ya tura a motar. "Ka kyale ni!" Na faɗa ina kokarin fitowa daga motar, ya danna ni sannan ya shiga bayan suka bar wurin, cikin gidan muka koma. Faruq yana tsayawa ya fisgo hannuna muka nufi cikin gidan, har gaban mai babbar daki ya kai ni ya ajiye ni. "Bata hakuri!" Wani irin kuka na fashe da shi. Ya juya ya kalli Nady da take parlourn! "Zaki iya fita" ya nuna mata hanya ba musu ta fita don ta lura ya gama cika hanyar fashewa yaƙe. Ba musu ta fita tana murmushin keta. "Ummina gata ki yi duk yadda kike so da ita. Ya ciro biro da yar karamar memo ya ajiye a gabanshi. "Ummina ki umarce ni da kome xan aikata!" Ya tura takardan da biron gabanta. "Idan ka sake yanzu sunana ne zai lalace, kuma za ayi ta bina da sharri. Ka ajiye ta nan da wata biyu zaka auri Yarinyar da zata so ka kamar hauka, wacce zata haifa min jikoki masu tarbiyya, wacce ta samu tarbiyyar da ya dace, wacce zata wanke min raina da abinda wannan yarinyar take yi. Sannan ka kira min Ubanta da Uwarta su zo nan na gaya musu abinda Yarsu take min." Da wani irin nauyin zuciya yake kallon Mai Babbar daki. "Faruq!" Ya kwala mishi kira da ƙarfi wanda tunda yake bai tab'a mishi irin kiran ba. "Kira Malam Junaid kace yazo da Matarshi!" Mai Babbar daki ta fada tana kallon yadda na firgita, a duniya ina tsoron fushin Allah ina tsoron fushi iyayena. Jikina har rawa yake na rarrafa gaban Faruq cikin kuka na ce mishi. "Don Allah kada ka kira Maluma kada ka kira Abba, na yarda duk abinda mai babbar daki ta ce zan yi! Na rantse da Allah zan yi kome ta ce don Allah kada ku kira su don Allah! Maluma bata da lafiya don Allah kada ku kira ta." "Kada ka kira su!" Naji ya faɗa, "idan bai kira su ba sai dai ka sake ta ashe rashin kunyar karya take kira su." Ta daka musu tsawa, "Ummina don Allah!" Ya fada a raunane. "Kira su!" Ta fada tana mikawa Faruq hannu ya bata wayar, kira yayi ya mika mata. "Junaidu ka zo kai da Hajara, ka ga irin abin kunyar da Yarka take min." Iya cin zarafi Mai Babbar daki tayi min, haka nake kuka ina juya kaina, bayan kamar minti talatin suka iso har da Ya Abid. Tunda suka iso Mai babbar daki ta ke basu labarin abinda ban aikata ba, kawai don ta kuntatta min. Tsaf suka gama sauraronta, Murmushi Abba yayi ya ce mata. "Bata kyauta ba, sam bata kyauta ba, ban yi mata irin wannan tarbiyyar ba. Amma haka ba yana nufin duk abinda abokiyar zamantakewa ta fada shine gaskiya ba, Maryamu ni mahaifin Zainab ne, na sani bata jin magana, akan mijinta ne zan yarda bata dauki nasiha ta ba."
"Malam me yasa zaka ce haka? Ina farin ciki Allah ya dauke mun ita ya kawo ta gidan aurenta yarinyar nan zata wulakanta gidan aurenta da danginsa? Wallahi Billahi azmin idan kika kashe aurenki, sai dai ki nimo wata Uwar na gaji da maganar da nake ji akanki. Kafin ki yi aure bamu huta ba, yanzu kin yi aure bamu huta ba gaya min kashe mu zaki yi ne?" Ta taso tare da rufe ni da duka ta ko ina take dukana tana faɗin. "Ko jiya na gaya miki, ki yi hakuri da rayuwa kika ce tow amma baki ji ba, wallahi idan kika sake aka kara kiranmu akanki!" "Idan kin kashe ta sai ki kwantar da hankalinki. Zainab tana da taurin kai baya daukar reni, haka yasa na yarda bata kyauta ba, amma batun abinda kike fada Maryamu ni ba sakaran uba bane da xan wofantar da Y'ata kema uwa ce. Kuma nasan wata rana haka zai zo gabanki, Salmanu Faris! Idan baka jin dadin zama da ita sawwake mata." Ya fada yana tsare shi da idanu. "Ka ji in gaya maka Zainab bata kyauta ba. Amma haka ba yana nufin bana kaunarta ba ne, idan ka sake ta kafin nan da wata uku Allah da girma yaƙe zata samu maza sama da goma da zasu aureta." Yana fadar haka ya mike. "Akan danki kike yaki, akan Yata na shirya fada da kowa! Muje Hajara kuma kasa ki sake ki fada mata wata magana akan Zainab zan muzanta miki!" Ya tsaya a gaban Faris ya ce mishi. "Kai na aurawa Zainab bayan mahaifinka ya bukaci haka, ba matarka ko Mahaifiyarka ba, idan bata maka ba kasan akwai masu bukatar ta kuma suke son aurenta a duniyarsu da rayuwarsu. Idan aka kara kirana domin Zainab zan yanke duk wata alaƙa da take tsakanin Attahiru da ni Junaid!" Daga haka suka fita suka bar ni a gaban Mai Babbar daki da kunya ya kamata, suna fita ta fara faɗa tana faɗin. "Ka ga irin gidanta ba?" Yadda take shi ba nan take fita ba sai da ta min zagin kare dangi, sannan ta ce. "Ku b'ace min da gani na!"
A can mota kuwa Abba fada yayi tayiwa Maluma ya ke gaya musu wacece mai babbar daki idan bata sonka tow ka shiga uku, don bata son Zainab ba zai wulakanta kanshi ba, domin abinda Maluma tayi kamar haka ne. Hakuri ta bashi ita sai yanzu ta fahimci haka idan rashin kirki ne taya za a ce mutum daya kullum yake faɗa wane yayi kaza..
*
Tunda muka nufi gida na kifa kaina a cinyata, ko don Abba dole na daina fada da kowa, haka nayi ta kuka duk da wani gefe kukan farin ciki ne yadda Abba ya nuna min bai yarda da abinda ya faru ba, har muka isa na fita dauko min jakata yayi ina shiga cikin parlourna na zube na cigaba da kuka lokacin ana kiran sallah Magariba. Ajiye min jakar yayi ya fita.
N a rasa waye zan gaya mishi abinda ake min, daki na shiga nayi sallah sannan na fita na haɗa tea na sha,.duk da kaina yana ciwo. Ina gamawa ana kiran sallah isha,.ina yin sallah na kwanta ko wanka ban yi ba,.Data na bude ina kallon sakon da yake shigowa a Whatsp dina, sakon Uwais ne ya shigo wayata. "Matar Manya?" Hawaye ne ya cika min idanu, na shiga sakonshi na danna voice ina shashekar kuka, ina gaya mishi halin da nake ciki, nayi sakon hamsin na sake mishi. Ai kuwa yana jin muryata, sai ga kiranshi. "Autar Maluma?" "Na'am!" Na amsa cikin kuka, "kina ina yanzu?" "Ina dakina!" Na faɗa mishi. "Me ya faru?" "Kasan bana sonshi?" Na faɗa ban sani ba ko maganata ce ta zo mishi a bazata ba amma naji yadda ya rud'e wato shima maganar ya dake shi. "Ina jinki" "don Allah taya zan boye abinda zai cutar da ni, Hmm kasan ba zai yiwu ba amma haka ya mare ni tare da gaya min magana bayan wanda Mamanshi ta min."
"Ni dama nasan za a yi haka." Ya fada nan nake gaya mishi har dukan da Maluma tayi min, sai da yayi ta fada yana gaya min nayi hakuri. Daga nan ne muka shiga hiran yaushe gamo, sai wurin karfe biyu saura ya bar ni na kwanta.
Wannan abun da ya faru ya kara min ilimi akan Wacece nake zaune da ita, makaranta kuwa bana jiran Faruq domin na fahimci tana son ganin zan rabi kayan mijinta ta hau gaya min magana, ranar da ta gaya min magana har cewa. "Aje wurin tsohon da yake daurewa yarsa gindin tayi iskanci a gidan mijinta ya saya ba dai motar mijina ba."
Murmushi nayi na ce mata. "Dama ban ce zan shiga motar Mijinki ba, ni bana kula irinku domin baki san kanki na har yau!" A ranar na daina shiga motarsu, kuma na ce Faruq kada ya gaya mishi ya kyale zancen bana son a kara tab'a min mutuncin Iyayena. Wani lokaci idan ina zaune a harabar gidan ina ganin wanda suke kawota, wani lokacin shima yana ganin zasu kawo ta bai tab'a magana ba, sai ranar da Tauhid ya kawo ni gida, sannan ya shigo na bashi ruwa ya sha. Ranar na ga bala'in da ban tab'a gani ba domin shi baya gida, ita na samu a gidan, tana kallon yadda muka shiga Tauhid yana rike da jakata tana jin yan kirana da Aunty Ikhlas, don rokona yake akan na ara mishi kudi, ina mishi dariya na ce mishi. "Ba zan baka ba, ka dawo kirana Zainab tsohuwa talo-talo ta hana mata shiga gari!" Ya ce min. "Allah ba zan fada ba!" Ina bakin get din makaranta ya kira ni wai na bashi aron dubu goma. Idan nace muku ba ma shiri da Tauhid nayi karya a da ina gida duk wani abin da ya shafi wayata laptop dina bankina Yaron nan ya sani kuma duk da haka bai tab'a min wani abu na rashin ji ba duk da ina jin Iram tana fadar yana kwashe mata kudi ta banki. Dariya nake musu domin itama tana da bala'in rowa. "Dubu goma kawai Gimbiyar Zanzabira!" "Tauhid ban da matsi ta kama ka ai nasan ba zaka tab'a zuwa ba." "A'a Abba ya gaya min bakya jin dadin gidan aurenki ne,.yasa naki zuwa don zan iya baje mutum ya miki abu akan idanuna."murmushi nayi mishi side hug, parlourna muka shiga na fara kwaso mishi abin tab'awa, sannan na ajiye mishi wayar. "Ka shiga ka tura abinda yayi maka ban sauya password da kome ba. Ka diba iya yadda kake so idan ma rabawa zaka yi Bismillah ka ɗauka na fada ina shigewa dakina. Ruwa ya sha sannan ya dauki wayar ya bude data. Sakonnin Uwais ya gani , ya juya ya kalli kofar a hankali ya buɗe. *Kin san ina sonki*
*Zan cigaba da sonki! Please mu hadu a wani wurin!* Fita yayi ya koma kan Apps din, sannan ya cigaba da zaman jirana har kusan minti talatin, sannan na fito da abin sallah ina kallonshi fuskar shi babu fara'a. "Ya Ikhlas! Ki rabu da Uwais, kin ga da aurenki na ji kunya na ji babu dad'i, idan Mommy da Iram sun lalace tow don Allah kada ki fisu lalacewa kin ji!" Ya fada min yana mikewa. "Sorry Ibrahim! Na daina." Idanuna suka cika da kwalla. "Ya wuce kin san girman soyayyar da Abba yakewa Aurenki? Kada ki yi abinda zai juya miki baya, na dauki dubu goma na. Sannan kada ki illata rayuwar aurenki da wannan abin zai iya shafar martabar Aurenki domin idan Mijinki ya gani zargi zai bayyana a zaman ku koda baki sonshi its okay amma ya fahimci da Aurenshi kina dater wani guy zai shiga damuwa kuma zai ji ciwo sosai ni idan ni wallahi sai na kashe gayen Please im trust you, na sani har da sharrin shaidan ki kore shi ko fatattke shi Allah zai kare ki daga fadawa komarsa"
"Allah baka isa ba!" Fita yayi da gudu na biyo shi a main parlour muka hadu da Mai babbar daki ta shigo gidan a fusace. Gaishe ta yayi nima na gaishe ta na ce mishi. "Wallahi baka isa ba Tauhid sai na kara maka." Da gudu ya nufi Motarshi yana fita ashe su Faruq ne suka kokarin shiga dole suka yi baya, na karaso har bakin get din ina d'aga mishi hannu. Wani irin farin ciki nake ji, juyawa nayi na ga ya tsaya a hanyar da xan koma. Rab'a gefenshi nayi ya ce min. "Wani d'an iska ne kika kawo min gidana?" Sororo nayi kafin na tab'e baki na wuce shi dawo da ni gabanshi yayi yana faɗin. "Waye shi?" Wani irin bakin ciki ne ya cika min rai da b'acin rai na ce mishi.."Ibrahim Junaid Gobir Tauhid daga shi sai ni, my blood brother!" Na faɗa hawaye na zuba min. "Shi shakiki na ne, Muhrramina ne, ko na mutu yana da ikon tsayawa akan gawata! Jini daya ya samar damu!" Maganar Tauhid ya tabbata yanzu yake min fada ashe ya san irin haka zai faru fisge hannuna nayi,.wanda shima ya saka shi