Showing 81001 words to 84000 words out of 304445 words

Chapter 28 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

89

gadon na dafe kanshi da ina jin yanayin zafin jikinshi. Juyawa nayi zan fita ya rike hannuna. "Kira Faruq." Da sauri na fita, na duba Faruq din waje nace mishi. "Ka zo inji Boss dinka!" Na faɗa ina nufar cikin gidan, kusan a tare muka shiga parlourn na shiga dakin na ce mishi. "Yana parlourn!" "Ki ce ya shigo!" "A'a ba zai shigo ba!" Na faɗa ina kallon yadda yake kallona, kauda kai nayi ina me kallon waje. "Shi kenan" ya fada yana me mikewa daga gadon, ya fito parlourn ajiyar zuciya na sauke ina jin kamar ya sauke min nauyi.

Fitowa na samu basu nan, ashe asibiti suka tafi ina na sani. Wurin karfe biyu da rabi aka daura auren shi da Ijlal, anan gidan ya dauki shewa, da yake son ga baya nan haka suka yi ta bidiri an kawo abinci daga can gida amma ban taka naje ba, nawa nayi domin Yan uwana sun zo Aunty Nu'aymah da Aunty Sajidah, sai Aunty Shukrah, suka saka ni gaba na shirya tsaf, sannan aka kira mai kwalliya har gidan tazo tayi min, bayan sallah la'asar kenan,.muka nufi cikin gidan kamar yadda Mai Babbar ta bukata, an yi hidima sosai sannan ban san ya aka yi ba domin muna bangaren Mahaifiyar Ilham ne Fulani karama, matar nan naga so a cikin idanunta, na ga kauna da ban zaci zan gani ba. Domin kuwa ta gaya min na dauke matsayin Nadiyyah ne. "Na gayawa Mahaifiyarki, da yan uwanki su miki abinda ake yi za a kawo miki Amaryan, duk da ke ba ayi ba,.amma iyayen yarinyan sun bukaci al'ada. Don haka ki tanadi kudi a jikinki yadda zaki wanke kanki!" Kallon Aunty Shukrah nayi nace mata. "Bari na turawa Tauhid kudi ya ciro min banki!" "Abba ya bamu wannan mu baki!" Suka mika min wata karamar jaka, budewa nayi kudi ne da normal gold wanda kanana a dunkule aka yi su. Kudin kuwa da ya bada ya bani mamaki. "Aunty Nu'aymah a ina ya samu kuɗin haka?" Zungure min tayi tana faɗin. "Me kika mai da Abba? Yana da akwai!" Daga haka na sake murmushi har wurin karfe shida saura aka kawo ta, da rakiyarsu Iram da Ikram, Iman, Ilham, suka iso parlourn. "Mun ji Babbarku bata nan, ga yarmu mun kawo ta amana!" Kusan mate dina ake bani amanarta. Murmushin yake nayi na ce masu. "Allah ya bamu ikon zama da juna da amana!" Aunty Sajidah ta mika min jakar na bude a hankali na fara ciro abin ciki ina zubwa a gabanta. Ina murmushi sai da na zazzage jakar, Aunty Shukrah ma ta zuba bunch na kuɗi guda uku, sai Aunty Sajidah, kafin Aunty Nu'aymah. Sai aka fara gud'a ana shewa. "Zainab Ikhlas Uwargidan Hakimin Fara ƙasa ta sayi bakin amarya da kudin da ba a tab'a zata ba." Balbla dai aka yi ta yi ina jin su kafin Magariba muka bar gidan, na koma can tare da rakiyar Yan uwana, sai lokacin na tuna ashe baya gidan ko ina ya je oho, ana sallah suka min sallama suka tafi. Can naji hayaniya alamar sun kawota kenan sai shewa suke suna fada nan da wata tara su zo suna ina jin wata tana faɗin. "Ina fatan nan da wata bakwai ma!" Shewa suka saka ina jin su, can na ji ana buga kofar dakin na baza books ina nazarinsu, na ce. "A shigo!" Tura kofar suka yi, wasu yan mata ne irin kawayen Amarya bayansu Ilham ce. Kallonsu nayi fuskata dauke da murmushi. Na bude baki kenan zan yi magana aka yi Faruq yayi gyaran murya, matsa mishi suka yi, nasan dai gashin kaina a bude yake, Boss dinsa ne a bayanshi, wani irin kallo ya min wanda yake tattare da jin haushi ne ko wani abu oho. Wucewa dakina yayi shi kuma Faruq ya ajiye min bag din magani. "Yana son abinci me ruwa, mai kuma dumi ko zai samu!" Mikawa nayi na amshi bag din maganin na wuce ciki, na ajiye a gaban Mirror na dauki dan kwallina na daura. "Duk ranar da na kara ganinki babu hula ko mayafi wallahi sai Malam Junaid ya shiga tsakaninmu." Ban kula shi ba na fito na samu su Ilham din suna parlourn har zuwa lokacin. Tattara kayana nayi na wuce da shi extral room din nayi na ajiye sannan na fito, suna kus-kus. "Ikhlas me yake damun Yayana?" "Why not ki shiga ki tambaye shi?"
Na bata amsa na wuce waje, takaici duk ya ishe ni, wai abu me ruwa-ruwa? Bani da garin kunu, Shinkafar tuwo na shiga na dibo na jika, sannan ba duba nikakken gyada da aka saka min a kayan jerena, na diba daidai na fito na zuba a blender din Bunchy mix, na zuba daidai ruwan da zan dama kunun na sake tsinkar da gyad'ar, sannan na tacce na daura akan wuta. Na koma na ciro kayan kamshi kanunfari, citta, cennomin na wanke na zuba a cikin ruwan gyad'ar. Sannan na saka wutar daidai na wanke blender din na kara zuba shinkafa da zan damma kunun da shi, na tacce shima na ajiye sannan na fita zuwa parlourn har lokacin suna nan, dakin na shiga na samu yana kwance idanunsa a rufe, juyowa nayi zan fita ya ce min. "Kina bukatar wani abu ne?" "Kana shan sugar?" "Hm!" Na juyo zan fita ya ce min. "Girki kike ne?" "Hm!" Na ce na fito abuna, kitchen din na koma na cigaba da aikina, wurin karfe tara da rabi na gama na kai dakin. A hankali na saisaita mishi zuwa lokacin mayyun sun koma bangaren Amarya. Ina fama da kunun yayi sanyi na ji sallamarsu. "Kada wata ta shigo min bedroom."
"Wajen Mijina, na zo ba wurin ki ba, don haka." "Ki koma dakinki!" Yadda yai maganar a kausasshe yasa ta yin shiru ya kara da cewa. "Aina'u!" "Na'am!" Ilham ta amsa mishi, "idan kika sake na fito baki wuce gida sai na karya ki, kada na kara ganinka a gidan!" "Tow, kayi hakuri!" Ta fita da gudu. Ina ji har da su sauran yan matan. Daga nan ya cigaba da shan kununina juya mishi. Yana gama sha ya koma zai kwanta na ce mishi. "Da dai ka hakura da kwanciyar ya fada maka!" Na faɗa ina kumbura baki. Zama nayi na dauki pillow na saka mishi a bayanshi sannan na haɗa mishi magani ya sha, kafin na gyara wurin na fita zuwa daya dakin, ban kuma komawa ba har dare yayi sosai. Wayata na ji yana ringing na dauka da yake mun kusan fara exam, sai na ke karatun dare kuma dama can duk wani dalibi ya saba karatun dare, bakon number na gani a hankali na dauka ina dafe goshina. "Please ina bukatar wani a kusa da ni!" Ya fada yana sauke wani irin nishi. Ware idanu nayi na tashi da sauri zuwa dakin na same shi yana wani irin zuba, idanunsa a rufe. "Sannu!" Na faɗa mishi a rud'e. Kafin na kunna Ac saboda yadda yake gumi, haka yayi ta gumi ina goge mishi. Ina son tambayar shi amma ina jin tsoro. A hankali ya cire rigarshi ya wurga can gefe. Har lokacin gumi yaƙe. Tab'a tafin kafarshi nayi naji sanyi kalau, amma jikinsa da zafi sosai. Wardrobe dina na bude na dauko garin magarya na fita zuwa kitchen na dibo ruwa na koma dakin, na zauna a gabanshi na fara karanta Ayatul shifa, sannan na tashi na nufe shi ina me bashi ya sha sosai kafin na tsaya ina kallonshi. Gyada min kai yayi Ni kaina jikina wani irin rawa ya fara, koda a kuskure babu namiji da hannuna ya kai kan nashi bayan ahalina, amma shi sai na kasa yin kome jikina yana rawa. "Dauki waya ki kara Faruq!" Da sauri na dauka na ga Hafblood. "Sunanshi?" Na tambaye shi, "haf!"a hankali na kira shi. "Sir!" "Bashi bane ni ce ko zaka zo!" "Right now!" Ya fada, na koma gefe ina kallon yadda yake dafe kanshi, a hankali ya mike ya fara amai bakikirin yayi kafin ya koma ya kwanta. Kallon wurin nayi na ji haushi ba karya amma haka na fita na kawo abu na goge dakin tare da saka burner na saka turaren wuta, sannan na zauna ina jiran Faruq, koda ya iso shigowa yayi dama da Hijab a jikina, mika mishi ruwan nayi na ce
"Shafa mishi!" Shafe shi yayi, yana kallona ya ce min. "Ko zaki taimaka mu kai shi asibiti?" "A daren nan?" "Eh!" Ya faɗa, "a'a ba sai mun je ba!" Ya fada yana wani irin b'ari kamar ana kad'a shi, tabbas mazaje ba lafiya, domin daga yadda yake irin wannan rawan sanyin na kara fahimtar yadda yake ji. Kusan akanshi muka kwana, sai karfe hudu na asuba ya samu barci Faruq ya tafi masallaci ni kuma na shige ban daki nayi alola na wuce nayi sallah.

Ina idarwa nan jira azkar ba na kwanta barci yayi gaba da ni, sosai nayi barci domin a gajiye nake, shima ashe bai tashi ba sai wurin bakwai, yana tashi ban daki ya shiga yayi wanka da alola, ya fito ya gabatar da sallah, ni ban sani ba.

Wurin karfe goma na safe naji hayaniya sama sama, a hankali nake jin muryan kuka na tashi, dirowa nayi daga gadon na fito waje, karamin tsaki na ja a raina ina kallon yadda Yarinyar nan take kuka kamar an mata mutuwa. Bude baki nayi tana durkushe a parlourn ya fito jiki a mace, ganin yadda na tsaya ya kalle ni. Zama yayi. Ashe Mai Babbar daki tana babban parlourn shine ta turo yarinyar ta kira shi, tazo tana kuka. "Mai Babbar daki tana waje!" Ta juya tana mai harara na kafin ta fita, komawa dakin nayi na kwanta don Allah ya gani barci bai ishe ni ba. "Zaianb!" Yadda ya kira sunan ya sani tsaya ba tare da na juyo ba. "Ki same ni a can." Na shiga uku ni wai ba zan huta ba ne?

Haka na shiga bayan ya tafi na bi bayansa. Ina isa parlourna na ganshi zaune a kusa da Mai Babbar daki duk da ya kishingida ne, sannan kamar yafi jin dadin kwanciyar. "Ijlal ta kira gidansu wai baka kwana a wurinta ba?" Gwalalo idanun nayi ina mamakin yadda ta gayawa yan gidansu bai kwana a ɗakinta ba, sannan mai babbar daki ta kara da cewa. "Wannan makiran ta saka ka kwana a wurinta?" Ya kasa magana yana kwance lumo kamar ruwa ya cinye shi, nima ganin ba wani abin arziki na samu ba sai zagin makira da munafuka yasa nayi shiru. Yana son yayi magana amma baya jin karfin jikinsa. "Ina magana baka ce min kome ba?" "Bani da lafiya ne!" Daga haka ya mike zai tafi dakinsa ya ce min. "Zo ki gyara min dakina!" "A'a na ita ba, Ijlal dai." Mai Babbar daki ta nuna Amarya, da sauri ta mike ta nufi bayansa, ni kuwa magana ta gaya min tare da faɗin. "Idan ma wani abu kika bashi tun wuri ka san yadda zaki yi domin wallahi na fahimci wani abu akan ciwonshi sai an jimu da iyayenki munafika kawai, daren yarinya kika dauke mara kunya mara tarbiyya." Haka ta kama zagina, ta bar ni awurin ko a jikina sai ma sosa kunnena da nayi domin maganarta ba zai dame ni ba.

Nima bangaren na wuce na dumama kunun jiya da nasha, sannan na koma daki nayi wanka na kwanta tuni barci yayi gaba da ni. Wurin karfe daya na rana naji ana ta buga min kofa, bude ido nayi na fito ina hamma. Ita ce tsaye a bakin kofar parlourna. "Inji Honey wai ki bani maganinsa na kai mishi!" Shiga dakin nayi na dauko, na mika mata sannan na koma na gyara dakin tsaf, kafin na fito na share parlourn na fara aikin gogewa, sannan na saka turaren wuta, na shiga kitchen yau kwadayin tuwon mutanen Ghana nake shi, don haka na fito waje, Faruq da ya shigo gidan rike da manya warn abinci ya gaishe ni. "Sannu ya gajiyar jiya?" "Alhamdulillahi yabi lafiya, ya mai jikin kuma?" "Da sauki sosai! Hmm don Allah idan ba zaka damu ba ko zaka taimaka min da wannan kayan cefanen?" "Tow!" "Ina son plaint amma ba nunane ba danye sai rogo." Na mika mishi, sannan na koma ciki sai da ya kai kayan abincin sannan ya fita aikana, ni kuwa na wuce na fara aikin daura miya. A cikin kayan da ya sayo na cefane wnada yasa Chef Brandy ya kawo min akwai namar rago don haka miyar namar rago nayi amma ba mai kauri ba,.na kuma saka a pressure pot, da kayan miyar bakiɗaya ta dawo. Haka kawai nake ji a jikina kamar da mutum bayana da sauri na juya sai da na razana. "Babu sauran kunu?" Yadda yayi min maganar alamar yana bukata ne yasa na duba tukunyar da nayi kunun da saura, na kunna gas din ya kara dumama mishi na juye mishi. A hankali ya fita daga kitchen din ban san me ya faru ba, sai dai tana zuwa ta wurga min kofina ai kuwa ya fashe. Murmushi nayi ban ce mata kome ba, haka na cigaba da aikina sannan na share wurin na dafa zobo da kayan kamshi, duk girkina ya cika gidan. Sallah na tafi nayi har Faruq ya shigo ya ajiye min a kofar parlourna, ina fitowa na samu kayan a wurin dauka nayi na wuce kitchen cire kayan nayi sannan na wanke na bare rogon sannan na bare ayabar na cire zaren tsakiyar na yanyanka na zuba a blender na nikka su bakiɗaya, na juye a tukunya iya cikina sai yaya, haka na faɗa kome tuwon kuwa sai da na tuke shi tsaf sannan na barshi ya turara, kafin na kwashe a leda kamar malmala shida. Sannan na fito na yi wanka na gyara jikina na cancad'a ado cikin wata riga da wando yan katin wandon palazzo ne har kan cikina sai rigar ma yar karama ce amma ta sauka har cinyata, hula na saka wato idan zan baku labarina bani da kiba fa, amma kuma ba za a kirani ramammiya ba, sannan ina da halittar kirji me kyau zuwa cinyoyina don ma dai ba zan boye ba kirjin ba wani girma ne da su ba, cinyoyina sun fi daukar hankali sama da kirjina idan babu rigar nono, don har ana ce min ci ba kiba asarar gari. Hijab na saka saboda naji muryan maza a gida alamar kannensa ne suka zo duba shi. Komawa kitchen nayi na sauke miyar kubewa danyen da nayi, domin har da ita a lissafin, "Assalamualaikum!" Na ji sallama, daga kitchen na amsa ina juye abincin. "Karamin ango, Abdullahi ne nazo duba Sadauki da jiki." A raina nace. "Hmm sadauki Manya!" Na ce mishi.."karaso sai dai kada kayi kamshin girki Yan matarka ta ce bata yarda ba." "Ai kuwa ba ruwana cewa xan Uwargida ta ciyar da ni! Madam kamar fufun Ghana!" "Bari na sako maka!" Na zuba mishi, ya masa yana faɗin. "Ai na gode sosai yau bani ba cin abincin cikin gida dama Allah ya kawo min sauyi!" Nan yayi ta zuba na ce mishi. "Bari na hada maka da zobon!" Haka na hada mishi a tire, har ya fita parlourn ya samu sauran yan uwansa da suke Uba daya mazan sun iso suma Yayan nasu yana kwance a dogon kujera. "Matsala ta da kai mugunta sai ka gaya mata ba kai ɗaya ba ne!" Inji daya daga cikin Yan mazan. Daidai na leko kenan. "Laa kuna dayawa kenan? Tow bari na kawo muku kawai." Na juya zuwa kitchen Allah yaso na dauki daya, na ajiye sauran na kawo musu a wasu warmer masu kyau da flat na ajiye musu, kowa ya dauka, sai ta rage saura Malmala biyu, Faruq ya dauki daya ya saka mishi, ya koma gefenshi yana barci yana ci a hankali har ya cinye sauran ɗaya, Faruq yana so shi kuma Rumbu bai ishe shi ba. "Na kara maka?" "A'a kai ma kaci!" "Uwargida daga yau na tare a gidan nan dole na kawo Cutie-cutie pie ta koyi girki, daga yau kwanona yana gidan nan safe rana da dare." Dariya suka saka Salim da yake aiki a Jos ya ce min. "Nima dai nayi transfer nan sai na koma can zan cigaba da cin na Madam dina!" Wasa wasa suka yi ta santi basu bar gidan nan ba sai da suka hada min dubu hamsin, suka ce na kara maggi domin gobe suna hanya, nayi godiya ban so amsar kudin ba shi ya amsa y ajiye a gefenshi. Bayan tafiyarsu na kwace kayan na nufi kitchen na gyara ko ina na wanke, sannan na koma dakina na ci nawa nayi sallah isha. Abincin da suka kawo karshe Faruq ya mai da shi wurin Mai Babbar daki, washi gari na zata ba zasu zo ba, amma sai ga kiranshi ina azkar na zata ciwon ne kuma sai ya ce min. "Yaran nan zasu zo!" "Hm!" Na ce na fito da sauri, tanda garin da saura. Wanke wake nayi na markade shi tas. Sannan na dama musu kunun alkama wanda na dafa Yayan da ruwan gyad'a. Sannan na juye a manya jug din kwalba wanda na saya a wurin Janafty EXCLUSIVE AVAILABLE kayanta ba karya suna da kyau. Sannan na wuce da shi parlourn shi na bangaren shi na ajiye, kafin na dawo na karasa alelen da nayi da Farfesun kayan ciki, sai manja da na soya da jan yaji, ita kanta Alelen da kwai na dafa, sannan na dawo na gyara kitchen din na wanke ko ina na shiga nayi wanka wurin karfe tara sai gasu har da su Aneesah. Ina shirya cikin riga da skirt na atamfa ya tsaya a bakin kofar ya ce min. "Idan da saura kaiwa Ummina!" "Hm!" Nace na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login