Showing 147001 words to 150000 words out of 304445 words
ko kuma a dawo da ita da dare, wannan ya bani lasisin buga nawa wasan yadda nake so, domin kuwa na shirya shagali. Tun ranar Talata aka fara bikin, mun fara da bride show, mun yi wanka cikin wasu kayan barci wanda aka mana oda, d-1 haka muka yi shagalinmu, washi gari d-2 muka yi cocktail night, tare da abokan ango ni ban ma san waye ya gaya masa ba, sai gashi nan ya zo, koda yake ba mamaki Nadiyyah ce domin na bata iv din tace ba zata samu zuwa ba tana ta fama da kanta da kuma zirga-zirga. Washi gari juma'a muka ranar d-3 muka yi kamu shima yana zo nayi mamakin yadda yake bina like tail nayi ƙoƙarin na hana shi zuwa amma haka bai cimma ruwa ba, ranar juma'a walima aka yi, da yamma da dare kuma kuma yi Mother's night. Maluma da ta kasance mai bude taro da addu'a sai Mai Babbar daki mother of the day, kafin aka kira Uwar Amarya sai ni da na kawo tarihin amarya duk wannan abin da muke ni sanye da wata burmemiyyar alkyabba nake, yadda nake bada labarin rayuwarta, ina kuka na juya ina kallonta. "Bestie idan Sir Yazid ya miki ba daidai ba, kada ki gaya kowa ki gaya min sai an jimu da shi," na manta da su Mai Babbar daki na ce, musu. "Kusan cewa Bestie bata da mutunci? Ranar nan mun fita amma na dawo na ga idanunta kamar tayi kuka, da na tambaye ta ya what'sp ashar ta dura min, Yar airport da airplane, amma mutuniyar kirki ce, shegiya kawata. " Sai kuma aka saka dariya, haka aka tashi ina zaune ya turo min sako. *Ina mota!" Na zata gabar zata cigaba ne na tafi inda motoci suke horn ya min na tawo bude min yayi ta ciki na shiga, tunda na shiga bai min magana ba, bai kuma ce min fita ba. Haka na gaji da zama ya juya da ni zuwa gida ko kayana bam dauka ba, na muka wuce gida.
Ranar asabar aka yi daurin aure, muka shiga cikin hidimar sosai ga abokan aikin mu na gidan rediyon, duk wanda ya ga yadda muke fa sai ya tausaya mana domin ana daura auren muka fara kuka, haka gidansu Yazid suka turo ɗaukar Amarya, a lokacin da aka zo daukar amarya har da shi a cikin masu daukar amarya ina ganin yan mata sun cika motar wasu ma ba kawaye ba ne. Leka motar nayi yana hidimar danna waya bai kula su ba. Bude motar nayi fuskana a hade na ce musu. "Ko zaku samu fitowa ba ya cikin abokan ango mijina ne!" Na faɗa ina kallonshi da wutsiyar idanun shima ni yake kallo amma bai ce uffan ba, ina jin wata tana tsaki. "A fita min a mota." Suna fita dai ga Hidayah wata cousin din Yeemar yarinyar ta cika rawan kai, bude motar zata yi na ce mata. "Ki fita waje motar amare nan wannan motar mijina ne!" Na shiga gaba na kame, na ce mishi. "Muje!" Bai ce min cikanki ba muka bar gidan, har gidan amarya muka nufa, ana aka hi shirin dinner. "Ai kuwa, daya yau bikin ya kare ma, Mayu ba dama su ga namiji ya hadu duk su kama rawan jiki!" Na faɗa ina hararanshi, haka ya kai ni gidan iyayen Yazid ashe su gobe ne wuninsu, na yi shiru kafin na nufi dakin da take muka, shirya dariya yayi yana faɗin. "Ke Abdulwahab kanin shi ya ce kin yi mishi fa."
"Baki gaya mishi da Mijina kamar jela ba." Na faɗa ina gyara zaman rigana!!" Tsaki wata cikin yan Yeemar suka yi wanda na ce su fita min a motar mijina, suka yi bai dame ni ba, na gyara zaman rigana na juya ta gyara min ya kamani tsam, yan nonuwar nan da aka masu ciki suka fito cur, hotuna muka yi na daura a status. Kafin mai kwalliya ta kara gyara mana Makeup dinmu da dan kwallin kanmu, haka muka fito cikin nutsuwa ka wuce wurin Dinner, wani cikin abokan ango ya min magana ga motarshi ba laifi motar tayi kyau amma ni ba shi ne nawa motar ba, dan gidan Mai Babbar daki nayi da shima ya hade cikin wasu kaya masu kyau kallonshi nake yayi kyau kamar wani ango. Tun kafin na isa ya taso ya riko hannuna. Kallonshi nayi shima kallona yake fuskanshi dauke da murmushi nima haka, muka shiga motar aka wuce da mu, kusan amarya da ango suna gaba muna binsu a baya har wurin event center din, ba laifi wurin yayi kyau anyi biki amma ni Mijina ya hana ni rawa, sai dai fa dole na fita muka taɓa har da shi domin kuwa kare ni yake, har aka gama na gaji, tun da muka fito hall din ma cire takalmina, ya dauke ni cak, ya saka a motar, sannan muka nufi gida da shi, koda muka isa cire ni yayi a motar ya kai ni dakina ya haɗa min ruwan wanka da kyar nayi ma fito ko towel din ban iya cirewa ba na kwanta, tashina yayi na gabatar da sallah isha dakyar ina idarwa sai barci, washi gari sai yamma muka wuce aka yi budar kai aka raka amarya gidanta, daga nan da na dawo muka daura rikicin mu daga inda muka tsaya.
Kusan wata biyu Faruq ya kwashe yana jinya kafin ya dawo, koda ya dawo ya murmure kamar ba shi ba, goshin layya suka dawo suka cigaba da harkan gabansu. Ni dai nasan na gaida Faruq na kuma mishi ya jiki txt da kiran waya, bayan nan na bashi hakurin rashin zuwanaa. Ya ce ba kome amma Uba Teresa haushina yake ji, ni kuwa na tattara shi na watsar.
#Goodnight
*Account Details:*
*08130269641"
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500₦
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 48
Duk da ni da faruq ba mu da matsala amma Uban Faruq ya dasa gaba a tsakaninmu. Tun bayan gama bikin Yeemar sai takun sakarmu ya sake kamari yadda duk abinda yasan ina so ya shiga ya fita ya hanani raina ya kara b'aci lallai, sannan a gefe guda ji da matansa biyu yake haka yasa nima na ja kaina gefe, ya zata ko zan haukace ne nayi ta jin haushinsa ina takalar rigima sai ya ga ba haka bane, ana cikin wannan yanayin matar Abdullahi ta haihu, Safnah aka shirya zuwa suna da ni Mai Babbar daki ta shirya za a tafi amma yayi ruwa yayi madaukiya ya hana ni tafiya, ya cusa Ijlal a tafiyar. Ban san yadda aka yi ba Mai Babbar daki ta ce na hakura tunda mijina baya son nayi tafiyar na ji haushi Kuma na ji babu dad'i ita mahaukaciya sai murna take mijinta ya barta ta tafi Kano ni kuma ko oho da yake a can Abdullahi yake aiki a cbn na Kano.
Ina kwance ya shigo ya samu ina shan tea, hankali kwance da cake. Yadda yayi sallama kasa-kasa yadda iya kunnena ya ji nima haka na amsa mishi kasa-kasa, ya nime wuri ya zauna yana kallon tv da yake ina da Netflix a wayata kuma an hada min shi, sabon movie din da aka sake nake kallo wato Kpop demon hunter, na zuwa tv idanun. Ganin tunda ya shigo ban mishi magana ba, ban ma san yana wurin ba yasa shi, dauke flat din cake din ban damu ba saboda bani da lokacin da zan kula shi kuma na lura kamar hankalinsa ya dawo jikinshi. Ko nace iskanci ta ciyo shi,to shine bari ya zo ya latsa ko zai samu yadda yake so. "Me yasa ba ki iya bada hakuri ba?" Juyawa nayi na kalli wayata da tayi haske na dauka ina murmushi, sakawa nayi a kunne na ce mata. "Amarya ya amarci?" Na dauki kafa daya na daura a Center table din parlourn ina kallon tv. "Ya me ake ciki ne? Kin kuwa duba grp!" "Me ya faru?" "Hmm wani labari nake ji, kafin nan zan tambaye ki, da gaske Joy Moses ta kira ki?" Inji Yeemar, "Me yasa kika tambaye ni? Wani abu yana wari ne?" Na kuma tambyarta, murmushi tayi kafin ta ce min. "Beb mutuwar Joy Moses yana da nasaba da wani research da take yi akan Zanzabira Kingdom, abinda ya faru ranar sallah ya sa, na fara wani bincike ba na gaya miki ba? Tow abinda ya sa na tambaye ki zancen Joy akwai wani bayani da ya fito ne, da aka alakanta haka da duk wanda yayi ƙoƙarin bincike wani abu da ya shafi Zanzabira yana iya facing mutuwa ko wani abu, sannan wani abin da na kara fahimta, kamar akwai cursed a masarautar, duk wanda ya shiga cikin masarautar imma ya mutu akan gaskiya ko kuma ya mutu akan son rai." Shiru tayi kafin ta cigaba da cewa. "Ikhlas aurenki da Prince Salmanun Faris, it was trap. Ban san yadda xan miki bayani wallahi ba zaki gane ba, domin abin kamar theory ne. Ove 300yrs ana nimanki now sun same ki, shine step na farko da Joy ta dauka sai ta fadada bincikenta har ya kai zuwa wani babban al'amari da ya fado kanki, yanzu haka akwai wasu gamayyar kungiyoyin CULT suna nimanki!" "Innalillahi wainnalihir rajoun! Beb a ina kika samo wannan tatsuniyar?" "Ba story ba ne Baby da gaske ne ana niman ki ne, amma shi kenan tunda kin dauke shi da wasa Allah yasa mu dace!" Kamshin turarensa da nake ji tun dazun yasa na kasa fahimtar meke faruwa ashe tun da na fara wayar yake kusa da ni, na rantse ban lura ba ashe idan na matsa sai ya matso." Kallon renin hankali nayi mishi ina kokarin janye jikina ya matso tare da tambayata. "Wace ce Joy?" Matsawa nayi baya ina kashe wayar. "Meye nufinka da jin abinda nake yi a wayata?" Tashi yayi kasancewar bai ji sauran bayanin ba, amma kuma ya ji yana son sanin wacece Joy din.
Bayan sallah isha ina kitchen, Nady tana zaune akan kujera gefen kitchen Island din, tana gaya min Mamarta zata zo duba ta. Murmushi nayi na ce mata. "Me zaki mata to?" "Hmm ni ban san kome da xan mata ba kawai na ji na mata oda ne!" "A'a sai dai mu mata abincin anan!" "Da gaske?" Yaji muryanta tana tambayar Ikhlas, dariyar ikhlas yayi tana faɗin. "Da gaske mana, kawai ayi anan kada a kashe kudin a waje." Karasowa yayi ya jingina da kofar kitchen din yana kallon yadda suke zaune Nady sanye take da wata doguwar riga yar kanti yayinda, nake sanye da riga da skirt na Material ba hula a kaina gashina har bayana. "Hey Prince!" Ya d'aga mishi hannu, murmushi yayi ya iso tare da sumbatar wuyarta yana ƙoƙarin niman idanuna, ganin naki kallonshi sai hada mata omelette din da nake na kara dan gudun wutar, yana kuwa yi da sauri da sauri, wani irin bugu zuciyata take kamar zata b'allo daga kirjina, juya musu baya nayi ina dafe da kirjina. "Sis lafiya?" Nady ta tambaye ni tana kokarin buge hannunshi, amma sai tab'a kirjinta yake na ce mata. "Ba kome ina zuwa na manta abu a daki!" Na fita da sauri, ina shiga na rufe kofar Parlourna zama nayi akan kujerar kamar wacce aka zarewa laka. Ina jin kirjina yana min wani irin zafi, daga shi har Nady haushinsu nake ji haka yasa na rintsa idanuna. Wasu irin surutai nake ji yana shiga kunnensa. *Shi din nawa ne shi ɗaya! Zan farauci raywuarki da duk abinda yake da nasaba da ke nayi ta lalata rayukansu har sai kin gudu da kanki! Ba zan mutu ni daya ba. Kuma ba zan barki ki rayu da shi ba, ina tabbatarki na rantse da harshen magabata sai soyayyarku ta samu cikas a kowacce rayuwa da kowace karni sai na hanaki sakat na kuma hana ki samun shi domin anyi shi ne domin ni Aojana domin ni Aojana aka halicce Sadauki! Awatif lallai ki gudu lallai ki gudu* dafe kunne na nayi da ƙarfin gaske karfi ina jin sautin muryanta har cikin kaina, ban san yadda aka yi jini yake fita ta hancina da kunnena ba. Sai da na rarrafa na fito da dan kuzari na bude kofar, Nady ce a tsaye. "Baby!" Ta kwala mishi kira, tana tambaya ta. Kallon yanayin fuskartar nake ganin yana juya min na kara dafe kunnena da karfin tsiya, a hankali na zube a kasa, wanda yayi daidai da zuwanshi,
Haka suka wuce da ni asibiti, akan lokaci ta waya Nady take gayawa Mai Babbar daki, tunda muka isa asibitin aka wuce da ni dakin gaggawa, aka shiga kokarin ceto rayuwata. Kaf yan uwana suka zo har da Aunty Sajida mai fama da nata cikin. Domin sai yanzu Allah ya bata ciki, tsawon shekaru goma sha daya da aure. Wuni aka yi a kaina, sannan shima kuma ya amshi nashi bangaren inda aka yi dace yayi min scanner din kaina bakiɗaya bai ga kome ba, sai dai yadda abin ya faru ya bashi mamaki, haka aka wuce da ni dakin da aka ware min, Mai Babbar daki take tambayarshi me yake faruwa. Hannunshi a baki yakar kallonta ta window glass din dakin da take ya sauke wata ajiyar zuciya, domin shi kanshi cike yake da dinbun mamaki, taya za ace kome lafiya bayan ta ga yadda hanci da kunnenta suke zubar da jini, yadda aka zuba mishi idanun ya dawo nutsuwarshi, ya ce musu. "Lafiyarta lau, babu wani abinda ya same ta." Yuuu suka mishi da idanu, Mai Babbar daki da bata da hakuri akan abinda ya shafi ciwo ta ce mishi. "Yanzu ma wasa take a kwance?" Murmushi yayi wanda ya bayyana hakoranshi ya ce mata. "A'a da gaske duk wani organ na jikinta yana lafiya, sannan ita kanta system na jikinta lafiyarshi lau, abinda ya faru ana iya danganta shi da sauyi yanayi domin yana iya faruwa a kowacce yanayi, sai ta farka zamu ji meke damunta!" Sunkuyar da kai tayi tana jin shi. Gabanta yana faduwa ba dai abinda Adade ta fada ba ne yake shirin faruwa da Ikhlas din ba? Juyawa yayi tana faɗin. "Ubangiji ya bata lafiya, yasa zakkar jiki ne!" Nady kan kuka take tana tausayin Ikhlas. "Ya isa Nadiyyah zata tashi fa!" Inji Umma tana dafa kadafarta. "Muna tare da a kitchen muna magana ta ce tana zuwa kawai na ji shiru shine na je duba ta kawai naga ta fito rike da kunnenta tana niman hanyar fita. Anya ba wani abu yake faruwa ba?" Ta fada tana kara fashewa da kuka. Shiru Mai Babbar daki tayi tana jin Nadiyyah na kuka. "Allah ya kyauta " ta fada tana mai barin asibitin. Yana biye da ita wannan shine karon farko da tazo asibitin don koda suka gama takaba bata fita ko ina ba yau ne ta fara fita waje har haka bayan idin da suke je. Bude mata kofar motar yayi zata shiga ta kalle shi. "Baka ga wani bakon lamari a tare da ita ba?" Girgiza kai yayi yana faɗin. "Babu kome da yazo a tare da ita asalima suna ta hira ne ita da abokiyar xamanta." "Abin da mamaki!" "Ummi naji Ummanta tana fada kwanaki Maluma ta ce tayi mafarki tayi ta ihu. " Ya fada a hankali, "Me yasa baka tambayi ita Yarinyar ba?" Shiru yayi yana sosa kanshi. "Salmanu Faris!" Kallonta yayi kafin ya sunkuyar da kai. "A da can ina son ka nashi wurinka, amma saboda wasu dalilai ina ga kayi step down kada ka ce zaka amshi abinda yake naka, for sake of that child tana bukatar a kare ta." "Ummi akwai wani abu ne?" Kallonshi tayi tana faɗin. "Akwai wani al'amari da yake shirin tashi ne bayan dogon barcin yayi, Salmanu bana tsoro akanka but ita din innocent ce da bata san kome ba, Mahaifinka ya yi involved dinta cikin wannan lamarin ta sanadin Mahaifinta, amma zuwa yanzu na fahimci daga ni har kai ko yana raye ba zamu iya ba, mun zata iya rayuwa ce muke gwagwarmayar ashe ba yau aka fara ba. Ina tsoron kada yar mutane ta rasa rayuwarta."
"Ummi me ya faru?" Shiga motar tayi ta ce mishi. "Masarautu masu karfi irin namu, kafin sarki ya auri mace sai an bincika taurarinsa da kwanan watansa da wacce zai aura, kai da ita tauraronku ya hadu, amma ba kai ne naku yayi matching. A wannan rayuwar Salmanu Faris ba kai ne kake daidai da ita ba, tauraronta ya hadu da na sarki na tara wanda babu kowa da yasan sunnsa, domin yana barci ne, shine tauraronshi yayi daidai da na Ikhlas. Idan ana son naka yayi daidai da nata." Kifa fuskarta tayi a tafin hannunta wani irin kuka take son tayi amma haka ta hadiye idanunta yayi jajjur. "Nan da lokaci ƙalilan za a fara nimanta, domin ita din ta musamman ce. I'm sorry Son amma ba zan tab'a give up akanka ba. Ka kula da ita Allah ya bata lafiya!" Ta ja murfin motar ta rufe, tana mai kauda kanta hawaye na zuba mata. Bata san lokacin da aka kulla ba, amma waye yayi musu irin wannan barnan? Ciwon lips dinta tayi, kamar yadda Salmanu Faris yake yi, ana zaka fahimci a wurinta ya dauka, haka suka isa har gida tana jin soyar a ranta.
Dreamland.
Zan iya cewa wannan shine duniyar mafarkina, ga ni ga matar da na tab'a mafarkin fuskarta. A zaune can gefe tana kallon wasu yara ƙanana da suke cikin wani irin ukuba. Duk da yanayin da take ciki bai hana ka ga murmushi a kwance fuskartar ba. "Kin iso?" Ta tambaye ni. Kallonta nake tana zaune a wurin. "Yaushe zan fita a wannan wurin?" Ta tambaye ni. Kallon wurin da take a sahara take mai zafi da rairayi. Kafarta an saka mata karfe an turke kafarta. Yaran ma haka, "yayi watsi