Showing 234001 words to 237000 words out of 304445 words

Chapter 79 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

66

Haka na ci abincin sannan na mata sallama ta ce min. "Zan turo mai kwalliya an jima!" "Allah ya saka da alkhairi!" Ha fito daga dakin na samu Aneesah da Daulah sai Ilham. "Ke yanzu baki ji kunyar wanzuwarki anan ba? Kin shiga kin fita kin hana mai haihuwa nutsuwa da mijinta, fisabiilillahi haka ake rayuwa?"
"Lokacin da ta gyeta muku karyan namiji zata haifa baku yi mamaki ba wanzuwar Ya mace ba? Sai ku rufe idanunku kuna niman aibuna, idan kun ga ba zaku iya bata shawaran arziki ba, shi kenan amma kada wata yar renin hankali ta min Magana na gaya muku!"
"Ke bama son rashin kunya uban waye zaki gayawa magana?" Inji Ilham. Murmushi nayi nace mata. "Kada ki sako iyaye cikin wannan lamarin. " A fusace ta ce min. "An sako don Ubanki!" Ai kuwa na kifa mata mari. Daidai fitowar Mai Babbar daki. Su Aneesah sun mike dole suka zauna suna kallon takaici. "Kika mare ni?" "An mare ki, zaki rama ne? Rama tow!" Na isa gabanta.." Ubana ba sa'an wasanki ba ne, idan kika sake barin jakin bakinki ya zagar min uba sai na gurje shi tas!" Na juya na cewa mai babbar daki. "Na barki lafiya!" Na fito, Faruq ya kawo ni gida, sannan ya bani hakuri, ashe bayan fitana Mai Babbar daki ta kira shi ya shigo ta gaya masa abinda ya faru, idan bai dauki matakin cin zarafin da Ijlal take kawowa cikin zuri'arsa ba zata yafe musu shi, ba shiri ya hukunta su sannan ya ce suka sake wani abu ya taso sai ya haramta musu shigowa fada na tsawon shekaru goma, ita kuwa mara kunya ya ce ya bata wata gudu ta fitar da miji ko ya bada kyautata. Yayi ta bawa mai babbar daki hakuri.

Tunda na koma na kwanta wurin karfe sha biyu aka zo aka amshi kayan da za a zuba abinci na tura Wildat da su, domin a kula min da kaya na. Bayan tafiyarsu wurin ƙarfe daya sai ga Kanwar Maman Ijlal ta shigo suka ban santa ba ta kawo min soyayyen nama da hanji, Jakadiya ta amsa ta ce min. "Dama muna son don Allah a bamu aron kula ne ashe basu ga nata ba. Ina ga an sace ne!" A hankali na tashi zaune na sake murmushi na ce mata.."Na gode Hajiya amma ni Iyayena sun hana ni bada aron kaya ki yi hakuri yanzu a je kasuwa a sayo mata matar sarki guda bata da abun fita kunya ai akwai matsala!" Na faɗa ina gyara kwanciyata. Haka suka fita jiki a mace.
Wurin karfe biyu aka kawo min abinci a wasu rubabben kular da suka sha duniya mikewa nayi na ce musu. "Ku yi min waje da su!" Na ja mayafina na rufa musu baya kai hatta duk wani kayan da aka kai can sun kai mata, ina shiga na gansu a tsatsaye. Ina ruwan tauraruwa mai wutsiya. Murmushi na ji na cewa bayin. "Waɗancan sune Malam Junaid Gobir ya sayawa yarshi Zainab Junaid Gobir, maza ku wuce da shi nace!"
"Haba baiwar Allah!"
"A'a sai dai baiwar shaidan, maza ku yi min waje da kayana. Gudun gori Ubana da yake tootpie dinku ya saya min. Wai ma wani isasshen ne ya baku shawaran daukar kayana?" "Ni ce!" Inji Aneesa tana wani famkama. "Ai ko Salmanu Faris bai isa ba, balle ke kanwarshi, wallahi kika takale ni zanzabira da kewayensa yayi mana kaɗan, Aneesah kin yi kad'an kin yi tsararo na yi da ke, kaya kuma nawa ne, idan kika sake na d'aga muryata ba iya zanzabira ba Unguwar Malamai sai ta girgiza." Na taka gabanta. "Dube ni da kyau Ubana bagobiri ne, ko zuwan Musulunci ba a ci mu da yaki ba, ke turawan mulkin mallaka basu same mu da sauki ba, idan kika kara min shigar sauri zan rufe idanuna na miki dan kutumar buran duka a cikin gidan nan, i don't care kin girme ni amma zaki ga bita uba idan ban hana ki shigowa Zanzabira har na tsawon rayuwraki ba ki shiga sabgata ki gani!" Na juya ga Ijlal da take zare idanu na taka gabanta. "Wallahi kika kara shiga kasuwata ba tare da na kasa kayan gwarina da ke ba, zaki sha mamaki ke sunana idan kika ji sai kin bazama da gudu, idan kina can kasa ki kiyayye na shuri, idan mace ta isa mace da kayanta take alfahari ba da na kishiya ba, ana alfahari da kayan kishiya ce idan da zaman lafiya yadda baki so zaman lafiya ba har abada ba zaku tab'a samun zaman lafiya ba ." Na saka aka tattara min kayana muka bar bangaren wata babbar mata a cikinsu ta ce musu. "Idan da kunso zaman lafiya da kun fitar da Yarku kunya me yasa zaku tab"a mata kayanta? Kusan cewa basu zaman lafiya, duk da Hansai ta je ta ce ba zata bada ba me yasa zaku daukar mata kayanta kome ta ce fa ta fiku gaskiya kayanta ne kuma irin wannan gidan dole kowacce mace ta shirya kayanta da na fita kunya, ni ban san me yasa kuke haka ba, tun kafin haihuwar nan ake cewa tayi kaza yanzu kuma don kuyi amai ku lashe zaku amshi kayanta. Allah na tuba har iyaye da kakanni abin gori ya zauna."
Janta daki suka yi har da Aneesah ta ce mata. "Maza kira shi ki gaya mishi ya dauke miki kular abincin da aka kawo miki, yazo don ta ce zata aikata kome ki yi kuka."
"Ai kuwa wallahi ba zai tab'a bata kular Ikhlas ba sai dai ku hada su faɗa." Inji Amrah. "Lallai ma baki san yadda yake son Baby Amiratul Zaitunah ba ne!" Inji Aunty Fa'iza,
Aikuwa Daulah tana shigowa ta rike hannun Ijlal. "Kada ki kira shi kayanta ne, idan aka bincika aka san gaskiya tow wallahi na lahira sai yafi ki jin dadi Aneesah, ke kuma zaki zubar da sauran darajarki." Fauce hannunta tayi tana mai girgiza kai. "Idan da ina da hali sai na kashe ta, ko na rabata da mijina har abada. Mafita kaunarshi na fita son shi ko wancan juyar don nasan ba zata tab'a haihuwa da shi ba ne yasa nake kyaleta wannan da koda yaushe zata iya mallakarshi ta hanyar haifar Yara maza, don haka sai na kirata tunda tsoronta kike ji." Ta danna numbershi..................
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 77
Idan akwai babban kuskuren da Mai Babbar daki tayi shine na aurawa Salmanu Faris Ijlal domin kuwa tayi haka ne don cusawa Yar Malam Junaid da shi kanshi takaici sai gashi reshe ya juya da mujiya, sannan kiyayyar da ta nunawa Ikhlas farin zuwanta gidan laifin Ikhlas ne ko yayya bai da ce ta rena Mai Babbar daki ba, wannan abin ya saka Yaran mai babbar daki suke against sun Ikhlas babu dan da zai so a rena Mahaifiyarsa, wannan yasa Aneesah take jin haushin Ikhlas, har take hada kai domin ayiwa Ikhlas abu, sai dai bata gane cewa hada kai da Ijlal shine the worst part na destroying Dan uwanta.

Yana d'aga wayar Ijlal ta fashe da kuka tana faɗin. "Don Allah ya kake so nayi? Ya kake so nayi da rayuwata? Ya zan yi na nunawa matarka bana son tashin hankali.? Ya za a saka min abin suna a cikin kuka tazo cikin al'umma zata tozarta ni don an saka min abinci a cikin kularta. Don an saka min abinci a cikin kayanta haba don Allah me nayi da zafi ne?"
Murmushi yayi mai sauti ya ce mata. "Kuskuren kenan tab'a mata kayanta, kowa ya tsaya akan abunsa, sannan kowa ya tsaya a inda yake Zainab bata shiga harkanki ina tsammanin tunda kika haihu nan sau biyu ta shiga bangarenki ko? Haka yana nufin ita tasan kanta, batun wani ya tab'a abun wani na haramta tun ba yau ba, abinci kuwa kowa ya rike kansa na yi magana da Chefs ke da ita da Nady, bana son ki kara kirana kina gaya min ta miki wani abu tunda nake da ita bata taɓa kirana ta gaya min anyi wani abu a cikin gidan ba, amma ke dabi'arki ke shaidaniya ce. Idan kika ishe ni zan sauke igiyoyinki da yake kaina, wallahi na gaji da halinki." Ya kashe wayar bakiɗaya, sai kunya ya kamata, tayi ta zare idanu. "Na gaya miki kada ki kira shi, amma Aneesah ta zuga ki, idan da baya son Ikhlas da tuni sun yi waje da ita, tunda ya dage yana tare tow kaf duniya babu me iya dakatar da wannan lamarin, ki godewa Allah yana son yarki wallahi yadda yake jin kanshi akanta kaf duniya babu me tab'a ya sha da lafiya. Tunda Uwar miji tana tare da ita!"

Shiru suka yi daula ta cigaba da cewa. "Ni daga yau na fita harkanku, tunda baku da burin da ya wuce hada husuma duk fadar da ake yi a gidan nan Zainaba ce da gaskiya, duk da haka baku gani ni ba zan iya zama cikin munafunci ba!" Ya saka kai ta bar dakin tana fitowa ta samu Yar aikinta da Yarta suka wuce wurin Ikhlas.
Ina gyara parlourn sai ga Yeemar, murmushi nayi mata ina fadin. "Yan mata Bro Yazid!" "Ke kyale ni!" Ya shigo tana nuna min kaina. "Ke fa kina wuta ki ga yadda kika hadu shegiya ta ji kayan aiki na musamman, wato Ubangiji yasan dalilin da ya halatta aure ya haramta zina da wasu dangoginta." Murmushi muka yi muja, na kira Wildat suka tawo daga kitchen. "Allah ya baki nasara gamu nan!" "Bakuwa zaku zubawa abinci!" Haka suka shiga kitchen suna zubo mata kamar yadda na gaya musu, muka baje a parlourn. Hira da ya shafi makaranta muke da bayanin da muke zamu shiga makaranta da batun zuwa bautar kasa. "Assalamualaikum!" Juyawa muka yi cike da mamaki, Daulah ce da Kubrah tare da Bilqis suka shigo sai wasu bayi shida dauke da kayan da zasu kaiwa Mai jegon, "Wildat!" Na kira sunanta, ina mai mikewa na ce musu. "Amin waalaikumunsalam, barkanku da zuwa ku iso ciki!" Na fada ina mai juyawa na kalli Wildat kafin nayi magana ta juya kitchen din, sai gata da jakan ruwa ta zo tana ajiye musu cikin girmamawa ta koma ta kawo musu snacks tana jera musu, bayan ta koma sai gata da abinci tana kawowa ta ce min. "Allah ya baki nasara an gama;" "Na gode!" Ta juya zuwa kitchen, yadda na musu Barka da zuwa na ga sun waji share nima haka na share nake ta hira sama-sama da Yeemar, tana gamawa ta mike zata kitchen na amshi flat din muka wuce tare, sai lokacin suka sake suna cin abincin. Amma daga can aka kawo fa. Hayaniyar da muka ji a parlourn yasa muka fito, Ijlal ce take musu rashin kunya, ganin haka na juya abina. "Tass!" Naji ƙarar mari, fitowa nayi naga Bilqis a tsaye tana tsumma. "Idan Aneesah ta sayar da kimarta ni jinin zanzabirawa ke yawo a jikina, kazamar yarinya da ke zaki zage mu ki ce mana kwadayi ya kawo mu! Ki sani ni ban daukar reni ko hayaniya na gaya miki, bangaren Zainaba muka ga zamu zauna kazama da wannan low life dinki an wanke ki an kawo ki cikin arziki da yake baki iya ci ba zaki zauna kina iskanci akanki aka fara haihuwa? Banza kazama wacce bata san ciwon kanta ba. Ke kuma Aneesah kin manta abinda Ya Faris ya fada kenan?" Rudewa tayi ta fara ƙoƙarin bayani tasan Bilqis ba sa'arta ba ce dayawa suna faɗin da ace Bilqis a Namiji ta zo tow za a sha fama da ita domin mulkin yana bala'in tasiri kanta kasancewar Uwarta yar Sarkin Hadejia ce. Suna cikin manyan empire na kasar hausa.
Fita suka yi, na wuce kitchen muka gama abinda zamu muka fito parlourn. Wayata da take hannun Yeemar tayi ƙara dauka nayi. "Ki zo ina jiranki!" "Tow Allah ya baka nasara!" Na koma dakina na sauya kaya atamfar Sharaton na saka wacce aka mata dinkin riga da zani, rigar har gwiwata na yafa babban mayafi na gyara fuskana a madubi sannan na shafe jikina da humra da turare na fito, "bari na je na dawo yana kirana!" "A dawo lafiyar Uwar Magajin zanzabira!" Inji Yeemar. "Ke dai Allah ya wadaran bakinki!" "Banda gardama ko na agwagwa za a sake dauka ba laifi muna nan tare!" Juyawa nayi na kalli gefensu Daulah suma Murmushi suke na fita da sauri don ya sake kirana ina sakawa a kunne ya fara mita, da sauri na nufi bangaren shi daidai shigowarsu Umma da Hajja da yan gidan. "Sannunku da zuwa ina zuwa!" Na wuce bangaren shi. "Ina zuwa " na samu Ijlal tana kuka zama nayi ina kallonshi. "Zainab lafiya?" Ya tambaye ni a sanyayye. Zama nayi a kafet a gabanshi na daura kaina akan cinyarsa. Shiru nayi tare da lumshe idanuna. Yadda take kuka sai na tsinci kaina da sake wani irin kuka mara sauti har har jikinsa yana wani irin rawa. Bakiɗaya ya rufe tare da janye kafarshi ya cincibo ni daga kasa ya ajiye ni a kujerar da yake zaune, bakiɗaya ya kidime ita kanta sai gashi ta daina kukan ta tsaya tana kallona. "Kawai zan bar maka gidanka, ka ji da Matarka na gaji ba zaku kashe ni ba, ni dama can ba son aurenka nake ba. Asalima kai kanka kasan bana sonk..." Bakinsa naji a cikin nawa, cikin wani irin tattuasar kiss yake cinye min baki da harshena kamar zai hadiye ni. Cak ya dauke ni zuwa dakinshi domin har lokacin ture shi nake zan kwace bakina. Yana zuwa dakin ya ajiye ni a bakin gadon. Har lokacin ban daina kuka ba. Kanshi ya daura a kirjina. "Kiyi hakuri!" Ya fada a hankali, wani irin kuka ne ya kwace min wanda ban san dalilin yinsa ba. "Kayi alƙawarin hanani kuka, zaka tsaya min dare da rana me yasa ka gagara tsaya min a yanzu? Ka manta Awatif ba zata iya cutar da koda kwaro ne! Ka manta yadda ja ajiye ni na tsawon ƙarni me yasa?" D'ago kai yayi, hasken da ya gani cikin idanunsa har cikin kansa yaji shi a hankali ya dafe kanshi da karfi yana mai rintsa idanunsa, d'ago kai yayi idanunsa Jajjur. "Me aka miki kike kuka?" Ya tambaye ni, "Kawai!" Rike hannuna yayi yana shafawa. "Ya isa haka! Ki mishi uzuri shima dan adam ne kamar ke, Idan ya tsaya miki rayuwarki su tafi haka shiga hatsari, yana sonki sosai kuma zai so ki, ki mishi uzuri shiru da kika ji kwana biyu b son rai ba ne, shiri ake kanku." Shafa fuskana yayi ya cigaba da cewa. "Salamanu Faris yana sonki, sai dai duk yakin da yake a tsorace yake kada ya rasa ki! Boye rauninsa yake wanda ke ce rauninsa, ke yake boyewa amma kin kasa gane haka. " Yana gama fadar haka ya daura kanshi akan cinyata, tare da zama ya kama barci. A hankali nake shafa kanshi ina jin wani irin tausayinsa.

Ganin barci ya dauke shi, a hankali na gyara mishi kwanciyarshi, na saka mishi pillow a kanshi. Wannan ja bargo daga gadon na lullube shi domin yana kwance a kasa ne, koda yake kasar akwai darduma mai laushi, haka yasa ya cigaba da barci, a hankali na bar dakin na ja kofar na rufe a bakin kofar na samu Faruq. "Don Allah yana hutawa kada wani ya shiga."
Gyada min kai yayi, na nufi bangarena, sai ban shiga ta babbar kofa ba na bi ta baya, na wanke fuskana sannan na nufi parlourn da ake ta hira ana raha. "Kaga Fulani Babba mai kwalliya tazo tana ta jiranki!" Gyada kai nayi na nufi wurinsu Umma na gaishe su naga gabansu da abinci. "Sannu Ummana, Kawata ya kike?" Na tambayi Hajja, tsaki tayi ta juya min kai tana faɗin. "Ban da cin amana kina ganina kika dauke kanki" "kiyi hakuri takawa ne ya kira ni!" Tura baki tayi tana faɗin."ai shine kenan kulawa da Murja zasu zo an jima!" Murmushi nayi na dauki wayata da ake kira. "Ok shigo mana!" Abinci aka kawo min wanda na bada odar, aka min. A hankali aka yi ta shigo da shi. Aka sake zuba musu Wildat suka shiga da abincin kitchen, nima na wuce daya parlourna aka min kwalliya bayan na sauya wata lace na cikin kayan aurena. Sannan aka kifa min dauri ya zauna gashina ya sauka a bayana.

Lokacin da na fito masu gyara wurin walima yayi, na ji yana cewa zata yi walima a harabar gidanmu, don harabar gidanta bai da girma nawa kuma ya haɗa da na Nadiyyah ne, haka yasa aka fara gyara wurin kamar farin balloon pink da white, sai ga wurin kafin wani lokaci an gyara wurin ko ina yayi kyau, da yake lokacin da ake kawo abincin yan uwan Ijlal sun gani ba sai rikici ya tashi ba, har wurina Hajiya Mardiya ta shigo wai a tunaninsu abincin da za a yi a wurin Walima ce aka kawo min na rike. Lokacin da suka shigo an gama min kwalliyar. Kallonsu nayi yadda Hajiya Mardiya take hura hanci yasa na zuba mata idanun. "Abincin da za ayi rabonsa a wurin Walima muka ga an kawo miki!". "Maman Amrah ke babba ce kuma duk lalacewa Amrah mun yi zaman makaranta da ita, sannan abincin da kike magana a kai ni na bada kudina ayi min, don Allah ku tafi kada ku kirkiro wata fitina!"
"Su waye fitanannun? Su waye zasu kirkiro fitina?" Murmushi nayi na koma kujera na zauna na daura kafana akan ɗaya. "Jakadiya!" Da sauri ta iso. "Maza ki ce sarkin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login