Showing 216001 words to 219000 words out of 304445 words

Chapter 73 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

48

ta kai bakinta ta shanye ruwan, sannan ta sauka a kujeran ta min godiya kanta a kasa. "Daga yau mun zama kawaye ko!" Na mika mata karamin yatsana, mike ko min hannun tayi na sakala da nawa ta ce min."Kin yi alkawari?" Gyada mata kai nayi da cewa. "Nayi!" Na faɗa mata daga nan ta juya zata tafi na ce mata. "Baki rungume ni ba!" Tana zuwa ta rungume ni, sannan ta fita nima na mike, na ce musu. "Shi fa rayuwar nan sauki ne da ita!" Na nufi bangarenmu.

A yadda Mrs Lilly ta musu bayani, murmushi Faruq yayi ya ce mata. "Indai fiye da haka ne zata yi domin tana da kirki. Nayi mamaki da su Mirah suke cewa bata da kirki daga ita sai Madam Nadiyyah suke da kirki kuma suke kyauta domin ita wannan kyautarta har yayi yawa. Lashe baki William yayi ya ce mishi. "Gaskiya Allah yasa ta mana kyautar yanke talauci!" Dariya Faruq yayi ya ce mishi. "Idan kayi hakuri zaka samu!" Duk bayanin da na mata tayi musu.
Karfe uku na yamma suka dawo, ina daki ya shigo. Ina ta kokarin duba wayata. Da sallama ya shigo yana waya ne. Yana shigowa ya mika min koda bai gaya min ba nasan Mai Babbar daki ne. "Ummina nayi kewarki!" "Da gaske?" Ta tambaye ni, "Allah da gaske Ummina!" "Me yasa baki kira ni ba, kowa ya kira ni!" "Allah sarki Ummina wayata ce ban san meye matsalarta ba, ina ta kokarin ta dawo amma taki." "Ok ba kome ya kuka isa?" "Alhamdulillahi!, ya muka bar ku?" "Masha Allah, sai godiya." Nan muka shiga hira, nayi ta zuba mata shagwab'a. "Mijinki ya ce kwana biyu kina skipping abinci me yasa?" Idanuna ne suka cika da kwalla na ce mata. "Bana jin dad'i ne, amma da sauƙi!" Shiru tayi sai tayi murmushi ta ce min. "Idan kina jin wani ciwo ki mishi magana ya kai ki asibiti kin ji ba a zama da ciwo kin ji!" Kamar tana gaba na na gyada mata kai, ina murmushi domin ina jin yadda take ja na a jikinta. "Na ji Mrs Lilly ta ce kin zaga cikinsu ko?" "Eh!" Na faɗa a hankali ina kallonshi, da ya kafe ni da idanu. Wani irin abu nake ji akan shi ba zan iya cewa ga girman yadda nake jin shi, abu daya na sani shi din wani sinadari ne da yake hada da jini da numfashi na, mika mishi hannu nayi, a hankali ya taso tare da nufo ni. Rungume shi nayi ina sauke ajiyar zuciya, ina murmushi hawaye na cika a idanuna. "Ki yi hakuri idan wani abu ya faru kada ki yi fushi da shi, domin wannan yaran ban sansu a idanun ba, amma nasan da zama su. Ban san me yasa bai gaya miki ba, amma koma yaya ne haka ba yana nufin ya boye miki abu mai muhimmanci ba ne,ba wai basu da muhimmanci ba ne, sai dai su a duniyarsu shi din Santa ne, kin san abinda ake nufi da Santa." Kanshi ya daura a kirjina. "Ki kula da mijinki, bai gaya miki dalilin zuwanku nan ba ko?" Girgiza kai nayi kamar tana gabana ta cigaba da cewa.."za a duba Nadiyyah ce da alamun zasu mata IVF." "Meye shi?" Na tambaye ta ina kallonta, murmushi tayi sannan ta ce ta fara min bayani kamar haka. "
. *IVF* In Vitro Fertilization wato hada maniyyi da kwai a dakin lab. Ana cire kwai daga mahaifar mace, a hada da maniyyin namiji a waje, sai a mayar da ƙwayoyin halittar izuwa ga mahaifar mace, sannan ana amfani da wannan hanyar idan akwai matsalar da mace ba zata iya daukar ciki ba, sannan idan ya kasance bututun kwayoyin halittarta ba zasu wuce zuwa bututun da kwayoyin zasu zauna kafin su zama halittar da zasu shiga mahaifa" shiru nayi ina jin ta sai zare idanu nake a hankali na ce mata. "Ummi su waye suka san da wannan batun?"
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 71

"Iya Mijinki ne sai ita Nadiyyah!" Gyada kai nayi kamar xan yi kuka na ce mata. "Allah ya sa a dace!" "Amin Ya Allah!" Ta furta tana tambayana ko yana kusa na ce mishi. "Gashi nan!" Ya amsa. Can kasa yayi magana da bana jin me yake faɗa kafin na ji ya ce mata. "Madallah!" Ya kashe wayar tausayi yake bani, da alamu barci yake ji. "Tunda na fita ban zauna ba!" Shafa kanshi nayi nace mishi. "Sannu da ƙoƙari!" Yadda na fada ina shafa kanshi ya d'ago kai yana kallona. "Shine kike dauke min kafa?" Murmushi nayi n ace mishi. "A yanzu da na fahimci cewa kai uba ne a gare su ai dole na kula da lamarinsu." Na faɗa ina ƙoƙarin tashi riko hannuna yayi na zauna ya ce min. "Magana kika gaya min?"
"Amma kasan yadda mace take ji?" "Ina zan sani na dai san na dawo da su, daga Party da aka yi na Helina!"
Gyada kai nayi na mike zan fita ya ce min. " Zainaba kin cika kishi, na hana su zama a wurin cin abincin." Dawowa nayi yana zaune a bakin gadon na rike fuskarshi ina shafawa a hankali. "Dole nayi kishinka, dole na guji wata mace akanka musamman wacce ba muharraamanka ba, sai dai idan tazo a ƙaddaran kishiya na yadda na iya xan karɓe ta hannu bibbiyu. Tunda Allah ya halitta maka ita a cikin harkarkarinka."
Kifa kanshi yayi a kan cikina yana faɗin.. "Gobe zan dawo me kike tanada min?" "Hmm!" Na ce ina shafa kanshi. "Nace me kika tanada min?" "Something special!" "Bana son special ke nake bukata?" Fita nayi ya biyo ni da sauri yana mai janyo ni waje, ya rungume ni ta baya. "Me kake yi haka?" Inji Ijlal da ta ga mun fito ina dariya. Bai kulata ba, kallonta yayi yana faɗin. "Akanki muke?" Yadda yayi maganar babu wasa yasa ya kame kanta, haka muka isa parlour ni na wuce kitchen, abinci na fara ci na ji tana ta ihu da masifa, lokacin da na gama na fito na samu yana zaune abinsa bai kulata ba.

"Ina Nady?" Kallon sama yayi idanunsa yana kan jaridar. Can da ya gaji ya bar gidan, dakin Nady na shiga na samu tana kuka. A hankali juyawa nayi zan fita ta min alama da hannu na koma waya take kamar da Iyayenta. Yadda take maganar kawai abar jajjantawa ne balle kuma da take fadar laifinta. Har suka gama magana ta kashe wayar, share hawaye tayi tana faɗin. "Kin ji labarin za a yi min IVF?" Gyada mata kai nayi, hawaye ya zubo mata ta ce min. "An dace dashen da aka yi ya amshi jikina, sai dai inda matsalar take mahaifar bata da kwarin da za ayi IVF, idan aka yi dace aka yi dole zan zauna a asibiti na tsawon wata daya zuwa biyu, Ikhlas na gama sarewa!" Ta fada hawaye na zuba mata sosai. "In sha Allah zaki haihu kema lokaci ne kome yake bukata!" Share hawaye tayi tana faɗin." Na gode sosai!" Murmushi nayi mata domin tafi bani tausayi akan kaina.

"Dazun ake cewa kin zaga gidan nan!" Murmushi nayi na ce mata. "Eh na zaga kan!" Na faɗa muna fitowa daga dakin Ijlal ce ta fito wuce mu zurf. "Wai me yasa kike haka ne? Me yasa kike mana labe?" Inji Nady Da yake cikin ya gama budeta kamar ta rufe Nady da duka, sai ta ce mata.."Wai gara nayi labe kafin ayi tinanin kashe ni da d'ana!" Nayi alƙawarin ba zan kara shiga harkanta ba, amma sai da nayi murmushi na cigaba da tafiya har muka iso kasa, babu wnada ya kulata. Yanayin garin alamar za ayi yayyafin dusar kankara haka yasa ni da Nady muka saka safar hannu da wani hula da ta amsa a wurin Mrs Lilly ta bada kudi a sayo mata. Muna tsaye a wurin na ji saran itacce. Juyawa yayi ta kalli Mrs Lilly ta ce mata.."Mrs Lilly My lord yana can ne?" "Eh shi ɗaya ne!" Juyawa nayi sama da gudu na shiga dakinsa na dauko mishi jacket, na sauko kasa, har sun isa wurinsa ga Mary tana wasa a inda yake fasa itaccen, ina zuwa na nufe shi da Jacket din. "Saurayi kai ne da fasa itacce haka? Barshi ka saka rigar sanyi!" Na mika mishi ina karban gatarin. Amsa yayi yana faɗin.."Ana sanyi ku shiga ciki!" "A'a muje tare!" "Ina son fita farauta ne idan na gama!" "Zan bika!" Na faɗa, "a yawo dare yayi ki bari gobe da sassafe sai mu shiga!" Gyada kai nayi ina murmushi, tsaki Ijlal tayi ta koma gefe ya saka rigar William da yake can ya zo ya kwashe itaccen. "Saurayi me zaa yi da shi?" "Zaa parlourn za ayi amfani da shi wurin shan dumi!" Gyada kai nayi. Ya taso muka wuce ciki, don Jaraba ana wannan sanyin amma ita nanike miji take. Haka muka isa ciki aka kawo mana hot chocolate da cookies, muna ci muna hira, har sun gane ta kofinta yafi na kowa girma, yana kallon yadda take yin abu kamar tana jin ciwo. "Wani abu ne?" "Cikin ne yake min ciwo?" Shiru yayi yana kallonta. "Ko zaku je asibiti ne?" Inji Nady, "ina ga!" Suka mike daga shi har ita suka tafi, da rakiyar Faruq. Ita ina ga tunaninta yau girkina ne, ya ja shi suka fita wasa gaske basu dawo ba sai wurin karfe sha daya na dare. Ta kuwa tashi dawowa da kaya niki-niki, ina can dakina ya biyo ni yana kallon yadda nake kallo a wayata. Jingina yayi da bangon dakin yana mamakin yadda na share shi. Nima kallo ɗaya nayi mishi, na sauke kai ina mai cigaba da aikin da nake. Ko haushi ya ji ya saka kai ya fita, tab'e baki nayi. A bakin kofar ya same ta tana tsaye. "Wai ke Yaushe zan gaya miki, ki daina makalewa mutane? Wallahi kika ishe ni gida zaki koma ki haihu a can!" Jin haka yasa ta kame kanta ta wuce daki.

Washi gari ina barci Bayan sallah asuba, ya shigo dakin ya kwanta a bayana yana lallubana, buge mishi hannu nayi ina faɗin. "Kin ce zaki bi ni farauta!" "A'a ni babu inda xan je da wannan uban sanyin." Murmushi yayi ya janyo bargon ya rufa mana, ya juyo da ni ina fuskantarshi. Muna ta hira sama-sama. "Nady tana cikin damuwa ita ta koro ni nan!" "Me yasa to?" "Mahaifar ce!" Tashi zaune nayi na kalle shi na ce mishi. "Ka nimo mana ruwan zam-zam, da dabino. Sai ya'yan zaitun man habbatusuadat, da yayanshi." Gyada kai yayi janyo ni jikinshi. "Za a nimo!" "Yanzu nake so!" "Dole ne yanzu?" "Dole ne fa!" Ganin na dage sai ya mike tare da fita a dakin, na sauki kasa. Na samu Mrs Lilly na gaya mata abinda nake so da wanda zata hada min, sannan abincin Nady a sauya mata daga wanda muke ci bakiɗaya. Bayan awa guda sai gashi nan ya shigo. Karkad'e mishi kafada nayi na amsa. Na wuce ɗakinta tana kwance. "Idan kika kashe kanki a damuwa akwai gurbin mata biyu ki rufa min asiri ban shirya rike muƙamin uwar gidan mai Capacity ba." "Zainab Please ki je waje bana son magana!" Ta fada tana kara jan bargon, zama nayi a dakin kafin na hada kayan. Na fito kallonshi nayi na ce mishi.."yaushe za ayi aikin?" "Sun ce nan da kwana goma sha biyar!" "Ina da chance na sauka kenan?" "Tare zamu yi?" Ya fada yana rungume ni. Gyada kai nayi muka cigaba da zama na ce mishi. "Kayi mana istahara idan da alkhairi tow idan babu alkhairi sai mu barwa Allah kayansa." Gyada kai yayi.

Daga ni har shi azumi muka dauka, kamar Ijlal tasan abinda yake damun Nady ta shiga wasu abubuwan. Ana gyara gidan da alamar an kusa haihuwa sannan ana kara gyara dakin Babyn da yake cikin nata. Idan ta ga Nady tayi ta abinda zai saka Nady barin wurin. Ranar da muka tashi da azumi muka fara sauka shi ya dauki izu talatin ni talatin itama ganin muna azumi bata san na meye ba ta shiga cikinmu,. A wannan kwanakin ban tab'a ibada ya bani wahala ba kamar wannan ranar yake gaya min, yai istahara amma bai ji kome ba, sai dai tausayin Nady da yake ji, nima kuma tausayinta nake ƙara ji. Haka muka cigaba da yi abubuwan da aka sayo na bashi ya bata ta fara ci idan zata yi bude baki da sahur, kuma ya gaya mata abinda nake yi, sai ta kasa magana haka muka yi ta yi har tsawon kwanaki goma sha biyar din nan suka cika cib. Na yarda Ubangiji ba a yi masa dole kuma ba ce mishi ga abinda ake so ya bada cikin sauki. Allah shine Allah babu wani halitta bayan Allah, kudirar shi tafi ƙarfin hasashen mai karatu ko lissafin kimiya da sauransu. Wato da safe ranar da zasu koma asibitin ayi aikin. Suka shirya ina daki ya shigo ya same ni, kallona yake a narke domin rabona da shi tun a adis ababa, koda muka zo ma babu abinda ya shiga tsakaninmu saboda matsalar Nady hakuri yayi ya bar ni. "Do you know i miss you?" "Na sani muje ka karya sai ku tafi." Na faɗa mishi ina rako shi waje, Ijlal ne a tsaye a bakin kofar. Wato a wannan kwanakin da muka yi da na bi na yarinyar nan sai na mata shegen duka, domin babu irin sunan da bata kira ni da shi ba,amma na share ta.

Bai kulata ba wurin karyawa muka isa. Na samu Nady tana karyawa itama a hankali jikinta a sanyayye. Haka muka zauna muna cin abinci, ina zaune a kujeran da take fuskarshi, ita kuwa Iya mai tumbi tana gefenshi ashe girkinta ne kada a ci amanarta, idan nace zan rama abinda tayi min gidan nan yayi mana kaɗan amma na kyale ta bani da lokacinta, haka muka karya da zamu fita ya ce min. "Muna da abubuwa biyu, ni da Nady zamu asibiti ke kuma da Faruq zaku kai Mother makaranta, Please a gama kome cikin aminci!" Gyada kai nayi, muka gama shiri muka fita, ana ajiye su a asibitin muka wuce makaranta yarinyar sai murna take, bayan an gama kome sannan muka nufi asibitin, amma da yake zasu kwantar da ita na tsaya a wani ƙaramin kasuwa muka yi sayayyar.

A can asibitin kuwa kafin su yi aikin sai da aka sake daukar jininta da mata sauran gwaje-gwaje, cikin ikon Allah da kudirarshi sai ga al'amar ciki a jininta, abin ya wuce a fada likitan da zata yi aikin mikewa yayi ya koma Lab din,.aka sake gwajin kai karshe ita ka a kawo Lab din, aka fara mata gwajin, aka yi scanner ga shi can dan tik, alamar bai wani gama zama ba, likitan ya kalleta cikin jinjina da al'amarin Ubangiji ya ce mata. "Me kuka yi haka cikin ya shiga a cikin kwanaki goma sha uku?" Zare idanu tayi tare da dafe kirji sai kuma ta shiga faɗin. "Ciki ko hauka? Ba zaka min aikin bane?" Ta tambaye shi a masifance domin tana kallon kamar likitan ya zare. "Ma ki kwantar da hankalinki ciki fa ya shiga babu amfanin yin wani IVF!" Sauka tayi daga gadon ta dauki mayafin abayarta ta fito bata kara mishi magana ba, Yana tsaye a jikin Lab din ya ga ta fito rai a b'ace. Rike hannunta yayi yana kallonta. "Lafiya?" Komawa tayi jikinshi tayi wani lub, sai ajiyar zuciya take saukewa Likitan ya fito da sauri yana faɗin. "Sir congratulations 👏🏿🎉 Madam tana dauke da juna biyu!" Ji yayi abin ya zo mishi bazata, kallonshi yake kafin ya ciro wayar ya kira Ummina ya ce mata. "Don Allah ki saurari me yake faɗa wallahi ina ji kamar bana ji!" Ya sake tambayar mutumin ya gaya mishi abinda ya fadawa Nady. "Alhamdulillahi! Alhamdulillahi Ubangiji ya inganta, bari na saka mai Bauchi ya min visa nazo na ganta!" "Ummi ciki ne da ita da gaske?" "Baka fahimci maganar da yayi ba ne?" "Ummi wannan cikin na Ikhlas ne nawa bane!" Ta fada tana kuka tare da kiran sunan Allah. Kuka take tana kiran Allah. Har muka iso rungume ni suka yi suka kara kai ni wurin likita ya min bayani, ina ji ban tsaya ba na fito waje na kalli gabas nayi sujudul Shukrah. Nayi kafin na tashi sai kallona ake a asibitin, zuwa yayi ya rungume ni itama ta rungume shi sai kuka muke. Bamu saka rai ba amma bamu cire tsammani ba, haka yasa daga mu har ita muke kuka kamar an mana mutuwa, shi da Faruq da suka fi mu karfin zuciya, basu yi kuka ba, amma idanunsu ya yayi jajur. Magani aka bata tare da gaya mata ta kula banda aikin wahala ko rough sex, haka yasa ta fara sunkuyar da kai, na kalle shi ina faɗin. "Kun dai ji tantabaru!" Suka yi ta min tsaya. Haka muka dawo gida cikin wani irin kauna. A hanya ya kalle ni ta glass ya ce min. "Gaya min me ya dace nayi?" "Ayi sadaka, sannan mu tashi da azumi har a can Nigeria ayi yanka da sadaka a rabawa mabukata!" Haka kuwa aka yi nan gidan Marayu aka kai abinci sadaka, babu wanda yayi wani alamar da Ijlal zata fahimci kome. Washi gari ni da Maid na gidan muka tashi da aikin abincin ana yi ana park dinsa a take away, a katon mota aka.yi ta fita da shi sadaka. Da yamma muka shiga cikin gari yawo kome na gani sai na ce tana so? Gyada kai take haka samu saya ta kasa ci. Wani ikon Allah sai ita ta fimu daukar hakuri da lamarin cikin domin ta dauka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login