Showing 294001 words to 297000 words out of 304445 words

Chapter 99 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

44

Ya fita da sauri sai ga shi da wata irin mage mai shegen kyau, mika min ita nayi ta ce min. Meow, "Baby ismaha!" "Daga yau babu me miki gori, ki saka idanun akan mage na domin zaki ga abin mamaki idan ya faru ki kira tasi'u;" gyada kai nayi ya dauki goron ruwa a daki hannunsa kawai yake sakawa sai ya dauko abin ya tofa addu'a. Yana murmushi. "Malam Junaid yayi ƙoƙari!" Ya bani na sha sosai ya ce min. "Daga yau ko a ina zaki yi kwadayinki babu me kallonki har ya damu. Har Ubangiji ya raba lafiya." Murmushi nayi na ce mishi. "Ai sun kunsan haihuwa yanzu haka yara biyu da kara mishi kaga ya zama hudu kenan!" "Uwargidanshi ba zata haihu ba, saboda sun gama shirinsu a kanta kada ki sake ki bata wani abu ko ki mata wani abu kada ki yarda ki fito idan kika ji an kira ki sau uku ki kalli Ismaha zaki fahimci abinda nake nufi! Kada ki amsa ba ita zata kira ki ba." Dariya yayi ya cewa Ummi. "Sun gama shiri tsaf, Allah ya kawo min ke a daidai gaɓɓar da ya dace. Idan Allah ya sauketa lafiya, kafin a bawa Yaran kome ki basu sauran wannan ruwan goran, gashi nan Meramo domin ko zata dawo ba nan kusa ba ne, zata zo da kanta ne da kafarta ba kawota zaki yi ba, wannan ruwan tun daga madina na zo da shi." Kai jama'a yanzu fa ya dauko min a dakinsa. "Kina ganin kamar fada na yi, daga nan zuwa zanzabira tafiyar Kwanaki arba'in da tara ne kuka zo a cikin awa biyu da rabi!" Wani irin zumm naji, mai babbar daki ta janyo ni jikinta a hankali ta ce min. "Tunda kika ga nazo kin ji nayi magana? Amma saboda yanayin ki ya barki kike magana da shi, shi baya magana ana magana da ba don yanayinki ba da ya kore ki tuni! Baba ba cikakken mutum ba ne, Uwarsa ce mutum kuma jinin zanzabirawa ne, asalin manyan hadiman masarautar, mahaifinsa shehun malami ne a duniyarsu, shi din da sauran yan gidan daga jinsin fararen rauhanai ne, amma basu cutarwa." "Amma Ummi!" "Shiii!" Kallona yayi ya ce min. "Zaki yi yaki da kanki da hannunki, a duk lokacin da kika ji kina son mara mishi baya ki zo ki samu sadi ki zo nan, Uwar Hassan!" Hannu Mai Babbar daki ta saka a jakarta ta dauko katon leda ta ajiye mishi. A hankali ya ja ta buɗe fararen goro ne guda shida, ya dauka yana kallonta. "Ina miki ta'aziyar rasuwar da za ayi miki. Nan da kwanaki talatin ko sama da haka ku tashi ku tafi!"
"Baba titi waye haka? Yarana ne?" Yadda tayi tambayar a rikice ya sake murmushi ya ce mata. "Yaranki zagaye suke da Addu'arki ba dare ba rana in sha Allah sai dai su rakaki ba dai ki raka su ba." Mikewa muka yi muna mishi sallama ya ce min. "Ki yi hakuri kafin a koma tsuhuwar ganuwa zaki ga abinda baki zata ba. Amma don rayuwarki da lafiyarki ki yi hakuri ga wannan ki cinye tas!" Wani ciyawa ce na amsa ya ce mata. "Ku yi hakuri Allah ta sake sadamu da alkhairi, kai kuma Sadi sai naci kaniyarka ba abinda na tura ka ba kenan." Ya cilla ta mishi wani abu ya dauka ya wurga a bakinsa duka. "Ba zasu sake ganinka ba in sha Allah!"......
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 96

Duk yadda naso rike zuciyata kada nayi kuka, sai na tsinci kaina da wani irin ajiyar zuciya, domin ko a cikin hidimar bikin nan sai da Daularha ta zagi Ijlal tas, akan yadda take min tsiya, yadda take ta min iskanci da gori kala kala. Ba halin ta ganni da mutane mun fito da yake bikin ya haɗa manyan mutane, ga Khairat da ta makale min taki yarda da kowa haka yasa nake rungume da ita nima. Matar sakataren gwamnatin jihar zanzabira da ta zo bikin da yake suna da alaka da Fulani karama. Lokacin da ta zo ina can Fulani karama ta saka aka kira ni, ina zuwa na gaishe ta ita da wasu matan. "Masha Allah ita ce surikarku Fulani Babba ko?" Kaina a kasa ina rungume da Khairat ta ce min. "Masha Allah yarki ce?" Kafin na bata amsa Ijlal da ta hango ni ta iso dai-dai matar tana tambayata ta ce mata. "A'a ai wannan sai dai ta ci tayi kashi Yar yarima Abdullahi marigayi ce Khairat!" Daga haka bata kara magana ba tayi gaba, sai aka bar ni da yaƙe. "Ke din baki haihu bane?" Cikin wani irin karfin hali na rungume Khairat na ce mata. "Allah bai kawo ba tukuna!" "Ina sane da ke, domin shi rayayyen nan ne da baya mutuwa, ta ce min kin san yadda Allah ke ciyar da ya'yan kazar da bata da nono?" " Allah yake ciyar dasu, har su girma su kai haifar masu yaran. Kada rashin haihuwa ya saka ki jin kamar Allah baya sonki ne. Yana sonki yana kaunarki shi yasa ya baki Khairat don ya ga karfin imaninki. Ita wancan din Wacece?" "Abokiyar zamanta ce bata jin magana, don tana da ciki ne take mata haka!" Murmushi tayi ya tana faɗin. "Ai sunanta ya dace da ita Fulani Babba taya na zata fuskanci b'acin rai da damuwa ba? Ashe was Queen sauran kuma Concubines ne, shi yasa suke jin kishinta!" "Kai Hajiya Hamdiyya!" "Eh gaskiya ne je ki Allah ya baki ladan hidima da Zainab!" Ta ciro yan tari bibbiyu ta bawa Khairat ta sha chocolate, Ni dai ban ce kome ba karfi da yaji nake danne kukan da yazo min haka na fita cikin mutane da yake walima ake yi, can wajen da babu kowa na nufa ni da Khairat, a hankali na ji hawaye na zuba min. Sai da na lalata kwalliyar sannan na wuce na wanke fuskar na koma daki na kara gyara fuskana. Domin a cikin fadar ake walimar, da nazo zan fito Maluma da suka gayyato a matsayin wacce zata yi nasiha ga Amarya ko ni ban sani ba, na ganta a parlourn Mai Babbar daki suna gaisuwa da yake a gaggauce na wuce ban lura da ita ba, ina ganinta na je na rungume ta ina fadin. "Maluma shine baki nemi ni ba?" Na fada ina jin wani irin sanyi sai tsaya suke ta min mai babbar daki tana ta kallona saboda yadda ta min sanin da ko yaya na sauya tana iya gano ni. "Zainaba ina kwalliyar?" Ta tambaye ni, dariya nayi nace mata"na goge yaya yace nayi kama da yar babyn roba!" Kwafa nayi tun farkon kwalliyar ya kushe, sai na fada mata haka. "Maluma lokaci na tafiya!" Na mike zan tafi ta ce min. "Auta kamar kin yi kuka?" "Ni a'a babu kukan da nayi!" "Ba dole tayi kuka ba, tare suke da Amaryan dole tayi kuka Allah ya bawa Fulani Babba nata rabon!" Inji Jakadiya Iyaami, da ta gyara zama zata fara min addu'a. "Jakadiya Iyaami zo mu je akwai sakon da zan baki!" Tasowa tayi muka fita na ce mata. "Kina tsaye tayi wanann shirmen kada na ji kada na gani!" "Ki yi hakuri Fulani Babba, amma.yadda suke yunkurin ganin bayanki yana da kyau ki fahimci su waye abokan zamannki, Fulani ki bani dama na gaya miki gaskiya!" "Iyaami da nake tsaye akan kafata, akwai wani abu da ya same ni ne? Allah yana kare ni duk wata tsanani yana tare da sauki Jakadiya ki min alƙawarin ba wanda zai ji!" Matar nan yar duniya ce,.sai ta kauda kai tana faɗin. "Ni da zan gayawa Takawa nasan sarai har Umara zai biya min!" Zare idanun nayi na ce mata."Jakadiya umaran zaki ke so?" "Ras uwar dakinmu!" Ta zube a kasa hankalin kowa ya dawo kanmu. "Wayyo Allah na zaki karawa barno masu, Jakadiya zaki a watan azumin nan in sha Allah fatana ki boye maganar nan kin ji!" Wato da ta rangad'a gud'a sai da gidan ya tashi da wani irin yanayi da sauti, kowa sai da ya leko, ta shiga kirari.
"Kai jama'a ku bani fili na wasa ta, dawisu mai ado na musamman, Giwa kike mai tafiyar kasaita. Hadarin kaka razana magirba, tururuwa uwar tattali. Juma'a mai ranar alkhairi. Fara mai farar aniya. Zinariya mai shakin ban mamaki. Zuciya mai kaunar kowani jinsin. Hawainiya mai launin ban mamaki. Iyatu mai yaya dayawa. Kece karamar su kece Babbarsu. Uwar Magajin zanzabira, Babar Yarima Abdullahi, Mamar Yarima Innar shehi. Kun ga Uwar Waliyyai bayin Allah. Jikan kundi jinin Magadan Annabawa, Jama'a ku bani fili na wasa gwanata. Ku bani aron hanci na rangad'a gud'a, Fulani Babba da babban murya kece Zaki cika ahalin Yayari da diyoyi maza da mata, ki haife masu tagwaita." Ban tab'a sanin Salim da Abdulhafiz zasu iya min wannan karar ba, suna cikin gidan sai gashi sun fito kowannensu idan ya saka hannu a cikin aljuhu ya ciro kudi zai dunkulawa Jakadiya Iyaami, tayi gud'a tayi rawa ta kawa tace musu. "Farar safiya mai wayewa da arziki, Umaran da kika bani na amsa!" Wato bakiɗaya wurin ya kaure da wani irin shewa da kabbara, da kyar na sulale na gudu, murmushi Mai Babbar daki tayi tana faɗin.."Ai tunda Iyaami ta tsayar da ita nasan ruwa bata tsami banza Zainaba kenan, hannunta a bude ga zafi a jininta amma zuciyarta sanyi ce da shi kyauta da khairi kamar ba Malam Junaid ya haifeta ba." Wurin walima na koma, ina jin Ijlal tana min magana da gaya min magana ban kulata ba, haka ranar kamu.

Anan tayi a gaban Daularh wanda ya janyo Daularh kifa mata mari, tare da kiranta trash. Anan kowa ya bata laifi kowa ce mata yaƙe. "Da haihuwar irin Amiraah gara ita da Allah barta haka bai bata haihuwar ba domin baki san yadda hidimar Yaran yake ba ne." Bata sani ba. Shi yasa har aka gama bikin muka wuce illori haushina take ciki kamar zata kashe.
Wannan kenan.
Ina shiga motar na rufe idanuna gam, kallona yayi yana shafa gefen fuskana. "Ban san me ta gaya miki ba."
"Ni mai nayi da Allah bai kara bani haihuwa ba?" Rufe min baki yayi da hannunsa, kuka na saka tare da jin kamar zuciyata zata buga duk yadda na so na daure abin yaci tura abin ya dame ni, ya tsaya min a raina. "Ashe kina nufin Allah ba zai jarabce ki ba? Kina tsammani kafin ke ba a jarabci mutane baya bane, Nana A'ishah Allah ya kara mata yarda har Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yayi wafati bata tab'a hauhwu da shi ba, saboda haka Mala'ika Jibrin yake cewa Manzon Allah, ya gayawa Nana A'ishah Allah yana gaishe ta, Allah yana jin kunyarta domin bai bata haihuwa ba. Kin zata Allah baya sonki ne? Ina sonki ya baki miji ya baki dangin Miji, ya baki Uwar miji, ya baki al'umma kowa ya zauna dake sai ya ce miki Alhamdulillahi da ke, kowa sai ya miki fatan ku haihu kema. Kin san gudar da Jakadiya Iyaami tayi na farko ta taso da abubuwan dayawa a cikin gidan. Har Fada aka zo kawo miki gaisuwa. Ana sonki mutane suna sakonki Sarkin baka ya gaya min akwai al'ummar da suka kasance cikin zanzabira suna sonki, saboda ke ce kika kasance kamar Awatif. Ke lu'ulu'a ce, ke uwar Yan uku na ce. Kuma ina jiransu ina jiransu ba zan tab'a sarewa ba, zaki haifa min Yara masu albarka, zaki min gida da Yara yadda za shiga Fada da Yaranmu a kafad'ata, ina kallonsu ina jin kamar na dawo da Mahaifina. Zan kaunaci Yaran zan so su. Kamar yadda nake sonki!" Wannan kalman ya saka na manta da maganar abinda aka min na kwantar da kaina a kirjinshi, har muka isa gidan, har lokacin na kasa sakewa. Bayan sallah isha muka shiga babban asibitin, inda muka hadu da wata likita ina ga shi ya mata magana a ranar sai bamu bar asibitin ba sai karfe daya, washegari da safe muka kara komawa, kai a takaice sai da muka kwashe kwanaki uku masu kyau kafin muka gama ganin likitan tana murmushi ta ce mishi. "Lafiyarta lau, lokaci ne fa amma ai kamar ta tab'a b'arin wasu lokutan ana iya samun haka, wani lokaci kuma ana barin ake mai da cikin, amma idan ta cigaba da shan wannan maganin mu ga ni!" Ta rubuta mana mana magani ta bashi, muka mata godiya. Haka muka fito jikina a mace haka ya bawa Faruq takardan ya sayi maganin ya kawo muka dawo, tuni yan bikin suka tsufa a can, itama Nadiyya ta koma don tunda ta isa ta ga bamu dawo ba, tayi ta jidali da bala'i kai har da kai ƙara.

Sannan wani abu da ita bata ganewa, zuwa yanzu ba wani burge kowa suke ba. Sai da ya gama abinda ya kawo shi muka koma zanzabira. A gajiye sai da nayi kwanaki uku cib ko waje bana fita ina xan iya da wahala. Amarya kullum muna makale a waya, sati daya da bikin sai ga ango har Fadar Mai Martaba, suka zo shi da abokansa, yana shigowa ya cire takalmin shi, kwanciya yayi yana godiya. Tare da karban Ilham hannu bibbiyu, yadda abokinsa yake faɗa da yadda suka ga tarbiyyarta. A bisa al'adar da mace ta zo da irin wannan alfarman, kyautar ban girma suke mata..sannan yau a can dangin Mamansa suna kara cigaba da biki domin Yanzu Ilham ta zama zuciyar Familynsu. har sun saka mata suna da iyawo Funmilayo wace ta bani farin ciki, wannan abin har cikin gidan suka shigo har parlourn Mai Babbar daki, daga nan suka isa dakin Mahaifiyarta suka ajiye mata kayan da suka kawo na godiya, sannan ta ce musu. Su tafi gidan mai Martaba su yiwa Fulani Babba godiya , haka aka kawo su,dama tun jiya take gaya min zasu shigo godiya, tun da Takawa ya gaya min shima, sun iso yadda ta nuna min na tarbe su haka yasa na shiga kitchen na yi musu abinci na musamman, suka kuwa samu muna jefawa. Sun gaishe ni cikin girmamawa tare da godiya, na gabatar musu da abinci da kome. Haka suka yi ta godiya sannan suka ci. Ban tab'a sanin ana kyautar dollar bunch dinsa haka ba, sai da suka ajiye min guda biyu ya zuba gwiwarshi yana faɗin. "Aunty Fulani, ban san me kika hango kika ce nayi nazari akan Zainab ba, amma macen da zan yi alfahari da ita ce ko bana kusa zata iya kare min kanta da martabarta, Aunty Fulani na gode na gode sosai, Kin bani kyauta ni kuma na rike har abada idan kika ga Zainab tayi kuka ni dai ba zan sakata da gangan ba, zan yi kokarin kiyaye abinda zai sakata kuka, ni da Familyna muna son Funmilayo, muna kaunarta she bring joy to my whole life and my family. Na gode sosai na gode sosai, na gode sosai!" "Allah ya sakawa zamanku albarka ya baku zuria ta gari na gode sosai!" A kan kular abincin suka ajiye kudin suna masu min sallama, suka fita, matan gidan sun ji shigowarsu, haka Ijlal ta ga fitarsu. Bayan sun fita na kira Mahaifiyarta ina ta godiya nace mata. "Umma wannan abin ya min girma dayawa!" "Takwara kenan, ban da Allah ya so ta da arziki ya janyo hankalinta gare ki da na daya abokiyar zamanki take bi da ba a haka zata lalace ba, hmmm baki san kome ba ne Yarinyar nan ita taso lalata auren nan da kuka yi ta fadi tashin ya tababtu mai zan gaya miki da ya wuce haka, shi takawa ya sani ai Matarshi da hadin bakin kawayenta suka tura hoton da zai lalata auren duk da boyewan da kuka yi. Kafin bikin shi Abdul din ya gayawa Mijinku yadda kome ya faru har yace ya so fasa auren kece kika mishi magana yayi bincike sai ya samu a cikin gidan nan aka yi abin ya bada number abokiyar zamanki. Mai Babbar daki ta kashe lamarin!" "Allah ya kyauta!" Na furta wallahi sai na ji na mutu a tsaye kambu ana bura uba a Lagos, wato zamani ya zo da kowa son ganin bayan duk wnada ya rab'e ni yaƙe.

Kasancewar bani ce da girki ba, da ya shigo na zauna ina gaishe ya ce min. "Sun je fada suna ta godiya da cewa idan kina sha'awar bude gidan Abinci zasu yi sponsor dinki." "Saboda an ce je ki kya gani mayyar kuɗi nawa ne wannan kuɗin?" Na mika mishi. "Laaa yarinyar nan kudi kike ji da shi tow bani aro!" Ai kuwa na fara kiciniyar kwace kudina. Ya saka cikin babban rigarshi, ai kuwa na ajiye mayafina na shiga niman kudina ni ce har cikin babban rigarshi, na ciro kaina ta wuyar ina murmushi na ce mishi. "Kasan!" Jin hannunsa kan kirjina na yi maza tare da fara ƙoƙarin fita kada a Wildat ta shigo ta gannmu haka, na fara ƙoƙarin fita yayi irin matse ni. "Please ina mahaukacin jin yunwarki ce ba zan iya hakurin jiran gobe ba." Idan aka min ba zan ji dadi ba, na ce mishi. "Idan suka min ba zan ji dadi ba!" Ina jin hannunshi yana d'aga rigar sama." Ni kuma idan ban yi da ke ba ba zan iya rayuwa ba." "Amma a parlour?" "A cushion ma kuwa!" Ya fada a hankali yake rad'a min yadda yake matse, sama sama aka fara kafin wani lokaci ni kaina na fahimci a buƙace yake, wani irin tausayi ya bani yadda yake birkicewa da kuma zumudin kasancewar shi a jikina, bai tab'a irin wannan abin ba sai yau duka-duka da abin da kome minti talatin cib ya kifa kanshi a kirjina yana faɗin. "Yanzu na ji sauki da kamar zan mutu zuciyata kamar zata fashe nake ji!" " Ko baka da lafiya ne?" Na tambaye shi ina kwashe kayana ya rage daga ni sai doguwar riga. "Lafiya lau!"
Ai kuwa da ya wuce bangarenshi zazzaɓi ne mai zafi ya rufe shi, haka suka tafi asibiti da Ijlal ban


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login