Showing 231001 words to 234000 words out of 304445 words
bai wuce minti goma kacal ba, sai ga Alhaji Yarima da kanshi yana yana zuwa ya daka musu tsawa tuni kowacce ta kama gabanta suka koma gidan Ijlal ɗin. Ta kowa yayi ya ce min. "Y'ata muje fada!" Ba musu na shiga motar muka nufi cikin gidan, Mai Babbar daki tana kishimgid'e idanunta lumshe, Ijlal tana zaune tana ta kuka. Abbana da Umma suna gefe baban Ijlal yana zaune sai Hajiya Mardiya,kaina a kasa sai naji na muzanta. Ga Aunty Fa'iza da Goggo Zubaida. Zama nayi Ummi tasa aka bude taron da addu'a..
"Me ya faru ne?" Inji Abbana, kirarin da ake alamar sarki yana tawowa yasa kowa ya shiga hankalinsa.
Da sallama ya shigo parlourn ya zauna a can gefen Ummin, Alhaji Yarima ya labartawa Abba abinda suka gaya mishi tun ranar da ta haihu nake jibgarta. Sannan suka kara da cewa jiya tafiya nayi na barsu babu abinci. Sai da suka gama tas sannan suka tambaye ni meye dalilana. Shiru nayi kafin na fara magana.."Na farko naga ba wani zaman lafiya da ita muke yi ba, batun duka kuwa idan ta ce bakinta ba zai daina saka iyayena cikin lissafinmu ba Allah ya gani ba zan ina.zagi ba amma ni da ita za a rasa mai gaskiya."
"Kun ji ba! Ita Yar masu karfi da iko ko?" Inji Mahaifinta. Kasa magana nayi saboda abinda ya tokare min kirjina. Na ce musu " ya kuke so nayi? Idan akan yarinayr nan ce na ce xan rama abinda take yi sai dai a wayiwa gari gidan ya kama da wuta. How comes Yarinyar nan zata rufe ni da duka akan tana da ciki? Da a lokacin na rama sai an rufe ni na daki mai ciki, a haka na barta ta haihuwa ya zama topic of discussion, da aka ce na bar su da yunwa su me suke yi da ba zasu yi girkin ba, saboda kawai nayi magana ace bani da gaskiya." Kawai na fashe da kuka ina faɗin.."na gaji wallahi ba zan zauna ba. Idan na cigaba da zama ban san me zuciya zata saka ni ba."
"Jiya ya muka yi da kai Salmanu Faris?" Ummi ta tambaye shi, "kin ce ta tafi sunanta za a kawo abinci." Ya fada a hankali, d'ago kai nayi ina Kallonshi a wani irin yanayi. Ban san lokacin da na kara fashewa da kuka. Ina faɗin. "Wayyo Allah na, na shiga uku wallahi gara na mutu ba huta da wulakancin nan!" "Me yasa jiya ka kira ta a gidan sunan?" "Ummi sun ce babu abinci, ba a kawo musu abinci ba."
Juyawa tayi ga Kanwar Ubanta ta ce mata ."ya muka yi da ku?" Gyara zama tayi tana faɗin. "Tabbas an kawo abincin karyawa karfe sha daya an kawo na rana karfe biyu saura, na dare ma an kawo!" "Ikon Allah!"
A hankali ta zuba min idanu ganin yadda nake kukan har da shagwab'a ina kara rungume Umma. "Hajiya Asma'u, yarki sai kin bata mama fa!" Aka saka dariya. "Kun dai ji abinda ya faru. Mai ya faru har Ikhlas ta mare ki?" "Wai kawai don nace tana kafa mana sharuddan akan kada a dawo mata da sauran abinci, nace ai ba daga gidansu tazo da shi ba!"
"A'a ba daga gidan Ubanta ba ko?" Da sauri ta d'ago tana faɗin.."Allah ya huci zuciyarki ba zan kara ba!" "Da ke da ita waye yake niman wani da rigima?" "Ni ce, na je har bangarenta."
"Alhamdulillahi, ina ga ku maza me zamu ce?" "Malam Junaid kayi wani abu!" "Ina ga zan tafi da Auta gida domin hankalinta baya kwance. Da sauri ya d'ago kai yana kallon yadda nake lafewa."ana jibi suna zata zo!" Kallon Mai Babbar daki yake yana son tayi magana amma bata ce kome na domin bai ga dalilin da zai saka a ɗauke mishi mata ba. A hankali ya buɗe baki zai magana Abba ya ce mishi. "Gidanka ne amma kuma har yanzu baka san yadda zaka tsaya ba, Zainab ba za a tab'a tayi shiru ba, sannan kai kuma ba zaka iya da gidanka ba akan me zan barta ana irin wannan zaman? Har ga Allah da Attahiru yana raye da babu abinda zai hana ba a warware auren nan a ayi ba." Gashi dai bai yi al'amar fushi ba, amma kuma maganarshi kamar wuta.
"Malam ba za ayi haka ba, tayi hakuri girki ne kowacce tayi da kanta ba kare bin damo, tunda haka ba zai janyo zaman lafiya ba tow kowa ta girka da kanta, shima kuma ya san inda zai tsaya da kafarshi. Ya ci albarkaci mai babbar daki ta zauna ta kula da nauyin da yake kanta!" Inji Alhaji Yarima, yayi ta bawa Abba hakuri Nima Abba yayi min tas akan saurin hannu, anan yake bani labarin wani da saboda saurin hannu aka kai ga yanke mishi hukuncin zaman gidan yari har abada. Duk da haka na zata maganar girki ya kare ai ana sallamarmu da dare ina kwance ya shigo yana tambayana. "Don Allah ko zan samu farfesun bindin saniya ne Maman Gimbiya ce bakinta yayi kuraje an yi mata a wurinta bata iya ci ba shine nace ko zaki min na kai mata.....
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 76
Kasa magana nayi ban san lokacin da na kama dariya ba, na ce mishi."ba zan yi ba." Na faɗa kai tsaye, zuba min idanu yayi cike da mamaki yadda na fada mishi ba zan yi ba. "Ai ka daina mamaki na daina maka girki kamar yadda nake da, matarka ce ka koma wurinta ka zauna idan ka gama kwana biyunta ka dawo amma ba zanyi girki ba don ni ba baiwa ba ce ba kanwar Uwarta da Ubanta suna nan ba me yasa sai ni? Ok bari na kira Ummi na gaya mata abinda yake faruwa!" Ba musu na janyo wayata zan kira Mahaifiyarshi ya rike hannuna. "Na zata nafi karfin kome a wurinki ne?" "Saboda an maka haihuwa zaka lalata alakarmu? Saboda yarinyar can ta koma yar kunama mai ladabi da biyayya shine zaka manta da alkhairina har kana gaya min ina niman gindin zama? Saboda kyautattawa kake gaya min na zama mai yin abu don a san ina yi?" Murmushi nayi na zare hannuna.."Matarka ce ita, kuma uwar Yarka ka je ka yi duk yadda kake so idan ka dame ni sai na bar gidan nan!" Wannan kalmar kamar watsa mishi wuta nake idan nace sai na bar gidan sai ya zare hannunsa cikin nawa yana mai mikewa ya bar dakin.
Daga wannan ranar na samu kaina, sai ya dauki fushi fa. Ni kuma na ce mishi bai san sunan masu sunan ba, na tattara kome na watsar, ban san yadda aka yi labarin ya kai kunnen Mai Babbar daki, sai dai tazo har gida ta bani hakuri ta ce min.."kiyi hakuri ki yi hakuri, nasan kina hakuri gaskiya na sani Zainab a matsayina na Maryamu matar Attahiru marigayi nake baki hakuri ba a matsayin Uwar shi ba, Zainab zan zuba kafaffuna a kasa don Allah ki yi hakuri!" Ganin zata sauka a kujeran na yi maza na rike kafar. "Wacece ni da zan ga wannan ranar? Allah ya dauke ganina akan ganin kin zuba kafafunki a kasa! Duk inda Uwa ta ke sunanta Uwa ko da kuwa ba ita ta haife ka ba, Ummi don Allah ki ce ya farka a barcin da yake yi, wallahi bayan nan bana bukatar kome sai addu'a."
Addu'a kuwa tana yi,kuma tana kara yi kawai wata jarabawa ce idan ta zo sai Allah, haka muka rabu cikin amincin Allah. Ashe shima wanke shi tayi gaba da baya, ta yi mishi zagin tsamar miya, tare da gaya mishi ya kula da kansa ko yana ji yana gani a mai da shi sakarai. Sannan ta nuna mishi matuƙar iyayena suka ji zai san Allah da girma yaƙe. Haka yasa ya sauko yayi ta niman shiri nima a lokacin na dauko wuta na nuna mishi ai bai isa ba.
Saura kwanaki uku suna ya dauke ni zuwa wurin mai babbar daki, bayan mun gaisa ta ce min. "Yawwa Zainab sannu ka maimaita abinda ka ce da safe!" Shiru yayi yana kallon inda nake kafin ya ce mata. "Dama na ce ko zaki roke ta ne tayi musu kayan snacks?" "Mai nace maka?" "Kin ce ba zata yi ba!" "Zainab me kika ce?" Ta juya gare ni.."Ummi kin yi gaskiya ba zan yi, nima wanda xan yi taron dangina na gama biyan kudin dazun kin gani!" Na tura mata payment recipe din sannan na ce mata. "A bangarena kuwa abincin da zan yi shima na janye abinci zan bada a ayi min domin kada a ce nayi na hana su nima kawo min za ayi! Jiya na shiga wurinta na ji tana faɗin wai na kananenaye shi tow ya je ga ta ga mijinta, su tsara kome ko Nady ce ta min haka kin ji na rantse da Allah sai na kyale ta balle shi da nake zaune a kasan shi,yarinyar da bata kyale shi ba bata kyale kowa ya zauna lafiya ba. Idan aka takura min wallahi zan gudu domin yanzu ji nake na bude idanu na ga bana cikin zanzabira yadda nake jin zuciyata tana ci da wutan nan." Mikewa zaune Mai Babbar daki tai ta ce min."zuciyar na zafi har haka ne?" Tashi tai ta wuce dakinta can sai gata dauke da goran ruwa fari tas ta mika min na amsa na shanye sai lokacin na ga an rubuta zam-zam, can ta kara kawo min wani ruwa a cikin goran ma amma shi wanan baki ne alamar rubutu. "Wannan sauka aka yi akanshi, wannan mahaifinki ya kawo a baki." Sannan ta juya gare shi cikin nutsuwa ta ce mishi. "Gashi nan idan kaso ka nuna musu cewa yar kake mutuwa akai zasu kore maka matar rufin asiri kuwa!" Ta haɗa min addu'a sosai sannan muka dawo ta kuma ce a nan cikin gidan za ayi abincin sunan, muna dawowa yayi ta niman shiri naki kuwa domin jikina shine makamina da ya matsa min nace mishi sai dai ya min da karfi tunda yana da karfi, jin haka zai ya share ni.
Ana gobe suna aka zo aka min lalle da gyaran kai, har da jinina Aunty Yana, aka kuwa yarfa min kitso irin na kanuri, ya zubo har gaba. Lokacin da ake kitson da lalle ya shigo ai sai ya kasa nutsuwa masu kitson da lallen kyauta dubu dari dari ya basu, ni duk abinda yake kallonshi nake na san abinda yake yiwa haka. A bangarena gyara jikina nake shi yasa naki bashi hadin kai, bayan tafiyarsu, ina dafa taliya naji marana yana ciwo koda na duba bakona ne, haka yasa na gyara jikina na sha magani, nasan zai kwaso kafa yazo na ajiye park din always a gefen wurin kwanciyarshi, ai kuwa yana ganin haka lokacin da ya shigo ya kwanta rub da ciki domin naki yarda na bashi damar da zai rage zafi, wannan abin ya tab'a shi ainun. Da asuba, lokacin maran ya tab'a ni na farka na ga abin a tsaye, dauke kai nayi na sauka zuwa ban daki na gyara jikina nayi wanka. N a shiga kitchen na hada tea mai zafi na sha ba sugar ina tsaye sai gashi rungume ni yayi ta baya yana mai daura kanshi a kafadana. "I'm sorry!" Ya furta a hankali, tsigar jikina ne ya mike na yi shiru yana ta goga hancinsa akan wuyana. "Nasan nayi kuskure ki yi hakuri kinji, na gaji da wannan shirun naki is kill me every moment of Sec ina jin shi kamar fitar numfashina, am sorry Maisha!" Juyawa nayi na cire hannunshi a jikina ina kallonshi. "Ni ban yi mamaki ba, amma a zo a tsara maka magana a matsayinka na shugaba ka zauna a kai kayi min adalci? Meye baka sani akanta ba? Ko don ta haihu ko?"
Bakinshi ya kai kan nawa ina jin ko brush bai yi ba ya haɗa bakinmu, kai wannan mutumin mugu ne, daga haka fadar ya ƙare, muka shiga shirin suna ya tafi massalaci, ni kuma na gyara gidana, na karya sannan na kara wanka domin naji daɗin jikina, masa aka kawo daga fada, a gurguje ya karya sannan ya shirya cikin wata farar shadda, ina zaune ya kawo min kayan nima, wata farar lace. Na shiga muka shirya a tare ya ce min, "maza mu karya zamu shiga cikin gidan tare ne." "Tow!" Haka na shirya tsaf, muka karya sannan na shirya cikin wata alkyabba muka fita, duk da ban yi kwalliya ba muna isa muka samu mai jego an cab ado cikin wata irin lace, ni kuma da mijin kayanmu kusan ɗaya, yadda na ga fuskarta yasa na gano akwai wata a kasa, can musu dakin mai babbar daki na shige na barta da yan uwanta, tana ganina ta sake fara'a ta ce min.."ya ce bakya jin dadi?" Gyada mata kai nayi ta miko min ruwan addu'a na sha, sannan ta sake tofa min fatiha na sha, na dan kwanta. Can wurin karfe takwas aka fara shelar an rad'a sunan Yarinyar Zaitunah, kallona Mai Babbar daki tayi ya mike min wani tire rufe da mayafi golden alamun ya tabbatar min duk lokacin da zan ga wannan tiren sako ne mai muhimmanci da kuma daraja. "Yanzu za a so a gaya miki sunan yarinyar ke kuma sai ki bada tukuici da wannan na samar." Ta daura min envalop, sannan ta cigaba da cewa. "Ita kuma Uwar Yarinyar zata kawo miki yar a bisa al'adar masarauta zaki fadi sunanta da kuma sunan da ya dace da ita a kirata. Sai ki bada wannan tiren tukuici da wannan, na sunan Kasancewar Fulani Babba!" Gyada kai nayi na cigaba da gyara alkyabba na, sannan muka fito waje, ina mamakin wannan abun wata rana haka nima xan saka dan wurin Nady haka. Murmushi na sake muka fita zuwa a parlourn, kirari ya iso ya ce. "Kirari ya zo ga Fulani Babba, ina son al'ummar gidan nan su shaida, an rad'a suna Zaitunah, Fulani Babba ki albarkace ni da abinda Allah ya baki!" Mikawa Jakadiya Iyaami nayi ta mika mishi ta d'ago takardan sama taba fadin. "Fulani Babba ta bada tukuicinta, sannan ta fita ta bude takardan aka fara kirga kudin kowa na ji ana rangad'a gud'a dubu dari cib, Hajiya Mardiya ta kalli Ijlal da take zaune ta ce mata.."ba a gaya miki cewa zaki kai yar ga Fulani Babba bane?" Yadda tayi maganar a dan fusace yasa ta mike a hankali ta kawo Yarinyar gabana, amsarta nayi na sumbaci kumatunta da goshinta, ina son yarinyar saboda kamar da suke yi da shi, na ce musu. "Allah ya raya Amiratul Zaitunah." "Sultanah dai!" Ta fada da karfi. Murmushi nayi na ce mata."Gimbiya Zaitunah kika samu tun shekaranjiya Babanta ya kirata da gimbiya na kirata Amiratul Zaitunah ne don gyara sunan da larabci." Na mika mata yar Amrah Yar wurin Hajiya Mardiya ta zo na mika mata tiren na rad'in sunan, ta ce min. "Mun gode! Allah ya kara lafiya da nisan kwana, ya bada zaman lafiya mai dorewa!"
"Amin Captain!" Dariya tayi ta juya ta kai tiren sai gata ta dawo kuma ta zauna a kusa da ni. "Head girl, Amirah, Fulani Babba, Queen of Troublemaker! Sai gashi kin aure Sarki guda!" Murmushi nayi na ce mata. "Haka Allah ya nufa!" Murmushi tayi tana faɗin. "Na ji irin zaman da kuke yi, nasan kin ki ke mutum ce akan gaskiyarki, na san wacece mahaifiyarmu, abu daya zan roke ki, please ki rage saurin hannu, sannan sai wani abu daya da suke amfani da shi, duk wutar da Mijinki zai kwaso don Allah kada ki yarda ku yi fada a gaban jama'a ko a gabanta. Da ace kece kika same ta zan iya tayata fadar sai kin fita amma tunda ita ce ta same ki, zan biya alkhairin da kika yi min muna makaranta duk da bamu yi rabuwar dadi ba, wannan shine abinda zan gaya miki Please!" "Na gode Captain kuma Class president!" Girgiza kai tayi tana faɗin. "Na gode!" Ta juya gare su, murmushi Mai Babbar daki tayi yadda muka yi hira cikin fahimtar juna, sannan aka ce mu koma can gidanmu,suka fara tafiya na tsaya muka dan gyara bangaren Mai Babbar daki, na shiga ɗakinta na mata sallama ta riko hannuna ta ce min.."zauna anan ci abinci!" A hankali na bude masar ce ko ta gidan nan wani ci ba, a hankali na fara ci ina bata labarin inda muka san juna. "Na sani!" Ta fada tana murmushi. "Kin tuna ranar wata laraba da kuka yi fada da ita. Ya ga miki hijab kika ce ko Zanzabira zata hadu ba zaki yarda ba!" Kallon mai babbar daki nayi masa a bakina. "A ranar mun je ziyarar gani da ido, aka yi ta baki hakuri kika ce ba zaki yarda ba! Sai da Principle Hajiya Nuratu Abdulsalam ta zane ta. Sannan aka baki sabon hijab din kika hakura!" Murmushi nayi ina sosa kaina. Ta kara da cewa. "Shi kenan fada ya ƙare a lokacin kuna aji biyu ne ko uku?" "Biyu ne Ummi!" Na faɗa ina kokarin danne dariyar ta cigaba da cewa. "Da na dawo nake bawa Mai Martaba labarin yayi dariya ya ce ai kun tab'a haka da Abdullahi lokacin da ya ture ki ranar juma'a kun zo yawon juma'a ya bata miki takalminki, kika ce ba zaki yarda ba sai an biya miki! Wato ke a biya miki abu bai damunki haka aka wanke takalmin kika yi ta ihu da kuka ya lalata miki takalminki sai da Malam Junaid ya ce miki, ki yi shiru ko ya kira miki yan sanda wai a duniya kina tsoron yan sanda." Rufe fuska nayi ina dariya.