Showing 90001 words to 93000 words out of 304445 words

Chapter 31 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

63

ma zata fito . Daga nan cikin gida ya wuce tun a shigar shi a yadda yake takawa fadawa da sauran al'umma kowa ya shiga hankalinsa. Kai tsaye bangaren mai babban daki ya wuce, tana zaune bayi na mata tausa. Da sallama ya shiga parlourn d'ago kai tayi tana kallon sanyin idaniyarta. Mikewa bayin suka yi shiga yi, aka barshi da ita, kara sanyin AC yayi ya zauna da kyau. "Salmanun Faris!" D'ago kai yayi a hankali ya zuba mata idanun da suka yi jajjur. Gyara zaman shi yayi kafin ya amsa mata da . "Na'am Ummina!" Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce mishi. "Kamar ranka a b'ace yake?" "Eh Ummina!" "Me aka maka?" "Ikhlas!" Tashi tayi zaune ta zuba mishi idanu. "Me yasa meta Kuma?" Kura mata idanun yayi kafin ya ce mata. "Tun fil azal Nasan bakya so na aure na baki fahimci wani abu da saura lamarin auren zuwa Ikhlas ba?" Shiru tayi tana kallonshi mace ce mai kaifin basira amma wannan karon sai aka kifa kanta cikin tukunya. "Ban fahimce ka ba!" "A lokacin da aka nima min auren Iram ba fadi waye ba saboda an san cewa na bar gida sama da shekaru ashirin baya, wasu suna tsammanin na rasu ma. Sannan bayan barina gida akwai Salim da Abdulhafiz, Adam da Abdullahi amma dayawa lissafinsu bai basu ni ne za a bawa Yarinyar ba." Gyada kai tayi rabonta da ta ji yayi irin wannan maganar da ita, tun kafin ya bar gida. "Ina jinka!" " Da farko kowa yasan dole mai martaba ya sake daya mata hudu nan kafin ya samu damar aure ta hudu, , kuma mai martaba bai sake ba mace daya ba balle ayi tunanin zai sake ta hudu ya kuma cika ta hudu ba, kin manta ne?" Mikewa zaune tayi. "Me yasa ban fahimci kome ba!" "An tilastawa Abba auren bayan haka shi kuma da kunya ya auri yar cikinsa ko jikarsa haka yasa ya saka auren wanda a daren Malam yazo suka gana! Bayan fitar shi Mai martaba ya fadi bayan an sanar da tsige shi a kan kujerar shi. mai martaba ya tabbatar ya ajiye wasikar ko yayya wani abu ya biyo a daura auren kada a fasa."
"Kai da baka nan taya ka san da wannan zancen abin shekara daya da wasu watanni!" "Shekara daya da kwanaki dai;" ya furta yana murmushin bakin ciki. "Tow me yasa anyi magana akan Iram aka sauya?" "Saboda bukatar kansu, Mahaifiyar Iram kanwar Alhaji Nafi'u ce, Alhaji Nafi'u ya rasa yadda zai yi tunda Babu Alhaji Saddam wanda shine aka yi yarjejeniyar za baiwa Khalifa auren Ikram, shi kuma Alhaji Nafi'u zai bawa Uwais Auren Iman, Abba kuma ya nemi auren Iram. Ba tare da sanin meye nufin Abba da Malam ba, amma tabbas yarjejeniyar auratayya ya kullum a tsakaninsu, sai dai bayan nan ne aka ji labarin auren da aka daura da Ikhlas wanda a nawa lissafin Alhaji Nafi'u yayi amfani da kanwarshi wurin bijirewa Imam Junaid Gobir wato , Malam ya sadaukar mishi da kyautar yarshi." Kura mishi idanun tayi kafin ta ce mishi. "Kawai aka wayi gari Alhaji Saddam ya ce ya fasa bada auren Ikram ga Khalifa. Wanda haka ya janyo kome kenan?"
"Idan lissafinki haka ne tow ba haka ba ne, Ummina har yau baki harbo kifiyar ba, a daren Malam ya hadu da Abba da Alhaji Saddam, a daren Alhaji Saddam ya rasu, kafin nan sun rusa kamfaninsu na F&F, ma'adinar hako gwal an rufeta. Ummina zan barki haka amma kiyi tunani da kyau,!" Shiru yayi kafin ya ce mata. "Zan kawo ta nan bata da lafiya! Sannan kada a kara hadata da wani likitan ƙwaƙwalwa!" Sannan ya mike yana barin parlourn bayan ya daure ta da lissafin da yasan zata jima tana niman sanin mafita. Ba karamin aikinsa ba ne, haɗawa mutane theory sannan ya yi step back ya zuba muku Idanu kuyi ta lissafin da yasan kafin ku gano gaskiya ya kafa muku hujjar da ba zaku iya cewa kome ba. Zurfin tunani da kaifin basirarsa yasa ake kara riritatta shi a Zanzabira domin gani ake ba za a kuma samun mutane irinsa ba, sannan a bangare guda wannan halin nasa yasa ake farautar rayuwarshi ba dare ba rana wanda ya janyo yake killace a cikin gidansu wanda yake dauke da manyan matakan tsaro. Ko wannan maganar da yazo da ita ba ita ba ce asalin dalilin zuwan na shi, ya zo ya gaya mata zai kawo mata Ikhlas ce. Yasan yanzu sai ta fara bori da dangana laifin ga Iyayen Ikhlas.



Tunda ya fita ya barmu da ita, matar nan take bala'in kamar zata doke ni aikuwa sai ga Ijlal itama, haka yasa na koma gefe guda idan na tuna rayuwarmu ta baya sai nayi ta ganin kamar mafarki nake aka kawo ni nan, amma me yasa ni? Ihun da ya ccika min kai da shi yasa na fara jin kaina yana bala'in ciwo da nauyi, a hankali na d'ago kai, duhu dakin yayi wani dogon abu na gani saboda tsawon ihun da na fasa wanda yayi dai-dai da shigowarshi dakin. Sunkuyarwa da abin yayi sai da kanshi ya shige karkashin kasa, haka yasa na mike da gudu zan fita yayi wani irin fisgo ni. Tare da rungume ni. "Sake ni! Fita zata yi sai ta bar gidan nan!" Yadda nake maganar babu In-in-ina, yasa shi hadani da bango ya fisge dankwalin kaina, ya rufe min idanuna da karfi. "Me kuke bukata?" Shiru aka yi, ya kara daka min tsawa, kuka na saka mishi ina ƙoƙarin magana. "Ni.....!" Ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon Nadiyyah. "Taimaka min!" Wani tsalle ta yi tana faɗin. "Ni Allah ya rufa min asiri ina ganin yarinya ta haukace." Hawaye ne ya zubo min, wannan yanayin da matukar ciwo sosai.

A hankali ya gyara min dan kwalin ya riko hannuna, muka bar gidan. Cikin gida aka kai ni, tunda muka shiga bangaren Mai Babbar daki, ya zauna can wayarshi tayi ƙara. "Ka shigo!" Ya fada yana kallon yadda na takura a wuri guda. Ya sashi kallon kofar ganin kamar akwai mutum a wurin. "Ilham!" Ya kira sunanta, a hankali ta shigo tana raba idanunta. Don Allah ya daura musu shakkarshi ba shiga harkan kowa yake ba, amma idan ka sake ka shi harkansa zaka gane Allah da girma yaƙe. "Ya.... Salman.." zuba mata hargitsatten idanunshi yayi, zubewa tayi akan gwiwarta. "Kayi hakuri!" Bai ce mata kome ba, har Mai Babbar daki ta fito tana kallonsu. "Tayi maka wani abu ne?" Juya kai yayi yana faɗin. "Labe take!" Da mamaki Mai Babbar daki take kallonta. "Akan me?" Cizon lips dinsa yayi yana kallona. "Assalamualaikum!" Sarkin gida ya shigo da Abid da nawwas. Zama suka yi a kasa. "Barka da hutawa Mai Babbar daki." "Hmm barkanku!" Kallona Yaya Abid yayi kafin ya kira sunana. "Ikhlas!" A hankali na amsa mishi. "Na.....'....ma" "Tawo nan!" A hankali na janye dankwalin, sai dai me wasu irin Yaran gwaigwai na gani a gabana cikin jini, ƙaran da na saka yasa dukkansu suka toshe kunnensu, a hankali na zube a wurin a sume. Jijjigani, Ya fara yana kiran sunana.
"When ta fara wannan abin?" Abid ya tambaya ,Nawwas da yake can ya ce musu. "Zai iya daukar sati biyu zuwa uku."
Cike da mamaki yake kallon Nawwas. "Tsawon wannan lokacin ka sani dama? Nima sai yau na san da ciwon?" "Eh na sani amma Mai Babbar daki da Maluma suka ce ba wani ciwo ba ne kawai don bata son auren." D'ago kai yayi ya zubawa Mai Babbar daki idanu. Shiru tayi kafin ta ce musu. "Idan na fito da wannan maganar yan gidan nan dariya zasu min, sannan wasu zasu dauka ko tana haka ne don bata son auren." Zuciyarshi tayi bakiririn. "Idan abu ya faru irin wannan maslaha ake nima ba ayi shiru ba!" Juyawa yayi ka kalli ilham da take zare idanu. "Me yasa kika mana labe?" "Babu kome!" Ta fada muryanta yana rawa. "Bani wayarki " da sauri ta mika mishi video record ya gani zata fara, a hankali ya fara bin wayar wurin kiran ya shiga ya ga Ijlal ta kira, saka wayar yayi a cikin aljuhunsa sannan ya mata alama ta bar parlourn. Tana fita aka fara dambarwa tsakaninsu da aljanun, sosai aka yi ta bata kashi wanda ya haifar da jin ciwonshi domin aljanun sun ji zafin yadda ya hana su sakat, suka dauki wani karamin wukar yanka lemo suka soka mishi a gefen cikin, ba wai ita ta ɗauka ba, kallon wukar tayi kawai sai gashi ya caki gefen cikinsa bai ji tsoro ba, kasancewar shi din tsohon military server ne, Allah da ikonsa suka raba ni da munafukai da suka ce an biya su jinin dan adam suka zo jikina, bai nemi sanin wanda suka turo su ba, amma kuma ya rantse matuƙar suka kara dawowa zai ga bayansu. Suma sun rantse matukar na fita a cikin gidan tow sai sun dawo, duk da yasan zasu iya dawowar amma ya dauki haka matsayin barazana. Daga nan aka wuce da shi asibitin da yake cikin masarautar dayawa sun ce da kafarshi ya je ya kuma koma gida. Yayuna suma sun tafi abinsu bayan sun bada magani ana bani da na hayaki da addu'ar da zan na amfani da shi.

Tunda abin ya faru sai na ga Mai Babbar daki tana kulawa dani, sannan sau biyu tana zuwa duba shi, gefe guda yan gidan kowa ya je ya duba shi, sai yar karamar gulma da yake fita na cewa duk abinda yake faruwa dasu Mai Martaba duk sanadin Abba ne yanzu gashi nan zan raba Yarima Salmanu da Matanshi Ijlal Yusuf Yarimar gabas da Nadiyyah Jamil Chiroma,sannan abin da ya kara basu haushi itama Ijlal yar cikin gidan ne, domin Uwarta kanwar kawar Mai Babbar daki ce. Uban wanda Mijin kawarta Yayanta ne, Ranar ina barci naji tashin hayaniyarsu, ban fito ba domin ihun Ijlal kawai nake ji, abin da ta fada da ya dame ni. "Ummi ban damu ba ya tara mata karuwai da kwarkwarah da sauransu amma yarinyar can ji nake kamar na kashe ta matukar na samu dama zan kashe ta." "Wa'iyazubillahi! Baki da hankali ne?" Can kasa kasa ya ce mata. "Kin gani ba! Ita zabinki ce amma haka na zauna da ita, bayan laifuffukan da take min. Itama wancan zabin Mai Martaba ce haka ya sa zan zauna da su bakiɗaya amma maganarta zai daure ta wata rana. Duk wannan haukar da take Nady bata yin irinsa, me yasa su suka kama kansu ita bata iya kama kanta ba." Tun daga nan ban kara jin duriyarsa ba.
----------------
Yau kusan sati uku kenan, ban saka shi a idanuna ba duk sai na damu musamman da aka ce min ya ji ciwo sanadin rashin lafiyata. Haka yasa na saci jiki na fito tare da nufar unguwarshi, a hankali nake tafiya kasancewar almuru yayi haka bai hana ni fitar ba, kuma an hana ni fita dai-dai wannan lokacin. Idanuna ne ya cika da kwalla, hango yar tazarar da take tsakanin babba gida zuwa na shi. Akwai yar duhu da take tsakanin hanyar gidan haka yasa naji kamar na koma saboda tsoron yadda zan ɗauki hanyar nan ni daya, abu daya ya zo min, na kwafta a guje yadda zan isa ba tare da tsoron kome ba, haka kuwa nayi bakina da ismul azam wato kyawawan sunayen Ubangiji tsarkaka. Na a tarta a guje, gudu fa mai sunan gudu nayi wallahi cikin abinda bai wuce minti goma ba, sai gani a kofar gidan, tab'a get din gidan nayi aka ce. "Waye!" Sake bugawa nayi yadda nake yi idan na fita. Da sauri ya bude yana faɗin. "Barka da zuwa Uwar dakina!" Murmushi nayi ina kallonshi gaskiya na kwana biyu da barin gidan sai naga kamar gidan ya sauya min. "Ba......ba.....!" Na fara In-in-ina. "Yarima yana nan!" Gyada kai nayi ina murmushi. "Allah ya kawo miki sauƙin wannan laluran uwar dakina." "A.....a...a...a...min!" Na fada ina nufar cikin gidan, a yar ma shigar cikin gidan na tsaya na danna bell. Zuwa Mss Doris tayi ta buɗe. Ciro Yar karamar jotter na nayi na rubuta mata. "Na zo ganin Prince ne yana nan?" "Ya ce kowa ya zo kada a barshi ya shiga yana hutawa ne." Gyada kai nayi na rubuta mata . *Ok bari na shiga part dina* "baki da labarin an kwashe kayanki zuwa cikin gida ne?" Ware idanu nayi cikin wani irin rudewa na fara ƙoƙarin. "To ........to...... To ..... To ..." "Kin ga ba gane to to² dinki nake ba, tunda ba waka ba ce dalla bar nan!" "P....l.....e...a...s." garam ta rufe gidan, hawaye ne ya zubo min ban san yaushe suka dawo da Miss Doris ba, can gefe na zauna. A can dakinsa yaji ƙarar rufe gidan garam. Yayi mamaki domin yasan a rules na gidan hatta kwarkwaran motsi is avoid balle kuma ayi ihu ko ƙara me karfi. Wayar shi ya dauka ya latsa number hukuma. "Allah ya taimaki magajin zuriar Yayari! Takawa lafiya Angon gimbiya Nadiyyyah da Ikhlas miji a wurin Ijlal." "Karar me nake ji?" "Ikon Allah karar kuma?" Bari na duba Allah ya baka nasara!" Ya tashi da sauri ya nufi mashigar, hango ni yayi na tsuguna ina shashekar kuka. "Uwar dakina kece kike kuka? Waye ya hana ki shiga wurin Mai garin Zanzabira?" "Ba.......Ba'....tso.....tso ....ro.... Zan.....je gi...."Sarkin kofa a shigo da ita!" "An gama ranka shi dade!" Danna bell din yayi Mss Doris ta bude cikin hayaniya da masifa turus tayi ganin Sarkin kofa a bayanta. "Ke ba na ce ki tafi ba ranka shi dade ba zai ga kowa yau ba." "Wuce ki shiga Uwar dakina, jinin Malamai!" Rab'a gefenta nayi zan wuce, ta tare kofar. "Wannan umarnin Princess Nadiyyah da Ijlal suka ce ta kada a sake ta kuma shigowa gidan nan!" "Ahmm!" Ya fada a bayanta da sauri ta zube kasa tana faɗin. "A gafarce ni My lord!" Juyawa yayi yana mai faɗin "ki shigo!" Ya juya baya yana me barin wurin, shima Sarkin gida ma ya juya ya barta zube a hankali na tsalleke ta na wuce, ina tafiya a sanyaye daidai ana kiran sallah Magariba. Yadda yake ratsa manyan parlourn shi haka nake binsa har cikin study room dinsa. Zama yayi ya juya yana kallon yadda na ke share kwalla. "Sit down!" Dan dofana mazaunaina nayi akan kujeran dakin, ya koma bakin kofar ya ce. "Zan wuce masjid." Ya nufi wani kofa ya tab'a a hankali sai ga wardrobe ya bude hijabs ne sun kai kala sama da goma ya ciro min milk colour ya ajiye min, sannan ya ciro abin sallah, ya ajiye kafin ya rufe ya bude min kofar ban daki sannan ya fita. Ban dakin na shiga nayi alola tare da gabatar da sallah Magariba, ihun da na ji yasa ni mikewa Nadiyyah da Ijlal da alamu sun hade kansu ne sun fahimci ina gidan, sannan a tunanina basu gidan sun dawo kenan, yadda naji ana buge-buge, ya sani fahimtar kofar dakin take bugawa.

Tashi nayi na isa bakin kofar sai lokacin na fahimci ashe kofar da password, ware idanu nayi na ga ana ta jera password amma.yaki budewa ai nasan Nadiyyah ba mutunci ne da ita ba, da sauri na shige ban daki na zauna, ina cikin har aka yi sallah isha ban fito ba, domin Allah ya gani ba zan iya confronting Nadiyyah da Ijlal ba, tsoronsu nake ji. Ina fitowa nayi sallah ina cikin sallah naji an bude kofar ban dakin nasan dai na kai raka'a na uku, ban kai ga yin sallama ba jin yadda suka shigo yasa na sake Sallah na shige banɗaki da mugun gudu ba rufe kofar , jikina yana rawa.. "fito ki cigaba da sallah " dakyar na fito na kalli dakin shi ɗaya ne yana kan abin karatu, sake Sallah nayi ina idarwa na cigaba da shafa'i da wutiri. Wurin karfe takwas, "me yasa baki gayawa Mai Babbar daki zaki zo ba?" Da sauri na nufi wurin sidebag dina, na dauki jotter na shiga rubuta mishi. *Kayi hakuri ban san cewa zan kai warhaka ba ne, nazo duba ka ne naji baka da lafiya ne.* Na mika mishi, kallo daya yayiwa rubutun ya turo min littafin. "Ki mai da hijab dinki, zan mai da ke wurinta." *Tow na gode amma ya jikin naka?* Kura min idanu yayi bayan ya karanta. "Da sauki!" Ya furta hankali yadda yayi maganar ya sani sake kallonshi, hankalinsa yana kan abinda yake yi. "Ban cika son ana kallona ba!" Da sauri na mai da jotter din kirjina, ina mai dauke kaina daga gare shi. "Kada ki kara fitowa Ummina bata sani ba kin ji ko!"....
*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500N
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: Sunkuyar da kaina ƙasa nayi, ina wasa da littafin da yake kirjina. "Gobe xan tafi wani aiki Abuja!" Yayi maganar da alamar yana son ya ga reaction dina ne sai aka yi rashin dace sam ban ji wani abu a tare da haka ba, motsa bakina nayi nace mishi. "Allah ya tsare" da mamaki ya ke kallona kafin ya kauda kanshi. "Ki tashi Faruq yana jiranki;" sai lokacin na samu damar d'ago kai na saci kallonshi a hankali kafin na mai da kaina ƙasa, "ina jin tsoronta!" Shiru yayi kamar bai ji me nace ba, ya cigaba da aikinsa can ya d'ago kai ya kalle ni kafin ya ce. "Goya ki zanyi?" Mikewa nayi da sauri, ina gyara zaman hijab dina, ya saka kai zai fita nayi maza na rufa mishi baya, har kamar zan ci tuntube na fadi a bayanshi. Sai da ya ja ya tsaya kafin nima na tsaya. "Ki nutsu!" "Tow!" Nace ina me sunkuyar da kai, a hankali muka ratsa koridon mai dan duhu. "Prince!" A


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login