Showing 243001 words to 246000 words out of 304445 words

Chapter 82 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

101

kuma kafin ya sake ni yana faɗin. "Amin zan yi kewarki!" Shafa fuskarshi nayi na ce mishi. "Nima haka!" Na fada ina murmushi. Haka ya gama tsayuwarsa sannan ya shiga motar.
**
A bangaren Ijlal kuwa ba wani kulawa take samu na jego ba,kawai sun mata sanadin ta bar gidan Mijinta, Hajiya Mardiya ta watsar da ita, sai da Amrah ta gaya mata ta ce mata. "Kin a biye musu zasu kai ki su baro wallahi ko ya koro ki barinki zasu yi ki ta fama da kanki!" Kuma abinda ya faru kenan. Duk wani kulawar da ta dace ta samu bata samu, sai faman daurata akan yadda zasu ga bayan Ikhlas. Kwanta biyu wata yayarsu Hajiya Mardiya wato Hajiya Karima tazo daga kano, Hajiya Mardiya bata gida har lokacin Ijlal bata ci abinci ba, ta ganta sai a hankali yarinyar ma bata yi wanka ba. Fada sosai tayi mata sannan ta saka Ijlal ɗin tayi wanka ta kwashe namar sunanta ta shiga kitchen ta dafa mata tuwon masara miyar kukan wnada ya ji daddawa da kayan kamshi ga nama, sai ga shegiya ta cinye tas, ta dama mata kunun tsamiya ta shanye domin tazo da kayan. Ta kama yarinyar ta mata wanka ta saka mata kaya, kayansu da suka yi datti ta wanke tayi ta mata faɗa kamar zata dake ta, sai dare Hajiya Mardiya ta dawo ganin yayarta sai ta fara kame-kame, ta mata wankin babban bargo sannan ta ce mata. "Kin san ba zaki iya kuka da ita ba me yasa kika mata sanadin da mijinta ya koro ta? Sannan kin barta bata karya ba, har azhar wani irin zalunci ne haka? Gaskiya hakkinta kawai ya ishe ki duniya da lahira, domin ai ba haka kika yiwa Yaranki ba." "Zan kaita wurin Inna zan ajiyeta a can ta zauna zata fi samun kulawa." Kame-kame nan dai da ta saba ta cigaba da yi. Washi gari asuban fari ta haɗa ruwan wanka ta yiwa babyn sannan tayiwa Ijlal ɗin, kafin karfe takwas ta gama gyara su sannan ta kawo musu abincin da ya ji man shanu, ta ci ta koshi. Ta daura da kunu ga ruwan surki, ba sai ga yarinya ta sha ta koshi babu yunwa.

Da yake Hajiya Karima masifaffiya ce, lokacin da ake bata labarin Ikhlas tayi tsam da ranta, ta ce musu. "Ba zan tabbatar ba sai na gani da idanuna. Don haka xan je gidan!" Haka ta shirya da tsarabatar, domin ita irin mutum nan ne masu fada amma bata iya cutar da kowa sannan Allah ya mata wani irin baiwa matukar kai mugu ne kai tsaye take jin haka a ranta, kafin ta fita ta kalli Hajiya Mardiya ta ce mata. "Mugun nufin da kike kulawa ba zai kai ga nasara ba, wallahi ki daina wallahi ki daina kafin lokaci ya kure miki, sannan ki bar janyo Yar Zaitunah cikin lamarin nan!"

Haka ta fita zuwa Fada.

Ina kwance wurin karfe biyu na rana aka buga min kofa, Wildat da take parlourn a kusa dani ta mike tana me nufar kofar ta bude, Jakadiya Iyaami ce tare da wata mata suka shigo tashi zaune nayi ina murmushi duk da yanayin fuskartar ya nuna min kamar nasanta amma bana ce ga inda na santa ba. "Sannu da zuwa zauna Hajiya!" Domin da hakorin Makkanta har guda biyu, murmushi tayi tana me zama tana faɗin. "Na gode Zainab Fulani!" Murmushi nayi, sannan na kalli Wildat ta wuce kitchen. "Sannu da zuwa Hajiya ya hanya?" Kafin ta bani amsa na kalli Jakadiya. "Daga ina take?" "Yayarsu Maman Fulani karama ce!" Haba ashe da Hajiya Mardiya take kama, murmushi nayi a karo na biyu bayan ta amsa min tana kallon gidan. "Sannu da hkauri!" Ta ce min lokacin da Wildat ta kawo mata kayan sha. Jakadiya ta juya ta fita daga cikin gidan. Zama yayi da kyau tana kara kallona. "Kina da kirki, yadda kika ji an ce ni Yayar Hajiya Mardiya ne baki sauya fuska ba balle ki kawo wani abu ranki. Sannan kin amshe ni hannu bibbiyu ba tare da tsoron kada na miki wani abu ba, lallai Allah yana tare da ke domin nasan da ace Mardiya ce da an samu matsala, na ji ana ta labarin mugun halinki da son fitar da Ijlal waje shine na zo na ga wacece haka me kika taka?"

"Allah ne a gabana, Allah ne a bayana Allah ne a dama na, Allah ne a haguna, rayuwata ta Allah ce ba ta namiji da zai kai ni kogon halaka ya baro ba, ni Iyayena basu koya min kome ba sai rokon Allah idan na roke shi zai bani idan bai bani ba jinkirta min yayi, akan me zan damu kaina da lallai sai na mallaaki abinda bani da shi? Akan me zai na samu abinda bani da iko da shi? Shi fa Allah shine rayayyen nan da baya mutuwa, shine wanda yayi sama ba tare da taimakon kowa ba, Hajiya idan ban yi kashi ba Allah ya kulle min cikina kaf duniya babu me iya saka ni dole na haihuwa. Wannan rayuwar kaf dinta dan kaɗan ne bai kai wanda zan zalinci kaina da shi ba, idan kika ga mutum yayi zalinci aron lokaci Allah ya bashi domin ya gyara kafin lokaci ya kure mishi, Alhamdulillahi da ni'imar da Allah yayi min ya kuma kara min lafiya!" Gyada kai Hajiya Karima take, tana murmushi ta ce min. "Indai yadda kike ne, ba dai mutum Zainab sai ta Allah ki zama mai yafiya da niman Allah ya yafe miki kuran-kuranki!"
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 80
A hankali muke hira da har aka kawo mata abinci, ta ci sosai sannan da zata tafi na hada mata kaya itama ta mika min kayan da ta kawo min tana faɗin. "Na san zaki ji tsoron amfani da su, idan ranki bai kwanta da kayan ba ki yi kyautar da shi ba laifi ai kare kai ne. Yadda ta fada sai kunya ta kama ni na mata godiya aka dauke ta a motar har gidan Hajiya Mardiya. Nan ta shiga ta kalli yan uwanta da suka zo gaishe ta, zama tayi a hankali tana faɗin. "Yarinyar nan kada ku matsa lallai sai kun fitar da ita domin Allah yana tare da ita!"
"Hajiyar Kano kin san makircin yarinyar nan kuwa?" Girgiza kai tayi tana faɗin. "Bata kai ku makirci ba, a buɗe take idan har kasan ni tow yarinyar nan kusan yadda nake haka take!"
Duk yadda suke so mata bayani fir taki sauraronsu.
***
A bangaren Alhaji Nafi'u, ya rasa yadda yake ji akan wannan lamarin domin akwai abinda yake bukata amma yawan yadda Faris yake damunsa yasa shi cire ranshi akan kome sannan Yaron nan yana da sanayya a ƙasa, duk yadda yayi tsammani abin ya wuce haka don haka ya kira Musharraf. "Ka kyale shi yayi yadda yake so, kada ka sake ka bashi goyan bayan gwamnati idan ta kware mishi muna nan zamu zare kanmu!" Da wannan ya ajiye maganar Sarki Salmanun Faris.

***
Da yake kanshi yayi zafi bai da lokacin kanshi wani bin daga ya fita ba zai dawo ba sai dare, sai na masa uzuri. Ina zaune bayan Isha sai ga kiran Ijlal ya shigo min. Ban da numberta gaskiya da na gani sai na dauka na kara a kunnena.
"Azzalima muguwa, Allah ya isa tsakaninmu da ke, shegiya jinin karuwai, yar matsafa Jikar yan bori, in sha Allah kamar yadda kika hana shi zuwa ganinmu ke da haihuwa sai da ki ga wani yana yi in sha Allah."
Dariya na saka na ce mata. "Lallai Abba ya iya aiki alhamdulillahii tunda bai je ba aikina ya ci kenan, zaki maimaita bayanin nan a gaban jama'a da ni kike zancen." Na fada mata, maganar banza da cin mutunci babu wanda bata min ba. Daga karshe ta ce min. "Ai gaki ga mijin bari muga yadda zaki yi da shi karuwa kawai!" "Alhamdulillahi tunda ma kifar da mijin ya kasa motsi fa sai dai hakuri, batun xan gani kuma zan baki mamaki." Har ga Allah maganar zan gani ya dame ni, amma sai na kira Maluma na gaya mata yadda muka yi da Ijlal dariya tayi tana faɗin. "Ai ba kome ba ne akan wanda Uwar mijinki ya gani, kin tab'a jin labarin irin azabar da ta sha a hannun Fulani Balkisu da Fulani Hadizatul kubra? To ba zan baki labari ba, koda jinya kike idan har akwai abinda zaki rike ya baki Mijinki da Masarautar ba tare da kin sauka akan turban Annabi Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, ki rike akan Salmamu Faris baji ba gani Mijinki ne alfaharinki ce, kece suturanshi kece rufin asirinsa, kuma kece nutsuwarsa, na haneki da dukar kowa amma idan aka ce kishi ne ban hanaki yi koda kuwa da sa'ata ce kiyi ƙoƙarinki domin rike Mijinki, na ji labarin Hajiya Mardiya da aikinsu da nufinsu har nan dakina aka biyo ni, ni dai ba zan kai ki wurin malami ko boka ba, domin nasan saukarki na farko a gabana kika yi na biyu a Riyadul, don Allah na hadaki da babban malamin malamai Alqur'ani domin a cikinsa babu maganin da babu sai na ajali, idan kin sake Mijinki ya juya miki baya kece idan ya tsaya a bayanki kece, nawa kuma zan hana idanuna barci domin ke! Don haka barci ba naki ba ne azkar dinki yafi hiranki yawa. Daga yau kuma a fara yin abincin sadaka ana fitarwa wani yayi rawa balle ɗan kamad’i!" Wato Allah yayi mana ni'ima da ya bamu iyaye na gari, tun da muka yi haka na fara karatun Alkur'ani, na raba shi gida shida, izu goma duk bayan sallah lokaci biyar, wanda ya bani damar kwana shida ranar na bakwai na saka a matsayin ranar sadaka da sauka.

Ina farawa kuwa mijin dama ya zama busy, nima kuma nayi wanka sai na rungume bautar Allah ba dare ba rana, a cikin kwana biyar na wayi gari da bana shakkar kowa bana jin wani tsoron kome kawai Allah gabana Allah bayana hagu da damana Allah ne, sama da kasa Allah ne. Ranar da zan gama ya fahimci sauka nake ina zaune ya ce min. "Saukarki zai kai kwana nawa?"
"Ina ga na tsawon wata shida ne? Ko ya zama na har abada ina yi sai ranar da na kwanta dama!" Jinjina min kai yayi ya ce min. "Kin ce zaki fara abincin sadaka ko?" Murmushi nayi na gyada mishi kai, zama yayi a gefena ya ce min.."kina ta guduna!" "Ni ban guje ka ba." "Ok shine kika dauko saukar Kur'ani?" "Don kai fa dani da future kids dinmu nake yi fa." Jan hancina yayi ya ce min. "Good girl! Ok Mai zan samu?" Ban san lokacin da na ce mishi."ai fa ka ji matsalarka kenan baka iya samun wuri ba!" Tashi yayi ya dauke ni cak zuwa dakin ƙoƙarin sauka nake ya ce min. "Amma kin san nayi hakuri ko?" Shiru nayi na rike kanshi, muka shiga raya farillan soyayya daga wancan corner zuwa wancan daga karshe muka dira a gadon sunnarmu.
Washi gari kuwa ya saka aka yankan rago da abincin sadaka, aka gama kome aka zuba a takeaway, koda na gani nace a raba, a hankali kome yake zuwa min a cikin sati biyu da muka yi bai tab'a gaya min baya samun zuwa wurinsu, sai ranar wata juma'a da na shiga fada gaskiya inda na tawo ma Mai Babbar daki dambun nama da kilishi, an kawo min daga gida ne, ta amsa da farin ciki, muka yi ta hira da ita anan take tambayata. "Kinji labarin Amiratul Zaitunah ba lafiya?" "Innalillahi me ya same ta?" "Kin san da yake aiki ya sha kanshi baya zama kuma ya gaya min kullum yana waya da ita amma tana gaya mishi tana kuka, mun zata irin na rikicin nan ne ashe yarinyar bata da lafiya ne, hmm amma da sauki domin ko jiya yana can tare da su." Sai yanzu abin ya fado min ashe jiya da yayi dare a can ya makale, da ya dawo ya ishe ni da fita cikin dare ashe abinda ya faru kenan, murmushi nayi na ce mata. "Ban sani ba, da na sani zan bishi muje Allah ya bata lafiya!"
"Amin Ya Allah!" Ta amsa min muka cigaba da hira, abin ya dame ni amma sai ban yarda na gaya miki ba ko na mishi magana, da dare ina zaune a parlourn ya shigo ya shirya zai fita cikin kwalliya. Kallo daya nayi masa na dauke kai ina cigaba da abinda nake. Ko ya tsargu ne sai ga shi ya dawo ya zauna yana ta kame-kame. "Ban gaya miki ba. Amiratul Zaitunah ba lafiya." "Mai Babbar daki ta gaya min!" Yadda nayi maganar ya sashi dan razana. "Ta gaya miki?" "Eh wani abu ne?" Na tambaye shi ina kallonshi. "A'a kawai nayi mamaki ne, da kika sani baki yi confront dina ba." "Akan me? Zan fuskance ka na tambaye ka me yasa baka gaya min yarka ba lafiya ba? Ko me?" Na tambaye shi ina juya kaina yana wani irin ƙara. "Hmm!" Ya ce na ce mishi. "Allah ya bata lafiya." A raina kuwa zai ga bura uba, ya dawo min gidan nan cikin dare da ni yake zancen. Haka ya mike ya fita na tashi na rufe kofar gidan na saka key a jikin kofar shiga gidan na wuce na kwanta. Kusan raba dare nayi ina addu'a da karatun Alqur'ani. Kafin na kwanta wurin karfe daya saura ya shigo yana buga min kofa, Omo na gyara kwanciyata kamar ban ji shi ba haka ya gaji ya koma bangarenshi. Da asuba na tashi nayi wanka nayi sallah har sai da garin yayi sake na kwanta. Ina jin yana buga kofar ban bude ba, sai da naji al'amar ya bar gidan na tashi na bude masu aiki suka shigo suka gama aiki, da na gama kome iya cikina na rufe gidan, bayan na sallami kowa karfe bakwai ya shigo ina jin shi yana kirana a waya wallahi ban bude ba.

A jere na hada kwana uku cif ba sai ga Maluma da Hajja ba, ranar wata juma'a ranar da na cika kwana na biyar. Maluma tana zuwa ta min dakuwa na kama mata dariya, zama tayi tana faɗin. "Kina hauka ne? Taya zaki saka mutum da girman shi ya janyo wasu abubuwan a fada, jiya ya turo Alhaji Mamman Abba yayari ya zo ya bawa Abbanku hakuri ya miki laifi yau da ana saukowa juma'a sai gashi da kansa ya zo me kike so?" Murmushi nayi na ce mata. "Maluma me xan yi mishi? Ta tashi ina ihu kamar mahaukaciya? Maluma ni ba zan yi irin kishin da matasa suke, amma wallahi billahi azim ya sake ya kara min abinda yayi tow ya daina ji ko gani daga gare ni, shi mai baki har ya kai kara!" Ashe Mai Babbar daki tana bakin kofar itama an turo ta biko. "Maluma Matarshi ce, ban hana ba ban tab'a mafarkin hana shi sabgar iyalinsa ba. Amma taya zai tayi can ya raba dare sannan ya zo nan ya ce zai d'aga min hankali, shi ta rike shi ni nan ya hana ni barci haba gara ta dawo idan kishin zata yi sai tayi da hujja ai tayi banza tunda ta zauna a can tana iko, Maluma ki kyale wannan yakin tsakanina da shi ne, idan aka cigaba da haka kowacce ta kwaso shararta zata zuba mishi kuma nima zai watsa min. Taya xan yi shiru na zuba mishi idanun akad'a shi a can ya zo ya min rawa anan!" "Kaniyarki, sai me mata dubu nawa aka yiwa haka?"
"A'a Hajara kyaleta ta kwace kanta, Mardiya bata da mutunci idan ta kyale su zai zame mata abin tsoron nan gaba Kuma da nasan haka ne tow da ban zo ba." Ni dai ban hana shi zama ko zuwa ba, amma ni b aza a hanani barci ba, ina girmama barci Hajja ta ce min. "Kin kyauta haka duk wata mace da tasan ciwon kanta take, idan kika bar karamar matsala tow wata rana zata zame miki babba kuma ba yadda kika iya gara ki maganceta. Tun kafin ta ishe ki!"
Ba sai ga Ummi da Hajja suna daura ni akan hanya, Ummi tana gaya min wasu sirrin suratul Yusuf da Rahaman, tare da sirrin Fatiha, akan nayi ta karantawa ina tofawa a zuba ko na rubuta da zuma ina sha, kan Uba tuni Maluma ta ce zata kawo min, bayan tafiyarsu ya shigo yana wani kame-kame sai ya bani tausayi haka Allah yayi shi a wurin maza dodo ne, ga mata kuma lusari ne. Bai da katabus akan mace mayen mata ne ko nace namamajo ne shi, kina bude mishi wancan wurin wallahi zai manta da kome, a daren ya jiyar da ni dadi da ban hakuri, washi gari ya rufe min idanu, hmm mutumin nan passport ne na zuwa umara. Sai na kasa magana ina rungume da shi, muka sake lulawa duniyar dad'i. Har gidansu Ijlal ya kai ni na ga babyn ta rame sosai, sai manya idanu irin na Ubanta. Da yake ba'a son na taɓa ta nima ban karbeta ba, na bar taba hannun Ubanta, kayan da muka zo da shi ta ajiye mata, sannan ya ajiye kudi ina latsa wayar hannuna. "Zamu yi tafiya na sati biyu zuwa uku ni da Zainab!" Jin sunana yasa na d'ago kai. "Bura uban can! Wallahi ba zai yiwu ba akan me zaka tafi da ita don munafunci! Sai ka dauko min ita ka kawo ta!"
"Sadauki ina jiranka a waje!" Na mike na bar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login