Showing 57001 words to 60000 words out of 304445 words

Chapter 20 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

81

shiga ya zauna, yana nazarin abinda yake faruwa. "Major Emeka Ize zan kira?" Kallon gefen hanya yayi, jin yayi shiru yasa shi tuna kalmansa. "Wa kake gani zamu kira?" "IG!" Faruq ya bashi amsa, "shi kenan!" Ya furta a hankali, kafin suka cigaba da tafiya suna isa cikin gidan ya ce mishi. "Kafin a kawo yarinyar nake son jin ya fito!" "An gama!" Faruq ya amsa mishi, yana nufar kofar cikin gidan masu busa algaita da kad'e kad'e suka fara, bai wuce haka ba sai da ya ciro kudi me yawa daga aljuhun wandon rigarshi ya damkawa Sarki kofa ya wuce.
Bangaren Hajiya Hadiza ya nufa ya gaida ita, cikin girmamawa yaranta suka taso, suka rungume shi aka yi hoto dasu, daga nan suka nufi bangaren Hajiya Balkisu itama gaishe ta yayi sannan yayi hoto da kanenshi na bangaren, bai yi da iyayen ba kasancewar suna takaba sannan sati biyu kenan da rasuwar Abbansu, koda ya ce ba zai yi wani abu ba wasu ba zasu yarda ba, tunda gidan Alhaji Rilwanu yanzu haka biki ake sosai.
Sai dai a na shi baa wani saka za ayi bikin can ba, wanda bai samu na farko bane aka matsa sai sun mishi. Bangaren Fulani karama ya shiga Ilham da yan uwanta suma su kayi hoton ya fita tare da nufar bangaren Mai Babbar daki, ba laifi an cika sosai, yana shiga ya gaishe su sannan ya nemi wuri ya zauna a can gefen Mai Babbar daki. So take tayi magana amma ta rasa yadda zata yi, wata cousin din Mai Babbar daki ta ce mishi. "Banga Hajiya Hamaza ba, kuma ita ta kamata a ce tazo an shirya tafiya dauko Amarya da ita!" Mai Bauchi da kanshi yake kan wayarshi ya ce mata. "Ai suna gidan Bbaa Mamman sun ce zasu zo, suna shirya kayan saka lalle ne da ba a kai ba jiya!"
D'ago kai Mai Babbar daki tayi cikin fushi ta ce mishi. "Kada ku manta dai makiyin mu ne Junaid. " Mikewa Faris yayi zai bar parlourn ta ce mishi. "Zaka tafi ba don na zagi Masoyinka!" Komawa yayi ya zauna yayi shiru. "Ba dole kayi shiru ba, idan ni ce Nadiya wallahi sai ka ga iyakanka!" A ranshi ya ce ita. *Mai Babbar daki tafi Nady daukar kishi*
Haka tayi ta masifa tana gaya mishi ita bata dauki Ikhlas a matsayin Suruka ba, tun wuri kada ya kawo mata ita, Nady ce zabinta, sannan ya kwana da sanin ba wai zata kyale shi ba, itama bayan Nadiyyah akwai matar da ta mishi ya sani aure bayan sallah za ayi shi. Kallonta yayi kafin ya ce mata. "Allah ya kai mu!" Abin ya bawa kowa mamaki wato shi dai ba zai tab'a musu ko bijirewa ba, kome aka ce mishi amsar daya ce Allah ya kai mu. Jin haka yasa ya kwantar da hankalinta. Amma ko zata amshi Ikhlas kai ita bata jin zata amshe ta nan kusa never.

Tashi yayi ya bar parlourn har ya isa bakin kofar Daula ta ce mishi. "Ya Yarima!" Juyawa yayi ya kalleta. "Dama nace maganar budar kan." Juyawa yayi ya zuba mata idanun. Sosa kai take tana zungure Aneesa da kafa. Yana kallonsu kafin ya ce mata. "Wani abu ne?" "Yawwa dama abinda za ayi ne babu wadataccen fili, shine nace ko za a kama event center ne!?" "Budar kan ne a wata Uwar duniya?" "Mai Babbar daki, don Allah ki bari mu yi yanzu."
"Nawa zai isa?"
"1.5M!" Inji Aneesa,
"Faruq zai bawa Abdullahi."
Yana gama fadar haka ya bar parlourn, ai kuwa Mai Babbar daki ta rufe su da fada kamar zata rufe su da duka, kiri-kiri Abdullahi ya ce mata. "Ummi sai dai kiyi hakuri, tunda Abba ya zab'a mishi ita kaf duniyar nan babu me hanawa, sannan a cikin wasiyyar shi ya ce ko da a ranar da ya rasu ta kama a daura auren, kuma ayiwa Yarimar Faris biki kamar auren Fari, wannan kawai abin burgewa ne, kuma dole mu cika burinsa." Kalaman Abdullahi ya kashe mata jiki musamman da ya kasance yana tare da Marigayin, har ya rasu yadda yake basu labarin kafin rasuwarsa har da cewa Allah yasa kada Junaidu ya fasa aure, Abba yayi dace da aboki na kwarai kusan kullum sai Junaid ya kira shi,.idan lokacin kiran yayi bai kira ba. Shi yake sawa a kira mishi Junaid.
Ana gobe zai rasu sai da ya kira Junaid duk da maganar baya fita, sai da ya ce mishi. "Junaid alƙawarinmu!"


Sai jikin Mai Babbar daki ya mutu. Haka yasa ta yi shiru amma maganar gaskiya bata son Ikhlas kuma ba zata tab'a sonta ba.
Faris
Koda ya isa inda motar yake, shiga yayi ya zauna. "An sake shi!" Faruq ya gaya mishi, bai ce kome ba ya kwantar da kanshi a jikin kujeran motar. Har gida suka isa idanunshi a rufe yake. "Faruq!" "Na'am!" Ya amsa mishi. "Me ka fahimta da zuwan Alhaji Nafi'u!" Shiru yayi kafin ya ce mishi. "Yazo ne yaji me zaka ce, sai aka yi dace baka ce kome ba." Gyada kai yayi, "Ba haka ne!" Kallonshi Faruq yayi kafin ya ce mishi. "Zan so na ji me zaka ce?" "Abu biyu ya kawo shi!" Cikin dauki da son sanin abu biyun. "Zamu yi magana a hankali!" Gyada kai yayi har suka isa gidan ya fita, ya zagayo ta wurin drive. "Zan baka wani abu gobe in sha Allah, ka tuna min in sha Allah."
"Allah ya kai mu!"
Shiru yayi sannan ya juya cikin gidan, wato akwai wani abu da faruq ya manta. Shi ne a yanzu da kowani lokaci za ayi ta bibiyar rayuwarsu, kuma lokacin da Faris ya tawo zai shiga motar ya ga wani bafade a jikin motar, jikinshi ya bashi akwai wani abu. Don haka yayi shiru bai ce kome ba, domin shima bafaden ya waske kamar ba kome. Don faruq yana cikin motar ya zauna bai san me ke faruwa a waje ba.

Lokacin da ya isa cikin gidan, Nady tana dakinta ta sha kwalliya cikin wata arniyar lace, gashin nan an zuba shi har gadon baya. Ya sauka akan kugun nan kamar wata yar babyn roba. Murmushi yayi a ransa, yana girmama rigimarta kafin ta hauka ce mishi. "You look gorgeous!" Ya furta a hankali, yadda ita ɗaya zata karancin kalamansa. Telan da yayi dinkin shi kaɗai yasan shad'ancin da yayi a jikin kayan. Domin doguwar riga ce, amma daga gabar rigar wani bude shi aka yi kana ganin boons dinta wanda suke tsaye ba karamin kyau tayi ba, farin fatar nan ta karawa shigar kyau domin lace din golden ce, daga kugunta kuwa an bada wani irin tattara, sai gaban cinyarta a yage yake tayi bala'in kyau sannan daurin dan kwallin ya bala'in kara mata kyau. "Yaushe me kwalliya ta zo!" Murmushi tayi tana kallon madubin. "Ka manta ni din miss California ce, idan ban iya kwalliya ba taya zan ci gasar kyau!" Sumbtar bayanta yayi yana kara rungume ta da kyau ya ce mata. "I know!" Yana sake mata mishi a hankali, "ka yi min alƙawarin babu wata mace bayan ni?" "As you wish!" Ya fada yana mikewa, riko hannunta yayi, ya jata suka tafi can garden anan suka zauna suna rungume da juna. Abin kamar wasa har aka yi la'asar yana ganin sakon Faruq ya tura mishi ka je xan yi a gida. Sannan a hankali yake manta da ita wata kishiyar da take ganin kamar zata raba su. Har wani nanike mishi take.

Ikhlas

An shiga rud'ani a cikin gidan tun aka tafi da Abbanmu, ni kan tsabar tashin hankali sumata biyu domin ban san yadda xan gaya muku waye Abbanmu yake a rayuwarmu. Wannan tashin hankali yasa gidan ya koma kamar zaman makoki, su Ya Abid sun bisu amma basu dawo da shi ba, haka suka dawo jiki a mace.

Karfe uku dai-dai, ina kwance ana min karin ruwa,domin yadda na gigice. Sai gashi yan sanda da suka dauke shi sun dawo da shi har cikin gidan, ihun da ake na murna. Yasa ni tashi na fito, ina ganin shi na fasa ihu tare da zuwa da gudu na rungume shi, "wayyo Allah na, Abbana ya dawo wayyo Allah na." Na kara rungume shi, hawaye ne yake zuba mishi. "Zainab kin girma fa, yau xan raka ki dakin Mijinki. Allah zaki godewa da ya baki miji irin Salmanu Faris, Alhamdulillahi ko ni na taya ki murna."
"Abba waye ya sake ka."
"Nima cewa aka yi daga sama aka turo a sake ni!" "Abba ba zan tafi ba zan zauna kada su sake zuwa su dauke ka." "Laaa kada mu yi haka!" Yadda nake kuka sai nake ji kamar ina tafiya da a kuma zuwa a Tafi da shi, ai kuwa nayi ta kuka. Dakyar aka sami kaina.

Karfe takwas aka zo tafiya da ni, fir naki sake Abba haka ya saka ni, a gaba har gidan Sarki, ina makale da shi. Gashi wankar da aka min sabon Sharaton ce a jikina wanda aka saya a wurin Tarasulu, turmi biyu ce Aunty Shukrah tasa aka min dinkin riga da zani, sannan aka yi wata irin mayafi me kama da alkyabba da zanin aka shiga da ni kofar Hajiya hadiza aka kai ni, yadda ake gud'a tare da kirari. Abba yasa aka kuma Hajiya Hamaza da Ummar Abba Yayari, ya ce musu. "Ga yarku nan na kawo muku ita, ni ba suruka na kawo gidan Attahiru ba Y'a na kawo muku, amma ku gayawa Maryamu daga ranar da tace bata bukatarta xan zo na dauke ta." "In sha Allah ba za ayi haka ba."
"Na dai gaya muku!" Sannan ya tashi zai fita na rike shi jikina yana rawa. "Abba don Allah kada ka barni."
Shafa kaina yayi yana faɗin. "Ki yi hakuri, Allah yana tare da ke sannan babu abinda zai faru." Yadda ya fada haka na kara kamkame. Ina sauke ajiyar zuciya, "ka mai dani gida kawai!" Na faɗa a hankali. "Idan kika gaji, ki kira ni zan bar wayata a kunne dare da rana kika ce na zo zan zo na dauke ki, kin ji My Baby!" Gyada kai nayi amma naki sake shi. Wasa wasa naki sake Abba, ban san waye ya shigo ba sai dai naji muryan Abba a raunane yana faɗin. "Na baka amanarta amma daga ranar da ka ce min ka gaji kada ka turo min ita ka kira ni zan zo na dauke ta, Y'ata na baka kuma ina sonta sama da sauran Yarana. Idan ba zaka iya ba kada ka damu ka dawo min da ita da ta rayu cikin bakin ciki gara ta rayu tana zawarci!" A hankali ya janye ni na kara kamkame, dakyar ya cire ni a jikinshi ina jin aka riko ni tare da zaunar da ni a kujera bude ido nayi na kalli Abba a bakin kofar zai fita. "Abba kayi min alƙawarin duk lokacin da na kira zaka zo?" Na faɗa ina shashekar kuka. Bai juyo ba amma tabbas na san Abba shima kuka yake. "Abba ka juyo ka kalle ni!" Tafiya yayi na kifa fuskana a tafin hannuna ina wani irin kuka. Taya xan fara rayuwa a cikinsu? Waye shi wanda aka aura min? Haka xan rayu a cikin su zasu so ni kuwa?

Faris
Wannan soyayyar Y'a da Uba, ya tsaya mishi a rai. Duk yadda yake son haihuwa sai yake gani ashe ba haihuwar ba ce kana haifar y'a mace wani zai raba ka da ita, yanzu ka ga irin soyayyar da Uban yake yiwa Yar ba karamin ƙoƙari yayi wurin bashi yar ba....
*ina mata yan gayu ina mata yan yayi! Tow ku matso nesa ta zo kusa collaboration Tangaza_Perfume tare da Anum∆Luxury Perfume sun zo muku da kayan kamshi gida da na jiki kai ba iya nan ba hatta turaren kaya irinsu.*
Mamoul all colors are back in stock. Mamoul turaren turara kaya. Ga kamshi ga kama kaya da gida. Available in;
MAMAOUL MADINA,
MAMAOUL MARYAM,
MAMOUL BADAR &
MAMAOUL SABAYA. Each one 3500

*New Drop!*
*Nassem Oil – 100ml*
Rich, elegant & long-lasting.
This premium fragrance oil is everything your collection needs — and it’s only *₦8,000!*

*Luxury in a bottle.*
| Own Your Scent, Own the Room*

*Mosuf 50ml Body Spray*
Smooth. Fresh. Long-lasting.
Only *₦5000!*
✨💥
Smell amazing, every single day.
*DM to order!*

*Storm for Him & Her – ₦4,500* each
Fresh, fierce, and made to turn heads.
Whether it’s *Storm for Him* or *Storm for Her*, you’re getting bold confidence in a bottle — just *₦4,500!*

A perfect 50ml to carry your essence wherever you go. Subtle. Powerful. Unforgettable.
Now available: ₦2,300 per piece | ₦27,600 per dozen.
Available Just DM
08130269641

Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book.


*Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu ƙayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:*


*MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya haɗa da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.*

*AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen ɗin Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen*

*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*

*POSTING*
*Ɗaya: 500*
*Biyu: 1000*
*Uku: 1500*

*DOCUMENT (da zaran an gama posting zai koma)*
*Ɗaya: 1k*
*Biyu: 2k*
*Uku: 3k*

domin tura shaidar biya ko Ƙarin bayani, ku tuntuɓi:
*08130269641*
Ko
*08137311900*
Ko kuma
*09063467258*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 20

Yadda nake kuka tare da takura kaina a wuri guda yasa shi mikewa yana me kallon Aunties dinsa. Idanunsa ne ya kai kan Hajiya Malika Yayari yasan matar tun kafin ya b'ata tana da kirki da mutunci, murmushi yayi mata ya ce mata. "Ga karamar yarku, ni zan koma gida." Ya saka kai ya fita, don shi mutum ne da baya son ƙananan kuka, yana fita Hajiya Malika ta ce musu. "Hadizah nima zan koma masaukina ga yarmu nan, da fatan babu matsala?" "In sha Allah babu!" Fita tayi tana faɗin. "Shi kenan!" Ta bar parlourn, a hankali aka fara watsewa a parlourn. Kallon mutanen da suka rage daga yan uwana Matar sarki tayi ta ce musu. "Ga daki nan!" Rike ni Yeemar tayi tana faɗin. "Tow!" Suka nufi dakin da ni, tunda na shiga nake kuka. "Ke dalla can, kin ga Mijinki kuwa?" Inji Ihsan Kanin Abba da yake maradi. "Dole Iram da Uwarta su haukace, jar Uba?" D'ago kai nayi ina kallonsu da pale face dina. "Idan nace miki ban tab'a ganinsa ba sai zaki yarda?" "To ina ruwana? Wallahi ni fa idan aka hada ni da gayen nan ba zan yi kuka ba." Tsaki na ja na cigaba da kukana. Bayan kamar minti goma wayata, ta fara ƙara dauka nayi na saka a kunne. "Abbana!" "Na'am Uwata ki daina kukan haka kin ji!" "Tow Abba yaushe zaka zo?" Gyaran murya yayi ya ce min. "Zan zo amma sai kin yi hakuri kin zauna da kowa lafiya, sannan kin yi hakuri da kowa nan ne zan zo amma sai kin yi hakuri Ikhlas kada ki fada da kowa ki yi hakuri na manta ban gaya miki ki yi hakuri da kowa ba, hatta Matarshi gidanta a kazo!!" Sai da ya ja fasali kafin ya kuma cigaba da cewa. "Hakuri na kira na kara baki, duk wanda kika ji bai yi nasara ba tow bai yi hakuri ba ne idan yayi hakuri shine akan gaba, zaki bani labarin yadda kika yi hakuri amma kada ki zo min da yadda kika gaza hakuri kin ji ko? Kiyi hakuri duk wata mace sai da tayi hakuri kafin ta iso wannan matakin da take kema ina son ki yi hakuri. Ki rike sallah da azkar kin ji ko kada ki rike wanin Allah domin Allah yana nan shi ne rayayyen nan da baya mutuwa." Daga haka ya cigaba da cewa. "Nasan zaki iya min wannan alfarman ki yi hakuri ki zauna da kowa lafiya."

Haka muka rabu ina kuka yana jina, ya kashe wayar. Abinci aka kawo mana. Ilham da Ikram suka shigo bayan an kawo abinci. "An biyo kwadayi bayan kashe mana Iyaye da aka yi shine aka zo don niman kwadayin tow ki sani zamu ce miki welcome to the hell!" Bude baki Ihsan tayi na rike ta ina faɗin. "Kin manta Zainab Junaid Gobir nake, bagobira nake kin san tsoro ai ban san shi ba." Na kalle su da kyau domin har wani kyaf-kyaf idanuna suke ni fa ba zan yarda na zauna ayi min iskanci ba, wallahi sai dai idan an fi karfina.
"Bayan tiya akwai wata cacar." Na faɗa ina share kwalla da yake zuba min. "Ke Ilham dole ki kira ni Matar Yayanki, ke kuma dole ki ji haushi domin na auri wanda yafi Yayanki, and kashe iyayenku ni ban san shi ba domin mahaifina babu ruwansa, kuma abin burgewa na gaya muku ban ga wurin zama a gidan nan ba, ke ki gayawa Yayanki, kada ya sake jiki don ni mijin da nake da buri ba irinsa ba ne sauran wata mace,macen ma wacce ban san irinta ba, sam bai da irin zubin mazan da nake so, mutum a tsaye kamar gungunmemmen dutse!" D'ago labulen dakin aka yi duk muka juya shine a tsaye, sau daya na kalle shi na kwashe da dariya. "I fucking nonsense ko yau idan ya isa ya ce ya sake ni, jakuna kun zo kuna ihu akan wanda ko a kasar shoes dina bai burge ni ba, and sako makoki ku gaya mishi auren nan yayi mark din calendar ko nan da can ba zai je ba." Sake labulen yayi ya juya tare da kiran sunan Ilham. "Ilham ku fito!" A hankali suka fito kamar munafukai, waje yayi bai san ƙaddaran da ta kawo shi jin munanan kalamai ba.
Tafiya yake suna binsa kamar munafukai, har soron tsakiya. Shiru yayi kafin ya ce musu. "Me kuka je yi a bangaren?" Zubewa suka yi akan gwiwarsu. "Kayi hakuri ba zamu kara ba!" "Akan me kuka je tow?"


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login