Showing 285001 words to 288000 words out of 304445 words
yi aune ya yi sama da ni, abinka da bishiyar kuka, tsawo ne da su kamar wasu bishiyar dabino. Yadda nake kuka yasa shi sassauta rikon da yayi min ya fara rarrsshina, kafin ya ja hannuna muka wuce part dinsa. A hankali kome yake tafiya daidai sai dai me? Sai da ya rage kiris zamu zama intimacy with him sai yayi wani irin sanyi kamar ba namiji ba, a wani irin yanayi ya kalle ni. Ya sake gwadawa yaji taki tashi, ya kara gwadawa tayi sanyi bakiɗaya haka ya dauke ni daga gadon ya gwada ina wallahi salaf kamar an jika tsuma kawai ya ce min. "Ko impossible!" Daga ni har shi sai muka rasa mafita, haka ya ja wandonsa yayi parlour, yayinda nayi lumo akan gadon ina mamakin wannan lamarin, abu kamar a film kamar irin labarin da ake badawa nan, haka abin ya faru, lokacin da na fito bayan na saka kaya na same shi a parlourn yana zaune. Kallo daya muka yiwa juna sannan na fice daga part din, tun daga ranar lafiya lau yake da matanshi, amma ni kuma babu labarin mai kyau, haka yasa na fara wani irin shiga damuwa da rama. Ga kome na rayuwa zai shigo ya ganni zai tambaye ni akwai wani abu ko babu na bashi amsa daga nan kuma zai fita, bana tunanin daga gare ni ne domin Allah na tuba bana jin akwai wani sakacin da nake komi dare ina tashi ko bana sallah ina tashi nayi zama na musamman, haka muka cigaba da tafiya, har wata rana na je gida Aunty Sajidah tazo muka kebe anan take tambayar meke faruwa, kuka na kama mata ina gaya mata halin da muke ciki, shiru tayi kafin ta ce min. "Bana jin wa ke ayiwa shi kaa yiwa, kin san mata barkatai ba sanin waye zai maka kake ba, abu daya xan baki shawara shi ne idan kin je gida ranar girkinki, ki wargaza wurinsa da sunan aiki in sha Allah za a dace," haka muka rabu na dawo gida ranar girkina kuwa na shiga aiki gadan-gadan don ko mall ban leka ba nayi waje da kome, sannan na fara aikin fitar da kayan kamar mahaukaciya, sai da na gama da parlourn na ji zuciyata ta karaya, kamar xan hakura sai na shiga dakinsa kome na nan tsaf kawai na fara fitar da kome waje don Bala'i ni daya na wargaza bangarenshi, ina cikin wannan aikin na ga abu ya fado a bayan mirror dinsa, a hankali na dauka layya ce da kwado, sai na cigaba da aikina kamar wanda aka tunkud'o Ijlal ta shigo, na kara warzaga gadon nayi daya -daya da kome nan ana kasar katiftar na ciro wani kamar zata fadi haka take kallona, cike da mamaki na zazzage pillow din gadon guda hudu da sweet da heart duk na ciro layyu na ajiye akan dress mirror dinsa, na shiga aiki. "Ikhlas waye zai yi wannan aikin?" Dariya nayi na ce mata. "Hala nice nayi!" "Hmm baki yi kama da mai irin wannan aikin ba!" Ta fada tana mai barin dakin, ko kiran Nadiyyah tayi suka shigo suka samu na ajiye layyar a wurin. Nufar wurin Layyar Nadiyyah tayi na ce mata. "Wallahi kika kara motsi zuwa wurin Layyar sai kin yi haukar da babu magani!" Cak ta tsaya tana huci. "Gara ma kowa ya fita." Hakan suka fita can ina cikin waya da Abba, ina kuka ya shigo a fusace ina faɗin. "Abba na gaji wallahi na gaji xan bashi fili da Matanshi su yi yadda suke so tunda ni ne ban da amfani a wurinsa, Abba layyu uku har da na cire kasan gadon, mai na musu da suke kokarin ganin sun nisanta ni da shi?" Yadda nake magana ina kuka yasa shi jikinsa yayi sanyi ya dawo parlour, fitowa Parlourn yayi ya tara su, har ni ina gama wayar na fito zan koma ɓangarena na gaji da zama da shi, "ki dawo!" Haka na dawo, ya ce mana. "Idan baku fadi wacce ta saka min layya a cikin gidan nan, abu daya xan yi zan fitar da wacce ta yi wacece a cikinku?" Babu wacce tayi magana ya sake nanatawa, take suka yi shiru ganin ya fusata ya ce mana. "Zan yi hukuncin da ban tab'a yi ba, ku tafi wacce tayi zata iya kirana a waya idan kuma bata yi haka ba, wallahi xan mata abin da tayi 48hrs na baku!" Daga haka muka fita, na san ba wani abu zai yi ba don haka kafin ya b'ata min lokaci na hada kayana, na bar gidan bai ma san na bar gidan ba, na wuce gidan Ya Abid, na tafi babu wanda ya sani can na je na zauna. Sai bayan sallah isha ya leko ya duba ni na bar gidan Empty, bai tab'a zata xan iya barin gidanshi ba.
A can gidan Ya Abid kuwa kuka nayi ta mishi kada ya fadawa kowa, don Allah ya bar ni na huta. Da yake suna shirin tafiya Maradi ne sai ya ce min na shirya kayana cikin nasu. Ba karamin danne zuciyata nayi ba nasan ko ban rabu da shi ba wata rana zai rabu da ni, haka yasa na bar mishi gidans.
**
Har karfe sha daya ban dawo ba, yana tsaye a bakin kofata a tunaninsa cikin fada na shiga sai dai ya kira Ummi ya tambaye ta xan kwana ne ta ce mishi bana nan ai! Iskar bakinshi ya furza ta ina zai fara niman Zainab don haka ya hakura zuwa gine yasan tana gidansu, amma yasan Abbanta baya gari ne, kai Iyayenta suna tsaye a kanta basu barta ta kwana ba Tabbas da can ta nufa ba zata kai har haka ba, kiran Faruq yayi ya gaya mishi. Zare idanu yayi kafin ya ce mishi. "Ta ina zamu fara?" Faruq ya tambaye shi, kawai ya kira Abba ta fara kame-kame, sai dai tambayar da Abba ya mishi ya ji kamar ta nutse a kasa. "Ina Mamana?" Shiru yayi kafin ya ce mishi. "Tana lafiya na kira ne.ma gaishe ka," sannan suka yi sallama, zama yayi ya rike kanshi. "Me yasa zata tafi bayan ban yanke hukunci ba? Me yasa zata min haka?" Ya yi maganar kamar zuciyarsa zata fito waje. Ai kuwa a daren ya kara musu barazana, tare da cewa kada ya kara fitowa ya same su a gidan, jin haka Hankalin Nadiyyah ya tashi, bayan sun bar part dinsa yana zaune ya dafa kanshi. Nadiyyah ta shigo ta zauna tana zare idanu. "Baban Princess kayi hakuri, nima ban san cewa haka abin zai faru ba, wata ce ta bani da sunan maganin kariya daga mugayen mutane!" Kura mata idanu yayi yana wani irin takaici ya ce mata.."yanzu kin yi min adalci kenan? Nadiyyah na so zama dake tsakanina da Allah. Na so miki adalci amma yanzu kin wuce lissafina, mai Zainab ta yi miki haka? Kin san abinda kika saka ya hana ni mu'amalar aure da ita mai na miki Nadiyyah?" Kuka take tana bashi hakuri, ya rasa mai zai mata ya ce mata.."ki yiwa kanki adalci kin fini sanin abinda ya dace da ke amma ni ba zan iya cewa kome akan ki ba idan xan yi magana igiyoyinki zan tsinke su bakiɗaya!"
Ai bai iya kwanciya ba, ya kira Abba bai boye mishi kome ba ya gaya mishi yana bincike tai zuciya ta bar gidan. Don Allah ya saka baki ta dawo, yayi laifi na rashin bincike da wuri. Shiru Abba yayi bai ce kome ba, ya ce mishi. "Ka zo!" Ba musu ta tashi a daren da rawaninsa ya bar gidan, shi da faruq. Ai bai yarda ya tafi iya su ba ya je ya dauko mai babbar daki. Aka tawo gidansu Ikhlas, abin mamaki tunda ya gayawa Abba jikinshi ya bashi tana gidan Abid, yana kiransa ya ce mishi. "Kada ka sake na tambaye ka ina take ka daukota a mota a daren nan ku tawo na gaya maka!" "Tow Abba!" Ya fada, can kuwa sai gasu a daren, wurin sha biyu saura muka iso gidanmu, tun a mota nake kuka wiwi. Har muka isa gidan. A parlourn muka zauna, Abba ya zuba min idanu. "Uwata ina nan da raina zaki tafi gidan Abid ko Salmanun Faris ya kore ki, ki zo nan Abbanki yana jiranki ban tab'a rufe kofar gidana ba domin masana ina da Yara mata zasu zo ko za a kawo min su. Haka na saka a raina babu ranar da zan rufe gidana ko bayan raina A bar gidan a bude saboda Yarana mata musamman ke Zainab! Nasan wata rana zai dawo min da ke imma a cikin halin lafiya ko a halin rashinta, kofana a bude yake Uwata!" Yana fadar haka na matsa gefenshi ina kuka, na kasa boye tashin hankalin da nake ciki, kafin Mai Babbar daki ta ce mishi.."Malam ban san kome ba wallahi, amma kwanaki na ganta nake tambayarta ko jinya tayi ne ta ce min a'a ashe abinda yake faruwa kenan? Allah ya kyauta," Tayi maganar a sanyayye, domin ta kasa fahimtar lamarin. A hankali ya mai da abinda ya faru, sannan ya ce musu. "Ga kayan nan!" A hankali ya ajiye musu layyar....
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 94
"Ta ce min ita bata san!" Katse shi Mai Babbar daki tayi kamar ta rufe shi da duka ta ce mishi. "Ka kyauta min, Abdullahi har ya mutu ban bishi bashin magana akan gidansa ba akanka aka fara mata uku ne? Wai me yasa kake kunyatani ne? Me yasa?" Ta fada muryanta yana rawa. A hankali na juya gare ta tare da dafa rike hannunta. "Ummi!" Idanunta da suka cika da kwalla na ce mata.."Wannan tafiyar ba nawa ni daya ba ne, har dake Ummi kin san yadda zaki dawo da Yaya kan hanya da addu'a yake bukata, Ummi Yaya shi ɗaya ba zai iya ba. Da rikicin mulki ko da ta gidansa? Don Allah kada ki bari haka ya faru!" Na fada ina shashekar kuka, a hankali na ce mata. "Na janye karata!" Duk yadda taso danne hawayen sai da suka zubo, ta lumshe idanunta kafin ta bude akanshi. "Alfarma daya zaki min duk lokacin da irin wannan abin ya kara faruwa, ki tuna nima uwa ce kofata a bude take, zan karbe ki da hannu bibbiyu zan mai dake nawa dama tun can wata ce ke!" Ta fada tana murmushi, sannan ta kalli Abba ta ce mishi. "A bani ita mu karasa rigima a fada!" "Allah ya tashe mu," sannana akayi addu'a lokacin daya saura. Squad team dinsu na tsaro suka kewaye gidan, sai da suka raka Ya Abid. Sannan suka rufa mana baya don dama wasu sun yi gaba,haka muka isa fada suka raka mu har cikin gidan, sannan suka wuce cikin gidanshi. Dakin ummi yau ta ce mu wuce a can na zauna ina jan hancina. "Ummi kada ki yi fushi da shi kin ji."
"Tow Uwata naji!" Zamowa nayi zan sauka tace min. "Koma ki zauna!" "Ummi !" "Ni sallah zan yi!" Ta fada tana nufar ban daki, lokacin da zata shiga na fara kuka. Dawowa tayi ta zauna tana ganin yadda nake kuka ta ce min. "Me kike so?" "Ki ce kin yafe mishi kukan nan, don Allah ina sonshi ina kaunarshi, ban tafi don bana sonshi ba na bashi fili ne ya sha iska Ummi, kukan da yayi idan kika kalla yana da Yara mata biyu ga wasu a hanya. Ummi kada ki manta bai zauna cikin gidan nan ba, asalima da girmanshi ya dawo dabi'a ce irin ta turawa bawa mata damar su yi yadda suke so, sannan gefe guda yana ganin a muslunci idan ta tauye su Allah zai kama shi. Ko ni nasan yana nuna fifikonshi a kaina, amma." "Good girl, dama ina son naji hkaa daga gare ki ne, idan har kina son na daina fushi da shi sai kin yi min alƙawarin taimaka min a karo na biyu!"
Gyada mata kai nayi ina faɗin. "In sha Allah!" Murmushi tayi ta shiga ban daki bayan ta mike, alola tayi ta fito nima na shiga na fito, sannan na tadda sallah kamar yadda take, sai kusan karfe biyu da wani abu na kwanta.
Washi gari bayan mun yi sallah asuba nayi addu'a, na kara kwanciya barci yayi gaba da ni. A hankali na ji ana shafa ni musamman kirjina, abin ne ya dawo min kaina ma bude ido da sauri shine zaune, ya cancad'a ado kamar wani dawisu. Ture hannunshi nayi ina ƙoƙarin gyara rigana ya motso tare da cewa. "I'm sorry!" Takaici ya kama ni na kura mishi idanu, kafin na ji kwalla ya cika min idanun nace mishi. "Fita min a daki!" "Ok! Amma kin san nan dakin Uwata ce?" Ya tambaye ni yana ware min idanu. Wata Uwar harara na watsa mishi ina faɗin. "Ina ruwana, ka fita min a daki ka je can wurin masu haihuwa ni juya kuma!" Fisgo ni yayi yana faɗin. "Wallahi na kuma jin kin gaya min irin wannan maganar sai an san kin gaya min magana!" "Tow ka kashe ni ka bine gawata inda ba za..." Hade bakinmu yayi na gantsara mishi cizo sai da bakin ya fashe, ganin yadda jinin yake fita yasa ni zare idanu. "Jini a bakinka!" Na fada ina rufe bakina. Fisgo rigar da yake jikina yayi ya shiga matse min boons, tare da haɗe bakina da nashi yana cinye min tare da tura min jikinshi na shanye mutumin nan mugun gaye ne, kuka na saka mishi ina tutture shi. Murmushi yayi yana tsotsar harshena har sai da ya ga nayi wani irin laushi. Sannan ya sakar min murmushi. "Wallahi ki san yadda zaki yi da ita ta dawo min dake ko kuma nazo na baki kunya a gabanta." Kuka ne ya zo min na watsa mishi harara. "Zo ka fita min a daki?" "Ummu ina kwana?" "Da ban kwana ba zaka ganni haka?" "Ayya Ummi ku yi hakuri dai!" Ya furta yana murmushi yan kallon inda nake, ina share idanuna "wani abu ya miki?" "A'a abu ne ya shiga idanuna!" Na faɗa ina juya bayana. "Zainab yayi miki wani abu ne?" Girgiza kai nayi ina faɗin, "A'a!" Naki yarda na juya ne don kada ta ga yadda nake zubar da hawaye, zuwa tayi ta juya ni. Sunkuyar da kaina nayi ina shashekar kuka. "Anyi miki wani abu ne?" Ya tambaye ni, kamar bai san abinda yayi min ba, kirjina zafi yake da ciwo." Murmushi yayi ganin yadda nake kuka yasa Mai babbar daki ta juya, ranta ya b'aci." Allah ya haramta zalinci, shi yasa ya kira kanshi da Adali, me yasa kake kunyatani?" Ware idanun yayi kafin ya ce mata. "Ni Ummi? Me na mata kuma? Zainaba me yasa zaki min haka? Mai nayi zaki hada ni da mahaifiyata?" Like serious sai na rude tare da kallonta zan yi magana ta d'aga min hannu. "Kin hada shi da ni, sai me? Na gaji da wannan auren naka da kullum nake kwana da tararradin mai zai faru, tunda ka aureta bata tab'a kawo karanka ba, kai wannan kiran da zata yi ta gaya min ana.wani abu a gidanka bata tab'a yi ba, amma matanka suna ganin Abu zasu ce anyi kaza-kaza anyi kaza, ba halin ayi motsi a gidanka kafin wani lokaci har ya shigo inda nake, kai ba abin kunya bane a ce kullum ina zirga-zirga a cikin gidanka ba? Ka fita idanuna na rufe wallahi zan baka Mamaki!" Yadda take shiga ba nan take fita, sannan ita kanta ta kai makuran da ba zata iya hakuri da shi ba, rike hannunta nayi na ce mata. "Ummi kin ce ba zaki yi fada ba, ni fa zai min kome ba kawai ina kukan abinda ya faru ne akan." Kunya ce ta kama ni wai na gaya mata akan babys din da na rasa ko me? "Akan me?" Shi kan saukar da kai yayi ya durkusa yana bata hakuri, ni kuwa hararata yake ƙasa ƙasa, tare da cizon bakinshi. Haka tayi mishi tas sannan ya bar gidan, tun daga ranar ban kara saka shi a idanuna ba, domin da gaske yayi fushi sosai.
Irin fushin da ban san yana da irinta ba, sai da ya kwashe sati biyu ban ji labarinshi ba kuma ban tambaya ba, ranar ina parlourn Mai Babbar daki tana kallon Network news aka hasko shi a tv. Kurawa tv idanun nayi ashe wani kamfani Nadiyyah ta buɗe, ban wani ji zafin hakan ba domin dama can yar kasuwa ce, amma yadda yake tare tare da ita, yasa ni jin wani abu ya cika min zuciya. Addu'a da tasbihi na fara har ba ji sauƙi. Washi gari ina karyawa sai gashi tare da Ijlal ta sha kwalliya cikin wani lace Marron colour, takalmi da jakarta silver, tayi kyau ga na ciki, sau daya na kallesu na kauda kai ina karyawa. "Jira ni" ya ce mata, yadda yayi sallama ciki ciki haka na amsa mishi ciki-ciki. Ya wuce dakin Mai Babbar daki. "Ba dai kece kika saka layyun nan kike drama.kamar wani ne ya saka miki?" Ta tambaye ni tare da zuba min idanu, kallon Amiraah da take kan cinyarta nayi nace mata."Lulu!" Dariya yarinyar ta fara min. "Nunu!" Na fada mata ai kuwa ta fara tsalle da giggile kamar zata fado kan cinyarta. "Mammi!" Ta furta da ƙarfi tana wani irin mikewa da zillo zata zo wurina. "Nunun Mammi!" Ai kuwa ta calla kara mai karfi da kiran sunana. "Mammi!" Dafe kirjina nayi tare da rufe idanuna, ita kanta Uwar sai ta kasa motsi tana kallon abin al'ajabi yadda Ikhlas take communicate da yarta wacce bata da lokacinta. "Mammi!!" Wani irin abu nayi tare da rufe idanuna nace. "Auch!" Na dafe hannuna a kirjina ija faɗin. "Lulun Mammi!" Ai kuwa sai ga yarinyar tana kuka da ihu, ashe duk abinda muke daga Mai Babbar daki har shi, suna tsaye tun ihun, wani irin abu ne ya