Showing 108001 words to 111000 words out of 304445 words

Chapter 37 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

59

Gabas
Mai Babbar daki ne ta saka shi a gaba, ta rasa ta ya zata mishi magana don tunda ya so gabanta yake zaune. "Dazun Zainab ta ce kana barci!" D'ago kai yayi yana kallon yadda take kallonshi, kafin ya juyar da kanshi can gefe guda yana kallon wurin. "Ta ce kayi barci shine nace ta barka sai ka farka da kanka, yaushe ka fara barci haka!" Idanunta ne suka cika da kwalla. Bata manta farkon zuwansu da Nady take tambayarta yadda take, ta ce baya barci ita a saninta da shi aiki yake kwana yi idan zai yi barci bai wuce minti arba'in zuwa hamsin ba, yana farkawa, zai sha magani ya fita aiki. Da ta tambaye shi bai mata karya ba ya ce eh baya barci kamar sauran mutane, a lokacin da ta tambaya Abdullahi ko akwai ciwon da yake hana mutum barci ya gaya mata akwai laluran tab'in hankali ma sai ta ji hankalinta ya tashi, idan ta ce bata cikin tashin hankali tayi karya, rasuwar mai martaba yanxu da son ya samu mulki ya kara mantar da ita halin da danta yake ciki sai yau da aka ce yana barci, sai ta ji kamar tafi kowa sa'a. Kallonshi take da wani irin kauna da soyayya irin na d'a da Uwa. "Ya kake jin kanka?" Shaƙar iska yayi ya fesar, ya ce mata. Sai ya rasa me zai ce mata ma, abinda ya iya fada mata shine . "I'm okay!" Ya cigaba da juya kofin hannunsa. "Ko zaka iya gaya min dalilin da yasa ka kori Ijlal!" Bai san yadda zai ce mata ba, amma shi dai ya san cewa yarinyar ya kamata da laifin aikata abu. "Bata jin magana!" Ya fada yana rike kofin hannunsa, Mai Babbar daki ba iya ilimin mulki take da shi ba, amma kuma Allah ya bata ilimin fahimtar abubuwan da baki bai fitar ba, tana karantar yanayinsa, kafin b'atarshi abinda ya faru a daji, yasa ta ƙara fahimtar shi ba mutum ne da yake mai da abinda ya faru ba, don haka ta ce mishi. "Tayi maka laifi ko? Me yasa su Nadiyyah da Ikhlas basu laifi?" Ta kara jefa mishi tambaya biyu a lokaci guda. Murmushi yayi ya ce mata. "Nady" cizon lips dinsa yayi yana tsotsa, kallon wannan dan Yaron nan dai take mishi cikin wani irin shauki da soyayyar Uwa irin wacce ake kira da Mother affected, murmushi tayi ta ce mishi. "Me kake son gaya min akansu, mata uku ne da kai amma ace biyu kullum basu da matsala sai daya." "Saboda basu damu da ita ba!" Shine iya abinda ya iya furtawa. "Basu kishi da ita kenan?" Murmushi yayi yana kallon kasa. "Ko baka gaya min ba, nasan abinda kake so na san abinda baka so, idan ma kalle ka sai na ga kamar murmushin da kake yi ba ita ba ce a fuskarka. Ka tsane ni ko?" Girgiza kai yayi yana mai mikewa ya ajiye cup din hannunsa. "Zainab fa?" D'ago kai yayi yana kallon yadda take karantar yanayinsa. "Na barta tana karyawa!" "Ka dawo da Ijlal!" "Tow!" Ya furta tare da barin parlourn. "Idan baka da ra'ayinta shi kenan sai kayi niyya ta dawo!" Girgiza kai yayi yana faɗin. "Zan duba!" Ya fita, ba tare da ya kara cewa kome ba, a zaune a wurin Hajiya Mardiya ta kirata ya kai sau goma. Dauka tayi cikin haɗe rai ta ce mata. "Ki bawa Yaya Yarima!" Ba musu ta kashe ta kai mishi, sannan ta sake kiranta. Dauka yayi ya ce mata. "An gaida Uwar Sarki Matar sarki, Magajiyar Zanzabira. Me kike son gaya min?" Duk da wanta ne amma shi yake bata wannan matsayin da Allah ya bata. "Yaya?" "Na'ma Magajiyar Zanzabira!" Ka tambayi Matarka da Yarta me ta aikata har Salmanu Faris ya korota? Daga nan zuwa gobe idan na ta fada ta dawo ɗakinta idan kuma tayi shiru kafin gobe warhaka zan aiko mata da sakon da yafi ta mutuwa zafi." "In sha Allah zan tambaye ta." Haka kuwa yarinyar nan taki magana sai kuka take.
Faris
Yana tsaye gaban mara lafiya yana, mishi tambayoyi ya ce mishi. "Ya kake jin kanka?" "Likita da sauki ba kamar da, da nake ji kamar na kashe kowa ba, amma yanzu ina jin zuciyata tana samun sauki kaina ya dai na ciwo." Murmushi yayi, sannan ya rubuta mishi magani ya ce mishi. "Akwai wani therapy da yake asibitin kwararru ka fara zuwa wurinsa ko za a dace." Murmushi yayi yana faɗin. "In sha Allah!" Sannan ya sallami mara lafiyar, ya kuma cigaba da aikinsa, Nurse Nana ce ta shigo ta mika mishi wani file. "Doctor don Allah a duba lamarin nan tun last week suke son ganinka!" D'ago kai yayi ya kalli Yarinyar. "Me yasa ba ku bawa Bashir ba?" "Doctor Bashir yana wurin Tiyata! Kusan a satin nan sau takwas ya shiga tiyata!" Shiru yayi ya cigaba da nazarin abubuwa da yake gani a cikin file ɗin, "sun yi Ultrasound da X-ray?" "Eh gasu nan!" Ta mika mishi. Duba hoton kan yayi yana mai kallonta ya ce mata. "When suka fara zuwa?" "About four weeks!" "Shine baku gaya min ba?" "Ka tafi aiki sannan." "Ko ma yaya ne sai ki gaya min yadda zan dakatar da kome!" Shiru tayi, "ku gaya musu za ayi mishi aiki nan da awa ashirin da hudu, ku fara shirin a dauki blood simple dinsa, a mishi duk abinda ya dace sauran kuma a bar min zan duba." Da sauri ta fita cikin farin ciki domin wannan shine karon farko da ya fara shirin shiga aiki da kansa, yadda ya nuna mata muhimmancin aikin yasa ta fita ta sanar da sauran likitoci, a take aka samu likitoci biyu da zasu yi assister dinsa. Wunin ranar shirin aikin ake yayinda wasu daga cikin likitocin suke ta cewa Allah ya ayi kuskure a aikin, domin ya kwashi kunya. Ba tare da sun san irin baiwar da Allah ya mishi a dakin tiyata ba.
Aikin da zai yi mai matuƙar hatsari ne, don haka ya nutsu a office dinsa yana aikin bincike da kuma wasu abubuwan, zuwan shi Abuja aiki uku yayi aka samu nasara amma dukkansu babu aikin da yayi kamar wannan su wadancan aikin daga jini ya shiga kwakwalwa ce sai wanda ya bugu a kai, sai wanda kashin kan ya danne ƙwaƙwalwar, haka yasa shi yin nasara akan wannan aikin. Shi fa Best likitan ƙwaƙwalwa ne kuma kaf Nigeria su hudu ne, Professor Abdul ya rasu, sai wani bayarabe a Lagos sai wani Dr Amin a Kano sai shi a Zanzabira, bayan ya gama ya fito kallon Nurse Nana yayi ya ce mata. "Ina bukatar dalibai da wasu likitocin da suka zo Internship, da masu practical sai nurse da suke department na neurologist, idan zan yi aikin!" Kallon agogon hannunsa yayi ya ce mata.."zan tafi zuwa gobe da safe zu shiga aikin, Bashir ya amshi ganin marasa lafiya." "Tow Doctor!"
Sannan ya bar office dinsa ya nufi inda motarshi take Faruq na ganinsa ya fito ya bude mishi. "Barka da aiki!" "Yawwa!" Ya fada yana bude wayarshi kiran mai babbar daki ya gani, sai dai bai bi ba ya cigaba da duba wayar ko zai ga kiran Zainab amma bai gani ba, haka suka nufi gida. Lokacin da suka isa ya samu kome tsaf-tsaf har da karin kamshi. Daga kitchen naji dirin motarsu, don haka na fito ina kallon Faruq. Amsar jakar nayi nace mishi. "Na gode!" Na amsa, na bi bayanshi yana zaune na same shi, ajiye jakar nayi na kuma fitowa ma dauko mishi ruwa da kunun aya. Na kai mishi ya kurba ruwan kaɗan kafin ya sha kunun ayar da yaji dabino da kwakwa sai kayan kamshi. Kallona yayi ya ce min. "Yayi dad'i!" "Na gode!" Na furta tare da tattara kayan da yake cirewa wani abu da baku sani ba, nifa Allah ya daura min kula da kaina da kuma inda nake shi yasa yana cire kayan nake kwashewa, sannan na kai ban dakinsa na wanke duk da akwai dakin wanki amma na wanke pant da vest sai safarshi na shanya su, ruwan wanka na hada mishi sannan na fito na mika mishi towel. Mikewa yayi ya daura towel din. "Gobe ina da aiki 17hrs!" Ya fada cikin wani sabon yanayi. Rike hannunsa nayi ina murxawa. "Me yasa kake damuwa?" "Anan sun rena aikina ne?" Murmushi nayi na shafa kumatunsa na ce mishi. "Kansu suka rena, na san wanda yake gabana ba matsoraci ba ne, sannan maganar mutane baya damunshi, kada ka manta ni na gaya maka bana sonka bai saka ka sauya ba sai maganar wasu jahilai? Oya saka hannu a nan ka ce. Ni Salmanun Faris nayi alƙawari da Ubangijina zan yi aikina na ceton rayuwar al'umma bilhakki da gaskiya!" Murmushi yayi ya ja kumatuna ya wuce ban daki, bin sa nayi da idanuna sannan na gyara inda ya zauna.
Kitchen na dawo na shirya abinci, sannan na dawo dakin na zaba mishi kayan da zai saka sannan na fito main parlour na zauna jiranshi, wayata ce tayi ƙara na ɗauka muna waya da Tauhid. "Don Allah ki turo min 20k zan biya ki soon!" Kayi login ta wayarka mana ka dauki abinda kake so!" "Ni dai bana son haka ki turo min kawai" ya faɗa, kamar zai shigo ta wayar tura mishi nayi, har dubu dari biyu. Sannan na zubawa wayar idanun, har ya fito ya zauna a table ya fara cin abinci, karar cokalin yasa na d'ago kai, sai na ga ashe har ya fito, murmushi nayi na cigaba da kallon wayata.
Bayan ya gama na kwashe ina, tambayar shi ko faruq ya tafi ne? Ya ce min yana nan kiranshi yayi ya amshi na shi abincin, wurin Mai Babbar daki ya fita suka tafi bayan Faruq ya kawo kularshi, sai dare na fahimci Nady da Ijlal da basa nan, haka na zauna kamar mayya a gidan, can naji dirin motarsu, ajiyar zuciya na sauke sannan na fito na bude kofar, shiga yai ya na amsawa Faruq tare da gaya mishi lokacin da zasu fita, tuwo na kawo mishi yaci miyar kuka da ya ji kayan kamshi, kallona yayi kafin ya ce min. "Na gode!" Na lura da wani abu daga lokacin da na mishi wani abu ya faranta mishi zai ce ya gode. Nima tashi nayi na wuce dakin, ina ganin yana saka kaya, na juyo na dawo parlourn. "Kina bukatar wani abu ne?" Ya tambaye ni. "Ina Nadiyyah?" Sai lokacin ya kalli kofarta. "Tayi tafiya" "ba haka a rayuwa, duk da turawa suka rene ta amma yana da kyau tasan muhimmancin zaman tare, ita kuma amaryanka fa?" Sosa kai yayi tare da tsare ni da idanu. "Ina ruwanki da su?" "Ba ina ruwana ba ne! Dole nayi tambaya!" "Tana gidansu!" "Akan me?" Hade rai yayi yayi ya ce min. "Ina da aiki!" Ya wuce study room, ban sake jin duriyarsa ba, wucewa nayi don takaici na bi shi. "Bani key ɗin ɗakina!" Na faɗa ina hura hanci. "Na ga saniya ma!" Ya fada yana murmushi don bai dame shi ba, kamar na fashe da kuka haka nake ji, karshe fitowa nayi na koma dakin na kwanta barci kuwa ya fara daukata sama-sama, sai ji nayi kamar an danne ni, duk yadda nayi motsi sai naji kamar an kara tantame ni, innalillahi wainnalihir rajoun nake fada a cikin zuciyata tsabar azabar ji nake kamar an daura min katon dutsen abuja a kaina, gashi ni ba barci ba, ni kuma ba idanun biyu ba, haka nake ta kokuwa da numfashi ko min kashin motsin da nayi sai naji har cikin raina kwalla ne ya cika min idanuna da zaran na fara addu'a zai gudu kaina da zuciyata, kai na shiga uku haka nayi ta kokuwa amma ina ji kamar ana kara danne ni, ina jin motsin shigowarshi dakin wani ikon Allah shima wuce ni yayi duk yadda nake shure-shure, amma bawan Allah nan bai lura ba, ganin ni ɗaya nake wahala na fara ambaton Allah tare da kabbara, cikin ikon Allah sai ga kabbarar ta sauka akan harshena na fara yi da karfi, jin ihuna yasa shi fitowa da gudu da kumfa a jikinshi ya rungume ni, fashewa da kuka. "Sorry!" Yake faɗa a kai a kai yana shafa bayana. "Me ya faru?" "Wani abu ne ya danne ni!" Zungure min goshi yayi ya ce min. "Me yasa kike kwanciya babu alola, bayan kin san cewa kina da matsala." Ni dai kuka nake, shafa kaina yayi yana faɗin.."wani evil Spirit ne ake kiran shi Dannau da hausa, shi kawai yana danne ka ne idan ka kwanta maybe wannan shine na farko ko?" Ban bashi amsa na janye jikina ina kuka. "Idan ma ba zaki kwanta da addu'a ba yana da kyau ki na kwanciya da karatun Alkur'ani a gefenki, amma addu'ar tana kira ga Mala'ikun rahama ne, sannan itama karatun Alkur'ani haka take......
*Account Details:*
*08130269641"
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500N
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: Tashi nayi na wuce ban daki na fara ƙoƙarin cire kayana sai gashi nan ya shigo, da sauri na kare kirjina, "yanzu zan fita ba zama zan yi ba!" Ya fada yana juya min baya,cire towel din yayi nima na juya mishi baya, wanke jikinshi yayi har ruwan yana tab'a ni, kafin na yi maza na ƙara kame-kame jikina, ina jin ya fita na rufe ban dakin na hada ruwan na shiga cikin sai da na gasa jikina, sannan na yi wanka na leko ina dubawa ko yana nan? Ai kuwa baya dakin na fito na shirya a nutse na saka kayana,sannan na koma nayi alola na kwanta. Wani irin dad'i nake ji yana ratsa ni, ga karatun Alqur'ani da yake tashi wayata,ga kuma nutsuwar da nake samu. Haka yasa bakiɗaya na manta da wani damuwa ma cigaba da barcina bayan nayi addu'a. Yana parlourn aikinsa Mai Babbar daki ta kira shi, shiru yayi yana kallon laptop dinsa. "Kayi hakuri Babana, na san bata kyauta ba amma kuma." "Tunda kin ce ya wuce ai ya wuce." Ya fada yana mai sauke wani irin nishi na takaici, ya rasa yadda zai mata bayani kawai sai ya bita da tow da tow.
Kafin ya sauke wayar aiki a ake son yi amma bacin rai da bakin ciki sun hana shi aiki wannan yasa shi cigaba da kallon laptop din, can ya gaji ya nufi dakin wurin karfe goma saura, ya zauna a gefen gadon, sannan ya zuba mata idanu. Shafa fuskana yayi a hankali yake shafa fuskar wnada ya tilasta min farkawa, ganin shi zaune yasa ni ja da baya. Ina kare kirjina. "Ko zan samu wani abin tab'awa ba abinci me nauyi ba like tea da ko cookie?" Yadda yayi maganar bai min kama da umarni ya bani ba, alfarma yake nima don haka na tashi zaune tare da zura kafata kasa ina mai shuran takalmin da yake gaban gadon, na dauki hijab dina na fito waje, kitchen na nufa na hada daura tunkuyar tea, sannan na koma na dauko flour na fara aikin hada Cookie, na fara aikinsa ni daya can kuwa sai gashi ya shigo kitchen din,yana zaune ina aikin yana na shi aikin har wuraren sha daya saura na gama na zuba a flast sannan na ce mishi. "Zaka sha anan ne ko a parlourn?" "Muje can!" Ya dauki tiren na dauki laptop dinsa kallonta yayi da wutsiyar ido yana jin ina ma da ita kaɗai ce a duniyarshi, ina ma da babu wasu abubuwan a tare da su, daga shi sai ita ne a universe dinsu, yasan zai more mace kuma zai samu nutsuwar da bai taba samu ba, yasan zai samu abokiyar hira da Nishadi sai dai kash, yasan kuskure ne ba zai taba samun Zainab cikin sauki haka ba ajiyar zuciya ya sauke a boye yadda ba zata fahimci ajiyar zuciya yake ba, , muka fito zama nayi ina me nufar daki ya juya yana kallona. "Tafiya barci?" "Aa waytaa!" Na faɗa ina juyawa, can na dauko wayata sannan na ɗauki wayata na dawo parlourn, sannan na zauna ina mai bude data, ai kuwa kamar a mafarki na wani ya ɗan renin hankali ya min hacking din account Dina. Tsaki nayi ina faɗin.."Wani wahalallen ne ya min hacking Allah ya bashi saa tow babu kome da zasu ci mutuncina!" Murmushi yayi yana kallon yadda yake ta tsaki. "Akwai abinda kike boyewa ne da kike son ayi miki hacking?" "Wai ni?" Na nuna mishi kaina kafin na fashe da dariya. "Ai ni bani da wani abin da zai janyo min magana!" Kallona yayi ya ce min. "Me yasa bakya sona?" Ji nayi maganar tazo min bazata, ban san lokacin da na wani haɗe rai ba, na ki kula shi sake magana yayi. "Ina sonki!" Wani irin mikewa nayi zan bar parlourn ya ce min. "I know ba zaki tab'a soyayya da mahaukaci irina ba, wanda yake boye laluranshi domin kanshi " shiru nayi a hankali ya a taso daga gaban laptop din ya rungume ni. "Ki taimaki mahaukacin nan ya yi jinya tsoron a gano bani da lafiya nake! Ki min wannan alfarman ni kuma zan miki duk abinda kika bukata!" Juyowa nayi ina kallonshi, kaina a sunkuye na ce mishi. "Zan taya ka jinya da sharadina!" Murmushi yayi ya riko hannuna ya ce min. "Ke daya ce kika iya hango zahirina, daga ke sai Mai babbar daki kuka san yadda ke." Ya fada cikin wani irin yanayi, dunkule hannuna nayi ina kallonshi cikin idanunsa nake kallo ina hango tsoron da yake cikinsa, ina hango wani firgici da sarewa daga tsammani. Rike hannuna yayi yana murxawa yana mai son yin magana amma alamar shakka da tashin hankali yana kara cika zuciyar fargaba da kwararowar tsoro daga cikin idanunshi yasa na ji jikina yayi bala'in sanyi, rike hannunsa nayi cikin nawa. "Ina jin tsoron kada ki guje ni, ina jin tsoron ki san wani abu a kaina


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login