Showing 261001 words to 264000 words out of 304445 words

Chapter 88 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

116

sai a waya suke cinye juna kamar Au'zubullahi. Musamman ita Ikhlas da take danne shi.
***
Wato wani abu da na fahimta, shine Nadiya tana Dan bukatar mijinta zuwan shi Gombe sai da ta min korafi wato ni ba zan iya zama ba tare da shi ba, dariya na mata na gaya mata cewa. "Ki sakawa mijinki sarka kada ya zo min idan ba haka ba zai lalace a wurina!" Daga nan sai ta ce min. "Zainab kenan, kome dai lokaci yake bukata idan aka rabu lafiya kin ga ba mai yiwuwa ba ne samun shi haka!"
"Rai dai idan da nisan kwana babu abinda ba zai faru ba!" Daga nan na auna maganarta da kaifin basirara na fahimci mijinta take magana a kai! Murmushi nayi kawai na lallaba na zuba mishi idanun, da ya ce min zai zo na ce mishi ya zauna ina period. Wannan yasa shi hakura bai zo ba, nima na dakatar da hakan ne saboda wata rana kada na ji zafin idan ayi min haka.

Wasu mutanen ko me kake musu ba zasu tab'a gani ba, a yanzu na fara fahimtar wace ce ni me ya dace na yiwa kaina da rayuwata i need to love myself, sama da shi mijin namu, dole na kaunaci kaina koda kuwa ace babu yadda na iya ne.
Sati uku cimma muka dawo gida da sha tara na arziki, daga masarautar Gombe mutane masu karamci da son bako, Umma ce da kanta da Hajja da Tarasulu suka zo, suka min gyaran gidana, har da girki suka min ina isowa, Faruq ya dauke mu ya fara ajiye Yeemar itama da Mamanta ta zo mata gyaran gida, aka wuce da ni a gajiye na isa parlourna, su Umma suna ta hira. Na shigo."Ummana!" "Na'am Auta!" Da sauri na isa wurinta, na kwanta a jikinta ina faɗin. "Umma nayi kewarku!" "Har dani?" Inji Hajja, "ke da kike da Tarasulu?" "Bakin ciki kike min don Allah ya wanke ni ya bani aminiyar da bata tab'a cin amanata ba!" "Ai shi yasa nake kina.da ita fa! Nace wani abu ne Tarasulu?" "Ina fa kika ce son rigima ce irin na Hajiya Abu!"
"A'a Tarasulu kada ki ci amanata, na gaya miki yadda yarinyar nan ta min a sunan yar kishiyarta, sai ki kware min baya!" Na juya ina faɗin. "Amma ai mai martaba ya wanke ni ke da abu baya wucewa a wurinki!" Na fada ina mai tashi jikin Umma na nufi daki, a lokacin na ji ana kirari alamar zai shigo, nan Hajja ta kirkiro wata draman ana zaman lafiya wucewa nayi bana son ya same ni da kayan da na kwaso gajiya, ina shiga ban daki na fada na rufe kofar ban dakin don zai iya shigo min, sannan na yi wanka sosai, na fito na saka wata Pakistan da muka shiga wani mall muka saya a Gombe ruwan orange, don na ga kamar yana son ya ga na saka kaya mai zubin orange, kwalliya na cab'a na shafe jikina da humara, sannan na fito sanye da wata takalmi mai sauki mara tudu, na fito parlourn d'ago kai yayi ya zuba min, wurin abinci na nufa na zuba d'ago kai nayi ina kallonsh da nufin. "Na zuba?" Mikewa yayi ya nufi hanyar waje yana faɗin. "Umma Faruq zai mai daku, ku gaida Abba da jiki!" Ya fita wato na bishi, hada na shirya abincin a tire na ce musu. "Bari na kai mishi." "Kada ki shanya mu dai, sannan ya ce zai bawa Tarasulu kunkurumaita kat!" Kan Uba na fada a raina wato Hajja tana azabtar da turanci fiye da yadda baka zato, fita nayi na bar su Tarasulu da Hajja na raba hali, ina shiga na ajiye tiren na nufe shi da gudu yana tsaye a gaban table din da Computer dinsa yake bude min hannu yayi na fada kirjinshi ya dauke ni cak. "Na azabtu gaya min me ye sirrinki?" "Nasan kana haduwa da wata mace, zaka manta da wata Zainab!" K'amk'ame ni yayi yana sumbatar wuyana. "Akan ki nasan so, akanki na san hakikanin so, akan Nadiya nasan mace da yadda take, akan Ijlal na fara zama Uba, gaya min taya zan mance da ke? Ba zan mata da ku ba. Har abada." "Muje mu ci abinci!" "Ko kin ji zafin na kira sunansu ko?" Jan kumatunsa nayi ina faɗin. "Matanka ne idan nace ba zaka mu'amala da su ba Allah sai ya yi fushi da ni, ba burina na raba ka da kowacce ba, ka ji My Baby!" Na fada ina shafa kanshi abincin na bashi a baki yana ci ina mishi labarin goben, sannan na gaya mishi ina son na bude wurin gyaran jiki da kwalliya. Ruwa ya sha yana tambayata.."me yasa?" "No nawa na kaina ne, ba sai ina kiran mai gyaran jiki ba ni ce nake son na bude ba sai na kira wasu ba.".
"Shi kenan." Ya fada yana shafa kumatuna. "Shi kenan fa kace?" "Yes na!" Ya fada yana d'aga min gira, wannan gayen!" Tura baki nayi ina faɗin. "Sai kuma ka yi." Haka muka yi ta hira can ya ce min. "Mai Babbar daki ta ce min na dawo da Ijlal." Murmushi nayi na ce mishi. "Ko don rayuwar Amirah dole ka dawo da ita fa!" Gyada kai yayi yana murmushin farin ciki, na ce mishi."kana murna Matarka zata dawo!" "No Munirah ma ta gaya min Nadiyyah zata dawo itama and ko jiya Ijlal tayi ta kirana!" "Mu bar zancen nan matanka ne babu ruwana a cikin lamarinsu!" Yadda nayi maganar sai ya ga kamar ko ina kishi ne, gyara zama yayi ya ce min. "Kina jin ba dad'i ne?" Dariya nayi kamar xan kifa nace mishi. "Wallahi bana jin kome akan matanka, asalima ban dauke su a matsayin kishiyoyina ba, so ka daina tunanin zan rabaka da su. Ko zan ji hausuinsu."
Shiru yayi yana faɗin. "Allah yasa!" Zan bashi mamaki kuwa wallahi zai gane Annabi Isa ba dan Allah bane, haka na gama mike xan sallami su Umma, ya ciro kudi da takarda ya bani na kaiwa su Umma aka kai su gida, na nutsu sosai. Da la'asar can na shirya zuwa cikin gida na gaida mai babbar daki da tsarabarsu, sannan na dawo. Na nufi bangarena, abincin wurinsu Umma na kara ci na koshi. Da dare yana dawowa muka shirya zuwa asibiti na rikewa Hajiya Altine kayan motsa baki, shima ya saya musu kayan taɓa muka isa, yadda bata nuna min abin ranar yana ranta ba, haka nima ban nuna mata na rike ta ba, kowacce tana rike da abinta a ranta, mun sha hira da Hajiya Altine wacce rabin hiran rayywarta da irin gwagwarmayar da tayi na da'awa ce, bayan mun gama hira muka bar asibitin nasiha da jan kunne da tuna mana da akwai wata rayuwa bayan wannan, yasa na ji na watsar da kome na rungume kaina. Na kuma rungume rayuwata.

Koda muka dawo gida, a gajiye nake shi yayi min tausa bayan ya murkushe baiwar Allah. Kwanakin da suka biyo baya gyaran gidan Ijlal aka yi wacce zata dawo saboda Yarta, sannan ya sa Faruq ya kaita asibiti aka duba lafiyarta, bayan kwanaki Nadiya ta dawo, a ranar Hajiya Altine ta koma Jos, bayan ta akan sai anyi mata aiki zata dawo, a ranar na tattaro shirgina na dawo bangarena, duk da cikinta bai bai hanata amsar mijinta ba, sai dai fa da shiga wata duniya ciki ya ce bai san zancen nan ba, zai dirko duniya, a daren aka sake kiran Doctor Munirah wallahi har tausayi ta bani, ban san ta zo ba sai da ya kira ni n a shiga yake gaya min Nadiya ba lafiya. Doctor Munirah fada tayi sosai kaca-kaca tayiwa Nadiyyah ta gaya mata ko ta kashe kanta namiji ba zai fasa abinda yayi niyya ba...
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 86

Idan zata hakura ta hakura. Budar bakinta ta ce mata. "Idan ma mutuwa zan yi na mutu amma ba zan iya gani na kauda kaina ba!" Iya gaskiyarta ta faɗa, haka yasa Doctor Munirah tayi iya abinda zata yi, ni nasan Doctor Munirah tun da jimawa, amma bata hada mu ba sai akanshi, haka yasa gama abinda zata yi aka mai da ta gidanta.
Allurai da ruwa ta saka mata, ta barta don ta lura kishi na damun Nadiyyah ainun, washi gari da na shiga gaishe ta wani ciki ciki, tun da na fita ban kara bin ta kanta ba, haka sai ya bani damar fahimtar, bata son Ina shiga harkanta, ba fada ba zagi na janye jikina fiye da yadda ba a zato, a cikin san tsukun Ijlal ta dawo, tayi sanyi a idanun amma ni nasanta ba zata yi sanyi a badili ba, haka yasa na kame kaina na ki yarda na shiga harkan kowa, shi kanshi ganin yadda kowa take inda take sai yake jin babu dad'i, amma ya hakura kowa ta zauna a inda take.
Cikin ikon Allah na koma hidimar kasata a zanzabira, na zama busy domin wani gidan rediyon aka tura ni. Wanda ya kama har aikin dare ina yi. A hankali na janye jikina daga gare shi, sannan Ijlal kuwa abinda ya mata ba dad'i domin duk shi da kansa ya sayo alluran family planner, ya Mata na wata uku, ya rantse ba zai haihu da ita ba sai ta ji yadda kowa yake ji akan jinyar da Amirah take fama da shi. Kusan tsiyar da nayi mishi, tattara shi nayi na ce na bashi hutu ya kula da Nadiyyah da Amirah, na mai da hankali akan abinda nake da fari bai ki ba, musamman da Ijlal tayi kwantan bauna, ai kuwa aka fara tafiya rimi-rimi.

Ni nasan Ijlal idan ta ce zata yi abu kaf duniya babu me iya hanata sai Allah. Haka yasa ni ba zaman gida nake ba. Nadiyyah kuwa ita ce ke fama da kanta, wata ranar talata ana ruwan sama na dawo da yamma, na samu anyi wata irin rigima har an fasa window Ijlal. Taha rungume da Amirah sai kuka take, shiga nayi bangarena na same shi a parlourn yana zaune huci yake kawai amma kasan ranshi a b'ace yake, wallahi gabana da yayi wani irin faduwa wanda tun da na hango Ijlal rungume da Amirah a cikin ruwa tana kuka naji gabana yana bugawa. Daki na wuce ya ce min. "Zainab kashe ni zaku yi ne?" Wani abu ne na ji ya tsarga min a hankali na juya na kalle shi a hankali na juya na wuce dakina. Biyo ni yayi na wuce ban daki nayi fitsari, sai dai wani irin murd'a da cikina yayi hade da faduwar abu da jini mai yawan gaske na ce. "Ya Allah!" Da karfi, haka jini ya tsinke min kamar da bakin ƙwarya.
"Doctor!" Na kwala mishi kira da ƙarfi, ashe ya fita haka na kara kiranshi ya fita dakyar na iya fitowa dakina na dauki zanin gado nayi napkin da shi, na fito ina me niman wayarshi amma yaki dauka, a hankali na lallubi number Ya Abid. "Baban Imam zan mutu!" Na fada ina sake wayar wanda ban san me ya kuma faruwa ba.

***
Sai washi gari na bude idanuna na ji sautin Ac, ana faɗin. "Ai wallahi abin bai yi ba eh tow ita dai Munirah ta ce cikin ya lalace ne saboda damuwa da gajiya, sannan itama kamar bata san da cikin ba gaskiya!" Naji Muryan Umma tana magana. A hankali na fara ƙoƙarin tashi, Mai Babbar daki ta ce min. "Zauna Ummana Zainab, sannu Uwar Tagwaye!" A gajiye nace mata Ummi. "Na gaji!" Shafa kaina tayi na wani lokaci tana tofa min addu'a, tare da min sannu, shigowar Munirah yasa ta matsa aka kara min allura barci ya dauke ni, ban sake farkawa ba sai washe gari, na bude idanuna na ganshi rike da hannuna. "I'm sorry!" Ya fada idanunsa, suna cika da kwalla. Murmushi nayi na ce mishi.."for what?" "Nayi sanadin da muka rasa Babynmu!" Murmushi nayi na damke hannunsa. A hankali na ce mishi. "Allah zai kawo masu albarka da lafiya!" Shafa kaina yayi yana faɗin. "Baby dama baki san da cikin bane?" D'ago idanuna nayi na kalle shi, kafin na ce mishi. "Tun sunan Amirah rabona da period!" "A Gombe fa?" Ya tambaye ni, murmushi nayi ina faɗin. "Ai saboda ka zauna a wurin Nady na maka karya." Na fada ina dauke kaina. "Look at me!" Ya fada yana juyo da kaina. " Kin san yadda nayi kuka akan wadannan Yaran da na rasa me yasa baki bawa kome muhimmanci har da lafiyarki?" Yunkurin tashi nayi na zauna tare da rike hannunsa ya taimaka min sosai. "Wallahi ban san cewa ciki ba ne, domin bana kwadayi bana kome Allah ya kawo karshen cikin ne da sai dai yayi ta girma ban sani ba." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce min. "Saboda ke na rasa yara uku fa? Daya a gida, daya a cikin bedsheets din da kika daura daya kuma anan suka cire miki shi, Haba Zainab! Da nasan abinda zai faru kenan da ban fara d'aga miki hankali ba."
"Daga baya kenan na gaya maka Allah ne ya nufa!" Maluma ce ta shigo tana faɗin. "Kin tashi!" A yadda tayi maganar na ga kamar ranta a dan b'ace yake, yana gaishe ta sai naga kamar ranta bai so amsawa ba. Fita yayi ta ce min.."Sannu kin ji ko, tashi na gasa miki jiki!" Murmushi nayi na wuce ban daki ina kallon ledar jinin da aka kara min, sai yanzu na tuna shima na ga inda aka saka mishi plaster..
Juyawa nayi na kalli Maluma na ce mata. "Bai da lafiya ne, shima?" Tab'e baki tayi tana faɗin. "Da bai kashe ki ba ai da sauki." Shiru nayi na shiga wanka na cire kayan jikina, ai kuwa Maluma ta shiga gasa min jikina a hankali ina jin jikina yana wani irin ciwo a hankali, har ta gama sannan ta fito ta barni na yi wanka da gasa jikina, a hankali naji jikina kamar an warware ni, sannan na saka riga da zani, na fito ina goge gashin kaina. Kallon juna muka yi da shi, yana juya min tea. "Yaya baka da lafiya ne?" "A'a me kika gani?" Hannunsa na nuna mishi da idanuna, murmushi yayi ya ce min. "Jini kika bukata aka diba!" Murmushin farin ciki nayi ko ba kome jini daya muke dauke da shi, ajiye kofin tea din yayi ya nufe ni na zauna a bakin gadon, ya amshi towel din ya fara goge gashina, ina murmushi. "Maluma tana fushi da ni ne fa!" Sai a lokacin na d'ago kai ina kallonshi. "Ka yi wani abu ne?" "Ba ita ɗaya ba, yau kwana uku kenan Ummi bata min magana ko na gaishe ta bata amsawa." Zama yayi yana nad'e towel din tare da tattara min gashina. Yana kamawa ya dauko min tea na fara sha ina kallonshi. "Me kayi musu?" Hannunsa a sanyayye ya miko min bowl din farfesun kaza, a hankali na fara daukar namar ina ci. "Ranar da abin ya faru, na fita kenan ina wurin Ummi kika kira naki ɗauka, wallahi ban san kika cikin wannan yanayin ba ne." Shiru yayi na wasu mintina, bayan can ne Ijlal ta kira take gaya min ga yan gidanku nan, koda na iso bakin gate din fita daga unguwarmu na ga motar nayi ƙoƙarin tare shi amma yaki, dole tasa na bishi asibitin. Ashe ke ya dauko ya tsaya min karin bayani, yaki shine nace kada su tab'a ki sai ya gaya min hujjar dauko min ke, a lokacin kuma Munirah ta fito take gaya min ashe ya kirata dama kunsa juna ne da ita?". Shiru nayi kafin na ce mishi. "Eh na santa ita ce ya so aura sai aka yi rashin dace, Mahaifinta ya mata miji, shine har yanzu muke gaisawa sama-sama!" "Zainab gida na dawo na ga dakinki kaca-kaca da jini ga gudan jinina a ƙasa! Nayi kuka na yi bakin cikin asarar da nayiwa kaina! Me yasa kika boye min da kin yi ta kirana dole na dauka kiranki!" Ya fada yana kallon yadda nake kallonshi nima. Shiru nayi ina kurban tea a hankali, ina jin wani d'aci a raina. A hankali hawayen da yake son zubo min ba danne, har ya gama magana ban ce mishi kome ba, turo kofar aka yi Nadiyyah ce da Ijlal. Kallonsu nayi a hankali na sake murmushi. "Ashe kin farka?" Ijlal ta tambaye ni, na ga sauyi a tare da ita, fiye da dawowarta. Mikewa yayi yana shafa kaina yana me daukar mayafi ya lullube min kaina. "Ki ci abinci kada ki yiwa wasa da cikinki!" "Ok Sir!" Na fada ina sara mishi. "Silly girl!" Ya ja kumatuna, ya fita ba tare da ya kalli inda suke ba. A bakin kofar fita suka hadu da Mai Babbar daki, "Sannu da zuwa Ummi!" Dauke kai tai tare da shigowa. "Ummina baki ji yana gaida ke ba ne?" "Zainaba ya jikinki?" Yar dariya nayi ina faɗin. "Ummina da sauki fa!" Juyawa tayi tana kallonsu. "Kin biyo ta ku karasa ta ne?" Sunkuyar da kai suka yi, a hankali ya sake kofar ya fita. Ban yi magana ba, ina wasa da kofin hannuna. "Nace kun zo ne ko karasata? Ashe kishin naku na karya ce! Idan mace ta isa mace tana kishi ne da kanta da kuma zuciyarta. Ba irin naku kishin daga bin boka sai tashin hankali ba. Nadiyyah kin bani mamaki idan akwai wanda ya dace ya nime zaman lafiya kece mai fama da hawan jini. Amma har dake a bata gani ba, zuwa yanzu nayi walkiya naga kowa na kuma ga abinda yake ranku daga yau duk wacce ta kara tashin hankali da fitina ko duniya suka hada da shi sai sun rabu na gaji da fitinarku!" Yadda Mai Babbar daki take shiga ba nan take fita ba, har ta gama


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login