Showing 6001 words to 9000 words out of 304445 words

Chapter 3 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

124

an gama posting zai koma)*
*Ɗaya: 1k*
*Biyu: 2k*
*Uku: 3k*

domin tura shaidar biya ko Ƙarin bayani, ku tuntuɓi:
*08130269641*
Ko
*08137311900*
Ko kuma
*09063467258*


#Top-notch4
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: ROYAL POLITICS 🔥
_An yanka ta tashi_
Ramlat A Manga
Mai_Dambu
TOP-NOTCH SEASON 4
Sadaukarwa ga Auntyna RUKAYYA GOMBE 🥰 🤩 😍



02..
Suicide

"Kana tsammanin za a barshi ne ya cigaba da yadda yake so?" "Je ki!" Ya fada duk da duhu ne amma ta kara kallonshi. "Me haka yake nufi?" "Irin wannan abin Gwaska dakare ya aikata ya fada matsala idan kika yi wani abu tow da hannuna zanta yankar naman jikinki!" A rude ta ce mishi. "Kana nufin kashe ni zaka yi?" "Fita!" A hankali ta fito kafin ta ce mishi. "Shi kenan sai mun hadu kenan!" Ta fada tana me komawa cikin gidan sannan yar tsohuwar motar bar kofar gabas din.
***
Khlas.
Duk da part dinmu yafi kusa da na Mommy Turai, haka bai hana ni jin yadda take kuka tana magiyar rokon Abba ba, gaskiya Abba yaso kansa taya zai dauki Iram ya bawa Abokinsa da tsufa suka ci mishi, tsaki nayi ina nazarin program dina ta ce mishi. "Kaso kanka Junaid kada ka manta nima y'ata ce, taya zan yarda ka lalata mata rayuwa da auren matacce!" Rintsa idanuna nayi tare da bude su sakamakon amsar da Abba ya bata. "A'a gawa ne, idan kika fusata ni zaki ga b'acin raina." "Tow idan kuwa baka kyale min y'a ba wallahi zan maka ka kotu, akan me? Baga Zainab ba me yasa ba zaka bashi zainab ba?" "Ai hadin ma ba daya ba, Ita Iram din dai na zab'a domin ita Ikhlas har yau bata da hankali. Sannan da kike magana ita Ikhlas din kin tab'a jin labarin tana da wani saurayi ne? Sannan dukkansu Yayana ne, don Allah kada ki cigaba da raba min kan Yarana!" Ya fadi haka, tashi zaune nayi ina me kashe laptop dina domin fadarsu hana ni barci yake tunda da karfi suke na dauki bargona, na nufi bangaren Umma knocking biyu nayi ta bude min. "Khlas lafiya?" "Lau Umma yau ni daya zan kwana shi yasa na dawo bangarenki!" Kallona tayi kafin ta ce min. "Shigo tow!" Na wuce ta, aikuwa ta rufe kofar na wuce dakin da aka ware na daban na jefa pillow na a gadon. Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na kwanta ina jin kamar na sauke min nauyi. Wayata da na shigo da ita ce tayi wani irin ƙara, dauka nayi na ina kallon sunan wanda ta kira wayar.
Joy Moses, dauka nayi ina fada mata "fine girl." "Zeey Juh babu lokaci, I'm in danger, yanzu haka ina farautar rayuwata. Please zan bar miki sako duk abinda ya faru kiyi kokarin bincike. Domin zasu zo niman drive din." "Joy ban gane ba?" Cikin gaggawa ta ce min.."Zeey Juh ki duba gadona da kyau." Karar da na ji na ce mata. "Joy lafiya!" Katse wayar tayi koda na kira wayar bata dauka ba. Haka nayi ta kiranta amma bata dauka. Joy Moses abokiyar fada ta ce, saboda tana da kwazo amma a haka bai hana mu abota da juna ba. Domin tun kwazonmu ne yazo daya. Ita din iyayenta Christian ne, sannan makarantar mu daga secondry school tare muka yi, koda muka hadu a jami'a department ya rabamu ita suna bangaren Law ne ni kuma na dauki bangaren Mass communication, haka yasa haduwarmu a jami'a sai ya zama kamar ya mai damu abokai ne, Joy kyakyawa ce wacce ake kira da Fine girl. Duk da bana shiri can amma duk wani abin da ya shige mata kai tana tuntubata.

Sannan tana yawan bani labarin cewa. "Zeey Juh akwai wani boyayen al'amari a cikin makarantar nan, i think Dad ɗinki bai sani ba, sannan ina kan bincike ne ni da wasu mutane, idan bincike na ya zama daidai kece yar jarida zan fara bawa labarin ke kuma ki isar da shi ga inda ya dace." Kallonta nayi na ce mata. "Me yasa kike fadar haka?" "Saboda!" Sai ta mike tare da faɗin. "Manta kawai zamu haɗu." Yau wata biyu kenan da muka yi maganar sai ga kiranta, kusan har gari ya waye ban wani yi barcin kirki ba, sannan bani da wani kuzari abinda na sani raina ba dad'i. Kitchen na nuna Mama Zuwairah me yin aikin Mommy Turai tana ta jefa dan wake, ni kuma a duniyata na tsani aikin Mama Zuwairah. Wucewa store nayi na dauki kwai da indomitable guda biyu. "Ikhlas dauka da ni."inji Iram "Ke kuturwa ce?" Na tambaye ta, murmushi tayi tana cewa "ko daya amma nasan dole zaki dafa da ni." Tsaki nayi na wuce kitchen. "Ekilas ga dan wake ina yi ki ce zaki dafa wani abincin? Gaskiya zan gayawa Hajiya Turai ta san abinda zaki yi." Shiru na mata na kunna gas na cigaba da aikina babban abinda yake ƙara bani haushi bata iya fadar sunana ba, sannan tun tashina na ganta a tare da Mommy Turai. "Ke wacce irin mara kunya ce ga abinci amma sai kin dafa wani." "Mommy kin san bana cin mangyada kuma Abba ya fada idan za'ayi dan wake ko shinkafa da mai da yaji na nime abinda zan ci, shi yasa na dafa indomie sannan ai bani daya ba ce zan ci har da Iram!" Ina fada haka sai ta sake fuskanta tana kallon Mama Zuwairah. "Bana son kananan magana!" Sannan ta juya tare da barin kitchen din, kallon Mama Zuwairah nayi na ce mata. "Mama shi fa wannan rayuwar baka da iko ka hana mutum yadda zai yi, sannan kin san dai ba kawo ni aka yi gidan nan ba gidan Ubana ne. Sannan ni ban ga dalilin da kome muka yi zaki je kina hada mu da Mommy Turai ba, ita mun fi kusa da ita domin uwa ce a gare mu, ki ga yadda Mama tasalla take rayuwarta babu ruwanta da kowa, sannan dukkan mu yan gidan nan muna girmamata. Ban san wani abu kike bukata ba, amma matukar baki kula da harkokin ba zaki bar gidan anan." Na fada bayan na dauko wani gasashen nama, na bude domin tun safiyar jiya Abba ya bani amma na saka a frijin kitchen din nasan za a iya wani abin da bai ba, juyawa nayi a cikin indomie din na zuba kayan dandanon, sannan na bar bude tukunyar tea, na diba daidai cikina kafin na hada madara da cadbury, sannan na jera a tire na nufi dakinmu, anan na samu Iram tana kuka. Kallo daya nayi mata na cigaba da cin abincina. "Baki damu da halin da nake ciki bane?" " Akan me zan damu? Abu daya na sani Abba ya yarda da halayenki ne yasa yayi choose ɗinki, sannan ya tabbatar ba zaki kunyata shi ba yasa yake da Yakini akanki auren nan fa ba yanzu zaa yi ba, da sauran lokaci idan ke da Mommy kuka cigaba da matsawa kin san Abba kuma kin san waye shi da abinda zai iya." "Ikhlas idan kece ya zaki yi?" "Biyayya zan yi daidai gwargwado,amma fa ba sauki ina da wanda nake so!"
"Amma ai Abba bai sani ba!" "Eh ba kome ake fitowa da shi fili ba, kowa yana da nashi sirrin nima nawa sirrin Ya Uwais ne." Na fada ina mikewa daga flat din na nufi bangaren Malama. Da sallama na shiga tana lazimi, daki na wuce nayi wanka na shirya cikin riga da zani na atamfa, tsayawa nayi na kashe dauri sannan na dauki babban mayafi na yafa, kasancewar wancan dakin mu na yan mata ana shiga kuma ana dan zare mana abubuwa sai muka bar shi kawai a na kwananmu, sauran abubuwan kuma zamu dawo dakin iyayenmu, sai mu shirya. Kuma da jiya bangaren Maluma na dawo na kwana na rantse sai ta kwad'a min mari, domin zata ce na je ina jin gulmar fadar Mommy Turai da Abba, ina gama shiri na dauki jakata na wuce dakin Umma na dauki wayata da na ga miss call rututu. "Iram na tafi fa!" Na fada ina sauri. "Gani a bangaren Abba!" Ta fada, kallon shigar da nayi na kuma. Yanzu Abba sai ya ce na sauya shiga. Tsaki nayi na shiga bangarenshi. "Ina kwana Abba!" "Lafiya lau!" Na nime wuri na zauna. "Kin ji labarin ne?" "Wani labari kuma?" Na tambaye shi ina kallon Iram. "Na mutuwar kawarki!" "Kawata kuma? Wacce kenan?" Na tambaye shi a karo na biyu.."Joy Moses!" Rufe bakina nayi da hannuna biyu idanuna a buɗe. Jikina ya dauki wani irin rawa. Kamar xan sake fitsari. Hawaye ne ya zubo min sharr. "Ana tsammanin daren jiya ta mutu." Mikewa nayi da sauri zan fita Abba ya ce min. "Jira nima zan fita sai na ajiye ku a wuraren aikinku." "A'a Abba zan je na ga Joy ne ni ce last call dinta!" Na fada ina fashewa da kuka. "Abba ta kirani tana bukatar taimakona Abba wallahi ta kirani ka ga kiran?" Na mika mishi wayar. Kallona yayi kafin ya ce min. "Zainab!" "Na'am Abba!" "Bana son ko Mahafiyarki ta ji wannan labarin, sannan kema Iram ki rufe bakinki. Kada na ji kada na gani." "But Abba why?" "Case din kashe kanta tayi?" "A'a Abba kashe ta aka yi, na rantse kashe ta suka yi!". "Nace kiyi shiru! I believe what you saw not what you hear, kin ji ko baki ji ba?" Na ji nace ina shashekar kuka. "Ki wanke fuskanki muna jiranki!"

Bayan na fita Iram ta ce mishi. "Abba Ikhlas bata karya, sannan ka ce mu rufe idanunmu akan abinda ya faru Joy kawarmu ce idan muka yi haka bamu ci amanar zaman tare ba?" Shiru yayi ya goge kiran sannan ya mika mata wayar. "Ba kowani abu ake bukatar magana akai ba. Kin fahimta?" Ya tambaye ta, yana barin parlourn. A waje na same su, gaban motar na shiga tun muna Yara idan zamu fita da Abba tow gaba nake shiga. Al'adar zaman gaban mota ya kama ni. Don tun Iram tana jin haushi har ta daina ta fahimci ina son zaman wurin ne kawai ba don wani dalili ba. Ta kofar Jami'armu, muka wuce ina kallon yadda aka cika kofar musamman yan jarida. Wayar Abba ce tayi ƙara. "Dauka yayi yana faɗin. "Ina kan hanya ne?" Daga can aka ce mishi. "Nafi'u Abubakar Shaiba ke magana." "Nace maka ina hanya ne." "Ina jiranka." Kashe wayar yayi yana faɗin. "Muje na ajiye ki Iram!" Sai da ya ajiyeta sannan ya dawo ya ajiye ni saboda tafiyarmu ba daya ba ce. Lokacin da ya kawo ni.."Kada na ji kada na gani!" Gyada kai nayi har cikin station din ya rako ni. Daurewa nake amma kuka nake son yi, ina shiga ya fita.

***
Emirate meeting

Karfe yake d'agawa a hankali yana sauraren labarin safiya na gidan Tv Z, a hankali yake ƙara d'age karfen, yana jin mutuwar ya d'aga karfen kenan ya kusan subucewa ya fado kirjinsa, Faruq ya tare.."Sir!" "Na gode!" Ya furta yana tashi daga table din, idanunsa yana kan tv hoton dalibar da ta kashe kanta. "Ina file din?" "Suna study room!" Ya fada yana fita daga dakin. Goran ruwa ya dauka ya bude murfin ya fara sha a hankali. Shigowa Faruq yayi yana faɗin. "Gashi Sir!" Amsa yayi yana kallon file din farko. Ajiye goran ruwan yayi ya fara bude na farko. Kafin ya d'ago kai Faruq ya ce mishi. "Wannan shine na haɗin gwiwarsu!" Wato file din da yake hannunsa. Ajiye shi yayi ya dauki dayan file din. "Wannan kuma na rabuwarsu!" Shima nan ya ajiye, kai hannunsa yayi zai dauki na karshen sai ya fasa. "Shi kuma yana dauke da wasu." a hankali ya janye hannunsa yana me d'ago kwayar idanunsa akan agogon hannun Faruq. , shima kallon agogon yayi. "Taron majalisar fada!" Faruq ya fada yana kallon agogon hannunsa a karo na biyu. Shiru yayi yana nazarin abinda zai wargaza zaman amma yasan haka ba zai yiwu ba. "Baby!" Nadiyyah ta kira sunanshi tana tsaye a bakin kofar, gaishe ta Faruq yayi ya bar dakin. "Good morning Baby!" Idanunshi yana kan file sai da ya yi kamar bai ji ba, kafin ya ce mata. "Morning!" Cikin wani irin muskilanci da yake ji da ita yau ta motsa masa. "Baby nayi wani abu ne?" D'ago kai yayi ya kalle na wani dakika, kafin ya cigaba da kallon file din. "Kayi hakuri Baby." Magiya take tana ƙara bashi hakuri don ita tasan laifinta, ya hanata shiga anyhow tana zuwa gaban Faruq amma Nady bata ji, kayan barcin jikinta da suka kwana da shi ne har yanzu bata cire ba, da yake b a gantali zata je ba. Shi yasa take zaune har lokacin bata yi wanka ba. Yana da wata dabi'a yana son tsafta ya ga mace tayi wanka da safe ta shirya ko bata yi makeup ba, haka yana mishi dadi ta san halinsa sarai. "Baby bari nayi wanka." Bai ce mata cikanki ba ta bar dakin. Bin bayanta yayi da idanu, bai san me Nady take amfani da shi ba, kwana biyu nan idan tana kusa da shi sai yayi ta jin wani irin hamami. Wani bangare na zuciyarsa ta ce mishi. *Ko don bata yi wanka ba ne?* Mikewa yayi shima da file din karshe ya nufi dakinsa.

Cikin mintuna ƙalilan yayi wanka ya shirya tsaf, sannan ya saka wata shadda dark blue, ya ajiye mata farar hula, sai takalmin baka hafcover, turare kala uku ya Ciro daga cikin closet dinsu, Shumukh, Musk Khabib, sai na karshe clive Christian, ya fesa na karshe a hankali. Sannan ya mai da ya rufe, kallon fuskarshi yayi a madubi yadda ta fito fayau. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kwashi phones dinsa ya fito, a bakin kofar ya samu Faruq a tsaye, mika mishi wayar yayi, ya amsa da sauri. Nufar dakin Nady yayi cikin nutsuwa ya kai hannunsa kan handle din kofar ya tura a hankali, towel ne a jikinta tana shafa mayukan gyaran jiki, ga wasu wanda zata hadiya. Daga bakin kofar ya tsaya yana kallonta. Ban da yana da uzuri da ya tsaya sun cancare. "Baby ina zaka?" Ta juyo gare shi gaban nan babu towel ta sake karkad'a mishi bulla-bullan Boons tayi wanda yake ganin kaf duniya babu macen da zata kai Nady dinsa kayan jiki da iya gyara jikinta. "Fada!" Ya fada yana jan kofar dakin. "Baby Hasina James Nakewa zata zo!" "Don't go out!" Ya fada a kasaitacce. "Baby please!" Share ta tayi ta bar gidan. Tsaki tayi tana faɗin. "Lokacin da zan je na dawo kana ina?"

Tunda suka isa fada kusan babu matashin sai shi, duk sai yake jin shi a matukar takure, ga kayan da bai saba sakawa ba, ya kakamawa kansa. Duk da yana jin hiransu amma bai ce uffan ba domin ya fahimci babu wanda yake son yayi magana. Alama yayiwa Faruq ya sunkuyo. "Zan tafi!" Ya furta a hankali, kafin ya mike, ya zuba hannunshi duk biyu a aljuhun rigarshi. "Salmanun Faris ya zaka fita ba a gama meeting ba?" Kallonsu yayi da kyau. Ya kalli agogon hannunsa. Kafin ya motsa baki ya ce musu. "Na ga hiran taku bata kare ba ce." Ya fada zai juya. "Gaskiya hiran bata kare ba ce, ba yau ka saba juyawa ga asalinka ba, idan ka gadama ka zauna ayi maganar da kai idan kaso ka tafi." Kafada ya d'agawa Magajin garin Zanzabira wato Alhaji Rilwanu Abubakar Yayari. Ya cigaba da tafiyarshi. "Faris!" Jin muryan Wazirin Babansa Alhaji Mamman Abba Yayari yasa shi dakatawa. "Dawo ka zauna gwamnati ta bada wa'adin kwanaki a fitar da sakamakon wanda zai cigaba da rike kujerar masarautar nan." "Baba Waziri duk yadda kuka yi daya ne." Faruq ya faɗa. Kafin ya gyara tsayuwarshi ya cigaba da cewa. "Sir Faris yana da aiki a asibiti ne, sannan idan aka yi hakuri tunda mai Martaba yana raye bai kamata a ce an zabi wani sarki ba sai dai a bada rikon kwarya, wanda Babu wanda suka dace da wannan rikon ƙwarya kamar Alhaji Mamman Abba Yayari ko Alhaji Kabiru Hamud Yayari wato Baba Galadima, cikin ku biyu zaku iya zabar wanda ta dace, wannan shi ne ra'ayin Ubangidana." Dama shi kan ya bar fadar cikin gidan ya nufa.

"Kai kaskantaccen kare, kasan me kake cewa?" Inji Baba Salama. "Ba kalamanshi ba ne sallama, na wancan dan iskan Yaron ne. Ai shi kenan ga ku ga kujeran rikon kwarya daga nan ayi juyin mulki. " Inji Ahmad Rilwanu Abubakar Yayari da ga Rilwanu Yayari. "Kai ka bar nan kaga yara ne anan? Waye ya kira ka? Kada ka sake ce zaka yi rashin d'aa anan." Cikin wani irin fisga ya bar fada yana jin matukar ya hadu da Salmanun Faris sai ya cusa shi lahira ko baya so! Murmushi Alhaji Rilwanu Abubakar Yayari yayi ya ce musu. "Kusan dan yau ne?" Mikewa Galadima yayi Alhaji Kabir Hamud Yayari ya ce. "Ina taya Alhaji Mamman Abba Yayari murna Allah ya taya shi riko!" "A'a Kabiru Kada muyi haka da kai." Murmushi yayi ya ce mishi. "Anyi haka Ubangiji ya tayaka riko!" Take fadawa suka lullube shi ana faɗin. "Gyara kintsi Allah ya taya Sarkin rikon kwarya riko." Mikewa Ajiyar, Turaki, Barde da dan masani suka yi tare da shi kanshi Rilwanu Abubakar Yayari suka bar Fadar ransu a bace. "Kabiru akwai matsala ko?" "Baba sarki babu matsala, an gama kome babu wanda zai iya maka koda haushi ne." Inji Faruq.

Kallonshi Mai Babbar daki tayi kamar ta rufe shi da duka, "Me kake nufi? Akan me yasa zaka bar mulkin ga wasu? Akwai wanda ya dace da rikon kwarya bayan kai ne?" Gutsirar apple yayi ya kalleta da fararen idanunsa. "Allah ya huci zuciyarki!" Ya fada a hankali. Yana cigaba da cin apple din, tasan tun kafin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login