Showing 126001 words to 129000 words out of 304445 words

Chapter 43 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

49

mata. "Aunty Nady kada ki yi kuka muna kwanakin goma na biyu ne mu cigaba da addu'a." Haka nayi ta bata kwarin gwiwa, har muka isa gida wani abun da na fahimta zuciyarta ta karaya ne amma koda muka isa gida ta manta da kome ta cigaba da harkanta, ashe mun bar baya da kura domin mahaifin Ijlal ya zo ya ce zai dauki yarshi a canza mata asibiti tunda kishiyoyinta sun hada kai zasu kashe ta, Mai Babbar daki ta ce a wuce ita gaba da gida. Haka yasa suka nutsu amma ana ta yadawa mun hade kai zamu kashe ta don mun ji tana da ciki, yarinyar nan ta samu me daura mata pampas kashi zata yi, domin kuwa kwananta biyar aka sallame ta, wani abin da ya bani haushi ko ina ta samu zuba mana yawau take, idan muna girki ta ce yana mata wari.


Shi kuma Barde ya wani hakikance haka ne, sai ya fara mana iyaka da abinda ranmu yake so sai dai mu hakura da girki muna zuwa kitchen din waje mu yi, Nady ta ce ba zata iya ba sai gashi kiri-kiri yana gayawa Nady magana. Kallo daya nayi masa na dauke kai ina soya dankalin hausa, wai tazo na zuba mata idan bata ci ba zata iya mutu, ganin ban kulata ba domin abin da iskanci tana fita sai gashi ya dawo gidan. "Saka min na kai mata muguwa mai bakin hali!" "Gara da ka fahimci bakin halina sannan ka gano ni muguwa ce kana tab'a min kasko sai ma watsa ruwan man nan a jikinmu da kai idan kana ganin karya ne Bismillah!" Fada hankali kwance. Fita yayi yana faɗin. "Kina taya Nady kishi ne? Tow ai ba Ijlal ta hana Allah ya bata haihuwa ba!" "Eh saboda kasamu tana da ciki shi Ubangiji ba a mishi iyayi da alfahari ya buge banza ya zube!" Ashe wannan abin ya mishi ciwo ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min. "Dan nawa ne banza Zainab? Cikin sunnah ne banza? Zainab tafi gidanku sai na nime ki!" Dariya ya bani na mishi wani lalacin kallo na ce mishi. "Zan fita amma ka sani idan na fita na fita kenan?" Shiru yayi na kashe gas din na juye abincin na kaiwa Nadiya na sadakar na barwa Sailuba na dawo na fara hada kayana. Shigowa Nady tayi ta ga ina hada kayana. "Zainab lafiya?"
"Ba kome ya bani hutu ne ya ce na je gida zai zo!" Na faɗa mata shiru tayi kafin ta juya ta fita ina gama hada kayana kaf, sai ga Mai babbar daki ana shan ruwa, na fito da akwatin ta shigo zuba min idanu tayi. "Gidan Imam Junaid zaki koma ko fada zaki zo?" Ban san me ya saka ni kuka ba na fashe da wani irin kuka. "Ina yake?" Ta tambaye su a tsawace, kiranshi Nady tayi ina tsaye har jikina yana rawa. "Ummina ce min yayi na je gida sai ya nime ni!" "Akan me?" "Ummi tunda Ijlal ta samu ciki ya saka mu a gaba yanzu bamu isa mu yi girki a nan ba sai dai a waje idan kuma muka yi anan tow kafin mu sauke tayi ta zarya a bata cikin ta zai zube idan bata ci ba, yau kwana biyar da ta dawo ita bata yi girki ba sannan mun yi hakuri idan muka bata abincin karshe sai dai mu gani an fita da shi a shara ya kawo mata daga gidansu. " Inji Nady, murmushi Ummi tayi ta ce mana. "Ashe kuwa da sauranku, idan kuka sake ta yi amfani da cikin jikinta sai tayi waje da ku. Yarinya ce amma a gefe akwai masu tayata yaki." Murmushi tayi ta ce min. "Kira ta." Na tafi na buga mata kofa sai gata ta fito tana faɗin. "Au baki tafi gidan tsohonki ba!" Murmushin gefen baki nayi na ce mata. "Uwar mijina tana sona don haka ki saka idanun zaki sha mamaki." Ina kiranta sai gashi nan ya zo. Yadda ta je shiga ba nan take fita ba Mai Babbar daki tayi mashi tas tana gaya mishi. "Ba kanka aka fara haihuwa ba, kuma ba a kanka za a daina haihuwa ba na ya zaka kora musu yar mutane saboda Matarka tayi ciki?" A hankali ya warware mata abin da ya faru. "Sai me don ta fadi haka Alfahari kuke musu don Allah ya baku haihuwa, ka tab'a zuwa makabarta ga mutanen da suke kwance sun tafi da Yaransu ne? Balle har yaran su rasa wurin zama? Idan ka ce zaka lalata gidanka kai ne zaka yi asara domin kowacce mace da darajarta ka aurota. Haihuwa kuma ba Ijlal ta bawa kanta ba, Allah ya bata sannan bai yi shawara da ku ba, sannan ba rawa tayi Allah ya bata ba. Don haka ku kame kanku. Ke kuma Zainab bana son rashin hankali, taya zaki kira dan gwal banza, kada na kara jin haka sannan kuma tunda kace ta tafi gidansu Ni zan tafi da ita sai ka nime ta." "A'a Ummina ya wuce!" "A'a wallahi ta wuce muje! Itama Nadiya ai jibi zaka wuce Sweden Allah ya tsare." Mai Babbar daki ta saka ni a gaba, Nady tayi tsalle ta ce mata.."nima ba zan zauna ba wallahi!" Ya shiga daki ta kwaso kayanta muka wuce Fada, ba fada ba zagi Mai Babbar daki ta mishi horon da ya dace domin kuwa kiri-kiri ta kwashe mu zuwa bangarenta, tunda muka dawo yake zarya har ana gobe zasu tafi da alamu a can zasu yi sallah, Ran Ijlal ya b'aci kuwa sannan gefe guda mun bar mata gidan zata yi yadda take so.

***
Alhaji Nafi'u........
*Account Details:*
*08130269641"
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500N
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 42
Sai dai dan batalikin nan yaƙi barina, lokaci zuwa lokaci yana kirana a wayar Mai Babbar daki, kusan wuni nayi ina ɗaukar kiranshi. A raina nace mai yasa yake min haka, rike bakina nayi ina jin wani irin tseren da zuciyata take. Wato ba dai abinda ya faru ba ne ya saka shi Obsessed da shi ba, last call din da yayi min abinda ya ce ya wani na rud'e. "Kin san har yanzu na kasa amfani da yatsana tunda na tura shi!" Kashe wayar nayi na boye kaina a cikin matashi.

Hala ba ibada ya tafi yi a kasa mai tsarki ba. Ina jin mai babbar daki tana korafin ya hanata sakat, abin buɗe baki da muka yi, Ijlal zama tayi ta cinye tas da alamu iskancin da take yi samun wuri ne domin duk da son da Mai Babbar daki takewa Sadauki ya haihu ban ga tayi wani dauki akan cikin ba, wuni guda tayi tana saka Sailuba aiki, kuma nasan don kada ta taya ni aiki ne wai ta bani haushi. Da na gama abin buɗe baki nayi tuwo miyar kuka ya ji tantakwashi, yarinyar nan sai gata tana ci har da kari ga cikin ya sakata ci kamar mahaukaciya, sannan sau daya take amai a rana wato da safe. Ana shan ruwa na koma dakina, ina mai sallah da bude baki. Ban wani ci abinci ba Faruq ya kawo min magani, ban san ba ko yayiwa Faruq magana ne akan maganin sai gashi yana ta bani hakuri nace ai ba kome, bayan sallah isha ya kirani ya ce su lokacin su ana niman sha daya ne, ina jinsu da Mai Babbar daki, ta bawa Sailuba ta kawo min wayar. "Ki kuna wayarki ina son magana da ke!" "Anan ma ya isa!" Cikin wata ƙasaitaccen murya ya ce min. "Ki kuna wayarki right now!" Yadda yayi maganar sai na ji na kasa musanta mishi na ce mishi. "Tow na ji!" Na fito da wayar ba kunna yana jin ƙararta ya ce min. "Saura Data!" Yasan ba zan iya musu ba, na ce mishi. "Hmm!" Ina kuna datar sako duka fara shigo min. Katse wayar yayi ya kiran wayar yayi video call. Dauke kai nayi. Ina cika ina batsewa. "Hmm fushi kike ne?" Ya fada da raha, kamar bashi ba. Harara na watsa mishi, na cigaba da kallon gefe. "Ki cire dress din!" Juyowa nayi na kalle shi a nutse. "Ni dai ba zan cire kayanaa ba, domin musulunci bai amince da haka ba, idan kana son ganina haka ka jira ka dawo, amma kunya ya haife ni ba rashin kunya ba."
Na faɗa ina dauke kaina, shiru yayi kafin ya ce min. "Ba zaki yi ba kenan?" D'ago kai nayi na ce mishi. "Gaskiya ba zan yi ba, wallahi ba zan cire kayana ka kalle ni tsirara ta waya ba, idan kaso ka zo ina jiranka!" Na faɗa ina ƙoƙarin kashe wayar ya ce min.."ok na gode." Yadda yayi maganar kamar an mishi dole ya fada yana hade rai. Ban zata zai ji ni ba, na ce kasa kasa . "A sauka lafiya ruwa ya ci biri." "Kika ce?" "Bance kome ba!" Na kunshe dariya ta. Kafin na sake dariyar ina yi, na san fushi yake amma ban san yadda aka yi ya sake kuma yana kallona, ni dai ban san abinda ya gani ba kiran Yeemar ya katse video na ɗauka. "Yan mata ya dai?" "Shegiya an kawo sadakin!" Ihu nayi tare da tashi. "Da gaske?" "Wallahi bayan sallah za a kawo kayan aure, sun ce nayi layya a dakina." "Ra uba Malam yaki zagi. " Muka yi ta murna. Kafin muka yi sallah ashe bawan Allah nan yana online. "Kin gama wayar?" Tura baki nayi ya kura min idanu. "Kin san jiya kin cije ni a bakina?" Ware idanun nayi ina mamaki. "Ni!" Na tambaye shi. "Yes!" "Allah ya baka hakuri." "Baby ba zan yi hakuri ba sai kin nuna min wadancan abin!" "Tab!" Na faɗa ina ina wani juya kaina. " Allah im not joking please ko su kawai!" Shiru nayi naki kula shi, magiya ya shiga min da rarrashi na nuna mishi kirjina. "Kai da kake da mata masu manya manyan nonuwa me zaka yi da nawa kanana, masu girman lemun tsami?"
"Haka na gani na yaba!" Ya fada yana gyara zamanshi da kyau. "Please!" Wato ban tab'a ganin anace irin Faris ba, idan na kawar da zancen zai dawo da shi a cigaba tare da magiya. A hankali na janye wayar muryanshi ya katse ni. "No no, ki cire a gabanta. I miss them so much!" A hankali na balle botirin rigar zuwa tsakiyar kirjina na bar shi. "Please ki janye rigar." Shiru nayi na kasa motsi. "Ina jiranki don Allah!" Ya fada yana kallona. Kamar xan fashe da kuka na dan yi baya da rigar, damke kanshi yayi, yana faɗin. "Masha Allah, Allah na gode maka!" Rufe rigana nayi ina faɗin. "Dama nasan sha'awata kake ji, ni dai ka kyale ni na kashe wayar. " Na faɗa ina jin haushin kaina ga kirjina da yake wani irin punch kamar zai fado, wani muslmin tsoro ya cika min zuciya. "Kada ki kashe min waya don Allah!" Idanunsa ya kafe ni dasu yana faɗin. "Ki bada passport ɗinki, gobe Faruq zai kawo min ke!" "Ni babu inda zanje, yawwa ka ma daina wani batun dauko ni sai kace yar Iska!" "Waye dan iskan tow?" Ya fada a kausashe. Shiru naki magana haka yasa shi kashe wayar yayi zuciya. Nima kwanciya nayi, tare da yin limo kamar ruwa ya cinye ni. Abinda ya faru jiya ya tsaya min a kai, yadda zuciyata take nukurkusani yasa na kasa wani katabus, wani irin fargaba nake ji, Salmanu Faris Matanshi biyu da ni ta uku. Sai na ji babu amfanin accepting soyayyarshi domin shi sha'awata yake ji, yayinda ni kuma nake jin ba zan iya mallaka mishi jikina da rayuwata don bukatar ka shi ba. Ina kwance amma ƙwaƙwalwata tariyo min abinda ya faru yake, lumshe idanu nayi, sai juyi nake ina ƙara ji kamar nayi miss wani abu mai muhimmanci, domin dai barci barawo yayi gaba da ni, ban sani ba ko ya manta da ita ne, amma nasan gulmammen ba zai nime ta. Ina kwance har wurin sha daya na ga ta shigo min daki. "Zan iya amfani da toilet dinki?" Mamaki ta bani, ta wuce ban dakin hala ta ɗauka irin ban ɗakinta ne, tunda ta shiga naji tana wasu abubuwan kamar kuka ko nishi ne, shashekar da take yi ina jin muryanshi yasa ni fita a dakin, idan sun gama sheke ayarsu na koma haka kuwa na cigaba kwanciya a parlourn har wurin karfe daya saura ta fito tana tsantsame kanta, tashi nayi na koma dakin na ga yadda ta gama lalata min gado. Ban ce kome ba na yaye zanin gadon na shimfida wani na kwanta. Ciwon mara ya tashe ni a barci dama nayi ta zuba idanun ganinshi, sai gashi nan ya tawo. Wanka nayi na sha ruwan dumi na duba magani na sha, sannan na kwanta, magana irinta gaskiya ciwon mara na al'ada jarabawa ce babba ga Yaran matan da suke yi irina. Har lokacin sahur ban fito ba, da yake idan na tashi ina dumame, tow yau ban tashi ba, ina ta juyi haka Sailuba ta zo n ace ta yi kome bani da lafiya. Yadda nake amai yasa ta kira mai babbar daki, ganin yadda nake juyi yasa ta nimo Sarkin gida aka tashi sarkn mota aka fita da ni zuwa asibiti, daga ni har Mai Babbar daki kwana zaune muka yi, sai bayan sallah asuba na samu barci, an min allura da karin ruwa. Bata gaya masa ba, koda na farka Maluma da Aunty Shukrah na gani, mun dan tab'a hira har nayi wanka na fito, shima sai wurin karfe biyu na rana ya kira ni, duk ta shiga damuwa yana tambayata ko akwai wani abu ne, Allah sarki abinda ya fada ko saka min hannun da yayi ne, na girgiza kai saboda nauyin maganar.

Matarshi kuwa yana can da su Aneesah ana ta gurmi da yake labarin cikinta ya bazu, sai wani riritata ake yi. Kwana ɗaya na yi na kome, yadda Mai Babbar daki ta zuba min idanun yasa nima nake shan magani a kai a kai. Kullum zai kira mu ya ji jikina har na ware, ranar da na gama nima na shiga binsu sallah tahajjud, ina lura da Ijlal niman faɗa take yi da ni, domin har da gori ban tanka mata ba, domin ba zamanta nake ba, ranar ina jin tana faɗin. "Wasu sai dai su kare a bin malamai da yan tsubu." Cikin murmushi na ce mata.."wasu sun yi cikin amma babu amfaninsa tunda bai ga soyayayr uba ba, cewa aka yi bani da lafiya hmm!" Wanann maganar ya dake ta, don haka ta taso zata yi fada da ni..tana faɗin.."jaka dama na lura tun da hankali da ya dawo kaina da cikin kike hassada, banza wacce bata dauki aurenta da daraja ba!" Wannan maganar ya min ciwo." Domin mai babbar daki tana jin mu, "na gode da na kasance haka wasu kuwa, su da babu ɗaya suke a wurin miji da na kusa da shi. " Ihu tayi ta nufo ni. " Ni dai ban kulata ba aka shiga tsakaninmu Mai Babbar daki ta ce ta shirya a mai da ta gida ba zaman da tashin hankali, kuma abin haushi fadarta ba iya ni ba hatta su Sailuba da Wildat rashin mutunci take musu. Ga saurin hannu babu wanda ya isa magana saboda yan uwansa sun daure mata kugu. Shine Mai Babbar daki ta ce ta je ta gode.. dama tana son ta bar gidan ne domin akwai maganin da zata bani tunda ta zo aka dakatar da gyaran jikin haka yasa mai babbar daki, ta dakatar da Aunty Yanah da yin kome.

Bayan tafiyarta aka cigaba da aikin, kullum zai kira ni bama wani hira, amma a haka nake dan tana barin gidan na sake nake yadda nake so.
*
Saudiya.
Tunda aka bata takardanta, jikinta yayi bala'in sanyi, haka ta isa office ta zauna tare da kiran Number, can sai gashi har yana shirin bata masu lokaci haka ta cewa likitan. "Kayi bayani kawai idan yazo zan mishi." Ta fada cikin wani irin murya, mai ban tausayi. Tunda suka iso yake kaucewa haduwarsu. Koda sun hadu zai mantar da ita akan abin da su zo, tana sauraren abinda likitan ya ce, kusan chemical ne ya toshe mata hanyar shigar kwayar halittar, don haka sai an mata wani aiki kafin wani lokaci ta kara dawowa. Sunkuyar da kai tayi tana kuka cikin karfin hali ta mike tare da cewa ya saka ranar aikin. Sai da suka tsayar da maganar, za ayi aikin nan da kwana uku. Kiran Mahaifin Ikhlas tayi tana kuka tana gaya mishi cikin karyewan murya ta ce mishi. "Baban Zainab ina ganin zan hakura kawai. Don kamar Prince baya son haka. " "A'a duk wanda yake nima yana tare da samu, ki shirya zuwa aikin sauran kome mu barwa Rabbil Ka'aba." Haka tayi kuka ta koshi, da ce sayan ɗa ake tasan da an cika mata gida da Yaran, amma lamarin na Allah ne ba na mutum ne sai da ta fito daga asibitin, sai gashi kamata yayi a ce tayi fushi tana ganinshi ta manta da tarin laifinsa, ta fara dariya hawaye na zuba mata domin ba karamin kaunarshi take ba, lokacin aurensu tace ita bata shirya haihuwa, yau gashi nan ta kai kanta inda Allah bai kaita ba, hawaye ne ya zubo mata ta boye takardan ta yi hikimar sakawa a jaka. Koda an yi aikin dole sai tayi zuwa uku ganin likita. Gyada kai tayi tana kallonshi. "Me yasa kike kuka?" Murmushi tayi ta ce mishi. "Gobe zaka shiga Makka ko?" "Eh ina son zuwa umara ne, kin ga likitan kuwa mai ya ce miki?"
Murmushin gefen baki tayi tana faɗin. "Nima akwai wani aikin da zan yi a jidda, ina ga yau xan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login