Showing 3001 words to 6000 words out of 304445 words
health ko ba kome kin taya ni murna. "Ina ruwana? Iram bana son munafunci!" Na fada ina kallon gefe. Wani irin overtake dinmu aka yi ni kaina ya bugu da kujera Iram da gaban mota. Cikin tsananin masifa na ce. "Malam Babangida sauke ni, wallahi ban isa ba wani dan iska ne zai." Yadda motar ta wani cilla a guje raina yayi azabar b'aci nace mishi. "Ka bi bayansu." "Malam Babangida muje don Allah." Inji Iram ta fada tana danna wayarta. A fusace na ce mata. "Wani irin mu tafi? Taya za a yi mana haka ki ce mu tafi?" "Saboda kullum ba zaki na janyo mana abin fada a gari ba, kina abu kamar ba yar gidan Malamai ba. Mtseew?" Shiru nayi ina jin idanuna na cika da kwalla. "Dama Uban waye ya ce ni yar gidan Malamai ce? Wannan ku ne ya dama ku ta yafa nasabarku, ni rayuwata da duniyata ba nasaba take bukata ba." Na fada mata itama. Dariya tayi tana faɗin, "wannan dabi'ar zai ja miki danasani saurin fushi da rashin kunya, ko ni da nake dangin da suka tsaya min bayan Abba bana jin zan iya abinda kike?" Nima dariya nayi nace mata. "Allah shi yasan karatun kurma." Parking Malam Babangida yayi ya ce mata. "Mun iso!" Nuna mata hanya nayi na ce mata. "Tow Hajiya Iram an iso." Na fada ina kallonta. "Me yasa kike min irin wannan kallon?" Murmushi nayi mata kafin na ce mata. "Idanuna ne, ba taki ba taya ba zan kalle ki ba? Kin ga sai an jima!" Na juya ina dariya, ba yau na saba zolayarta ba, amma na yau ta bani haushi ne sosai. Itama murmushi tayi ta fita tana faɗin. "Ina tausaya miki?" "Muna dai tausayawa juna, kin gane ni ina raye cikin yan uwa da mutane, ba a killace ni ba an bani damar yin abinda nake so musamman wanda bai kaucewa shari'a ba, gaya min meye abin tausayi anan?" Na fada ina kallon idanunta. "Ikhlas ki daina cika baki kada mutanen da kike alfahari da su wata rana su juya miki baya." Juya idanuna nayi na ce mata. "A duniya nan mutane biyu ne zasu juya min baya na ji ciwo, Maluma da Abba, don ke da sauran dangi kun juya min baya a sauka lafiya ruwa yaci biri!" Kamar zata yi kuka ta kalle ni zata yi magana na tare ta. "Kin ga shiga ana kallonki!" Na zuge glass din motar muka yi gaba abinmu. Tun muna Yara mun taso da gayawa juna magana musamman ita,don tafi kowa iya bakar magana da gadaran tsiya, ni kuma mafadaciya ce Allah ya gani har idan nayi wani abu cewa ake ba Maluma ba ce ta haife ni, saboda bata fada bata iya ba, zai matukar wahala ka ga fushi a fuskarta don Allah yayi mata hakuri, amma ni fa har yayuna maza na shanye na dame su, har zuwa yau ba a tab'a kawo karansu ba, musamman Ya Abid da yake zauna lafiya da matarsa. Amma kaf gidanmu ni ce mafadaciya shima Umma cewa take nayi mugun gado ne wurin Hajiya Turai. Kai har kwanan gobe ina jidali domin kaf zuriar babu wanda bai san halina ba, sannan iyayena daga Maluma da Abba basu tab'a nunawa abinda nake kuskure ne ba, domin Abba ta sha fada mana. "Ku fahimci wani abu fadar Ikhlas akan gaskiya take, duk lokacin da za a kawo kararta ana bincike ita ce da gaskiya, bata taɓa fada babu gaskiya ba, sannan duk inda ta zauna babu wanda zai ce bai kaunarta haka take, Uwata akwai faɗa." Sunan Hajiyar Maradi ce da ni, wacce tana can matar nan akwai drama, domin akwai Yayun Abba a Maradi can take zuwa ta ce ta gaji da gidan Abba Turai zata kashe ta da miyar barkono. Ita Hajiya Maradi baka iya mata, duk yadda kayi abu matukar bai mata ba, tow zaka kashe ta ne.
----
Tunda ta fita a motar take tsaye a wurin, wayar Mommy Turai tayi cikin rawan murya ta ce mata. "Mommy yau ma naga wannan motar, saura kiris wancan Yar iskan ta ja muyi magana." daga can ta ce mata. "Tow kukan me zaki min? Tunda kin ga motar kin ga wanda yake ciki ne?" "Ban gani ba." "Shi kenan zan duba lamarin, yau ma kin yi fada da ita ne?" "A'a!" "Ai na gaya miki ki fita hanyar ta, kin ki ko rashin miji da kika yi sanadinta ne, gashi nan lokaci guda Uwais ya juya miki baya yana ta dawainiyya da ita."
"Mommy kiyi wani abu don Allah!" "Me zan yi? Bayan wanda nake yi kina rusa min " kashe wayar tai Iram ta cire a kunnenta, tana kallon ministry din da zata yi.
A hankali take takawa, cikin nutsuwa me fisgan hanklain duk wani mai cikakken lafiya, don ma tana sanye da Jalbab, a hankali ta isa gate din ma'aikatan, shiga tayi cikin girmamawa ta gaida dattawan da suke kofar, sannan ta wuce. Tasan kullum zata wuce sai yi gulmarta. Amma yau sai bata ji sun yi magana ba. Tana shiga cikin ma'aikatan, MD ta fara haduwa dashi. "Good morning sir!" "Morning!" Ya fada ba tare da ya kalleta ba, itama bata wani damu ba ta wuce cikin office din, abokan aikinta na ganinta suka shiga d'aga mata hannu, itama ta musu sannan ta zauna. "Barkan da safiya ya aiki?" "Lafiya lau yau ma kin makara?" Inji daya daga cikin manya a office din. "Aunty Ba laifina ba ne, Ikhlas na tsaya jira!" "Malama kada ki min sharri!" Muryata ta karad'e office din. "Idan zaki gaya musu gaskiya ki gaya musu, ni ban ajiye ki ba, yawwa dazun na ga kamar kin tsaya baki shiga office ba, har Malam Babangida ya kai ni nace ya dawo ni wani abu yana damunki ne?"
Mikewa tayi tare da jan hannun, muka fita daga office din, "Wai ke yaushe zaki yi hankali ne?" Cire hannunta nayi tare da cewa. "Yau da yamma!" Na fada ina kallonta. "Iram kada ki kara min karya, kowa yasan cewa idan gari ya waye kafin kowa yasan gari ya waye na gama shirina, na karya kafin nan." Toshe min baki tayi tana faɗin. "Don Allah ki yi hakuri surutu ga ya mace zubda mutunci ne!" Kwace bakina nayi ina mata wani irin kallo. "Iskanci nayi da mutuncina zai zube? Ko an ce miki ni din simi-simi ce irinki? Malama muna cikin 20 century ba zan tab'a zama irinki ba. Dama na ga yadda kika sauka a dame yasa na dawo amma tunda har lafiya lau kike gyata min karya sai an jima." Na juya abina a rayuwata idan akwai wacce nake so Iram ce, ita damuwarta daya ce matuƙar zata samu mafita tow ba damuwarta ba ne ta laka maka sharri. Koda na fito bakin kofar fita ina kallon wani mutum da yake min wani irin kallo. Har zan wuce sai na ji zuciyata bata yarda da shi ba, na dawo abinka da yar jarida. "Malam kallon na mene ne?" Girgiza kai yayi ya ce min. "Babu kome!"
Sannan na wuce idan na tuna gidanmu babu wata zaman lafiya sai naji kamar akwai abinda ya dace ma sani. Amma kuma sai nake ganin tunda Iram bata gaya min ba babu ruwana.
Lokacin da da na isa wurin aikina Oganmu ne ya zuba min harara cikin masifa ya ce min. "Sai da na gayawa HOD dinku babu abinda zaki iya, amma ya matsa min lamba na dauke ki gashi nan sai yanzu zaki iso." Cikin kunkuni na ce mishi. "Kai dai da katon tumbinka kamar an cika isa, ka fiye takura." "Me kika ce ?" Ya fada a fusace har yana dukar table din gabanshi. "Sir me zance fatan Alkhairi na maka, na ce Allah yasa ka samu promotion har zuwa BBC Hausa!" Na fada ina hade rai. Murmushi yayi ya fara faɗin. "Hmm ai yarinyar nan kina da kyakkyawar zuciya, ke daya ce kike min wannan fatan." A raina na ce mishi. *Da uban sankon kanka zaka BBC Hausa!* A zahiri kuma na sake dariya ina faɗin. "Mutum irinka me amana da adalci ai sai haka!" "Maza wuce ki duba shirin da zaki yi?" "Ok sir;" na wuce, ina fitowa Yeemar ta kalle ni tana dariya. "Yau ma kin hadu da tijarar Yallabai!" "Da katon tumbinsa kamar me cikin wata goma, ai oga yana kuntta min rayuwa wani dagajjaja da shi, ga sanko ga tumbi gashi kamar a rufe da kwandon kayan miya." "Zainab Junaid Gobir!" Wani irin daskarewa nayi ya tako gabana. Yana shafa sankonsa sannan ya daki tumbinsa da alamar kalamaina sun kunttta mishi. " Yallabai!" Na kira sunanshi. Dakatar da ni yayi yana faɗin. "A'a ba sai kin ce kome ba, nasan ni gajere ne, sannan ina da tumbi ga sanko. Amma yaudarata kika yi da kika min fatar aiki da BBC Hausa?" "Haba Yallabai kamata na yaudareka!" "A'a ba sai kin ce kome ba kowa ya koma bakin aikinsa."
A yau program din da muke da su, har da hira da Shahararriyar yar gwagwarmayar nan wato Nadiyyah Jamil Chiroma, sai dai shi ba ni ce zan jagoranta ba. Don karfe biyu zata su fara hiran su gama karfe uku. Haka muka yi aikin har karfe daya na rana sannan na yi sanarwar shirin Yancinmu wanda shine da a yi da Nadiyyah Jamil Chiroma, fita nayi Jonathan ya amshi ragamar tafiyar da na'uran, ban daki na nufa na gyara fuskata sannan na fito, wayata ce take kara, na dan juya na dauki wayar a daidai lokacin da naji muryan oganmu yana faɗin. "Ta iso!" " Ban san tana gabana ba, kawai muka yi wani irin karo da ita, wayar hannuna ya fadi ita kuma tayi wani irin baya kamar zata fadi security suka tare ta. "How dare you zaki bangaje Madam Nadiyyah!" "Sorry ba da gangan ba ne!" Na fada ina d'ago kaina. Kamar ance na ankara naji hannunta kiris a fuskata na kauce. Na sake baki galala kafin na kama dariya. "Bayan nace kiyi hakuri? Sannan ki ce zaki mare ni, tow na ture ki, kiyi abinda zaki yi mtseew!" Na bangaje oganmu na wuce. "Wacece ita? Ku kamo min ita!" "Madam ana kallonki, muje daga baya zamu ji da lamarin!" Cizon lips dinta tayi tana faɗin. "Sai na ga iyakarta!"
Massalaci na wuce abuna nayi sallah, sannan na koma cafteria naci abinci, sannan na wuce office don haushi ko tsayawa su gama program din ban yi ba, na bar radio station din na dawo gida, inda na samu Mommy Turai taba bala'i. "Ya Nuraim meke faruwa?" "Wai akan maganar auren Iram da Abba ya gabatar ne ashe mai martaba za a daurawa auren a turata can Germany." "Mai Martaba Mutumin da yayi jika da ita haba shi kuwa Abba, gaskiya ko ni ce Mommy Turai abinda zan yi kenan kuma fa akan." "Tafi can sakarya!" Shiru nayi na wuce part dinmu. "Wallahi idan na yarda Allah ya tsine min idan ban saka wuta ta kona kowa ba har ni da ita yar mu mutu zaka san dani kake zancen, na baka zabi zaka dawo ka same ni!" "Allah ya kyauta muka ce!" Amma ya kamata Abba ya sani Mommy Turai bata fadar abu ta kasa aiwatar da shi sai dai idan bata yi niyya ba.
***
DAUSAYI
Nan ne gidan gonar Sarki Attahiru Shehu Yayari,shiru kowannensu yayi kafin Malam Junaid ya mika mishi wasu files guda uku, ya nuna mishi daya. "Wannan ita ce asalin yarjejeniyar da muka yi tsawon shekaru talatin da wani abu, wannan kuma shine na kasuwancinmu, wannan kuma shine na mafarin raba kanmu. Amma ni da Mahaifinka mun ajiye wannan shaidar ce na ko karta kwana. Sannan abu na gaba da zan gaya maka batun auren Mai Martaba." D'ago kai yayi kafin kalman Baba Salama ya dawo mishi. "Malam ban gane auren Mai Martaba ba? Ko maganar da mutane ke yi kana yaki akan dukiyar nan ce?" Murmushi Malam Junaid yayi ya ce mishi. "Duk yadda ka ce!" "Mai Martaba da bai da lafiya, sannan a shekarun irin ta shi za a hada shi da mace? Yarinya da ya ribanya shekarunta kamar biyar? Mallam bayan Abba da Baba Saddam waye target dinka?"
Murmushi yayi a karo na biyu ya ce mishi. "Kai ne harina na gaba?" Sai kuma ya sake dariya irinta manya. " Nasan ba za a tab'a kashe ni ba, sai kwanana ya kare amma kuma zan yi ƙoƙarin tayaka tafiyar da baka san inda zata bulle maka ba, ka nutsu da kyau tun kana yaro ka gaya min kana mafarkin kuraye a zagaye da kai suna son kai maka hari. Amma akwai wasu garken zakuna da suka zagaye ka." Dafe kan Salmanu Faris yayi saboda sara mishi da yayi. Wani irin zufa ce take karyo mishi. "Sannu a hankali zaka fahimci kome. Faruq zo ka ɗauke shi!" Da sauri Faruq din ya iso, d'aga mishi hannu yayi ya dunkule hannunsa tare da mikewa ya kalli Malam Junaid. "Yawwa kaga na manta, wannan ita ce file da na kiraka domin ita duk wani abu yana cikin nan ka duba, Allah ya tsare."
Tunda suka bar gidan gonar, wayarshi take kara kamar zata idanunshi a lumshe ya ce. "Faruq dauka!" Dauka yayi yana faɗin. "Ma kina son magana da shi ne?" "Ina yake ?" Ya fada cikin hayagaga. "Yana jinki." "Prince kana ina ne? Kazo ZR station wata Yar iskar kyankyaso ce ta min rashin kunya ni zata bangaje." "Look Nady ki dawo" cikin masifa da Bala'i. "Taya zan dawo bayan anci mutuncina? Don ni bare ce a garinku? Dama abinda ake ta nuna min kenan?" "Faruq muje!" Ya sani ba zata tab'a barin wurin ba matuƙar ba a nimo yarinyar an mata kashedi ba. Tafiyar minti goma ya kai su, bude mishi kofar Faruq yayi ya samu masu tayata da wasu abubuwan suna waje, office din MD din ya nufa. Duk inda ya shige gaishe shi ake. A hankali ya tura kofar tana zaune ta harde kafa. Kuka ta saka mishi cikin rigima irin nata. "A kore ta a wannan gidan rediyon din, sannan a kuntatta mata." Ta fada tana kallon shi. Durkusawa yayi a gabanta ya ce mata. "Kin gamsu ayi haka?" "Idan aka mata haka tazo har office dina ta bani hakuri." "Ok MD Wacece ita?" "Zainab Junaid Gobir Khlash!" D'ago kai yayi yana kallon MD. "Aiki take ko me?" "Tana sanin makaman aiki ne." Idanunsa cikin na Matarshi. "Ka dakatar da ita sannan ta rubuta sakon ban hakuri ta kawo har office dinta!" "Tow Sir!" "Haka ya miki?" " A kore ta har a jami'a." Ta fada tana share kwalla da yake zubo mata. "Nady akwai line din da bamu isa tsallakewa ba, Babanta shine shugaban jami'ar da take karatu, Please a bar maganar a nan." Da wani irin takaici ta mike suka dawo gida, amma tabbas ya yarfata a sonta ayi ta ta ƙare, amma haka zata yi hakuri tunda ya ce ta hakura.
***
Nightmare
Sake glass cup din hannunta tayi jikinta yana wani irin rawa. Abin da kowa yake mata gudu ya faru ita yau Faris zai kalli idanunta ya ce an mishi mata saura sati biyu aure? Wani irin juyi kanta yake ta nime wuri ta zauna tare da dafe kanta. "Please Nady i don't mean to hurt you, nima auren nan Abba...." "I laugh aure on my foot!" Ya fada muryanta na rawa. "Why Dr? Why aure now? Dama kayi haka ne domin ka ci zarafina? Kasan yadda nake sonka? Kai ka min alƙawarin ba zaka tab'a kallon wata Y'a mace ba, why you broke your promise? Dama ka hadu da Banzayen zuriaraka da suka yi abondan dinka ne don ka yi aure?" "Nadiyyah ya ishe ka haka aure na fada babu fashi....." "Idan ina raye babu macen da zata hada kafada dani, kuma sai na kashe ta kowaye Ubanta." D'aga hannunshi yayi kamar zai mare ta farko daga munnunar mafarkin da take, zuciyarta tana wani irin gubawa. Kallonshi tayi yana barci, kasa hakuri tayi tana me tashinsa. "Prince tashi nayi mafarkin wai zaka kara aure da gaske ne? Please tashi!" Bude idanun yayi yana kallon yadda gigice duk da sanyin Ac amma zufa take kamar ta hadiye kunama. "Kwanta babu maganar aure ni naki ne har abada?" "Ya maganar yarinyar da ta min rashin kunya tow? Zuba mata idanun yayi kafin ya ce mata. "Amma tun jiya muka gama wannan maganar ko?" "But!" "Nady dare yayi fa barci nake ji." Ya koma ya kwanta.
***
Cikin Gida.
Dare mahutan bawa, amma a wannan lokacin masu shiri da shirinsu. Masu nima da shirinsu suke nima. Wasu mutane ne guda uku suka fita daga cikin gidan gaban wata mota suka nufa, kasancewar wurin akwai duhu me tsananin gaske. Wata mace ce ta fito ta kofar gabasa aka bude mata motar. "Saura kwana nawa Gwaska dakare ya fito?" Tayi maganar cikin wata irin murya wanda ya nuna alamar ta saka abu a bakinta. A cikin motar aka ce mata. "Tsakanin watanni ciki da haihuwarsa!" Inji mutumin ya faɗa. "Ina ga madadin ayi haihuwar guzuma da Junaid me zai hana shima a rufe mahaifarsa." Ta fada tana murmushi. "Na ci suna mikiya ne ba wai don ban san yadda zan yi ba amma abu me muhimmanci shine a sakawa gafiya hayaki domin ya fito daga rami....
Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book.
*Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu ƙayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:*
*MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya haɗa da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.*
*AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen ɗin Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen*
*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
*POSTING*
*Ɗaya: 500*
*Biyu: 1000*
*Uku: 1500*
*DOCUMENT (da zaran