Showing 171001 words to 174000 words out of 304445 words

Chapter 58 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

82

gwana ce, mtseew" ta ja min tsaki ta bar wurin, tun daga lokacin tsakanina da Nady ya zama babu shiri, zaman sai ya koma babu dadi sannan nima da na gayawa Yeemar shiru tayi kafin ta ce min na fita harkan kowa na kama kaina.
A cikin yan kwanakin Arfa ya kama, dama ban samu yin tun farko ba, saura kwana biyu rak na fara azumin, ina kwance da kur'ani nayi wasa da kwanakin don da na sauke kur'ani, shigowa yayi ya tsaya a bakin kofar yana kallona. Dauke kai nayi na cigaba da karatun, ganin haka ya shigo da sallama ya zauna shiru ne ya maye gurbin wurin bakiɗaya, can da ya gaji kuma yasan sarai ba zan mishi magana ba ya ce min, "An kawo saniya daya da raguna uku, na kune, kayan cikin kawai zaku ware min." "Hm!" Nace mishi na cigaba da karatu. Fita yayi na tashi zaune duk sai na ji babu dad'i, bayan fitar shi can kamar an wurgo Nady, har ta manta da kashedin da tayi na kowa ya zauna inda yake ta shigo tana min magana. "Zainab ya kike? Ya ibada," "lau!" Na faɗa a takaice, ina cigaba da karatu, can ta ce min. "Dama akan layyar ce baki ce kome ba." Ajiye littafin nayi na zauna tare da haɗe rai na ce mata. "A kaina kike da zan gaya miki abinda ya da ce? Zamana kike yi da zan tsara miki abinda ya da ce dake? Ke kika ce kowa ya tsaya inda yake and now me kike bukata? Don Allah fita min a parlour bana son tashin hankali." Tashi tayi zata fita har ta kai bakin kofar ta ce min. "Ranar naji haushi ne amma ba wai ina nufin haka ba ne." "Don Allah fita!!" Na nuna mata hanya ina mai juyawa ga karatuna, duk da ban ji dadin haka ba. Amma na nuna mata nima mutum ce akan namiji ɗaya gaya min magana na kyale ta ai ta ci banza.

Washi gari arfa, mijijn ya koma hannunta, haka tayi ta rawan kafa da na jiki, ni a tunanina ma Ijlal zata mata hauka sai naga ashe ni ce dai Ijlal bata kaunar na hada shimfid'a da Mijinta domin bata yi haukar da tayi ranar ba,, washi gari da aka tashi da ruwan sama kuma ranar sallah idi babba, don haka ban yi kome ba ina cikin shiri ya leko ya ce min. "Ki shirya zamu tafi tare!" "Hmm!" Na ce mishi, na gama cikin doguwar riga ta lace bubu,na fito sanye da farin hijab kasance lace din lemon green ne, takalmina da pose din duk farare ne, haka na fito na nufi hanyar waje, sakamakon buga gidan da ake, ina zuwa naga Sailuba ce da Wildat. "Barka da safiya, Uwar sakonni." "Barka dai ku shigo!" Na bude musu kofar kayan snack ne a manya-manyan bokatai har guda shida. An kawo su a mota ne, ajiye min nawa suka fara tare da cewa. "Inji Mai Babbar daki wai kawo muku, tasan bakiɗaya lafiya ba zaki samu damar yi ba." Murmushi nayi na amsa sannan na wuce ciki da shi. "Ina sauran matan gidan an kawo musu suma!" Suka fita waje,ina kai nawa kitchen na rufe sannan na fito na duba shi ko zai yiwa matansa magana sai gasu nan dama suna ji iskanci ne, komawa Parlourn nayi na zauna ina jiran naji me zasu ce, suma aka basu nasu ina ganin Ijlal take yatsuna fuska har lokacin fuskartar bata sauka ba, na cewa Sailuba. "Zo ki amshi sakona!" Ta bi ni, na juya na cewa Wildat. "Tawo nema!" Haka ta biyo ni, muka shiga cikin daya dakina na fita zuwa dakina na ciro dubu-uku uku na basu tare da cewa. "Ku mika min sakon godiyata ga Mai babbar daki!" "Na gode sosai!" "Yawwa tace a gaya miki idan aiki ya miki sauki ko zaki shigo ki san yadda zaki mata da namar?"
"Kada ta damu zan shigo!" Na rako su muka fito sai kallon fuskana Ijlal take ni dai ban bi ta kanta ba, mijinsu ya saka mu a gaba shi da faruq a gaba mu kuma a baya Nadiya ce a tsakiyarmu, har muka isa masallaci, muka zauna aka yi huduba sannan ka a yi sallah, sai da muka yi addu'a. Kafin muka taso zuwa gidan. A hanya yana zaune a gaban na ce mishi. "Sadauki!!" Juyowa yayi ya kalle ni Dan aro nutsuwa nayi na ce mishi. "Ko zaka taimaka min a ajiye ni a cikin gida anan nan yi aikin sallah na!" Shiru yayi kafin ya ce min. "Mai babbar daki ta gaya min amma na gaya mata tayi hakuri, ki yi aikin sallah nan za a kawo aikinta sai ki mata gobe kuma ki yi naki!" Yadda yayi maganar ya sani fahimtar ya gama magana kenan, gobe zan amshi ragamar shi, shine baya son na cinye kwanakin a hanya yawon aikin sallah, "mtseew yar shishigi!" "Su tunkiya an shiga abinda ba ayi da ita ba!" Ina fadar haka, ta juyo zata min rashin kunya na ce mata. "Kika yarda kika zage ni sai naci ubanki!" Na faɗa kai tsaye, "ba dai Ubana ba!" "Sai na wa?" "Oho!" "Na zata nawa zaki ce!" "Idan aka ce naki ne uban me zaki yi?" "Me zan yi? Sai na kunna miki wayata ki ji labarin yadda aka kwana a ragaya, tunda Ubana bai tab'a matse yar kowa yaci ya goga mata goga masu ba." Na faɗa daidai Faruq yana niman hanyar fita a cunkoso. "Wallahi baku yi shiru ba sai kun fita min a mota;" kauda kaina nayi ta ce min. "Idan bai bi mata ba ya kashe abokansa saboda abin duniya!" "Shi yasa yake yawo ko ina kuma yake abinda ya so, Uban wata kuwa ko aure ya je nima ba za a bashi ba, ragowar yan ga ruwa, yar ma kwakule Yaran Mutane" da yake bata da kunya dauka nayi zata share kawai ta yo kaina zata dake ni, yarinyar da na girmeta, ai kuwa na cire takalmina tana mikewa na kwad'a mata a goshinta sai ga jini ya wanke Nady, ita kan ta kasa magana, sai bin mu take da idanun. "Jini fasa min kai kika yi?" Tsabar gudun da Faruq yake bamu san ya iso gida ba, ashe Uba taresa ne ya ce ya sauke mu, haka muka fita tana ihu, shima ya fito ya tsaya a kofar get din ya ce min. "Ba gidana ba sai dai ku je can ki karata!" Wani irin malalacin kallo na yi mishi, sannan na ce mishi. "Ba zan bar kofar gidanka ba sai ka sallame ni, wallahi ka ji ba zan mia da iyayena kananun mutane ba." Zuba min idanu yayi yana mai dunkule hannunsa. Ita kan jin yace kowacce ta kama gabanta tayi shiru tare da rike inda jinin yake zuba, ni kuwa ko danasani ban yi ba. Zuba min idanun yayi ya ma rasa abin cewa kawai ya ce min. "Ki tafi gida nace," "idan na tafi wallahi baka isa ka dawo da ni ba, kuma babu me dawo da ni don haka bani hanya idan ka shirya korata sai ka bani damar tafiya bakiɗaya" Ni kaina na san ban kyauta ba, amma ba yadda na iya ne, don haka na shige cikin gidan, shi kuma ya fusata sosai don haka ya shigo tare da cewa. "Fita min a gida, idan kin gadama kada ki dawo!" D'ago kai nayi ka kalle shi, kafin na ce mishi." Ba zan fita ba, sai ka sallame ni!" Yau na gane cewa duk dadinki da kishi sai ta nuna halinta, ranar da Yake dukar Ijlal ni ce na hana shi, haka amma ni yau ina ganin Nady ta karkad'e jikinta, tayi gaba. Sai naji hankalina ya tashi sannan na kara hango wautata da nake zakewa, ban san ya aka yi ba, sai ga kiran Mai Babbar daki. Yana ɗauka ta ce mishi. "Kul naji ko na gani kada ka sake ka kore ta gida baka da hankali ne? Tayi min daidai da ta gaya maka ba zata bar gidan ba sai da shaida idan an gama hidimar sallah ina nimanku har da matanka!" Cire wayar yayi yana faɗin. "Wallahi zaki san baki kunya." Ya wuce ni yana min tsaki. "Wannan kuma ba matsalarka ce, na kara gaya maka har kwanan gobe bana sonka, bana kaunarka har duniya ta tashi ba zan so ka ba." Cak ya tsaya ba tare da ya cigaba da tafiya ba. Na juya nima na cigaba da cewa. "Ko jini na hada da kai sai na zubar balle kuma bana fatan haka ya haɗa ni da kai, daga lokacin da ka fara saka ni a gaba ni kuma sai na tabbatar maka da na zame maka tunani!" Daga haka na wuce shi yana tsaye, yana jin ya rabu da kalmar bana sonka amma ashe yana nan a ranta, me yasa ta bashi damar wasu abubuwan da ita? Yaudara ce ko me?

Haka aka yi yanka aka ce kowa ya zo ya dauki nashi, ni kuwa naki fita na bar musu kayansu a nan, ina jin hayaniyar Ijlal da Nady, amma ban fita ba. Ina kwance a parlourna. "Assalamu alaikum!" D'ago kai nayi ina mamakin waye haka? Maluma! Da wani irin ihu na nufe ta, ai kuwa ta kifa min mari sai da na zube, bina tayi ta riko kunnena ta kai ni uwar dakina ta rufe ni da duka bayan ta rufe kofar, sosai Maluma tayi min shegen duka, ta fito tana huci. A parlourn suka hadu ta tsaya tana sauke numfashi. "Kada ka kara kiran Abbanku ka gaya mishi, ya zo ya rarrashe ta ka same ni ta wayar Abid zan zo na ci mutuncinta, idan bata fita ta dauko kason ta ba ka raba sadaka!" Ta fita tana fada. Shima da yake munafiki ne sai gashi ya shigo dakin ganin yadda na cusa kaina cikin cinyoyina ina kuka, yasa shi cewa. "Ki je ki dauki kasonki!" D'ago kai nayi ina kallonshi kafin naji wani irin hawaye mai zafi ya zubo min. "Ka haɗa ka bawa Nadiya da Ijlal, ni kuma ka fita bana son ganinka!" Ya zata wasa ne haka ya rasa yadda zai yi da namar, ni kuma na rantse ba zan dauka ba, kuma ya tabbatar haka, sosai na dauki zuciya kuma ban ji a raina na dauka ba, shima da yake dan kanshi ne sai ya rabawa mutane namar, Allah almusweeru sai ga sako daga wurin mai babbar daki, rabin gudan saniya.

Fadar da yake tayiwa Faruq ya sani kasa kunne naji yana fadar, "duk abinda yake faruwa kai kake gayawa Mai Babbar daki duk yadda na yarda da kai sai ka ci amanata!" Yadda yake fadar na gano cewa shi ya gayawa Mai Babbar daki abinda yake faruwa. Tunda ta kawo min namar ma baza shi a kitchen dina na fara kwashe kayan cikin na fito fanfon waje, na fara wanke namar Nady ta kwaso yan aiki. Ni kuwa ni daya sai Ijlal da itama ta kwaso yan aiki, ana ta habaici Allah yasa basu san me ya faru da ni ba, domin sai wurin karfe shida na fara aikin. Na gama wanke kayan cikin saboda akwai kasa, sannan na koma cikin gidan na daura akan gas na rufe abuna. Shigowa yayi ya ga ina ta yankar albasa. Ya shiga zagaye kitchen din amma bai kai ga zuwa inda nake ba ya fita aka kira sallah Magariba na fita nayi, duk da ban dawo ba sai bayan an kusan sallah isha, ina dawowa na samu ya bude firji yana niman abinci, ban ce mishi uffan ba.
Na zuba kayan kamshi a cikin tafashe, domin na bude ne ya tafi da warin kayan cikin, sannan na dauki hanji na saka a pressure pot na tafasa shima na zubar da ruwan na juye a cikin sauran kayan cikin, yana zaune na saka kayan Maggi na rufe da su albasa. Shi namar layya baya bukatar iyyai dayawa, sai ban saka wani abu ba kayan kamshi da nayi amfani da shi tafarnuwa ce da albasa sai tyme, bayan nan maggi star da Ajina-motor kawai na saka sai gishiri. Daga nan na zauna na fara cire namar ina yankawa ina zubawa a cikin wata ƙatuwar tukunya ina gamawa na cire kaɗan na daura a pressure pot, na zuba kayan kamshi na rufe ina son yin shinkafa da miya ne, kayan miya na ciro a firji na fara gyarawa sannan na markade shi, kafin na shiga aikin abincin daren, duk da dare yayi sai na dauki kayan lambu na gyara na gyara.

Sannan na wanke shinkafar da na tashi dafawa na zuba mishi carrots green beans, da kuma masaran gwangwani. Mutumin nan yana zaune ina aiki yadda bai min magana ba, nima ban san yana wurin ba,ina jin alamar namar yayi na sauke na cigaba da miyana yana dauko nuna na zuba namar na cigaba da aikina na saka kayan dandano, ba sai kitchen din ya ɗauka ba.
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 57
Hankalina yana kan girkina ya tafi masallaci har na gama abincin, na wanke kayan da na b'ata tas sannan na juye abincin bakiɗaya na kwashe tare da kaiwa dakina na saka tare da rufe dakin har kitchen na dawo abuna, ko da ya dawo daga massalaci ya samu na gama babu alamar ma nayi girki. Girman kai irin na saraki yana damunshi yayi min magana yaki yayi nima kuma ina cike da shi ba zan tab'a shiga harkanshi ba.
Har na gama tafasa kayan cikin, na kashe gas din na gyara namar da aka kawo min na cire na soya sannan na cire na dambu, sauran kuma na kulla a leda na saka a firji, sauran kuma na barsu tare da bude windows na kitchen ɗin, na barsu. Har xan fita sai wata zuciya tace min kwashe kayanki, ki zuba a firji haka kuwa aka yi na zuba a firji, na shige cikin dakina bayan na rufe kofar Parlourna na bar key, sai gashi abin duniya ya dame shi, haka na kwana da takaici abincin da nayi na ci, tunawa da nayi da faruq na fito zuwa kitchen n adauki kular da nake zuba mishi na zuba na fita yana waje tare da oganshi, na dan leko nace mishi. "Yayana ko zaka taso ka amsa." Ba musu ya karba yana ta min godiya tare da min sai da safe. Haka na koma abina shima faruq ina bashi ya bar kofar gidan yasin ya gudu ya barshi.

Ina zaune a parlourn da yake ban rufe kofar ba, ya shigo ya samu ina chat da Yeemar, ban gaya mata kome ba amma nayi ta mita ina masifar babu gaira babu dalili, sai hakuri take ba ni karshe muka bige da hira. Kamar an ce na d'ago kai ina kallonshi rike da plat na abinci, ban san yadda aka yi zuciya ta kwashe ni kamar xan ce mishi idan ya ci ban yafe ba sai ka kyale shi, na barshi da Allah domin dai nasan ni aka zalunta. Ina zaune a wurin ya fita can sai ga Nady ta shigo tana kalle-kalle, ganin ban kulata ba sai ta ce min. "Amma Ikhlas ina ganin girmanki da hankalinki, shine zaki bawa Babe abinci bayan na mishi abincin? Idan aka miki haka zaki ji dadi? Gaskiya kina shiga al'amarina bayan ni ina ƙoƙarin kama kaina akan akamarinki." Kasa magana nayi ina kallonta. Na kasa magana sai da ta gama maganarta na ce mata. "Shi ya ce miki na bashi abinci? Hmmm Allah zai saka min kuma zai bi min hakkiina domin kuwa ban tab'a shiga hakkin kowa ba." "Kin shiga mana tunda ranar girkin Ijlal ta fada kanku, idan ba haka ba akan me zaki na shiga harkan namiji bayan ba girkinki ba ne, sai idan anyi magana ki na nuna kanki like ba a miki adalci ba!" Kaina a sunkuye saboda mugun ciwo nake ji a raina na ce mata.."Na shiga hakkinki kiyi duk abinda zaki yi?" Na faɗa mata tayi duk abinda zata yi. "Idan ban miki ba ai ke yar gwal ce, shafafiya da mai wacce take da goyan bayan Uwar miji, a tab'a ki ta tsaya kamar ita ta haife ki, ba zan yi kome ba balle har ki kai ga sakawa ya dake ni. Tunda ka lura lamarinki ya wuce hankali!" "Kin ga Nadiyyah Jamil Chiroma bani na kira ki ba, don Allah fita min a dakina tsaki tayi ta fita a dakin, wannan abin ya matuƙar min ciwo. Duk abinda suke yi yana jinta kuma yana jin mu bakiɗaya. Tana fita ya bi ta har daki tana mita ya ja kujeran kitchen dinta ya zauna yana cin abincin ya ce mata. "Tsakaninki da Allah na ce miki ita ta kira ni ta bani abinci?" Juyawa tayi a fusace kamar zata mare shi, amma ganin yadda fuskarshi take a haɗe ta ce mishi. "Amma maganar gaskiya ba a kyauta min ba!" . murmushi yayi ya ce mata. "Ina abincin da kika bani?" Sai tayi shiru tana kame-kame kamar tayi karya ya cigaba da cewa. "Ina ta jiran tun safe babu abin karyawa ita ma da tayi bata ce min zo ka ci ba, shiga ɗakinta nayi na diba saboda batan son magana kawai ta dauke a kitchen amma sai da kika bita da magana Nady? Ina murnan zaman lafiya ya samu a gidana shine kika bullo da tashin hankali, nasan dazun da zainab ce ta ga muna rigima da wata cikinku sai ta san yadda ta saka na daina amma ke har rabawa kika yi ta gefenmu kada ki shiga kema, kin bani kunya kin bani mamaki yau kike gaya mata magana har kina cewa mai babbar daki tana sonta Yes tana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login