Showing 135001 words to 138000 words out of 304445 words
Lalee!!! Lalee!!! Lalee wata tayi ja, rana tayi baki, dare yayi haske. Wata tayi ja wata yi ja jini ya zuba, mayaka sun fito , kuraye suna kuwa, kuraye suna kuwa. Jini ya zuba jini ya zuba sarki shago ya dawo? Barza ya dawo kowa zai mutu mai nasara zai rayu! Sarauniyar zata mutu da jaririn cikinta, lalee lalee lalee, lalee barbuza lalee kundara, lale janaka,lale jinryar. Sarkin Zanzabira bargaga ya dawo bargaga ya dawo!" Ta kama rawa da kanta a gaban Faruq da ya shigo da kaya a hannunsa. Dafa shi tayi. "Ka zabi mutuwa! Anya bargaga baka yi kuskure ba? Lallai zaku lallai zaku mutu!" Ta cigaba da rawanta.
Har ta saka kafa zata fita. " A daren sha hudu ga wata" ta juya da karfi. "Alqawarin Allah zai cika tarihi zai maimaita kansa." Ta juya tana kallon Mai Babbar daki sannan ta sake wata mahaukaciyar dariya ta ce a ranar kowa yana ji kowa zai shaida mai tabbatuwa zata tabbata kamar kiftawa da Bismillah, kimanin mintuna kafin zanzabira ta samu sabon ango ruwa mai albarka zai shiga cikin mahaifar Awatif zai tabbata!" Daga haka ta kama rawa tana girgiza. "Kina yaki domin ya amshi matsayinsa, ai dama wurin na shine jininsa ce, amma cin amanar gadaddiya ce tun kafin Yayari cin amanar haifaffiya ce tun kafin jinin Fulani da barebari, tabbas cin amanar ba sabon abu ba ne amma mutuwa ita ce sabuwa a cikinmu. Kin manta kome kin manta tarihi, kin barta yayi wankan zinari irin Awatif kin barta ta komawa baya irin Awatif, lallai Aojana tana cikin tafiyar bari mu ga zaki iya dakatar da rundunar shaidanu tsakiyar birnin ni ne. An binne kin tona kun tona sai kun girbi laifinku, daga ina za a fara mutuwa? Su waye zasu sadaukar? Amma mulkin......
*Account Details:*
*08130269641"
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500₦
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 44
Dariya ta saka tana tafiya tana rawa, har ta bar kofar mai babbar daki zuwa tsakar gidan. Buga sandarta tayi ta ce. "Lallai kuna sha'awar mulki, kuma zaku mutu." Ta fita tana dariya zasu mutu, daki Ummi ta wuce da ni, har zuwa lokacin jikina rawa yake. "Ummi!" Kamar tasan tambayar da zan mata ta bani amsar cikin gaggawa. "Mahaukaciya ce, Adade!" Gyada kai nayi ina jin kaina kamar zai fita. Cire min kwalliyar tayi da sauri kome da ya danganci Gwal sai da ta cire min, sannan ta rike hannuna tana faɗin. "Mahaukaciya ce, please kada haka ya dame ki. Yeemar ko?" Ta gyada mata kai. "Kula min da ita kafin na zo!" Ta kwashi gwal din ta fita da shi, har ta isa waje ta ce mata. "Ki sakata ta cire kayanta za a zo amsa!" A hankali na cire kayan bayan fitar ta na saka wani kayan ina kallon Yeemar. "Matar tana ta wasu irin magana." Shiru Yeemar tayi kafin ta ce min. "Idan muka yana da gaskiya fa?" Da sauri na kalle ta. "Me yasa kika ce haka?" Girgiza kai tayi ta ce min. "Lokacin muna secondry school an tab'a bamu labarin asalin Kingdom din zanzabira, before zuwan Musulunci over 300yrs anyi mulkin kama karya na zalinci, sannan anyi wani irin cin amana da kashe duk wani sarki a cikin gidan sarautar. Amma shima malamin yace ba a tabbatar ba domin ana zargin it was rumors!" Ajiyar zuciya na sauke na ce mata. "I'm glad da ya tsaya a rumors!" Na zauna ina a gaban madubi, yau da bai ta kirana ba, sai na dinga jin ba dad'i. Har zuwa la'asar muka yi ado muka sake fita kofar Fada, na sha kwalliya cikin atamfar Sharaton, mai tsarin ja da baki. Sai lafayyar da na saka shi baki me ratsin ja, yayi min kyau ga Yeemar ta min wani heavy makeup, a harabar gidan muka yi ta hotuna masu kyau, Abdullahi da Sulaiman sun zo fita suka dauke ni, sannan muka yi da mai babbar daki lokacin ta fito zata itama ta ga hawan kafin na gobe, haka yasa muka sha hoto da ita kaca-kaca, bayan fitarta Ilham da Ijlal suka fito, tsayawa tayi ta ga yadda muke hoton kusan iPhone da fitar da hoto, ga kwalliyar kamar wata aljana na koma. Haka yasa ta kasa hakuri ta kama wakar habaici, suna dariya bamu kula su ba. Bata bar wurin ba sai ga kiranshi ina gani na kashe na ki dauka. Shine ya kirata daidai zasu bar wurin ta dauka cikin son cusa min bakin ciki. "Papan Baby!" "Bata!" Ya daka mata tsawa, mika min wayar naki karba don na nuna mata ko a gidan giya akwai babba ina ganin shine na saka handfree. "Zainab! Zainab Zainab Junaid Gobir!" "Na'am!" Na amsa mishi. "Wallahi idan baki wanke makeup din nan ba sai na sab'a miki, na rantse ki wanke fuskanki." A shagwab'e na ce mishi. "Allah da gaske na cire kalliyar fa na kashe kudin yi? Gaskiya oo sai dai idan zaka biya ni. Daaadah!" Shiru yayi na zata ma ya sauka ne sai ce min. "Wallahi idan baki goge ba kuma ki cewa Abdullahi da Sulaiman su sauke hotinanki kin san Allah gobe zan shigo sai zuciyarki ta lalace na rantse da Allah ki goge n a gaya miki. Me yasa bakya jin magana ne?" "Gaskiya ni ba!" Rike ni Yeemar tayi tana faɗin.."Allah ya huci zuciyarka, Ubangiji ya dafa maka dan sarki jikin sarki. An gaida Hakimin Fara ƙasa, Matawallen Zanzabira Sadaukin Zainab Junaid Gobir. Ta amshi sakonka kuma zata goge muje a goge fuskar." Ta ja ni muka yi gaba ta bar Ijlal da Ilham a tsaye. "Sakarya gogewa zaki yi, ke baki iya cewa tow bane, sai kishiya ta zamu abinda zata yi against ɗinki. Kai ke dai baki da hali." Ta fada tana mika min kayan cire makeup din sai da na wanke tas sannan ta sake murmushi ta ce min. "Ko ke fa!" Zama tai a gabana ta ce min. "Kishiyarki Yarinya ce, amma tana da support din wasu daga cikin gidan, ke kuma uwar Mijinki tana tare da ke, me ya dace don rike Mijinki! Biyayya hakuri kissa. Tun dazun da nazo ina ganin kishiyarki a gaban mai babbar daki kamar zata shige cikinta, ke kuma lokaci zuwa lokaci tana sakawa a duba ki, Zainab yau da gobe yana saka mu fahimci su waye a gefenmu amma ke da yake rascal ce baki da hankali kin zauna kina hauka." Murmushi tayi tana faɗin. "Idan ni ce da wannan Yarinyar sai kullum na saka ta kuka, domin ita kanta Mai Babbar daki tana regret din hada auren, hmm bari na gaya miki ki yi biyayya ki kwace Mijinki domin aurenki da Salmanun Faris ba zai tab'a mutuwa ba, don na ji labarin asalin auren a cikin ku takwas da aka hada auren kece Allah ya tabbatar da naki, kin ga kenan babu saki babu yaji. Uwar miji tana sonki sai ki gyara zama ki.taya shi samo solution da zai gina kanshi da rayuwarsa. Ta hanyar kwantar da mishi da hankali, Ikhlas shi fa Salmanu Faris bai da mace domin ke kanki baki san yadda zaki sauke hakkin da yake kanki ba, Mijinki mace yake bukata kuma jaruma mai hakuri da koya kare kanta, na ji a labarin masarautar nan duk wata mace da ta samu damar zama Mai Babbar matsayi tow sai ta iya kare kanta da Yaranta kin zata haka kawai take zaune tana kallon Yaranta. Ya kamata ki tayata yaki the next king in sha Allah Mijinki ne, idan wancan zabuwar ta haihu ki taya shi kaunar abin da za a haifa ta haka ne zaki kara samun shiga jikinshi, babban aiki ne a gabanki domin dai dole ki koyi hakuri da zama da mahaukatan gidanki." Duk yadda zan fahimta Yeemar ta gaya min shi yasa nake sonta, domin ko zan mutu sai ta gaya min gaskiya. Kaf duniya bani da madadinta sai Ihsan.
Cire kwalliyar nayi na gyara fuskana, ina zaune ya kira ina dauka ko sallama bai amsa ba ya ce min. "Kin cire kwalliyar?" "Eh!" "In sha Allah next week zamu dawo, kin san ayi mata aiki ne!" "Allah ya bata lafiya!" "Amin Ya Allah!" Ya amsa daga nan ya shiga tambayana me na dafa me na ci, murmushi nayi ina kara nutsewa cikin matashin. Murmushi Yeemar tayi tana faɗin. "A soye a hankali kada a kone!" Hararanta nayi na ce mishi. "Papan Baby ka ji Yeemar ko, tana tsokanata." "Ki ce ta daina ko na saka Sarkin kofa ya fitar da ita daga gidan!" Murmushi nayi muka cigaba da hira kafin Yeemar ta mike. "Bari na raka!" "Amma ban da waje!" "Yawwa ni yaushe xan je gida ne? Kuma idan na je kwana zan yi!" "Hauka kenan, sai na dawo zaki za mu je tare!" "Kawai ka ce ba zan je ba sai an jima da yake matanka kana sonso su ni kuma dole aka maka shi yasa kowacce ka bata damar yadda suke so ni kuma na zauna a gida kamar Mayya Allah yana ganin abinda kake min." Na faɗa ina shirin kuka. "Na gaya miki maganata idan bakya ji sai ki je!" Daga haka ya kashe wayar, "ke dai ba zaki tab'a yin abinda zai ji dadi ba sai kun rabu dutse hannun riga!" Haka na rakata wurin mai babbar daki, ta mata abin arziki, sanan na rakata waje, ina tsaye sai ga Khalifa Nafi'u Shaibah tare da Ahmad Rilwani Yayari, Allah ya so Hijab ce da ni har kasa, inda muke suka nufo ta shiga motar suka tsaya a bayana kamar zasu hada ni da motar. Kallonsu nayi a hankali na ja da baya. Faruq ya iso inda nake rike da wata irin sanda da nake yawan ganinshi da ita kullum. Yana suna ganin shi. Suka kalle shi a wulakance. "Wild dog ba da kai muke ba, Bingo!" "Ikhlas!" Khalifa ya kira sunana. "Iram ta bani labarinki shine nake son ganinki, a kebance!" Wani irin duka Faruq ya kai mishi, sai da ya zube a kasa. Dukar da yayi mishi a gadon baya yasa shi suma. Yeemar sannan ya taso ni gaba har cikin parlourn Mai Babbar daki. Ya fita ya kai Yeemar, ba sai gashi an tare shi ba. Da yake yana da bindiga a jikinsa, jin harbin yasa suka watse ya iso gidan kafin wani lokaci gari ya dauka an daki Khalifa, Ni dai tunda na shigo Mai Babbar daki take waya koda ta fito ban gaya mata ba sai da Abdullahi ya shigo yake tambayata na bashi labarin, shiru aka yi a parlour kafin ya kira Yayanshi ya gaya mishi abinda ya faru. Hmm tashin hankali wanda ba saka mishi rana, dole ya kira mahaifiyar Nady ya gaya mata halin da Nady take ciki ya ce mata zai isa zanzabira cikin awa sha biyu.
A daren ta nime Visa yayinda shi kuma ya bar Riyard, ya tawo Zanzabira. Wannan abinda Khalifa yayi cin zarafi ne ina matar aure shi da Ahmad zasu tsaya a bayana kamar zasu hada jikinsu da ni, haka yasa Mai babbar daki daukar zafi kafin ya iso ta saka an kama Ahmad Rilwani Yayari an rufe shi. Ubansa yazo har kofarta ya zazzaga mata rashin mutunci, bata kula shi ba. Da sassafe aka tafi dauko daga airport ya iso gidan ya samu Alhaji Mamman Abba yayari da Alhaji Kabir Hammud Yayari da Alhaji Nuru Yayari, ana ta bawa mai babbar daki hakuri da sallama ya shigo ya gaishe su a hankali. Ya zauna yana kallon Mai Babbar daki. "Ni ba ni aka yiwa laifi ba, ga Mijinta kuma danku bayan nan bana jin akwai wani matsalar da ta haɗa ni, amma Rilwanu ya zo har kofar dakina ya min rashin kunya shine ba zan kyale ba." "Bai kyauta ba, tabbas yayi kuskure a yafe musu." Mikewa yayi ya shige dakin ina zaune daga bakin kofar ya tsaya muka zuwa juna idanu. Ban san me yasa naji tsoro ya kama ni ba. "Kin ga dalilin da yasa na ce ki cire Makeup din? Ina tsoron wani abu, amma sai da kika d'ago ni daga inda nake ashe ba zaki taya ni kare kanki ba." "Mene ne banbancinsu da kai? Abinda suke bi shi kake bi ban ga wani abun tashin.." tass ya wanke min fuska da mari. Ya hada ni da bango. "Any single words dinki, jin shi nake kamar narkakken ruwan Dalma yafi miki sauki, ki ja bakinki ki rufe ko kuma yau na miki rashin mutunci wallahi." Ya sake ni ya fita. "Salamanu Farisa!" Cak ya tsaya yana mai kallon dattawan parlourn. "Ka yi hakuri a yi magana!" Murmushi yayi sannan ya ce musu. "Ya wuce!" Ya saka ya fita daga parlourn. Da Faruq suka fita cikin tsananin masifa da fushi wanda ya game da zafin kishi ya ce. "Me yasa baka kashe shi ba? Me yasa baka kashe yan iska ba?" Ya fita waje daga nesa ya hangi Ahmad da shi ɗan iskan da aka cika gari aka ce ya suma, dama a buge yake. Bai tab'a jin bakin ciki irin na yau ba, ji yake kamar ya mutu, saura kiris su hada jikinsu da Matarshi, shi ya san yadda yake ji, don haka ina tashi wani irin katako ya ciro a inda ake aiki ya nufi Ahmad da zasu shiga cikin fada ya rufe su da wani jahilin duka idanunsa ya rufe kamar baya ji baya gani, zai iya kashe kowa akan Zainab Ikhlas ba tare da yayi danasanin haka ba, har cikin Fadar ya isa gaban Uban Ahmad da Alhaji Nafi'u da suka zo akan dukar da Faruq yayiwa Khalifa. Ihun da suke tare da gudun ceton ransu yasa kowa ya fito. Nuna musu sanda yayi cikin fusata. "Wannan ban yi muku kome ba, wallahi bana zuwa biyu idan na yi na biyu tow sai uwarka ta haifi wani!" Ya fada yana wurga da katakon. "Kai mara kunya!" Alhaji Nafi'u ya kira shi. A wani irin fusace ya juya wanda yasa shi razana yadda ya juya din. Hadiye yawun bakin shi yayi, Salmanu Faris ya juya tare da barin fadar. Yana shiga ya riko hannuna muka bar gidan gidan bakiɗaya sai yau na tabbatar da kishinsa. Cikin kasa da awa koma sha biyu ya shigo zanzabira. Yadda nake kuka anan ban ga laifinsa ba, domin kuwa yayi abinda ya dace amma a wurin azzalumai abin ya musu bazata. Sun yi haka ne don su ga yadda zai ɗauki lamarin, bayan mun dawo labarin dukar da yayi musu, anan labari yayi ta fitowa ai ranar sallah irin abinda suka yi ta yiwa Mutane. Ina zaune a Main parlour Ijlal ta shigo gidan tana kuka. Fitowa yayi daga dakinsa, ta zata wani abin arziki zata samu idan ta gaya mishi abinda aka mata, ashe ni mari, yadda yake cike da kishin nan, ta fara ratabo mishi bayani wato mari biyu ya mata masu kyau da lafiya wanda ya sakata zaman yan bori. Cikin bakin ciki da kishi mara iyaka ya ce mata. "Ki je na sake ki saki ɗaya!" Kai ba ita ba hatta ni, sai da naji cikina yayi wani irin juyawa da gudu na wuce Part dina. Ashe rashin kunyar da nake na bogi ce domin ga inda ake aiki da zuciya. Kambu ina jin ta fita tana ihu, abinda ya faru a wurin kallon hawan ranar sallah abinda ya faru ba dad'i domin su da Yaransu yan iska suke zuwa bayan mace idan ta juya su cire wando suna gogawa mace gabansu tana juyawa domin masifa zasu nuna mata wuka. Haka zasu gama tsiyarsu suna dariya, itama tana tare da Ilham suka musu haka, shine da yake mahaukaciya ce ta ji labarin sun tsaya a bayana shine ya dauki mataki, da yake mahaukaci ce ta fara bashi labarin bata san yadda ya kwashe min rabin fuska da mari ba, idan ni na sha mari don sun kusan haɗe jikinmu wuri guda ita kuma fa? Da suka goga mata abin, tsoron fitowa yasa na makale a dakin ba ruwana Mr Faris ya haukace kishi ya haukata shi, don haka na bala'in kama kaina.
Hmm Ashe rigima ake tsakanin Abba da su Alhaji Nafi'u, basu taba ganin fushinsa ba sai wannan karon haka yasa aka yi ta case wasu daga cikin malamai suka goyawa Alhaji Nafi'u baya, karshe ana cikin wannan rikicin aka kama Abba,, su a tunaninsu kama Abba shi ne mafita kuma zasu sami damar shiga gwamanti, abin ba haka ba ne domin ana kama Abba wasu daga cikin mukararaban Alhaji Nafi'u suka shigar da Abba kara akan yana tadda zaune tsaye, abubuwa dayawa aka zargi Abba da shi, wannan lokacin mutane dayawa sun koma bayan Alhaji Nafi'u da Rilwanu, haka yasa muka shiga tashin hankali da damuwa fa. Ranar da aka shiga kotu, karamin hauka ne ban yi ba, kuma a ranar Nady zata dawo, rufe ni a daki yayi bayan ya min allurar barci......
*Account Details:*
*08130269641"
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
My book isn't Free! 500₦
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 45
Wani sabon bakin ciki ya kusan min ya tafi ya bar ni, Faruq ya dauko Nady sai wurin karfe uku na yamma na farka, yana zaune yana aiki kallo daya yayi min ya dauke kanshi, kitchen na shiga na dafa shayi sannan na fito na wuce daki, bai san shirin da nake mishi ba. Haka yasa ina gamawa yana zaune har aka kira sallah la'asar ya saka kai zai fita ya shigo ya same ni zaune ya kurawa wuri guda idanu. Girgiza kai yayi ya fita, ina ganin al'amar ya fita nima na dauko key motatta, na kwashe kayana kala biyu na bar mishi gidan ina cikin gidanshi tashin hankalin halin a iyayena suke ciki ba zai bar ni na zauna ba. Haka na fito na shiga motar na bar gidan. Koda na zo fita daga masarautar bakiɗaya aka hanani fita, kifa kaina nayi a