Showing 51001 words to 54000 words out of 304445 words
ne domin mutane sun fito suna cewa basu so.
A wannan lokacin Alhaji Mamman da Malam Junaid suka kira shi a gidan Alhaji Mamman, sannan suka fitar da mishi last wish na mahaifinsa,kanshi a sunkuye bai ce kome ba. "Bamu san yadda zamu gaya maka ba ne, amma wannan shine fatar shi na karshe idan ma basu maka ba ka zab'a a wani wurin."
Girgiza kai yayi yana faɗin. "Ko karuwa ya ce na zauna da ita zan zauna da ita balle yar da ta fito daga cikin gidan Malam Junaid!" Ya fada a hankali, sannan ya mike zai fita. "Idan ka samu lokaci ka zo ka gansu!" "In sha Allah!" Sannan ya fita, "Alhamdulillahi mun gama namu, saura naka!" Inji Malam Junaid.
"Shi kenan!" Alhaji Mamman ya bashi amsa.
Kwana biyu a tsakanin Alhaji Mamman ya isa gaban mai babbar daki, ya gaya mata wasiyyar mai Martaba wnada Mai Bauchi ya tabbatar da haka shi da Fulani karama Hajiya Zainab.
"Amma wanann Munafunci ne, taya zai gaya muku bai gaya min ba d'a daya da nake ganin shi ne min kawai zaku hada shi da irin masifa da Bala'i, ban amince ba wallahi ban yarda ba."
Yadda Mai Babbar daki ta ke masifa zaka ɗauka ita za ayiwa kishiya, amma haka Alhaji Mamman ya kyaleta sannan ya turawa Alhaji Munir Yarimar gabas babban wanta ta gaya masa, halin da ake ciki ai kuwa yazo yayi mata tas, shine ta hakura amma fa ta saka a ranta sai ta taya Nady kishi.
Yadda zaka san Faris babu hidimar kowa bisa kansa, a cikin wannan yanayin ya gayawa Nady zai yi aure, kamar mahaukaciya haka tayi ta hauka, har wurin Mai Babbar daki tazo tana kuka akan ta hana shi aure, amma babu hali bakiɗaya auren saura kwana sha uku, sannan a gefe guda an rufe maganar auren yadda babu wanda zai ji sai na jikinsu. Mai Babbar daki ta gayawa Yaranta suka yi tsalle suka ce nasu ji ba, indai Yar Malam Junaid ce ba gidan ba. Suka bata labarin abinda ya faru lokacin rasuwar nan fa Mai Babbar daki ta kara hawa sama ta zauna, a yadda abin ya ƙara tsamari, suma sauran yan dakin suka mara musu baya. Gogan kuwa ko a jikinsa.
Ranar wata asabar ya je ya ga Ikhlas wacece tun daga nesa ya gano itace yar bala'i original babu sirki. "Sir ita ce tayi rubutun nan, sannan ita ce abokiyar fadar Madam Nadiyyah!" "Sunanta?" "Zainab Ikhlas!" Shiru yayi kafin ya ce. "Sa'arsu Ilham ce?" "Eh Sir!" Inji Faruq, "she too young! Muje!" "Baka same ta ba?" "Nop!" Ya furta yana jingina da kujeran yadda ake janta suna rigima da mai A daidaita sahu. "Haka take?"
"Gaskiya an ce bata da kunya?"
"Matakin karatunta?"
"Tana karatunta a fannin jarida, sannan ta haɗa haddan Alqur'ani tun tana sha hudu, sannan yar jidali ce bata da hakuri."
"Fiance fa?"
"Uwais Saddam Jatau suke soyayya!"
"Bayan nan fa?" Ya kuma tambyar shi,
"Babu!"
"Ok!" Ya furta tare da rufe idanunsa.
Tun bayan da aka yi maganar auren nan, kusan kullum sai Nady ta tashi hankalinta ko kwana uku da suka wuce tayi yaji, Babanta ya dawo da ita domin Alhaji Mamman ya je ya same shi suka fahimci juna, haka yasa ya dawo da ita da kanshi, Mai Babbar daki ma tazo tayi ta rarrashinta tana gaya mata tunda bata son kishiyar in sha Allah ita sai tayi sanadin barin yarinyar gidan, shi kuwa Gogan kuwa ko a jikinsa,.hatta kayan auren a gidan Alhaji Mamman aka hada.
Ana saura kwana biyar bikin aka kawo kayan.
Ikhlas
Abba ya sake tuntubar Mommy Turai wance bata zaman gidan da maganar auren tace ita ba ta son hadin bai mata ba, haka yasa ta share zancen domin kuwa burinta akan dan gidan shugaban kasa, haka yasa Abba ya sa na zo, tunda muka shiga keke Napep din na lura me Napep din dan iska ne,.yana kawo mu da Aunty Shukrah ya ce. "Gaskiya da nasan nan zan kawo ku sai kun bani dubu daya."
"Dari bakwai muka yi, kuma shi zan baka." Na faɗa ina mika mishi dari bakwai amma da yake dan jaraba yaki amsa, ni kuwa na wurga mishi, shine ya fito zai mare ni, ni kuwa na bude mishi idanun da cewa sai na saka an rufe shi a garin. Yan unguwarmu suka kashe rigimar na shige cikin gidan da Aunty Shukrah, tana shiga take bawa Nuraim labari, yayi ta dariya.
Bayan sallah la'asar Abba ya tara mu, yayi min nasiha sannan ya ce min, saura kwanaki aurena. Dariya abun ya bani domin ban yi kama da amarya ba, sai da ya fito min a mutum na yi shiru kafin na ce mishi. "Abba kasan!".rufe min baki Umma tayi, hawaye ne ya zubo min ya ce min.."Na sani kiyi hakuri!" Cikin shashekar kuka na ce mishi. "Allah ya bani ikon maka biyayya!"
"Bani zaki yiwa biyayya ba, shi zaki yiwa domin yarda Allah yana tare da yardan miji!" Gyada kai nayi na cigaba da kuka, a lokacin da na turawa Uwais sakon bai turo min amsa ba, haka na kasancewa cikin tashin hankali da damuwa.
Ranar da aka kawo kayan, Mommy Turai tana gida amma ko a jikinta, bata ma fito ba, domin lisafinta ba akan auren yake ba, ana.saura kwana uku aka tafi yin jere Matar gidan ta hana a shiga sai da Abba ya kira mijin, ai ina jin ance ina da kishiya kuma a fada zan yi auren na fashe da kuka ba ma karamin mutum bane wato babba dai ko dai Matawallen ne? Haka suka yi jere amma sun ga hauka da tashin hankali, kafin suka dawo gida ance wani mutum da wasu dogarai suka hana matar gidan haukata kome.
Aunty Shukrah da Sajidah suka shirya kamu, wanda aka turo dogarai daga fada, sannan babu dangin ango, washi gari kuma aka yi mother's night, danginmu ne na Zanzabira da na Maradi, sai kuma abokan arziki, ban yi tsammanin bikina zai zo a ƙurarran lokaci kuma ayi hidima haka ba.
Ranar asabar za a daura auren, amma har yau ban san waye Mijin da zan aura ba, wannan yasa nayi ta kuka har da zazzaɓi.
Washegari.
Tun daren jiya basu rintsa ba, domin haukar Nady, don haka ana sallah asuba, ya haɗa shirginsa ya wuce asalin gidan gonar Mai Martaba, ya je can ya kwanta ya huta. Abdullahi da Adam suna tare sai Faruq.
*ina mata yan gayu ina mata yan yayi! Tow ku matso nesa ta zo kusa collaboration Tangaza_Perfume tare da Anum∆Luxury Perfume sun zo muku da kayan kamshi gida da na jiki kai ba iya nan ba hatta turaren kaya irinsu.*
Mamoul all colors are back in stock. Mamoul turaren turara kaya. Ga kamshi ga kama kaya da gida. Available in;
MAMAOUL MADINA,
MAMAOUL MARYAM,
MAMOUL BADAR &
MAMAOUL SABAYA. Each one 3500
*New Drop!*
*Nassem Oil – 100ml*
Rich, elegant & long-lasting.
This premium fragrance oil is everything your collection needs — and it’s only *₦8,000!*
*Luxury in a bottle.*
| Own Your Scent, Own the Room*
*Mosuf 50ml Body Spray*
Smooth. Fresh. Long-lasting.
Only *₦5000!*
✨💥
Smell amazing, every single day.
*DM to order!*
*Storm for Him & Her – ₦4,500* each
Fresh, fierce, and made to turn heads.
Whether it’s *Storm for Him* or *Storm for Her*, you’re getting bold confidence in a bottle — just *₦4,500!*
A perfect 50ml to carry your essence wherever you go. Subtle. Powerful. Unforgettable.
Now available: ₦2,300 per piece | ₦27,600 per dozen.
Available Just DM
08130269641
Top_notch season 4 ROYAL POLITICS is not free, pay N500 to get a complete access to the book.
*Marubutan TopNotch Writers sun sake zuwa muku da sabon labarai masu ƙayatarwa a tafiyarsu ta Season Four:*
*MAI_DAMBU kuwa ta faso muku ne da labarin da ya haɗa da Sarauta, Siyasa da kuma Soyayya, duka a littafin ROYAL POLITICS: An yanka ta tashi.*
*AZIZAT kuma ta tattaro muku rikitacciyar soyayya ne da ya hawo jirgin JayKay ya dira a Kitchen ɗin Ziyada. CHEF ZEEY: Love in the Kitchen*
*Account Details:*
*5921536136*
*RAMLAT MANGA ABDULRAHMAN*
*Moniepoint MFB*
*POSTING*
*Ɗaya: 500*
*Biyu: 1000*
*Uku: 1500*
*DOCUMENT (da zaran an gama posting zai koma)*
*Ɗaya: 1k*
*Biyu: 2k*
*Uku: 3k*
domin tura shaidar biya ko Ƙarin bayani, ku tuntuɓi:
*08130269641*
Ko
*08137311900*
Ko kuma
*09063467258*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: Page 18
ZANZABIRA PALACE.
CENTRAL Mosque
Dandazon alumma ne kofar babban masallacin juma'a da yake kofar Fada wato kofar Fada, duk yadda inda ka kutsu al'umma ce ta ko ina. Mawaka, maroka, yan asharale, mawakan wasu kabilun jahar, bakin masallacin ya rikice da hidima ga matasa yan boko maza tare da wasu tawagar likitocin Nigeria da suka iso a wata doguwar mota, gefe can tawagar ango ne da ya kasance cikin shigar alfarma dogo a tsaye sambal. Sanye cikin alkyabba wacce aka yi aikinta da zare golden. Ga rawanin da aka mishi wanda aka nad'a mishi masu biyu. Idanunsu yana cikin bakar prada wacce ta boye asalin kwayar idanunsa..wanda suke jajjir kamar garwashi. Babban burinsa ya bar wurin nan domin bai ga wani fa'idar haka ba, babban tashin hankalinsa Nadiyyah.
Furza da isar bakinshi yayi cike da matukar gajiya. Yau dai yasan Allah kaɗai zai bashi sa'a a kanta. Daga cikin masallacin kuwa muryan daurin auren ne ya daki dodon kunnuwanshi.
"An daura Auren Salmanun Faris Shi Yayari tare da Zainab Junaid Gobir, akan sadaki Naira dubu dari biyu da hamsin. Allah ya bada zaman lafiya." A hankali aka fara fita a masallacin musamman manya mutane na fadar Zanzabira tare da wasu manya yan kasuwa malamai da wasu jami'an gwamnati daga Federal. "Sadauki!" Kallon wanda ya kira shi sadauki yayi. "Ko zamu karasa ka gaisa da mutane ne?" Lashe bakinsa yayi kafin ya taune lips dinsa a hankali. Yana me d'ago kwayar idanunsa very gentle, ya daura akan wanda ya mishi magana! "Hmm!" Tawagar likitocin abokansa ne sanye da fararen kaya suka rufa mishi. "Waye zai yi tsammanin Dr Faris zai ajiye mata biyu?" Inji wani daga cikin likitocin. "Wallahi kuwa Alawan! Gayen nan dan iska ne yadda yake ji da kanshi ban tab'a zata zai ajiye wata mace bayan Nadiyyah ba!" Ta cikin glass ya kalli wanda yayi maganar ya cigaba da tafiyarshi. Har cikin mutanen da suke kofar Fada, abokanshi sai zoyalarshi suke suna faɗin. "An dai ci amanar kaunar kuma muna team Uwargidan!" Murmushi yayi cikin girmamawa domin yasan yau akwai bidiri. Nadiyyah! Ya jinjina kanshi mahaukaciyar matarshi. Mika hannu yayi yana gaisawa da mutane masu hoto suka shiga daukarsa da mutanen da yake gaisawa. Murmushin yake amma idan da zaka fahimci yadda yake murmushin kasan dole ce. Kusan minti talatin kafin aka kawo wata benz wanda zai kasu su gidan Amaryan a gaida iyayenta.
Shi sai yanzu ya tuna rabonshi da yarinyar, tun da aka ce ya je ya ganta sau daya ya ganta shima daga can nesa ya ganta. Da shi da tawagarsa suka nufi unguwar Malamai.
----
Gidan Malam Junaid Gobir.
Hidimar biki ake wanda duk wnada ya ga yadda ake hidimar bikin zaka ɗauka irin bikin nan ne da ake yi na masoya. Amma kuma ba haka bane domin kawai ana yi ne yadda mai gidan ya umarta. Ana tsaka da kwashe abinci. Wani matashi ya shigo da gudu. "Jama'a an daura auren Ikhlas da Salmanu Faris! Ba Mai Martaba da yake can Germany ba." "Kai Nuraim ka fadi gaskiya ko ka yi shiru!" "Wallahi na rantse da Allah! Da wani ne Salmanun Faris ne?" Inji Mahaifiyarshi Hajiya Asma'u. "Waye Salmanun Faris?" "Ke kin san waye? Dan mai Martaba ne da ya b'ata shekaru ashirin da suka wuce!" "Wanda aka sace shi yana aji hudu na secondry school?"
Shigowa Abid yayi babban yayan gidan, ya ce. "Don Allah ku nutsu ga Prince Faris zai shigo da tawagarshi!" Ya fada yana me nufar cikin part din Mahaifinsu yana me gyarawa, sannan ya fito ya nufi Part din mahaifiyarsu wacce ita ce Uwargidan, sanye take da wani code lace, wanda aka mata buba tayi kyau matukar kyau, domin kyakkyawar buzuwa ce da take ji da kyau da nasibi. "Malama a gyara parlour don Allah kada ayi shirme ina Khlas? A shiryata ga su nan sun tawo." "Tow Abid!" "Ina Shkurah?" "Suna dakinsu Ikhlas da masu kwalliya!" Juyawa yayi da zafin nama, ya fita ya nufi Part din Yan matan ya shiga, ya samu ana ta mata makeup. "Don Allah ku gama akan lokaci! Auta kin yi kyau! Matar mai rabo kenan!" Ya juya ya fita, d'ago kai nayi na kalli Aunty Shukra idanuna cike da kwalla. "Kada ki yi kuka, Allah yana sane dake biyayyar da kika yi Allah ba zai kunyata ki ba!" Gyada kai nayi ina jin kamar na mike nima na ce ba zan yi auren ba, amma ba haka Malama ta koya mana ba, shigowa Nu'ayma tayi tana me faɗin. "Ikhlas! Wai da gaske ne ba mai martaba ba ne?" Cikin In-in-ina na ce mata. "A...unty ban...ban....sani ba!" Yadda nayi maganar muryata tana rawa yasa ta Kylae ni. "Ko ma waye da alamu Allah ya wanke ya baki domin ba tsoho bane!" Da sauri na d'ago kai ina kallonta. "Please ku bar maganar mu karasa makeup din!" Inji me kwalliyar,
Gud'ar da aka yi tare da busar algaita da kid'ad'an da ake yasa ni jin kamar da zuciyata ake luguden, rike hannun Aunty Shukrah nayi, daurin dan kwallin da mai makeup tayi min haɗe da saka min net din da da yake makale a dankwalin wanda aka mishi dauri kamar hula. Bayan ta gama aka saka min wata ƙatuwar gold wanda ya dauka har kan cikina saboda girmanshi ban da na hannuna da kunnena da zobenshi. Gyara min net din tayi tare da fesa min turare. Sannan suka koma suna jiran a ce a fito da ni.
--- Tunda ya shigo gidan daya daga cikin matan Sheik Junaid Gobir suka fito a fusace. Idanunta ya sauka kan kyakkyawar fuskarshi wanda ya cire mayafin da ya rufe mishi bakinsa. Cikin girmamawa ake gaishe shi, har ya isa parlour Sheikh Junaid, ya zauna a kasa. "Salmanun Faris! Allah ya maka albarka! Ubangiji ya baka lafiya da nisan kwana yadda zaka kamanta adalci, ga kanwarka nan ka saka idanun akanta, kayi hakuri rike mata biyu sai namiji jajjurtacce wanda ya san yadda rayuwa take, ai ko ban gaya maka mecece rayuwa ba kasan mecece rayuwa! Ni dai iya abinda xan faɗa kenan, na gode sosai. Ku shiga cikin gidan!" A hankali ya mike Abid yana gefenshi, "na gode sosai Abba!" Ya furta a hankali yana me barin dakin, ajiyar zuciya Sheikh Junaid yayi yana jin kamar ya samu nutsuwa domin, yaci karfin guguwar da yake gabanshi.
A lokacin da suka fito nufar part din Malama suka yi, suka gaishe ta. Addu'a tayi musu me yawan gaske sannan suka fito itama godiya yayi mata, a tsakar gidan nan ne kasancewar gidan babba ne mai yalwataccen fili, aka fito da ni sanye da farin lace me hade da gold, Aunty Shukrah ta kawo ni har wurin Ya Abid shi kuma ya isa da ni gaban Prince Faris kaina a sunkuye. "Dr za ayi hoto ne!" A hankali ya saka hannunshi akan kuguna ya janyo ni jikinshi, yana me kallon camera man din, aka shiga daukarmu, ni ba haka ba ma hannunshi da naji a kuguna wallahi ya hana ni nutsuwa, bakiɗaya ji nake kamar an daura min wani gungunmemmen dutse a wurin, yadda na jingina da jikinshi ba karamin haifar min da tashin hankali yayi ba, nayi alƙawarin wannan auren ba zai wuce inda na zata ba, iya nan za a yi ta kare ina da buri ina da wanda na gina rayuwata dominshi. Hawaye ne ya shiga cika min idanu, abin da na fahimta shi wannan son kanshi ya sani. Tab'a shi aka yi ya juya mika mishi wayar aka yi. Ya janye hannunshi, a hankali na sauke wani boyayen ajiyar zuciya, wnada yasa ni jin wani irin nutsuwa, da wutsiyar idanun ya kalle ni wanda nima na d'ago kai kenan muka yi ido hudu da da shi, da sauri na janye nawa ina kokarin barin wurin. Rigar jikina ya rike wnada ya hanani barin wurin, hade rai yayi ya saka wayar a kunne. "On my way!" Wannan sune abinda ya fada, sannan ya sake rigana ya kuma gaisawa da mutane, sannan suka bar gidan.
Suna fita Mommy wato Hajiya Turai ta fito daga part dinta cikin bala'i. "Junaid fito munafuki algungumi? Junaid fito burbushi kasar wuta. Wallahi ba zan tab'a yarda ba, ina raye zaka ci amanata? Bayan rufa maka asiri da muka yi shine zaka ci amanata? Kace Mai Martaba ne yake niman Auren Iram kai ba zaka iya hana shi ba, wato da nace ba zata sabu ba shine ka haɗa min shunku, ka dauki Yarka da kafi so ka bawa dan Mai Martaba, ashe kulle ni kayi wallahi ba zan yarda ba." Iram wacce ta fito tana kuka ta ce mata. "Mommy kin tuna wanda na gaya miki lokaci ya taimake mu da kudina ya zube a Dubai, wallahi Mommy shine mommy shine wallahi!" Ta fashe da wani irin kuka. "Tow yanzu Turai me kike so ayi?" Inji Kanwar Abba Goggo A'i. "A saka ya sake ta, a daura auren da Iram!" "Hauka kike yi amma!" Inji Umminmu matar Abba ta biyu Mahaifiyar Nuraim da Nu'aymah, "tabbas na yarda hauka kike tuburan, nan kika fito kika yi ta ihu sati biyu da suka wuce yau kuma ki ce an kashe auren da aka daura yau a bawa yarki? Lallai na yarda wasu mutanen mahaukata ne original me yasa baki gayawa mijin ba. Hmm idan kana iskanci baka san inda zaka yi shi ba."
"Wallahi billahi azim sai an kashe auren nan, idan ba haka ba zaayi biyu babu." Ta fada tana ihu. Ita kanta Iram din kuka take tana faɗin. "Mommy idan na rasa shi mutuwa zan yi." Cikin kuka, ni da dama can ban son tashin hankali gidanmu jikina rawa ya kama kamar an saka min lantarki." Ke relax babu abinda zasu, ai bata zata haka