Showing 159001 words to 162000 words out of 304445 words

Chapter 54 - Royal Politics Book 1 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

58

Ta fada tana kuka, "burinki zai cika tarihi ba zai manta da ke ba, zaki addabi duk wata soyayya kada a barta ta kasance tsinuwa ce ga duk wani basaraken, na ci alwashin ganin bayansu." Fashewa da kuka tayi tana faɗin. "Shi kenan nayi rakiyar soyayya kenan? Ki taimaka min kada na tashi a banza!" "Zan cika miki burinki, amma jininki da na Yaranki zan bawa wancan rauhaniyar ce itama zata ayi aiki ne, sannan itama zata bada rayuwar yarta ce domin ta kasance a tare da ita." Wata munnunar aljana ce tsaye a wurin, don haka a cikin daren aka yi wannan aikin kafin gari ya waye an gama, wurin hantsi Aojanah ta mutu haka Yaranta mata, an wayi gari kowacce ta mutu a gidan aurenta domin tsiransu kwana ɗaya ne.

Har yau ba san inda aka binne wannan masifaffiya tsinuwar ba, amma tana cikin Masarautar a binne wanda haka yasa babu halin sarki ya so mace, tun daga lokacin maguzawa har zuwa lokacin jahadin Shehu Usmanu danfodiyo, wannan ya saka ba a san inda yake ba, kuma sarakuna da suka gano matansu suna mutuwa saboda soyayyarsu, suma kuma sarakunan ana kashe su haka kawai, sai suka yakince matan da suke so, hatta da idan ka haifa dole ka janye idanunka akanshi domin kar a farmake shi.

*Wannan shine tarihin Zanzabira da yadda sarakunan suka fuskanci munnunar karshe don babu wani sarki tun daga lokacin maguzawa zuwa Fulani da barebari da basu fuskanci mutuwa ba! Kuma cikin tsananin kaunar matansu da jinya mai matukar naci! Sannan suma sarakuna sunan auren mata masu irin dabi'ar Aojanah don haka sannu a hankali al'amarin yana komawa tankar ita ce take raye saboda gurbataccen zuciyarta suma suna zama haka!duk Sarkin da aka kashe da saka hannun jininsa da Matarsa! Wani abu da har yanzu yake ƙara ƙarfin kauna a cikin Masarautar da sarakunan Zanzabira da matayen da suke so, shine Idan taurarinsu yazo daya! Sannan Sarki Shago da Awatif Lu'lu'a taurarinsu daya ne shi na shi Rana ita wata haka yasa ƙaddarasu take haɗe ko da ɗaya zai mutu tow ba makawa daya ma sai ya mutu domin tarihin yazo ba iya sarki Shago akwai Sarki Attahiru na farko shima ya rasu tare da matarsa yar aikin Rano Hawwa'u Jiddah*

Present
Hawaye ne yake zuba daga idanun Mai Babbar daki, tana kallon duk abinda ya faru kamar a mafarki,Malam Junaid ne ya fado mata yadda ta sakawa ranta cewa shi ya kashe Mijinta! Yadda take ji kamar ta kashe shi saboda kiyayya da gaba da kuma cusawa ranta damuwa.......
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 52

Kuka yayi sosai domin yau ba karamin kewar Attahiru Shehu Yayari tayi ba, ya sha ce mata. "Kina jin haushina ni da Inna ko? Ba haka ba ne, mun yi kirkiro wata hanya ce da ni ko bana raye zaki tsaya akan Yaranki, dukkanku nasan kowacce na san wacce ake haɗa baki da ita ana cutatta ba zan fada ba lokaci zai yi da zata bayyana kanta, nasan lots abinda kike tunani a kaina." Ya riko hannunta. "Ko bu jima ko bu dade wani lokaci zai zo da kowa zai samu yanci amma amma yanzu bamu da yanci ko da kuwa kaɗan ne! " Kuka ne ya zo mata tana yi tana karawa. Sai da ta gaji sannan ta mike zuwa ban daki ta wanke idanunta zuwa yanzu ta ji sauƙin da take bukata yana zuwa mata, sai kuma action da zata dauka. Akan makomar Salmanu Faris da Zainab bata fatan abinda ya faru daruruwan shekaru ya faru da Yaronta.

Hospital
Dauke kai nayi ina jin haushinsa yasan zai zo nan yana rawa jiki yayi ta kular da ni a gida, ina cewa gaba yake da ni. Mika min cup din tea yayi da farfesun kaza da Maluma ta kawo ita fa Maluma lamarinta sai an mata bayani dalla-dalla domin a yadda take daukata ciki ne da ni, haka yasa bakiɗaya take wani kaf-kaf da ni tare da tambayoyin me nake so, Allah na tuba idan cikin nayi ai ba zan fallasa kaina ba dole shi zai bayyana kanshi, haka yasa na zuba musu idanu, shi kuwa da na tattara shi na na watsa a gefe, yafi kowa rawan jiki domin gani yake kamar laifinsa ne na samu matsala.

Lokacin da Nady ta shigo kallon juna muka yi sannan muka sakarwa juna murmushi kafin ma ce mata. "Mom twins na saka ki jigila ko?" Girgiza kai tayi tana mika min wani cup na coffee, na amsa tana mai zama ta ce min. "Kin san kin bamu tsoro? Kawai sai ganinki muka yi kin yi collapse gaskiya akwai abinda yake damunki!" Ta fada tana d'aga min cup din nima d'aga mata anyi alamar cheers. "Ni lafiya ta lau!" Shigowar mijinta ne ya kalle mu yadda muka zauna muna magana. Takowa gabana yayi ya saka hannunshi a kaina, sannan ya dauki abin gwada yanayin zafin jiki, ya gwada min sannan ya je gaban computer din da suka saka min domin aiki ya duba ni a kai,.kafin ya kai hannu ya kwace Coffee din Hannunta ya wurga a cikin trash na cikin dakin. Nima amsar nawa yayi ya cilla a cikin trash din. "Kada na kara ganin kun sha wani abinda ya shafi coffee!" "Ok Sir!" Tunda ya shigo naki kallonshi domin wani abu nake ji yana dukar kirjina, kamar zuciyata zata fado daga kirjina, dauke kai nayi ina kara kallon Nady. "Kin san jibi sallah layya ki tashi mu koma gida!" "Eh dama ai na ji sauki kawai an kawo ni nan ne domin a azabarta da ni!" Na gayawa Nadiya haka domin nima na gaji da zaman asibitin. "Ina yake miki ciwo?" Dakyar na amsa mishi na ce mishi. "Babu!" Na cigaba da magana da Nady. "Nady ko zaki yi shiru ki huta da bakin ki?" Ya fada mata a yanayin bazata. "Ok My lord!" Ta fada tana murmushi, wannan abin da ban haushi yake don haka ni sai nayi ta takalarta da magana tana hmm da uhm, don masifa shima da ba abinda zai min kawai ya saka ni a gaba da fitina yasa ya shigo dakin. Can dai da Nady ta fahimci yana bukatar privecy sai ta mike tana faɗin.."Zan koma gida! Sai kin dawo!" "In sha Allah, amma me yasa zaki tafi?" "No ina da aiki ne" ta fita tana jan kofar. Tana fita ya mike tare da saka key a kofar ya nufo ni, ji nayi kirjina yana wani irin bugu kamar zai fado, nayi baya tare da dafe karfen gadon. "Me kake nufi?" Na tambaye shi a matuƙar razane, seriously ya bani tsoro kuma tsoron ce nake ƙoƙarin dannewa kada ya yi amfani da haka wurin cutar da ni don gaskiya ban yarda da shi ba at all. Shi din ba abin yarda ba ne haka yasa na kara yin baya ina mishi wani kallon ni fa ba tsoronka nake ji ba. Murmushi yayi yana kallon yadda nake baya kaɗan har gadon yana motsawa. "Ina zaki to?" "Kawai kada ka tab'a ni!" Na faɗa ina ƙoƙarin boye muryata da take dauke da tsoro. "Ok!" Ya koma gefe ya nad'e hannunsa a kirjinshi yana kallona, a hankali nake sauke ajiyar zuciya ina jin kamar na kwace a hannunsa dai zama yayi a bakin gadon ai tuni na tashi tsugul kamar mai shirin kartawa a waje. Murmushi yayi ya ce min. "Zauna!" "Akan me zan zauna bayan nasan cewa niman hanyar da zaka yi raping dina kake ina kauce maka!" Dariya abin ya bashi ya ɗan yi dariya sannan ya ce min. "Kin ga zauna ba abinda xan miki!" Ya fada yana kai hannunshi kafana zai janyo su nayi maza na ture hannunsa. "Kada ka sake ka ce zaka min wani abu, domin wallahi." Wayarshi ce ta yi ƙara. Dauka yayi bai damu da wanda ya kira ba, ya saka a kunnensa. "Yes!" Mikewa yayi a hankali ya kalle ni kafin ya juya ya fita ban san me ya fitar da shi ba, amma jikina ya bani babu lafiya yana fita kuwa na sauke ajiyar zuciya, cikin sauri da sassarfa, wuce juna suka yi shi da Uwaisa da yake dauke da wani flower basket, sai wasu tarkace da ya dauka. A hankali ya juya yana kallon Uwais wanda bai ma lura da shi ba, bai kuma kawo wurin Ikhlas zai je ba, haka ya cigaba da tafiya amma zuciyarshi cike da wani irin tsoro da firgici yake domin yasan idan idanunsa basu mishi karya ba wurin Ikhlas zai tafi. Can ward na mahaukata ya nufa anan ya samu tashin hankalin da ya mantar da shi wani Uwais da Ikhlas. Wani mara lafiya aka kawo mishi shi yasan ba normal hauka ba ce, it's like ya ga wani abu ne, ya firgita yake ta wasu abubuwan kamar na hauka shine danginsa suka kawo shi asibiti, kiran da aka mishi yazo mutumin yana ta buga kanshi da bango ne aka kira shi. Shiga dakin ya damu mutumin ya mutu kuma ya raunata nurse da wani likita. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonsu bakiɗaya. "Ku kai shi wurin ajiyar gawa, ku kira danginsa!" Ya fada yana mai barin ward din zuwa office dinsa. A ranar da ya fara ganin mutumin rike hannunsa yayi ya ce mishi. "Suna ta shiri akanka da nan, idan ban yi karya ba sun yi maka wani kazamin shiri wanda zai ta fashewa daya bayan ɗaya, ana son a shafa maka bakar paint din da dole sai ka dawo kana rokonsu kana musu biyayya, suna niman hanyar da zasu ja ka a a kasa. Na ga wani abu na ga abin tsoro na ga mutuwar da ake yi a hannunsu."

Zama yayi ya dafe kanshi yana jin wani wani irin ciwo a ransa, me zai yi su gane basu gabanshi? Mai zai yi su fahimci ma'anar rayuwa? Wanda suka fara da shi baya nan me zai saka shi su dame shi? Zuwa yanzu ya dace su tsaya a inda suke ya tsaya a inda yaƙe. Sunkuyar da kai yayi yana kallon kasa. Turo kofar aka yi ta d'ago kai yana kallon Nurse Farida ce. "Doctor mun kira dangin mamacin, amma basu dauka ba." Shiru yayi kafin ya ce mata. "Babu address dinsa da inda yake rayuwa kafin jinyar?" Juya kanta tayi kafin ta ce mishi. "Zan duba Dr!" Sannan ta fita daga office din ta turawa office na MD, su kuma suka cigaba da bincike akanshi. Wani abu ne ya fado mishi ya tashi da karfinsa ya fita.

-
Bayan fitarshi ina zaune aka turo kofar dakin, waye zan ganin ban da Ya Uwais. Kallonshi nayi ina kara kallon mutanen da suka rako shi. Ajiye kayan hannunsu sannan suka fita jan kujeran dakin yayi ya zauna, hijab dina na ja cikin hikima na saka ina mai kallonshi. Zama yayi tare da Crossing leg ya ce min. "Na zo duba ki ne, ance kin suma a gidanki, shi ne nazo na ji ko abinda ake zargi ne ya fara tabbata." Ya fada yana min wani irin kallo, murmushi nayi kafin na ce mishi. "Sai kuma aka gayyatoka ka zo ka ga ko na mutu ko?" Murmushi yayi ya ce min. "A'a kawai naji nazo na ga yanayin da kike ciki ne, wani lokaci ana aurar da Yara ne ba tare da an san inda za a mika su ba, wasu yan sari ne." Gyara zama nayi na ce mishi. "Ban fahimci wasu yan sari ne? Su waye yan sarin?" Na tambaye shi ina ga ya manta karatun da nayi ne a matsayinsa na lauya ya shigo da irin wannan maganar akan wanda nake nazarin hada rayuwata da shi. Yadda nayi mishi wata irin kallo yasa shi gyara murya ya ce min. "Ba zan fadi kome akan yan sari ba, amma a duk lokacin da kika rasa mafita ga number na nan ki kira ni! Zan zo a koda yaushe."

Kallonshi nake a hankali ina sake murmushi tashi nayi na bude mishi kofar ina murmushi. "Ga kofa nan zaka iya tafiya! Bana jin zan tab'a niman taimakonka domin Allah yana tare da ni, sannan zuwa yanzu ina son aurena." Na faɗa ina murmushi. Fita yayi daidai isowar shi. "See you!" Murmushi nayi a hankali na ce mishi. "Never!" Na furta ina kallonshi Dr Faris, kura min idanu yayi wanda suka yi jajjur ya d'aga min hannu yana min wave, nima haka nayi mishi, jan kofar yayi da karfi ya rufe tare da fisgo wuyar rigar Uwais. "Malam lafiya zaka rike min kwalar rigana?" "Na maka gargadi tun kwanaki amma kamar dakikiyar ƙwaƙwalwarka bata sittings na lura kamar kuna bukatar wankin ƙwaƙwalwa, ba ni da matsala da kai sai ma na ce ka kula da harkokin da mahaifinku ya bar muku, duk abinda kake gani a part dina da su. Ba matsalarka ba ce matsala ta ce ni na zaɓi haka domin na zauna lafiya. Idan ka sake suka yi wasa da emotional dinka, tsakaninmu za a samu matsala mara iya she is my wife! Na gaya maka matata ce, wannan ya zama last warning between I and you, idan ka sake muka kara haɗuwa, idan ba hakan ba" daga haka ya juya tare da komawa dakin ya wani daki kofar dakin ya bada wani kara bamm, ya shiga idanunshi a kaina nima kauda kai nayi ina mai kallon can, ya kai minti goma a dakin yana tsuma ya rasa yadda zai yi tsabar masifa, sai satar kallonshi nake yi ina tararadin yadda zai zo kaina, fita yai daga dakin na sauke ajiyar zuciya a raina ina faɗin. "Masifaffe kawai!" Bayan fitarshi sai gasu Umma. Da mamaki nake kallon abinda take domin haɗa kayana take. "Umma!" Zuba min idanu tayi, nayi maza na rufe baki na, wai masu iya magana suka ce fadar da tafi ƙarfinka idan da hali ka mai da shi wasa, ai kuwa haka aka yi domin zare idanu nake ta kuwa shiga mika min kayan da zan sauya , haka na amsa na saka, bayan mun gama sai gashi ya mikawa Umma paper bag, amsa tayi ya ce mata. "Ganinta ne!" Daga haka ya fita, ni fa ban wani kawo ya kullace ni aranshi ba, ashe mutumin nan kullata ta yayi, dab zai fita na ce mata . "Umma unguwar Malamai zaki kai ni?" Make ni tayi tana faɗin. "Hauka kike da zan kai ki unguwar Malamai, bayan ga dakinki abokiyar zamanki tana ta dawainiyya akanki gara ki koma dakinki dai!" Wani tura baki nayi ina kallonta, ganin haka yasa ta ce min. "Allah ya shirya ki!" Haka muka fita Faruq ya zo ya kwashi kayan ya fita da shi, har muka isa gida ina fushi, sai da Umma ta taya ni gyara parlourna. Sannan ta fita Faruq ya kaita gida, Nady bata nan kitchen na shiga nayi hada abincin rana, haka na yi ta nazari karshe na dafa fatensa, sai plaint da na b'are na soya, sai na ji ina sha'awar bread don haka na, kwab'a min donunt ban tsaya ba na kunna over sai da yayi dumi na kashe na saka donout din, kafin wani lokaci ya tashi sosai yayi kyau, sannan na buga shi da kyau na zuba mishi ridi da na gani a cikin kayan da aka kawo na abinci. Kafin na shiga duba wakena dama shi yasa na dafa a pressure pot, yanzu ya bani hadin kai.

Juyewa naso nayi amma sai na tuna da Nady, na zuba mata kafin na kai mata na ga bangarenta a bude ciki na shiga na ajiye mata ban tsaya duba cikin ba, na fito a hankali na wuce abuna. Sai da na ci abinci na koshi na yi wanka na yi sallah na kwanta.
Da yamma da suka dawo, Nady ta ga kula da abinci fitowa tayi lokacin mijinta ya zo yana zare min idanu, gashi kato amma akan abincin bai da hakuri, nima ramawa zan yi wallahi. Zuwa tayi main parlour ta zauna tana cin abincin tana bani labarin rabonta da ta ci dodo ta manta sai yau, kamar tayi kuka don murnar ga bread din yayi laushi wallahi haka take ci tana gyara min kai alamar abin ya mata dad'i. Faucets yayi ya saka cokali ya fara cin abincin, kallonshi tayi baki sake cinye waken yayi tas ya bar mata kular ya wuce dakinsa. Da dare a dakina ya zo duk da na ji wani iri amma kuma sai naga kamar Nady zata ce wani abu sai naga a wurinta lafiya lau.

Lokacin kwanciya yayi dakin da nake kwana anan ya tare yayi kane-kane, bude wardrobe nayi na dauko babbar duvet na shimfida a kasa na hada da blanket na kwanta bai wani damu ba, domin ni tunanina wani abu ne can shi kuma lissafinsa daban, haka na kashe wutar dakin na kwanta, cikin dare barci na yayi nauyi ya sauko ya dauke ni a hankali ya mai da ni gadon, dama kamar jira nake na makale mishi, haka ya mai da ni ganin haka na kara makale mishi, a hankali ya gyara min kwanciya a jikinsa, ban tab'a yin barci cikin aminci da salama kamar barci cikin jikinshi, naji wata irin nutsiwa da yarda da kai, gabakidaya na koma jikinshi na tare na yi kane-kane. Haka shima yayi ta murmushi yana kallon yadda nake rigima har cikin barcin. Kalaman mai Babbar daki ne ya dawo kanshi ta ce mishi.
"Tunda ka sallame ta, dole Nady tayi hakuri ka kula da ita for while ba ita ba hatta Ijlal su yi mata uzuri ka bata kulawa na wani lokaci, tana bukatar wani dama na dan lokaci yadda zuciyarta zata samu sauki daga yanayin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login