Showing 174001 words to 177000 words out of 304445 words
sonta saboda ko da bama shiri ta san yadda zata min abinda zai saka raina yayi dad'i, bata da kirki amma zuciyarta ba irin taku ba ce mai muguwar nufi. Ki cigaba da yi kuna ta murna don mun yi fada da ita bayan ita nan da kowacce ku ta watse kasa hakuri tayi ta ji mai yasa baku nan amma yau har waka kike na habaici Allah sarki." daga haka ya barta nan tsaye tana jin wani abu a ranta. Haka ya fita ya nufi kitchen dina ya ga a rufe sannan ya dawo parlourn, kuka nake a hankali ina jin kamar akwai abinda nayi da nake fuskantar kalubale haka, ina zaune ya shigo ya same ni, ganin har lokacin ban d'ago kai na kula shi ba, ya dauki key ɗin kitchen din ya je ya kai, sai da ya ga kitchen din ya duba ko ina babu matsala ya fita, kusan kwana nayi ina kuka don sai lokacin jikina yake ciwo, washi gari tun asuba na tashi don ana ruwa ina tashi na shiga store na dauko wani babban stove da aka saya min, ina fitar da shi hanyar waje na kafa murhuna, sannan na koma inda silingar gas dina yake na shiga janyo shi ina fitar da shi, ina cikin haka suka shigo da Faruq ganin yadda nake gungura shi yasa Faruq ya iso ya dauko ya kawo min inda na ajiye stove din, sannan na haɗa a gida ma da shi muke aikin wasu abubuwan, kuma mai kai biyu ne.
Ciki n a shiga na fara fito da kafet na shimfida, sannan na fito da sauran kayan aikin na ajiye su, na koma na fito da namar na kawo na bar shi ya sha iska, kafin na kuma shiga kitchen na fito da duk wani abinda zan bukata, doguwar riga na saka na material na, fara yanka albasa da tafarnuwa, sai attarugu da na dauko. Duk abubuwan da zan yi amfani da shi sai da na fito da su sannan dumama abincina ka fito da shi da tea na ajiye na fara aikina, na zuba nama, na bishi da sauran kayan hadi na rufe na cigaba da aiki, sai da nasha tea na cigaba da aikina. Don gulma sai ga Ijlal da yake masu mata aiki sun gaya mata sun ga ina aiki a waje, ta leko tare da tab'e baki, shi kuma yana parlourn, haka ma ban san ya aka yi ba sai ga Nadiyyah itama tana zuwa ta ce min. "Kin san motarmu tana nan zaki dauko aiki anan meye amfanin kitchen matar so!" Shiru nayi mara ban kulata ba, haka ta gama maganarta ban ce mata kala ba, tana ganinshi a parlourn ta zo ta min magana ta zata zai biye mata ne sai ya ce mata. "Ko fitar da motarki ya waje kafin ta gama nima Faruq zai fitar min da nawa da nata!"
"Wai meye matsalarka ne? Asirin da ake fada Ubanta yana yi ne zaka nuna min ya fara cinta." "Har yau Ubanta yana baki ruwan addu'ar wanda nayi imani da Allah ba don shi ba babu wanda ya isa ya iya miki wani a abu akan mahaifar da na san cewa cirewa kika yi aka kara dasa miki da wani? Chance dinki shine ki dauki ciki ko a miki dashen kwayoyin halittarmu, ko karya ne?" Wani irin razana tayi, ni kuma anan waje kukan zuci nake ana danganta Abba da suke yi da asiri. "Prince!" "Karya na yi miki? Amma dai kin san cewa nasan kin cire mahaifarki? Yanzu kin zo kina gaya mata magana, 100% nasan zan haihu da Zainab kece bana tunanin xan haihu dake tunda kin yi wasa da damarki. Asiri kuwa ko baki fada ba tayi min kuma shi ya sussuta ni so what?"
Ban ji me tace ba amma ta wuce bangarenta naji an buga kofar girb. Ajiyar zuciya nayi ta saukewa akai a kai, kafin karfe biyu na soyar nama, na fara da kayan ciki sai kuma na koma soya namar, na dambun ina cikin aikin sai gasu Wildat, tana zuwa ita da wata yarinya suka kama min aikin, na tafi nayi sallah na daura mana abincin rana taliya da miyar jiya muka ci sai tamarind juice da nayi mana kuka sha saboda maiko.
Wurin la'asar na gama aikin bakiɗaya a lokacin na daura tuwon madara tsari, miyar kuka danyen kuka saboda an shiga damina ne kuma sabon toho ne, sai ga Faruq nan da shi,.shine na mana tuwo miyar kukan na zuba dan ruwan nama kaɗan, kafin wani lokaci miyar ta karade gidan, har masu aikinsu na cewa gaskiya miyar ko baka ci ba sai kasan anyi miyar gargajiya. Bayan na gama ne na kwashe a leda bakiɗaya na cire na mai babbar daki zasu kai mata, sai na mai gidan domin tun safe yake nuna min zai dawo bangarena.
Da zasu tafi ne na zuba musu dambu da namar da kuɗi dubu goma, domin ina tsaye ne akansu amma su ne suka tuke min dambun nan tas, sannan suka tafi. Zan iya cewa ba karamin jin dadi na yi ba hatta inda nayi aikin sun gyara min tas, bayan tafiyarsu na hada cake nayi sai donuts da na ajiye kayan aikinsa gobe da safe nayi. Kayan abincin dakina na kai na rufe kitchen din na dawo daki nayi wanka tare da sallah isha, na kwanta ina jin wani irin gajiya. A hankali barci yayi ta daukata, kamar an ce na bude idanuna gabanshi nayi a tsaye tare da Ijlal da jikinta yake rawa. Tashi nayi zaune ina kallonsu.."me kika shigo ɗakinta?" "Wallahi nazo niman abu ne na ga tana barci!" "Zainab tashi ki duba ki gani!" A hankali na gama raba idanuna a cikin dakin ban ga kome ba, na ce musu ."babu kome a dakin!" "Bata shigowar banza akwai abinda ta kawo yarinyar nan na rasa yadda xan yi dake." Fita tayi kamar kazar da ruwa ya mata duka, ni dai ban san me ya faru ba don haka ya ce min. "Idan zaki kwanta kina rufe kofar idan na dawo zan buɗe." Haka ya fita abinshi, Ni dai kwanciya na cigaba da yi. Ita kuwa tana fita ta sauke ajiyar zuciya. Tana murmushi ai bukatarta ya biya tunda ta saka abinda zata saka, wallahi ko zata mutu sai ta haramta musu juna. Da ita suke zancen.
Shima dai da ya gama aikinsa ya zo dauki ya kwanta, duk da yasan bama shiri gudun kada wani rigima ya sake fitowa yasa shi kyale ni na, na cigaba da barcina har karfe biyu nafarka sakamakon mafarkin da nayi na Mai Martaba bani mantawa mun tab'a zuwa gaishe shi koda yake dama can muna zuwa fada muna yara,daga baya muka daina zuwa. Wai na je gaishe shi ne muna zaune ya kalle ni yana ta farin ciki, ga Salmanun a gefenshi ya ce mishi. "Zama namiji ba na ragwayen maza ba ne, kai dai ka zama adali ke kuma ki kasance mai biyayya, Allah ya muku albrka!" Na farka daga mafarkin, ban daki na wuce nayi alola da kama ruwa sannan na fito nayi sallah nayi mamakin yadda yake ya barci, sai da nayi har na idar na koma na kwanta sannan ya farka shima ya kalle ni, ya fita zuwa ban dakin yayi alolan ya zo ya gabatar da sallah.
Tunda na kwanta ban farka ba sai karfe shida na safe nayi sallah na koma na kwanta.
Ba zan iya cewa na gaji ba amma bakiɗaya jikina ciwo yake, da safe na tashi da aikin donuts na hada sannan na saka a oven, yana tashi na fara aikin cire shi ina sakawa a tire, ina gamawa na shiga na lullube da kitchen towel, sannan na daura tuwon shinkafa nayi miyar egusi da ya sha ganda da na zuba nama da kifi, ina cikin aikin ya shigo yana mai kallona ya ce min. "Zan yi baki Please ki taimaka min da nama da dambun da kika yi wallahi."
"Lallai fa ba zan bada wallahi ka ji na gaya maka, ba zan baka ba kai ba baki ba ko waye zai zo gidan nan sanadinka ba zan bashi ba, kai baka ji kunyar zuwa gabana da cewa na baka nama, ina cewa kayi idan ba zan dauka ba zaka raba ba? Ko b haka Maluma ta gaya maka ba? Don ga ni yar iska sai na dauka na baka." Cikin wani irin takaici na kalle shi na ce mishi. "Ka je wurin matanka!" Abinci da ya zama dole nayi tunda na shi ne, haka na kwashe tas na zuba a cikin manya plast na alfarma, n ajera a kitchen din na tafi nayi wanka da alola a lokacin da na zo na samu Ijlal tana son lallai ta shiga kitchen dina ta kasa bude kofar.."Ijlal wai meye matsalarki da ni ne? Wai mai na tsare miki ne a gidan nan? Zuwa kika yi, gidan nan kika same ni duk da haka ban yi fushi da abinda kike min ba me yasa ke kike shiga rayuwata ne? Ki wuce." Ba musu ta wuce tana sunkuyar da kanta..
Sai da bakinsa iso ni da shi muka zo muka fitar da abincin, na kunna gas na fara soya donuts dun, ina gamawa na zuba musu a cikin wasu plat na jera a ture yazo ya dauka. Sai namar yana ta kallona yana son ya min magana mana ki yarda mu kalli juna, abin da na sani shine na kawo snacks din da mai babbar daki ta kawo min, na kai parlour ina ajiyewa Nady ta kawo masu nama da dambu a cikin wani katon tambulam ta ajiye musu. Ban san me yasa yake k'in namar ba, ni dai ina gamawa na wuce kitchen na karasa aikina na wanke kayan tas sannan na kwashe kome na mai dasu muhallinsu, sannan na kira Faruq na bashi na Mai babbar daki ya kai mata nata, yana dawowa na zuba mishi har da dambunsa da namar na zuba mishi, kai karshe dai da na shiga kitchen na rufe store. Anan na ajiye namar don na gaji da barinsa a dakina. Lokacin da na dauki tuwona, na zauna zan ci ya shigo. "Please saka min namar da Dambu nan? Don Allah na Nady an samu matsala.......
*08130269641*
[7/26, 10:02 Safiya] Ramlat Manga41: 58
Kallon renin wayo na mishi kafin a raina na fara tunanin mai ya dace na mishi nima na rama wulakancin da yayi min.
*Dole ma kazo yau zaka ga wulakanci*
Shiru nayi ina jin shi amma naki na tashi. "Ina magana kin kyale ni ?" "Wai da ni kake?" Shiru yayi kafin ya gyara zaman zaman hularsa da ya sha irin daurin da Naziru Sarkin waka yake. "Please bar kallona mu yi magana." Ya katse min tunanina. "Dama na gaya maka kallonka nake yi? Kai yanzu da kwaso ƙafafuwanka kazo na baka nama ina cewa Maluma tayi ka raba don bakin ciki wanda aka bani baka kaunar nayi gaba shine kazo amsa ka rage min gaba da zan yi ba zan baka na ni zan sammasu ba dai ka ji kamshinsa ba " na fada ina mai daukar key, a dakin na wuce kitchen na zuba musu, a wasu takeaway sannan na fito na kai musu, muna kara gaisawa. "Jiya naga kin yi tamarind juice ko zamu samu?" Tsayawa nayi zan yi gardama amma yadda ake kallonmu sai na wuce tare da nufar firji din ina jin wani irin haushi, haka na fito da gora biyu da suke firji shigowa yayi yana mai kai hannu zai amsa na mai da baya na ce mishi. "Idanunka yana kan duk abinda nake yi wallahi ka fita idanuna tunda ni bana jin magana ka je can ka zauna da masu jin magana, kuma ka kara hada ni da Maluma wallahi sai na gudu kun nime ni kun rasa na rantse da Allah!" Bai wani dauki maganar da gaske ba,ya amsa ya wuce waye abinsa, lokacin da na fito na samu suna ta hira ban san lokacin da na ce. "Bu ra'ayi?" Duk suka juya suna kallona, wato namar da na kai musu mutumin nan ya zauna yana ci, su kuma suna cin na wurin Nady which mean babu abinda ya samu namar Nady tsabar kwadayi ne irin nashi, murmushi yayi yana faɗin. "Fulani Babba ko zaki taimaka ki min da karin dambun ne?" Kamar na rufe shi da duka don masifa idanuna har wani hazo-hazo yake, murmushin yake nayi tare da nufar dakina, yadda yayi maganar a gaban jama'a taya zan ki bashi haka na koma dakin na zuba cin-cin da snacks a cikin takeaway sannan na zuba nama da dambun na juya zan fita sai gashi ya zo amsa, "Don Allah kada ki kara fita, wallahi sai kallonki suke suna fadar wai kin yi kyau!" Harara na watsa mishi nace mishi. "Ina ruwana idan na so fita Allah fita xan yi!" Na faɗa ina shan ruwa sam ya hana ni cin abincin hankalinsa ya kwanta. Da zasu tafi ne ya kira ni na saka babban mayafi. "Madam muna godiya!"
"Sannan sunanshi Bashir, wannan kuma Mu'azzam, sai wannan kuma Jacob duk lokacin ƙwaƙwalwa ne muka yi aiki da su a can Amurka, sannan sun zo su taya ni wani aiki ne na shekara daya." Murmushi nayi ina faɗin. "Ayya Ubangiji ya dafa muku yasa a fara a sa'a, ya kuma kawo babban rabo." Murmushi yayi yana faɗin. "Amin Ya Allah!" Suna fita suka fara mishi tsiya. "Prince a ina ka samu kamila haka? Don Allah akwai yan uwanta ne? Wallahi ina son wannan ta dace da kai ba." "Zan dura maka ashar." Ya fada yana murmushi har waje ya raka su yana musu godiya Mu'azzam ya mika mishi sako. "Ka bawa Nady wannan, ita kuma Madam yadda ta ciyar damu ya wajaba a kaina na biya kudi me nauyi!" Jacob ya ce mishi. "Ai dole ne, dan iska ya d'aga mana hankali kamar zai zo ya dauke mu, gashi mun fito hannu holoko!" Murmushi yayi Dr Bashir da ya san ba yau ya fara cin girkin ba ya ce musu. "Ai Madam dole ma a mata kyau, kwanakin baya da yayi wani aiki kusan idan zai wuni sai an kawo abinci daga gida wallahi, ai ya godewa Allah da ya bashi kuku a gidansa." Shafa cikinshi yayi da yake jin wani irin dad'i yaci kalar namarta itama shegen rowa da ta fara koya cikin murmushi ya ce musu."Ya ishe ku haka yabon matata!" Ya juya yana mai barinsu anan. "Brain lover!" Cak ya tsaya sunan da suke kiranshi a can asibitin ya juya yana kallonsu kafin suka ce mishi. "Ka samu wacce ta maye gurbin brain din ko?" Hannu ya saka a cikin aljuhunsa yana me d'ago kafad'arshi alamar bai sani ba, amma murmushin da yake kan fuskarsa ya nuna hakan ce. Sai da suka bar gidan da unguwar sannan ya komo cikin gidan.
"Don Allah Aunty Nu'aymah zaku zo wunin sallah? Jibi?" Na faɗa da karfi ina tsalle domin zan bar wannan gidan kuncin idan na tafi sai nayi sati ban dawo ba, zai san ya tab'a ni. Kamar yasan meye a raina zama yayi yaji ina faɗin. "Allah tow me zan kawo muku?" Can ta ce inji Aunty Sajidah na kawo mata chocolate cake, sai Aunty Shukrah na kawo mata nama da dambu. "Inji Umma wai ki zo mata da masar gero!" "Wayyo ni, in sha Allah daga yau zan fara aikin don kada na samu matsala." Can ta ce min Allah yasa kada ya hana ki zuwa. "Ya hana ni zuwa kuma? Akan me zai hana ni zuwa? Cab dijam idan kika ji zuwa daya kenan. " Na cigaba da dariya na, har na gama wayar yana wurin bai ce min kome ba, mai yasa Ikhlas ta bala'in rena shi ne? Me yasa duk wani abinda zai yi don ya nuna mata shi ne sama da ita take nunawa shi din bai isa ba. "Zainab!" D'ago kai nayi ina kallonshi kafin na ce na'am. "Idan na hana ki zuwa akwai wanda zai fitar dake ne a gidan nan?" Yadda yayi min tambayar sai naji ina shakkar shi bakiɗaya, cikin sanyin murya da wani irin tsoro na ce mishi. "Babu!" "Good waye ni?" "Kai ne mana!" "Waye ni a gare ki?" "Mijina!" Na faɗa mishi ina kokarin ja baya domin yadda yake matsowa kusa da ni ya kara saka ni jin wani irin tsoro. "Mai yasa kika rena Ni?" Tashi yayi ya zauna a kujeran bakiɗaya. "Nifa ban rena ka ba!" Murmushin takaici yayi ya mike tare da cewa, "Ni salmanu Faris na haramta miki fita a gidan nan sai lokacin da kika yi hankali abincin kuma ki yi ki kai musu, gobe za ayi wunin fada shima ba zaki ba, sai mu ga zuwa ba daya ba, ba biyu ba." Daga nan ya fita. Na zata wasa yake wunin ranar bai ci abinci a wurina ba, a wurin Nady ya ci, yana ci ya kalleta yana faɗin. "Yanzu don rashin adalci kin bani abinci na ci, da ace ita naci nata da yanzu kina ta faɗa." Sai tayi shiru bai kuma magana ba, da dare yayi dumamen tuwo.nayi na juye a plat, ina fitowa parlourn na hango shi yana cin abinci Faruq yana bakin kofar. Ban kalli inda suke ba na cewa Faruq. "Don Allah ko zan baka aika ne?"
"Babu inda zai je!" Ya fada yana kallona, "Okay!" Na wuce a parlour na zauna na saka abincin a kasa na fara ci da zafi, wayata na ɗauka na kira Tauhid. "Dan rashawa ya kake?" "Alhamdulillahi me kike so? Domin zuwa miki aika zabi daya kudinsa!" "20k!" Na bashi amsa na ce mishi.. "ka yi record din abinda zan gaya maka." Na gaya mishi duk abinda nake bukata sannan na ce